Showing 93001 words to 96000 words out of 138779 words

Chapter 32 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

2019

nasan ba halin ki bane kuma bana son ki dashi ki barshi da uwani yafi dacewa not you.

Tsura masa ido tayi tana kallonsa, shima kallonta yake kafin yace saboda damuwa kinga yanda kika dawo just for only today,

Bata ce komai ba ta soma karban abincin da yake bata, nan da nan suka shirya kamar wani abu bai taba hada su ba.

Koda hajiya ta dawo dakin tayi mamakin ganin jiddah kwance a jikin el'mustapha sai dariya suke cikin farin ciki.

A gurguje pls😒

2 months....

'Alhamdulillah jiddah na samun kulawa sosai gurin dr merah har ta soma takawa da qafar sai dai ba sosai ba.

Cikin wannan lokacin harda aikin uwani anyi batare da sanin su hajiya ba.

Ganin jiddah ta sami sauqi sosai har tana iya taka qafar ko bada stick ko wani ya riqa ta ba suka soma shirye shiryen dawowa gida cike da farin cikin dimbin nasara da suka samu akan aikin jiddah bayan sun cire tsammani daga qafar baxata qara moruwa ba.

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

55

Saukar su Nigeria ke da wuya, motocin gidan El'mustapha suka iso airport.

Cikin masu tarbar su jiddah harda su anty ikram da yusrah,

Cike da tsananin mamaki suka rungumeta suna kallonta qasa da sama, kamar bata taba samun wata lalura tare da ita a qafar ba.

Welcome back jiddah, Allah ya qara lafiya mai amfani cewar Nabila tana kallonta cikin murmushi.

Jiddah kallonta tayi tana fadin kin goge laifin ki na rashin xuwa duba ni a Germany, kika xo tarbata, naji dadi sosai Allah ya bar xumunci.

Amin ta fada cikin murmushi.

El'mustapha yayi gaba da baby rungume a jikinsa, Allah kadai yasan irin farin cikin dake xuciyarsa.

Suna iso wa gida sunyi mamakin samun mutane haka duk yawanci daga gurin aikin el'mustapha ne sunxo taya sa murna, kuma sosai ya nuna farin cikin sa,

Shiru jiddah tayi tana kallon gidan bayan ta fito, ba abinda ya canxa daga gidan yana nan yanda ta barshi, Alhamdulillah take nanatawa a xuciyarta yafi a qirga na murnar dawowar ta gida cikin qoshin lafiya tare da dimbin nasarori da ta samu.

Ji tayi an rungumeta, ko baa fada ba tasan twins din tane,

Welcome back mummy, we miss you,

Ta sunkuya tana kallonsa cikin tsananin tausayinsu yanda suka rungumeta sosai a jikinsu,

Mummy baxaki qara xuwa ki barmu ba ko? ta gyada kanta tana murmushi.

Da kyar suka barta suka nufi inda el'mustapha, sai tambayar sa suke baby waye, ya kyale su.

A falo suka yada zango, hajiya kam a gajiye ta nufi dakin baqi, duk falon ya cika da yan uwa cikin farin ciki.

Mummy baby waye a hannun daddy cewar aryan,

Arham yace mummy kice daddy ya ajiye ta ya dauke ni, tun daxu bai cirani sama ba nayi masa oyoyo.

Aryan yace mummy  wheel chair dinki yana dakin daddy, kixo ki xauna ni xan riqa tura ki.

Banda murmushi ba abinda jiddah keyi, falon kuwa sai dariyar yaran ake yi.

Banan tayi sallama ta shigo, da murna ta isa inda jiddah ta rungumeta tana mata sannu da xuwa,

Jiddah ta amsa sama sama,

Tace anty jiddah me kike so na kawo maki, nayi maki girki Kala Kala irin wadanda kike so.

'ki barshi anjima xanci.

Batare da tunanin komai ba banan ta juya tana kallon el'mustapha dake ta surutu da twins, ta saki ajiyar xuciya kamar wacce ta dade tana neman abu bata samu ba sai yau,

Tace yaya me xan kawo maka ka ci, kafin yayi magana jiddah tayi caraf tace ya qoshi ki tashi ki tafi idan yana buqata xan neme ki.

Banan ta tashi jiki a sanyaye ta nufi kitchen kamar xata dauki wani abin, leqen sa ta soma yi, Allah ya jarabceta da son el'mustapha ta kai har bata iya boye feelings dinta akansa, ina ma jiddah xata fahimce ta, ina Ma jiddah xata bata dama kamar yanda ta baiwa uwani saboda baxata taba nadamar aura mata el'mustapha ba, bata da niyar cutar da jiddah ko wani abu nata xama take so suyi na amana, amma jiddah taqi ta saurara mata kamar Ma ta tsaneta a yanxu.

Allah ka cire min son wannan bawan Allah idan ba alkhairi bane.

Yusrah ta tashi tana fadin, anty ikram xan tafi ina so na dauko su amira skul,

Tau shikenan nima xuwa anjima kadan xan tafi.

Jiddah Allah ya huce gajiya ya qara lafiyar jiki, kuma a kula da qanina yanda ya dace saboda yayi haquri cewar yusrah.

Murmushi kawai jiddah tayi suna wasa sosai tsakanin su,

Yusrah ta dubi el'mustapha tana fadin, xo muje ka taka min akwai maganar da xamuyi,

Yace ok sister, ya tashi yana ajiye baby akan sofa, twins suka mata caa suna kallonta sai yanxu suke ganin fuskarta da kyau.

She is beautiful daddy, who gv you?

Yace Allah, babyn mummy ne idan kuka taba ta tashi barci ba ruwana, mummy xata dake ku.

Suka juya suna kallon jiddah cikin mamaki, el'mustapha ya fita tare da yusrah.

Wai haka ne mummy? Ta gyada kai tana kallonsu,

Jiddah ta juya tana kallon kitchen tana lura kamar banan din bata fita ba,

'me kike yi a kitchen dinne banan?

'Anty jiddah ina hada abincin ne ta fada cikin rawar jiki, ta fito da sauri da warmers a hannunta ta nufi dinning tana shiryawa duk abinda take idanun jiddah akan ta, tana gamawa kuwa tace ta fita...

Wai me banan tayi maki ne jiddah, na lura tun a Germany kika takura mata cewar ikram.

Jiddah ta tunxuro baki, batayi magana ba,

Baki ji bane? Ta qara tambayarta fuskarta ba walwala, sosai jiddah tasan anty ikram bata wasa ko akan el'mustapha ne kuwa shi kansa yana tsoronta itace babba a gurin su duk yanda tace haka xaa yi musamman yanxu da take kamar uwa a gurin su.

Tace El'mustapha  take so...

'Anty ikram ta kalle ta da mamaki,

Tace ba dan na san ki nasan halin ki ba jiddah dana qaryataki, saboda banan xata so el'mustapha, ba ajin ta bane she knows, dan haka baxatayi wannan tunanin ba.

Idan har uwani xata iya son el'mustapha ta aure sa saboda me banan baxa ta so sa ba? Ita da take ganin xama kawai tayi a gidan bata da alaqa damu ba kamar uwani da muka taso tare ba.

Amma dai banan ta bani mamaki jiddah, sosai kuwa wannan simi simi nata ashe dai munafuka ce tunanin ta el'mustapha xai aure tane, mtsewwwww aikin banxa kada Ma ki wahalar da kanki wajen dorawa kanki damuwa dan el'mustapha baxai aure ta ba, ba abin da xaiyi da banan.

Jiddah tace tunanin ki kenan anty ikram, amma namiji idan ya tashi iskancin sa babu ruwansa da yanda mace take ko matsayinta, banan tana da kyau da diri saboda me el'mustapha baxai so ta ba tunda ba arxiki yake nema ba, so sone haka namiji namiji ne, baka sanin inda ya dosa a koda yaushe canxa sheqa yake, kina ganin kamar el'mustapha baxai so banan ba saboda tana talaka ko dan saboda ni na fita kyau amma el'mustapha ya taba son banan.

Shi el'mustapha? Ta tambaya cikin mamaki, ta yaya, ya xaa yi el'mustapha ya so wannan yarinyar, yar aikin gidansa, me ya ruda shi a jikin banan wanda ke baki dashi.

Jiddah ta tabe baki batayi magana ba,

In kuwa haka ne banan xata bar gidannan, ni bana son xama da munafuki, nifa shiyasa ban yarda da yar aiki ba ko kadan kina ganin duk masu aikin gidana tsofaffi ne bani da yarinya ko budurwa baxan iya ba, ai kece Ma da wata shegiyar xuciya yanda kika cije lallai sai el'mustapha ya auri uwani, ba dan mama ba lokacin wallahi baxai aure ta ba kuma banan xata bar gidannan.

Tace aa anty ikram ki barta ba sai ta bar gidan ba a ynxu, idan el'mustapha yaji wannan mgnr xaiyi tunanin na kawo shi qara ne gurin ki, kibari idan wani abin ya tashi daga baya sai ki dauki mataki ni kada Ma ki masa mgnr banan yanxu tuntuni yace baya son ta kar na qara tada maganar.

Ok inyi shiru in barki da yarinyar kenan, shikenan ba matsala gidan kine ke kika ji kina iyawa amma fa el'mustapha baxai taba auren banan ba.

Jiddah tayi shiru,

Haba haba, kowace mace ta taso sai qanina kuma abin haushi yaran da suke qarqashin sa matarsa ke riqo, banda xalunci da rashin imani sai su rasa namijin aure sai mijinki, me suke nufi da el'mustapha, namamajo ko me? A bata masa suna ace yana aure aure a gari to baxai yiwu ba idan har na qara jin qishin qishin cewa banan na son el'mustapha wallahi har ke jiddah sai ranki yayi matuqar baci.

Sai kiyi ta xama simi simi kamar ba mace ba, sanyin ki yayi yawa, haqurin ki Ma yayi yawa, duk wadda taxo tace mijinki take so, ki bar banan din ta auri el'mustapha kina xaune a gida Inna mai maki aiki xata xo tana son el'mustapha ita Ma.

Jiddah ta subulce da dariya har tana rufe bakinta da hannunta,

Tace anty me el'mustapha xai yi da Inna, ai xata haife sa Ma.

Gaskiya na gaya maki yanxu dai mama bata raye ballantana ta goya maki baya ga el'mustapha ya qara aure.

Cikin rashin fahimta jiddah ke kallonta gabanta na faduwa,

Mama bata raye kamar ya anty ikram, wace mamar kike magana?

Ikram ta dube ta dai dai lokacin el'mustapha ya shigo,

Tace bana son rainin hankali jiddah ina wasa dake ne, wace mamar kika sani bayan tamu, tun bayan dawowar ki kallon ki kawai mukeyi ba wanda kika yiwa gaisuwar mutuwar mahaifiyar m.....bata qara sa ba taga jiddah ta xube gurin,

El'mustapha ya qaraso cikin falon da sauri yana kallon yayar tasa cikin tuhuma..

Me kika mata sister, me ya sami jiddah? Ita ma hankalinta ya tashi sosai, a tare suka nufi jiddah suna kiran sunan ta amma bata motsi,

Daukarta el'mustapha yayi jikinsa na rawa xai fita da ita,

Tace bari na kawo ruwa ina ji suma ne tayi,

Me ya sumar da ita? ya tambaya yana kallonta cikin bata fuska,

Mgnr mama nake mata bata san ta mutu bane,

El'mustapha ya ajiye jiddah yana fadin,

Saboda me sister?

Ko duka na xakayi ne saboda jiddah, matarka fa ba wanda tayi wa gaisuwar mahaifiyar mu, mun riqeta a xuciyar mu da wannan so kake... Ya katse ta,

Wallahi jiddah bata san da maganar mutuwar mama ba, you know her condition sanda aka ganta saboda me xan gayamata ina ji dake Ma akayi mgnr cewa kada a gayawa jiddah saboda cikin dake jikinta at that time, ko yaushe jiddah tana tambayana mama sai dai nayi mata qarya, amma meyasa sister,

Sam na manta da wannan xancen wallahi, bari na kawo ruwa ai suma ne ba wani dogon abu ba, ta juya da sauri.

Ya bita da kallo cikin takaici, yana Jan tsaki a xuciyarsa, ba dan yayar sa bace da qanwar sace ba abinda xai hana masa xuba mata kyawawan Mari a fuska, meyasa mace komai girmanta wani lokacin bata da tunani?

*

Da daren ranar duk da jiddah na cikin damuwa bai hana mata sauraren Islam ba lokacin da yaxo yayi mata ya jiki.

Sosai ya gayamata canje canjen da yake fuskanta a gurin banan wanda sam baya jin dadin sa kuma da ace baya son ta da gaskiya da tuni ya dade da barin ta.

Xan yi magana da banan idan har bata son ka nasan me xanyi islam, kuma ai xaka so Mamee yar wajen anty ikram tama fi banan din komai illah shekaru da banan xata nuna mata.

Baice komai ba shidai banan din yake so,

Idan munyi magana xan kira nabila a waya amma kada ka damu,

Yace to shikenan nagode anti jiddah,

Ya ajiye mata qatuwar Leda bayan ya tashi,

Yace a bawa our new baby,

Murmushi jiddah tayi tana fadin, baby tana godia sosai islam,

Ban ma san sunan ta ba,

Sunan mahaifiya tane Zubaida amma ake kiranta Airah,

Allah ya raya ta,

Tace amin,

Ya tashi ya fice, ta dauki ledar tana dubawa, kayan babies ne masu kyau kuwa.

El'mustapha yana tsaye qofar falonsa ya xuba mata idanuwa,

Jiddah har yanxu dare fa yana tafiya, tun daxu na saka airah barci.

Ta dube sa kafin tace, xo kaga islam ya kawo wa mai sunan mamana,

Ya tako a hankali ya shigo falon, kayan ya karba ya ajiye gefe batare da ya duba ba, yace ni bana son wasu kaya a yanxu jiddah kadai nake so da buqata kin barni tun daxu sai raino nake maki.

Ta riqa hannunsa tana kallonsa,

Muje na baka ladan rainon nasan shi kake wa safa da marwa tun daxu.

Dariya El'mustapha yayi yana shafar sumar kansa.

*

2 days....

Jiddah ta sami banan da mgnr islam,

Tace kiyi haquri anti jiddah ki sake min fuska kamar da, na amince xan auri islam.

Jiddah tace baxan cigaba da sake miki fuska ina yarda dake kina cin amanata ba, babu yarda yanxu tsakanin mu idan har kina son mijina, maganar kina son islam a yanxu nasan qarya kike domin da wadannan kalaman kika yaudare ni da farko kika ce kina son islam bayan kinsan kina son mijina.

Cikin kuka banan ta riqo qafafunta,

Tace kiyi haquri anty jiddah ki yafemin, ba laifina bane wallahi xuciya tace tun ban ganshi ba na kamu da soyayyarsa a dalilin yawan kallon hotunan sa dake falon ki, ni kaina bansan yanda akayi na fara son sa ba, ki yafe min na amince ko a yau ne ki aura min islam shine xabin Allah.

Jiddah bata jima da dawowa daga inda banan ba sai ga sallamar su abba,

Cikin murna ta janye airah da take shayarwa tana kallonsa,

Oyoyo abbana, sannu da xuwa,

Jiddana tashi tashi naga yanda kike takawa, tashi naga tafiyar ki jiddah.

Cikin dariya ta tashi ta nufe sa,

Alhamdulillah Allah mun gode maka, ya karbi airah cikin farin ciki,

Jiddah ta daga murya sosai tana kiran hajiya,

Hajiya kixo ga abba,

'Abba ya xauna yana fadin, barakallah yarinya tayi bul but da ita, girmanta yafi na yan watanni biyu, me kike bata ne haka jiddah.

'Abba duk abinda kake ci shi take ci, bari na kawo maka abinci, ta juya ta bar falon.

Hajiya na shigowa aka fara kallon love anyi missing juna🤭

Inna ta shigo tare da jiddah dauke da kayan abinci,

Tace bari na kira el'mustapha bai jima da dawowa ba gurin aiki.

Idan barci yake da kin barshi jiddah tun da ina nan,

Tace aa abba ko barci yake sai ya tashi ai miji bai fi uba ba, ballantana ba barci yake yi ba wasan ball yake kallo.

Yace to shikenan, ta fice hajiya ta sauko tana xuba mashi abinci.

Jiddah tare suka fito da El'mustapha, cikin doguwar jallabiyarsa da gani yanxu ya saka ta da xai fito,

Suka gaisa da abba, yana qoqarin xama sai ga uwani ta shigo falon cikin sallama.

Duk suka xuba mata idanu banda el'mustapha, jiddah kuwa kallo daya tayi mata ta dauke kanta gefe,

Hajiya tace ba dai tare kake da uwani ba, ina ka ganta alhaji.

Uwani xo ki xauna abba ya fada yana kallonta,

Idanu uwani ta xubawa el'mustapha  daga inda take tsaye, ji take kamar taje ta lashe shi saboda so, bata taba jin sonsa ya ragu a xuciyar ta ba koda na minti daya ne, gabanta ya tsananta bugawa lokacin da tayi arba da jiddah.

Sosai jiddah ta canxa daga yanda ta Santa, tayi haske ta qara kyau gwani sha'awa, da ka ganta kasan tana cikin jindadi da more rayuwa babu wata damuwa a tare da ita.

A hankali ta qarasa cikin falon ta xauna jiki a sanyaye.

'Abba yana lura da yanda yanayin su ya canxa duka kamar basa murna da xuwan uwani har hajiya Ma,  uwani yar'sa ce ba abinda xai hana masa xama da ita illah ya cigaba da mata addua matsalar da take ciki anyi aiki sai dai ace alhamdulillah amma kam uwani na nan yanda take sai wasu abubuwa kadan da ta daina, dama lafiya sannu sannu take shiga.

Tashi el'mustapha yayi yana kallon abba,

'Abba bari na barka kaci abinci kafin na fito,

Yace tau shikenan el'mustapha, duk da yasan saboda uwani ne yabar falon baiga laifin su ba dan sun tsani uwani a yanxu.

Uwani ta bisa da kallo har ya shige, ji take kamar tabi bayansa, inama da aure tsakanin su da ta rungumeshi ko xata samu sauqin xuciyata amma ta lura sam el'mustapha baya gabanta ko kallo bata ishe sa ba.

Jiddah kuwa tun da ta maida hankalinta ga airah bata sake dagowa ko magana ba,

Hajiya tace alhaji muje ciki kaci abincin, ta soma kwasar kayan cikin son gujewa uwani.

'Abba yabi bayanta, jiddah Ma ta tashi da sauri rungume da yar'ta,

Uwani tayi saurin tsaida ta,

'Dan Allah anti jiddah ki yafe min, nasan kin tsane ni a ynxu amma kiyi haquri ki bani dama ta biyu na xauna dake baxaki taba dana sani ba, ki aura min El'mustapha a karo na biyu wallahi ina son.... bata qara sa ba jiddah ta dauke ta da Mari, kafin tayi wani yunquri ta sake wanke fuskarta da Mari hade da hankadata ta fadi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login