Showing 123001 words to 126000 words out of 138779 words

Chapter 42 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

2007

ta anan, dubi fa abinda ke gabana, ina wani aiki ne kinsan fa xuwan nan na dole ne.

Ta soma kwashe takardun da yake aiki dasu tana fadin ko xuwan menene You must give me my time, ko girkin da na saka aka ma bakaxo kaci ba, ashe da gaskiyar qanwarka kafi son aikin ka dani.

Ya soma tafiya yana fadin kome xaki ce naji, kin san dani kika shanyani anan kina gurin  Uncle B sai yanxu kika tuna dani.

Ni na isa your Highness, kayi haquri, ta riqo hannunsa tana kallon sa da murmushi,

Kasan me Uncle b yake gayamin ma,

Ya girgixa kansa,

Tace xo muje, I will tell you later,

Suna fitEL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

65

A gurguje😏

'Washe gari su hajiya suka soma shirye shiryen tafiya, uwani harda kuka tana roqon su, su barta a gidan kakan ta ita ma taji dadi.

Idan tana cewa kakan ta abin dariya yake bawa abba, ya qara yarda uwani bata da hankali,

Sanda suka fito, sarki ne kawai bai fito masu rakiya ba, amma su jiddah da uncle b duk sun fito, rumaisa da sauran yaran gidan ma, afiya ce ma bata fito ba.

Uwani tayi tsaye baxata shiga motar ba lallai sai an barta inda kakan ta, suna mata baqin ciki da ta xamo jinin sarauta shiyasa basa son ta xauna a gidan.

Rumaisa dai bata ce komai ba sai kallonta take sam yarinyar bata birge ta bata da nutsuwa kuma bata respecting iyayen ta a yanda ta lura,

Jiddah ma batayi magana ba sai su hajiya ne ke ta fada akan ta shiga motar.

Suna haka afiya ta fito harabar gidan, tayi kyau sosai cikin farar alkyabba, fuskar nan tata babu annuri amma hakan bai boye kyawun fuskar ta ba, da alama fushin na rumaisa ne daga yanda take xuba mata harara tun da ta doso gurin.

Kallo daya uwani ta mata ta rikice a tunaninta itace take harara, ba shiri uwani ta soma qoqarin shiga motar ta qofar glass a rude,

Miye haka? Afiya ta tambaya sanda ta doso gurin tana kallon su.

Jiddah tace uwani ce tun daxu ake ta fama akan ta shiga motar taqi wai sai dai a barta nan,

Uwani ta fashe da kuka, yaushe nace haka, kada kimin sharri, ta soma kuka sosai har ga Allah tsoron afiya take.

Afiya ta tabe baki tana kallonta, bude motar ki shiga tun daxu kin batawa mutane lokaci, kenan duk gurinnan ke kadai ake jira kuma acikin su an rasa wanda xai baki mari biyu masu kyau da tuni kin dade da shiga motar.

Uwani na jin haka ta balle murfin motar ta shiga, da qarfi ta rufe gam, ta maida glass da sauri ta rufe tana maida numfashi cikin tsoro.

Yaran dake gurin suka dauki dariya, su abba suka yi godiya suka shiga motar suka fice.

Afiya tace tun daxu nake jiranki, mrng flight xamu bi kinsa ni amma dubi ko wanka baki yi ba, ta fada tana kallon rumaisa.

Rumaisa ta soma tafiya tana fadin sarkin rawar jiki ina sane kuma akwai time ai.

Afiya tace ki bata mana lokaci Allah tafiya xamuyi mu barki,

Sai me, ni bansan hanya bane, tayi shigewarta.

Jiddah tace wai yau xaku tafi gabaki d'aya.

Afiya tace eh mana mun bar yara acan, kinga ba wanda yaxo da yaro ko d'aya, dama two days muka xo muyi yau xamu koma.

Jiddah tace Allah ya kaiku lafiya, ni kam naso ki bani labarin ki da nabila bayan tafiyar ki, uncle merah bai bani wannan labarin ba.

Afiya ta dube ta tana fadin, not now jiddah kuma baa nan ba, amma nabila.... sai kuma tayi shiru ganin fitowar Merah da fadawa a bayansa.

*

Barci uwani keyi sosai a cikin motar, sanda suka iso gida aka tayar da ita, budar bakin ta sai cewa tayi.

Hajiya kinsan me, wallahi wannan sarkin ya hana min sukuni a barci sai bibiya ta yake, duk na rufe idanuna shi nake gani, ina gani fa ya kamu da soyayyata ne shiyasa naga yana ta kallo na jiya fa da kuna magana.

Hajiya tace iskancin naki har ya kai acan, tsohon mutum ma baki bari ba, me xaiyi da ke.

Aa hajiya kinsan fa ance idan kana mafarkin mutum tabbas son ka yakeyi, karki yi mamaki a yanxu yana can yana baqin cikin tafiya ta, ni nasan yana sona hajiya, kada kumin baqin ciki da gidan sarauta, ina ji a jikina ya'yana xasu xo cikin jinin sarauta suna alfahari dani, nima na xama kakar jiddah saboda ina sons.... Dukan da taji a bayanta ya saka ta yin shiru,

Wayyo abba kayi haquri,

Yace shiga mota, ba musu ta shiga da sauri tana fadin qila can xai maidata inda sarki.

Yace hajiya shiga cikin gida, xamu dawo bada jimawa ba.

'Abba yaja motar, inda wani babban malami ya nufa da ita inda yayi masa bayanin uwani sosai.

Malamin yace shedanun aljannu mu suna haka, sukan juya kwakwalwar yaro yayi ta yin abinda bai dace ba, yanxu xamuyi mata ruqiya insha Allah duk abinda ke kanta xai bayyana insha Allah.

'Abba yayi addua sosai, yana fatan ta sami lafiya ya fita waje ya bar uwani xaune cikin tashin hankali.

Malamin ya kira almajiran sa suka soma yiwa uwani ruqiya.

Ana ta karatu, idanunta wiqi wiqi sai kallon su take tana tunxure baki.

Malamin ya tashi da xungureriyar bulala a hannunsa yana fadin, aljannun dake kan wannan yarinyar da alama kangararru ne,

Uwani ta bude idanu tana kallon malamin da bulala kafin tayi wani yunquri ya aika mata ita iya qarfinsa,

Ta saki wata qara cikin gigicewa, ta fadi gurin ta tashi tana tsalle, wayyo abba.

'Abba tun da yaji ihunta hankalinsa ya tashi ya qara yarda lallai jinnu ne acikinta tun da suke da wani bata taba qara irin wannan ba, ya cigaba da karatun qur'ani a wayarsa yana nema mata sauqi.

Ku nawa ne acikin ta, su waye ku? Malamin ya tambaya cikin xare ido yana kallonta.

Uwani bata gane abinda yake magana akai ba, ga bayanta sai radadin ciwo yake,

Ganin taqi magana malamin ya qara kai mata wata bulalar, a gigice ta nemi hanyar ficewa, almajirai suka yi cikinta suka riqo ta,

Wayyo abba, wayyo hajiya xasu kashe ni, wallahi baxan qara ba, ko magana xan daina yi, dan Allah kayi haquri.

Malamin yace ku musulmai ne,

Da sauri uwani ta gyada kai, sau biyar nake sallah kullum, kuma ina xuwa islamiya ka tambayi abbana.

Malamin ya gyara hannun rigarsa yana fadin har yanxu jinnun basu tako ba, suna so su nuna min taurin kai, ni kuma xan wahalar da ku, kuna so ku batawa yarinya rayuwa.

Yasa wani almajirinsa ya riqa hannayen uwani ta baya aka banqare ta, aka daure qafafunta da igiya, ya riqe tsakiyar kanta ya daga murya sosai yana karanto mata qur'ani,

Ya jima yana yi sosai ya qara kallonta, su waye ku?

Uwani tayi wiqi wiqi da ido, hawaye da majina duk sun hade a fuska saboda tsananin axaba,

Tace wallahi nice uwani, sunana Aisha, ni jikanyar sarki ce, bani da aljannu, dan Allah kuyi haquri.

Daga inda abba yake xaune yana jin muryarta, tausayin yar sa ya mamaye xuciyarsa, Allah ya bawa uwani lfy, ya tashi a hankali ya nufi inda suke.

Ganin yanda aka banqare uwani hankalinsa ya tashi sosai ya shigo dakin da sauri,

Malam menene haka, meyasa kake dukan ta da wanna bulalar.

Uwani na ganin sa ta taso a wahalce ta rungumesa sosai.

'Abba karkaje ka barni kashe ni xasuyi, ni bani da aljannu, abba baxan qara ba na tuba, ka gayamasu baxan sake ba.

Ya dubi bayanta duk shatin bulala ne gurin yayi ja sosai abinka da farar fata,

Yace na kawo tane ka duba min ita idan akwai amma bance ka dake ta haka ba, mutum ce ba dabba ba, baa taba mata duka irin wannan ba.

Yace amma alhaji m.... Abba ya katse sa,

Shikenan ai ka riga ka aiwatar, yaja hannun uwani suka fita sai kuka take jikinta na rawa, da kansa ya bude mata motar ta shiga kafin ya shiga ya tayar.

Cikin kuka tace abba ina da hankali baxan qara ba, kada ka qara kaini wani gun a dake ni, ni bansan ina yin komai ba.

Abba ya tausaya mata yace ba inda xan qara kaiki uwani, xan haqura dake haka na cigaba da xama dake, inaji haka Allah ya tsaro maki taki rayuwar amma duk da haka uwani ki rage wasu abubuwa a kullum ina gayamaki hakan kuma xan cigaba da maki addua kinji.

Ta gyada kai da sauri tana fadin abba kada ka qara kaini a dakeni, baxan qara ba, na daina yin magana.

Yace idan kika qara ma nan xan dawo dake malamin nan ya qara dukan ki, kinga Malam guzuma ya huta da dukan ki.

Ta fashe da kuka har tana riqo hannunsa dake kan sitiyari, abba wallahi baxan qara ba kayi haquri.

Kafin su iso gida har tayi barcin wahala sai ajiyar xuciya take.

*

Cikin kwana biyu aka xagaya da jiddah taga dangi haka dangi sun ganta,

Daga baya suka dawo gida tare da kuyangu da sarki ya bata guda uku,

d'aya sunanta Xuwaira, sai Nafee Anka sai ta qarshen Lailah, masu hankali da nutsuwa.

Jiddah ta qara samun matsayi a xuciyar el'mustapha sai nan nan yake da ita cikin nuna mata wutar soyayyarta dake adabar xuciyarsa.

Jiddana mai iyaye da yawa, jiddana jinin sarauta ya fada lokacin da yake qoqarin xama a kusa da ita.

Iyayen nan xan raba su biyu na bawa el'mustapha rabi, iyayena ai iyayen ka ne.

Kefa yar gata ce jiddah, ni yanxu nafiki xama abin tausayi.

Ba uwa ba uba, ni maraya ne jiddah ki kula da ni da yarana shine farin cikin rayuwa ta.

Ta rungume sa tana fadin komai runtsi komai wuya, komai dadi a duniyar nan baxan manta da musty na da ya'yana ba, sune jibin rayuwata, farin cikina, ina matuqar son su baxan iya rayuwa batare da su ba, el'mustapha ya kwantar da hankalinsa, jiddah tashi ce kuma har yanxu da baxar sa take taka rawa.

Ya kwantar da ita a hankali hade da hada bakinsu guri d'aya.

*

Yusuf kayan menene haka, akwati nake gani kusan shidda kamar kayan aure.

Yace eh surry xo ki xauna muyi magana ta fahimta, akwai naki kaya akwati kusan uku hannun anty ikram na fadar kishiya.

Fadar kishiya ta fada cikin firgici tana kallonsa yayin da xuciyarta ta tsananta bugawa tamkar xata fado daga qirjinta.

owa ta soma kiran jakadiya, bata jima ba kuwa ta xo da sauri tana fadin,

Ranki ya dade gani,

Tace akwai wata yarinya dake kwance a falon nan ki sa a fitar da ita a falon yanxu.

An gama gimbiya yanxu nan xaa aiwatar.

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

66

Aure xaka yi yusuf? Wacece xaka aura, ina so na santa dan Allah ka gayamin.

Ya riqo hannunta yana qoqarin xaunar da ita, ta fisge da qarfi tana kallonsa,

Tambayar ka nake, just answer me, bana son dadin bakin ka wacece xaka aura, who is she yusuf, ta fada hade da riqo gaban rigarsa tana kallonsa idanunta taf da hawaye.

Am sorry surry, uwani ce, amma wallahi u.... Shut up ta katse sa cikin tsawa, idanunta sun juye sunyi jawur.

Uwani kuma yusuf, ashe baka barta ba, menayi ma, what did I do to deserve this? Menene bana yi ma, dame na gaxaka da shi a gidannan na kyautatawar aure, me uwani ta fini dashi,

Wallahi babu komai surayya babu abinda uwani ta fiki da shi sai hauka, haka kawai nake son na aure ta badan kin gaza ni da komai.

Idan aure xaka qara meyasa dole sai uwani, mata nawa ne a gari, kasan bata da hankali kake neman hadani xama da ita, You are not serious, nagane me kake nufi a yanxu, xaka auri uwani ku xauna ku wulaqantani saboda tun farko ba nice kake so ba, na amince na aure ka saboda tausayin abinda uwani tayi maka a baya, na xauna da kai da xuciya d'aya, na koyawa kaina soyayyar ka amma yanxu kake son nuna min halin ku na maxa, tabbas na yarda namiji ba dan goyo bane, kaje gaka ga uwani, ta juya a fusacce.

Hankalinsa ya tashi yabi bayanta yana bata haquri sam abinda take tunani bashi bane a xuciyar sa, idan har surry xata barshi tabbas xai haqura da auren uwani sadakin da ya bada ma xai yafe.

Kayanta ta soma hadawa tana kuka, duk rarrashi da ban baki da yake bata bai sa ta saurare sa ba, ko  ta kan yar'ta Mimi bata bi ta soma qoqarin fita daga dakin, ya riqota da qarfi suka soma kokawa a dakin, qarfi ba daya ba dole ta saduda ta fashe da kuka.

Tsura mata idanu yayi yana kallonta, idan yace baya son surry yayi qarya, macece da kowane namiji xaiyi alfahari samun irin ta, tun daga kan nutsuwarta haqurin ta da biyayyarta, kuma ya sani duk duniya ba macen da xai so kamarta har uwani kuwa domin son da yake mata baima uwani shi ba kuma yasani ko a mafarki uwani baxata masa biyayyar da surayya ke masa ba.

Idan bai manta ba shi uwani xatayiwa laifi amma shi xaije yana bata haquri, idan kuma shi yayi laifin duk shi xaije yana bata haquri, bai taba sanin dadin rarrashin mace ba sai akan surry da ta soma yi masa, baya manta har ganin uwani yake a mafarki ta tsare sa da fada yana bata haquri, to me akayi?

Ya dafe kansa da hannuwansa duka biyu tabbas idan auren uwani matsala ne a rayuwarsa da matarsa ya haqura dashi.

Yayi juyin duniya da surry ta kula shi taqi, yana fita massalaci ta dauki yar'ta da kayanta ta fice daga gidan.

Sanda ya dawo ya sami batanan kuma babu kayanta da ta diba daxu hankalinsa ya tashi sosai, kai tsaye gidan jiddah ya nufa, kallo daya tayi masa ta gane baya cikin nutsuwa.

Meke damun yusuf?ta tambaya lokacin da take qoqarin sakawa airah pampers.

Surayya ta guje ni anty jiddah, bansan ya xanyi ba, she left my house.

Saboda me?

Saboda aure na da uwani, ya xanyi?

Tace ka haqura da auren uwani, dole ne?

Yace aa, amma ita ma ina son ta, kuma kinga iyaye sun shigo maganar me xance dasu.

Kace masu ka fasa, ina maka sha'awar xama da surayya fiye da xama da uwani, banga laifin surry dan ta guji uwani ba saboda tasan abin da tamin, babu mai son kishi da uwani kai tsaye xata ga bayansa.

Yace hakane nasani wallahi, uwani tausayi take bani anty jiddah, bayan wannan ma bafa a gida daya xasu xauna ba, kowacce da gidan ta kuma na baiwa surayya xabi akan duk gidan da take so acan xata xauna, auren nan fa ba haramun bane ya halatta, hudu akace muyi ko.

Tace hakane amma baa ce kuyi hudun haka kawai ba, sai aka qara da cewa idan xaku iya adalci tsakanin su.

Insha Allah, Allah baxai kamani da laifin rashin adalci a tsakanin su ba, ki taimakeni anty jiddah nasan ke kadai ce mai sauqin kai da xata duba min anty ikram bata son auren nan ko kadan kinsani, ki shige min gaba muje mu rarrashi surry wlhy ina son ta.

Jiddah ta kira el'mustapha ta sanar da shi xata fita da dalilin fitar, yayi mata ixini kafin su tafi ita da yusuf.

Surayya sai kuka take a gaban mahaifiyarta tana gayamata komai da kuma halin uwani.

Addua xakiyi, abinda yafi xama alkhairi Allah ya tabbatar amma kada ki daga hankalinki dana mijinki ki sakawa xuciyarki damuwa surayya, maganar yusuf ya sake ki bana son ji kuma kada ki kuskura ki furta masa wannan kalmar.

Kiyi haquri dama aure ya gadi hakan, xama na tare dole sai ana haquri duk yanda kake da mijinka baxaka taba cewa baxai maka kishiya ba, wata Ma sai ta tsufa a gidanta da yaranta mijin xai auro mata yarinya sharkaf warin yar cikinta, illah kawai kayi addua Allah ya hada ka da ta gari.

Wallahi mama uwani ba ta gari bace, kinsan halin ta fa kinsan lokacin da take xuwa gidannan har ke da kanki kike min magana akan ta bata da nutsuwa da kamun kai, kuma kinji abinda tayi wa yar uwarta.

Duk nasani surayya, shiyasa nace kiyi addua mafi alkhairi nima xan tayaki, kuma abinda tayi wa yar uwarta a baya ba lallai bane ke ta maki shi karkiyi mamakin ta sauya daga yanda kika santa sai kuxo kuna xama na amana da ita.

'Surry ta share hawaye tana yatsine fuska, kowa yaqi ya duba mata duk wanda ta tunkara da maganar sai haquri yake bata, xata xubawa sarautar Allah ido ta kuma gwada yin haqurin tagani idan haqurin xai kaita ga riba.

Har su jiddah suka xo duk maganar da suke da mahaifiyarta tana ji komai bata ce ba har suka gama, da kyar tabi yusuf suka koma gida sai kuka take kamar ranta har wani haushinsa take ji.

Ya bata xabi akan gidan da take, sabo wanda ya gina ko kuwa wanda take ciki, kai tsaye tace sabo saboda tana ganin ai dan ita ya gina tun farko ba dan wata ba,

Yusuf sai godiya yake mata, burinsa yaga ta kwantar da hankalinta baya son damuwar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login