Showing 96001 words to 99000 words out of 138779 words

Chapter 33 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

2018

ragwaf.

Ko yawo xakiyi tsirara a duniyar nan kina bin bokaye, ko ciwo xakiyi kina aman jini kina mutuwa kina tashi baxaki taba auren *EL'MUSTAPHA* ba kuma kiyi gaggawar barin gidan nan kafin na fito nasa a wulaqantaki aΒ  gidannan.

*EL'MUSTAPHA*

*Haske Writers Association*

Home of experts and perfect writers

Fertymerh XarahπŸ’ž

_God bless this special best friend of mine with all happiness and accomplishment in life,Β  I’m truly blessed to have you as my best est buddyΒ  *khadija Ahmed KDEEY*_ πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚

_Happy Birthday to my best daughter, Thinking of you with love on your birthday and wishing you everything that brings you happiness today and always, I’m truly blessed to have you as my best est buddy *Sumayya Halliru Dikko*_πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚

56

Uwani ta xube gurin hankalinta a tashe,

Me jiddah ke nufi da ko xata mutu baxata taba aura mata el'mustapha ba, kenan jiddah tana nufin ko ma me xatayi sai dai tayi amma baxata qara auren mijinta ba.

Yaushe jiddah ta canxa haka? Waye ya bata mana jiddah ta xama mai xafi haka, da alama yanxu bata ma da haquri qila idan an bincika ko tausayi bata da shi, waye ya bata min yar'uwa haka? Indai ba ta sami qawa mai xugata irin jamcy ba.

Taja dogon tsaki kafin ta nufi dakin su hajiya dan ta lura hajiya ma na mata wani gani gani tana so ta tambaya dalili idan itama tana baqin ciki da dawowarta gidan uban tane ta sani, ko tana baqin ciki da xata dawo gidan mijinta ne oho.

Jiddah ta ajiye airah akan bed tana kallon el'mustapha,

Wani abin mamaki, Uwani ke roqona na barta ta auri mijina a karo na biyu, bata neman gafara ta sai ma ta mijina take.

El'mustapha ya matsa kadan inda ta shimfide Airah barci take, ya tsurawa fuskarta ido yana kallonta,

Yace ai nasan jiddah mai haquri ce da tausayi, ina tunani ma yanxu tausayin ne ya saka taxo ta gayamin uwani na son komawa dakin mijinta, nasan yanxu xaki fara kuka kina roqona na maida uwani yar uwar kice ciwon xuciya zaya kamata ke kuma baki so ki rasata saboda halaccin iyayenta.

Ta xauna da murmushi a fuskarta wanda bai kai ciki ba, batayi magana ba illah fadawa da tayi kogin tunani, banan da uwani sune matsalar ta a yanxu kuma tana roqon Allah ya taimake ta ya raba ta dasu lafia.

El'mustapha ya daqo yana kallonta,

Tunanin me jiddatulmusty take yi?

Tace ba komai,

Ya tashi ya cire doguwar jallabiyar dake jikinsa, kafin ya qara kallonta,

Ina so na dauko wata mai aiki saboda Airah ke kuma kiji dani,

Ta ware idanu tana kallonsa,

What? Mai aiki, wace irin mai aiki kuma el'mustapha? Kai baka ga halin da nake ciki bane, Dame xanji ni kuma me xanyi da mai aiki.

Ban fahimce ki ba jiddah, wane hali kike ciki wanda ni ban sani ba, menene laifin mai rainon da xan dauko?

Ta tashi tana bata fuskarta tana fadin babu amma ba yar iskar da xata qara xuwa gidannan da sunan aiki ana fakewa akan mijina, kowace mace ta taso mijina, dame el'mustapha yafi sauran maxan ne, why only you?

Sai yanxu el'mustapha ya fahimci inda ta dosa, ya tsura mata ido dubi yanda ta birkice masa daga magana, sam jiddah ta canxa sosai, amma shi baiga laifi anan ba saboda ya dauko mai rainon airah shi me xaiyi da matan ne.

Yace jiddah menene dan na dauko mai tayaki rainon airah, qaramar yarinya ce fa..... ta katse sa,

Qananan yaran ne kemin raino nima ina rainon su da sun girma basu da abin so sai mijina, ni xan iya rainon airah saboda ba abinda nake yi a gidannan sai girkinka da kula da sashen ka, idan ka matsa dole sai an dauko mai raino na amince amma fa namiji xaka dauko yayi rainon airah.

Ya bude idanunsa sosai yana kallonta bayan ya gyara tsayuwarsa,

Namiji jiddah? Wane irin namiji xan dauko yayi min rainon ya'mace? Me ma xai kawo namiji har cikin gidana da falona yana kallon matata.....

Tace nima babu macen da xaa dauko taxo tana kalle min miji, ban nemi xama da mai aiki ko raino ba, ni na gaji haka kuma bana so El'mustapha,

Ni fa wadda xan dauko Nanny ce, ibrahim naji yana magana xai daukowa matarsa shine nima n..... ta katse sa,

Oh God El'mustapha, nanny xaka dauko min ta xauna dani a cikin gida, in maka kwalliya na fito ita kuma ta saka mini skirt ko matsatsen wando ta fito xuwa raino, kai kuma kana kallonta ko?

Yace sharri kuma xaki min jiddah, idan ba kyaso ne kice ba kyaso amma banda sharri kin sanni bani da kallon mata ballantana ma qabila, me xanyi da ita jiddah.

Ta xauna tana fadin to bana so, I can take care of my daughter, in kuma ka matsa dole naji a dauko tsohuwa irin Inna wacce ko haqoran gaba babu a bakinta sai yawun goro na amince,

Ya saki dariya yana xama kusa da ita,

Oh ni El'mustapha duk yanda nayi da jiddah ban mata dai dai ba, nikam na rasa inda jiddah ta dauko wannan halin a yanxu.

Ta tabe baki batare da tayi magana ba.

*

'Abba ni ka saka baki kayiwa jiddah magana ina son el'mustapha ta barni na aure sa dan Allah abba,

Hajiya ta xare idanu tana kallonta,

Anya uwani na da hankali kuwa, kin san me kika fada?

'Abba yace bata da hankali kam, ai na gayamaki har aiki aka mata amma babu canji sai ma nake ganin abin a jinin ta yake ba wani faduwa da xaa fake da ita, an dai ci kudi na ne amma uwani kam sai addua.

Uwani tace Allah abba na shiryu nayi nadama kowa ma ya sanni, waccan karon ba laifina bane, laifin jamcy ne bani da niyar cutar da jiddah itace ta xugani, dan Allah ku taimakeni kada a nuna min baqin ciki a maidani dakina yau.

Hajiya tace sam bada yawu na ba wallahi, babu ruwana kuma idan aka dage da lallai sai uwani ta koma dakin ta baa min adalci ba ta tashi ta fice a fusacce,

Uwani ta bita da kallo kafin ta dubi abba, ita dai hajiya har yanxu abba bata daina nuna min baqin c.... bai bari ta qarasa ba ya bige mata baki,

Kul na qara jin wannan kalmar a bakin ki, ba mahaifiyar ki bace, meyasa ba kya tunani kafin ki furta magana, ki fa yi a hankali da duniya uwani, ki dawo cikin hayyacinki kisan me kike yi, Allah baya barin mai xalunci da kuma mai sabawa iyaye, kar na qara jin haka daga bakin ki.

Tau abba kayi haquri na daina, xanje ma na bata haquri.

Yace maganar el'mustapha wannan karon ma xan gaya maki babu yawuna babu hannuwana aciki kamar farko, kuma bani buri ko fatan naga el'mustapha ya aure ki domin baki cancanta ba, kince naxo dake ne domin kiga jiddah ki roqeta gafara ba wai ki roqeta ta maidaki dakin ki ba, ni babu ruwana duk abinda suka maki ke kika ja tashi kibani guri shashasha.

Ta tashi tana tunxure baki ta fice, tunda baxasu maidata dakin ta ba ita xata maida kanta, a bata key din dakin ta shiga daga yau ta xama matar el'mustapha ta maida kanta dakinta duk mai baqin ciki sai dai ya mutu amma sai ta haihu da el'mustapha.

*

'Washe garin ranar duk basu hadu da jiddah ba sai bayan jiddah ta fito raka el'mustapha xai je gurin aiki suka tsinkayo uwani tsaye a gurin motar sa, taci kwalliya abinta tana jiran fitowarsa.

Suka qarasa jiddah na kallonta,

'Anty jiddah an tashi lfy, yaya barka da fitowa cewar uwani dauke da murmushi a fuskarta,

Duk ba wanda ya amsa aΒ  cikinsu,

'Dan Allah kuyi haquri nidai a maidani dakina, a bani key xanje na gyara dakina, wannan karon bani...... tayi shiru sakamakon bugu da taji a tsakiyar kanta, ji kake tum.... ashe jiddah ce ta rarumo wani katon dutse ta buga mata aka...

Uwani ta xube gurin a sume, el'mustapha ya juyo yana kallon jiddah cikin mamaki, xai yi magana tayi saurin tsaida sa,

Kar kace komai, yar uwarka ko tawa, ba ruwan ka she is my sister, shiga mota kayi tafiyar ka.

Yanda idanunta suka juye abin ya bashi tsoro, innalillahi wai meke damun jiddah,

Ya xagayo da sauri yana fadin na tafi ina jiddah, idan kika kashe.....

Nace ba ruwanka el'mustapha,

Ya ja dogon tsaki hankalinsa ya tashi sosai ganin jini na fita ta goshin uwani, kada jiddah tayi kissan kai, yanxu fisabilillah idan iyayenta suka ganta haka ya xasu ji, ya kalli jiddah cikin takaici sai huci take, tsaki ya ja kafin ya bude motarsa tana kallo ya saka uwani a mota xai fita da ita.

Da gudu ta qarasa bakin gate ba inda xai fita da uwani, securities suka taso amma bata damu ba, ta tare hanya sai idan xai taka ta ne ya wuce,

Ko jiddah ta haukace ne, ya tambaya cikin xuciyarsa yana kallonta ta glass din motar, ya fito a fusacce,

Xaki matsa ne ko sai naxo na taka ki,

Wallahi baxaka kai uwani asibiti ba, sai dai ka takani ka wuce.

'Wannan wane irin abin kunya ne jiddah ke janyo masa cikin yaransa,

Yayi ma wani sergeant magana akan yaxo ya kai uwani asibiti, ta matsa tana sauke numfashi suna fita abba ya fito jin hayaniya.

Ni jiddah ni xaki wulaqanta,

Nima ka gama wulaqantani na daukar uwani ka saka a mota kowa yana kallon ka.

Yace tor shikenan, ya juya a fusacce ya nufi cikin gida bai jima ba ya fito dauke da wani key na mota, bai qara bi ta kanta ba ya fice, ta tabe bakinta kawai.

'Abba ya tambaya dalili, batare da tunanin komai ba tana yarfe hannuwanta tace uwani na fasawa kai an nufi asibiti da ita.

'Abba baice komai ba ya juya cikin gida ko baa fada ba yasan duk akan el'mustapha ne daga yanayin da yaga ya fita.

Yinin ranar sai taji ta damu el'mustapha bai kirata ba kuma ta kira yaqi ya dauka,

Tana ganin sanda aka dawo da uwani asibiti an daure mata kai da bandage πŸ€• amma dan qarfin hali irin na uwani sai cewa take sai dai na dawo dakina ko kashe ni xaa yi kuwa.

Jiddah ta kasa sukuni, ga kukan airah ya Dame ta, ta dauke ta, ta nufi sashen su banan da niyar cewa ta goya mata ita tana so ta daura girki.

Sai ta sami banan daki kwance tana waqa da tsananin farin ciki a fuskarta,

Idan ba kunnuwanta ke mata gizo ba kamar waqar da banan keyi harda sunan el'mustapha a ciki,

_farin ciki a yau ya sameni_

_Dadi na rayuwa ya riskeni_

_Majaujawa ta so da ta daukeni_

_Sai ta barni gidan da aka raineni_

_Ta bani wanda nake so a badini_

_Soyayya na xata xata barni_

_Sai akace min naje an kyaleni_

_'Na auri wanda nake so ya soni_

_Kullum da safe in har ya ganni_

_Da murmushi yake qawatani_

_Naxo Musty ka in gantani_

_Eh..... Gani gaka_πŸ’ƒπŸ»

Jiddah ta shigo dakin hankalin ta a tashe take kallon banan, idanunta a rufe take waqar fuskarta dauke da murmushi cikin farin ciki, jiddah na tsaye ta qara dauko wani baitin,

_Cikin gidan mu akwai wani d'an yaro_

_Dadin muryarsa shi nafi sauraro_

_Farin wata nake shiko tauraro_

_Sonsa a xuciya da shi naci karo_

_Al'bishiri kuce min dan goro_

_Ya dan uwa musty xan yo koyo_

_Nayo Mari akan sa na bijiro_

_Lambar girma musty baya cin xero_

_'Na baka xuciya baniyi kwaro_

_Mai kyau kamar fulani uban toro_πŸ‘πŸ»

_Yau gani gaka bana jin tsoro eh... Gani gaka._

How I wish nima na xama BanantulMusty ka..... tayi shiru sakamakon saukar Mari da taji a kuncinta,

Ta bude idanunta da sauri ganin jiddah a gabanta ta xabura ta tashi cikin matsinanciyar faduwar gaba.

Kafin tayi wani motsi jiddah ta qara dauke ta da wani Marin cikin bacin rai, sai ga jini yana fita ta gefen bakin banan,

Kashe ni kuke son kuyi, me nayi maku, meyasa kuke son mijina, meyasa kuke son ganin bayana, farin cikina ne bakwaso ko me, ku raba ya'yana da farin ciki, baxan taba yafe maku ba, kuma bake ba el'mustapha har abada sai dai ki xamoΒ  Banantulislam, kiji rani kiga hukuncin da xan yanke akan ki.

Ta fita a fusacce tana tafe tana sharar kwallah cikin tashin hankali ga wani xafi da xuciyarta ke mata,

Wayarta ta dauko, nabila ta kira cikin boye damuwarta,

Ki turomin islam gobe Nabila,

Lafiya jiddah naji muryarki wata iri.

Ba komai, ki turo min shi xamuyi magana.

Tace to shikenan jiddah.

Kuka sosai jiddah tayi, babu wata walwala ko sukuni a tare da ita, hajiya tayi juyin duniya tana tambayar ta taqi ta gayamata, haka ma abba, ganin yanda har idanunta suka kumbura.

Cikin qanqanin lokaci xaxxabi mai xafin gaske ya rufe ta, haka el'mustapha ya dawo ya sami airah gefenta tana ta kuka taqi ta kula ta.

Ya dauke ta da sauri yana kallon jiddah, yanayin ta kadai ya gane babu lafiya, ya kai hannunsa a jikinta ya taba xafi rau.

Me ya same ki jiddah, ta bude idanu da kyar tana kallonsa kafin ta maidasu ta rufe rub xuciyarta na cigaba da bugawa saboda tsananin tashin hankali.

Bai qara magana ba ya fita yana tambayar hajiya,

Nima nayi tambaya bata fada ba sai kuka take tun daxu,

Ya bata airah kana ya juya xuwa dakin,

Meke damun ki jiddah ya tambaya yana dago ta,

Batayi magana ba illah qara shigewa da tayi jikinsa, yana jin bugun xuciyarta ga jikinta yayi xafi rau,

Ko muje asibiti ne jiddah,

Ta girgixa kanta.

*

'Washe koda islam ya xo el'mustapha ya fita,

Tace ka gayamin gaskiya islam ka shirya auren banan.

'Na shirya anty jiddah, ki tambayi anty nabila tasan komai.

Tace ka turomin iyayen ka gobe suxo da sadaki, cikin satin nan xaa yi auren ka da banan.

Farin ciki ya mamaye xuciyarsa sai godiya yake mata, ya tashi ya fita,

Ta kira kakar banan ta gayamata tana son ganin ta gobe tare da kawun banan xaa yi auren ta cikin satin.

Duk shirye shiryen da ake ba wanda ya sani har el'mustapha da banan, sai bayan xuwan iyayen islam ne el'mustapha ya sani, shine ya xama kamar waliyin banan ya bada auren ta tare da wani kawunta.

El'mustapha bai san dalilin saka wannan auren da wuri ba kuma bai tambaya ba kada yayi laifi ace kuma son ta yake gashi jiddah cikin kwana biyu bata cikin walwala kamar wacce bata da lfy.

Banan kuwa da ta sami labari hankalin ta ya tashi sosai taga iyayen islam nesa ba kusa ba yafi qarfinta daga babban gida ya fito amma bata san meyasa take jin el'mustapha fiye dashi a xuciyarta ba, tayi kuka har ta gode Allah.

Ga sadakin banan cewar el'mustapha yana kallon jiddah.

Ka riqe hannunka, gobe xanje nayi mata duk abinda yace nayi a matsayina na mahaifiya na gayawa kakarta kada su wahalar da kansu ni xan mata komai.

Ni kuma me xanyi jiddah, abari na sami ladar aurar da marainiya jiddah.

Murmushi kawai tayi batare da tayi magana ba.

Cikin satin akayi komai na biki, kuma alhamdulillah biki yayi jama'a anyi komai lafiya an kai amarya.

Jiddah tayi mata hudu ba sosai, ta qara da cewa,

'Na xauna dake da xuciya daya banan bani da niyar cutar dake, tun kina qarama na dauki amanarki a wurin kakar ki, alhamdulillah na aurar dake ga mijin da nake ganin ya dace da rayuwarki, idan kika ci amanar sa Allah baxai barki ba, idan kika ci gaba da son el'mustapha a xuciyarki keda Allah kuma baxan taba yafe maki ba, ki rungumi mijinki da hannu biyu kuma ki so shi, mata da yawa a waje suna neman irin islam basu samu ba kada kiyi sake da damar ki, ko kashe auren kika yi kika fito baxaki taba auren El'mustapha ba hassalima baxaki xauna gidana ba sai dai kije qauyen ku kiyi zawarci.

Ta tashi ta fice, banan sai kuka take, ta dauki islam a matsayin qaddararta kuma xatayi masa biyayya ta xauna dashi da xuciya daya tasan jiddah baxata taba cutar da ita ba, el'mustapha ya riga yayi mata nisa har abada.

Jiddah na dawowa gida wanka tayi ganin dare yayi sosai, ta nufi dakin el'mustapha suna hada ido ta saki ajiyar xuciya tana kallon sa.

Ta kau da banan yanxu babbar matsalarta *UWANI* ce.........

Kallon ta El'mustapha yayi, kafin

Yace uwar amarya an dawo kenan.

Ta qarasa cikin dakin, shimfidar da airah tayi tana kallonsa,

Me ya hana ka barci tuntuni el'mustapha?

Rashin barci nawa kuma ya xama abin tuhuma yanxu jiddah, lallai

Sai ya gyara kwanciyarsa hade da lumshe idanunsa,

Ta tabe baki ta xauna tana fadi a ranta in ma banan ce ta riga ta xamo matar wani a yanxu.

Pampers ta soma sakawa airah, tayi feeding din ta kafin ta kai ta saman bed din ta, ta kwantar da ita, ta rage hasken fitilar dakin ta dawo bayan el'mustapha ta kwanta.

Haka take ji cikin kashi 70 na damuwar ta 30 ya kau, uwani ce babbar matsalarta a yanxu kuma bata san yanda xata bullowa al'amarin na ta ba.

Ta sauke numfashi a hankali tana kallon el'mustapha tuni ya jima da yin barcinsa, ta lumshe idanuwanta tana karanto addu'ar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login