Showing 138001 words to 138779 words out of 138779 words
Chapter 47 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
dace.
Abunda wasu daga cikin marubutan Haske sukace akan littafin el'mustapha."
*MEENA SLIMZY* Agaskiya uwnaii ta burgenii cikin wannan labarii sosaii take sani nishad'i akullum."
*ZAYNAB BAWA*" Abunda yafii birgenii cikin wannan labarii shine yanda el'mustapha yake gwadawa jiddah k'auna, haqiqa wannan qauna ta tsayamun arai sosai, soyayyace da kowace mace zata so samu wajan maigidanta."
Sannan kuma soyayyar Dr mera da matarshi yana tsayamun arai har nutsewa nakeyi cikin pillow tsabar burgenii dasukeyi."
Amma nikm sam uwanii bata burgenii."🤷 team jiddatulmusty😍
*HAJJACE*. hajja tace itadai duk jaruman cikin littafin babu wanda yake burgeta kaman uwani." sonta takeyii sosaii. Kamar yanda
*XOXO* tanayiwa uwanii sonso."
*Ummy Aysher* tace jiddah tana min a rayuwa Pherty.
*Ayusher Mohd* Allah ya raba mu da hali irin na uwani duk da tana saka ni nishadi pherty.
*Huguma* bana son uwani fatima
*Mmn Khady & Nuceey* bana so da qaunar Uwani ko kadan.
*Billy* Uwani abin sona.
*ME YAFI BIRGE MARUBUCIYAR* *fertymerh zarah*
Inda yafi birgeni a littafin inda jiddah ta kwantar da hankalinta ta rungumi qaddarar da ta same ta da hannu biyu batare da ta nuna wata katobara ba.
_Ta fashe da kuka tana kallonsu daya bayan daya duk sunyi xugum suna kallonta._
_Cikin kuka tace abba meyasa el'mustapha ke kuka, bai yimin bayanin komai ba, kaima kuka kake yi abba, na shiga uku, ku fiddani a duhu meya same nine?_
_'Abba yasa habar riga yana share kwallah ya kasa magana illa juyawa da yayi ya bar dakin, shima ibrahim kasa jurewa yayi ya fice da sauri._
_Dr bakori ya dube ta yana fadin take it easy jiddah, kibar kuka, ya shiga rattabo mata al'amarin da ya sami rayuwarta, kiyi haquri wanna ba shine qarshen rayuwar ba, yau ne kake mai rai gobe ne kake gawa, yau ne kake da amfani, idan Allah yaso gobe ne ka xama tarihi,_
_A rayuwar jiddah bata taba tsammanin wata qaddara makamanciyar wannan xata taba shafar rayuwarta ba to ina ruwan Allah?_
_Ta runtse idanunta da qarfi, ita kadai tasan axabtuwar da ruhinta yake, ita kadai tasan radadin da take ji a xuciyarta, al'amarin ya shallake tunaninta, lallai dan Adam ba abakin komai yake ba._
_Ta karbi qaddararta da hannu bibbiyu tana fatan Allah yasa hakan ya xamo kaffarar a gareta ya kuma bata ikon cinye jarabawar._
_Ta kai duka tafukkan hannayenta guda biyu a fuskarta ta saki wani gigitaccen kuka mai daga hankalin mai saurare,_
_Shikenan baxata qara tafiya ba, dr ya juya yabar dakin._
_Da sassarfa el'mustapha ya qarasa gareta, ya rungumeta sosai kamar xai maidata ciki shima kukan yake yi, da kyar ya iya bude baki yayi magana,_
_INA SON KI JIDDAH, cikin kowane irin yanayi cikin kowane hali ina tare dake, nothing will separate us, ba abinda xai ragu a xuciyata daga qaunar dana ke maki, El'mustapha naki ne ke kadai har abada._
Ana son kowane mutum ya riqa godewa Allah a duk abinda ya jarabce shi da shi, wani bashi da hannu, wani qafa gabaki daya, wani ido ya rasa, wani kuwa rayuwar gaba ki daya ya rasa, meyasa a kullum baxa mu godewa Allah a yanda yayi mu ba, meyasa idan ya jarabce mu baxa mu gode masa ba mu dauki qaddarar da hannu biyu, ya kamata mutane su gane hakan duk abinda ya faru da bawa rubutacce ne acikin qaddarar rayuwar sa kuma kowane d'an Adam Allah yakan jarabce sa ya gwada qarfin imanin sa.
Allah yasa mu dace.
Sai kuma yanda el'mustapha ya jajirce wajen nunawa jiddah soyayyar sa batare da ya guje ta da qaddarar da ta same ta ba, da wani ne xai iya wulaqanta ta ko ya sake ta ko kuma ya qara aure amma ya nuna mata a lokacin ba abinda yake buqata kuma yafi muhimmanci a rayuwar sa kamar jiddatulmusty, lovely husband👌🏻
*KUSKURE*. tabbas jidda tayi kuskure wajan sanya mijinta ya aurii uwani, shi namiji ba'asanyashii yin aure domin duk wani abunda yaje yazo tokaine za'ad'aurawa laipi ko kuma wani abun ma zai ringayi da gayyane, gara kabarshi idan shida kansa yayi niya to fa dama wannan babu mai hanashi, jiddah tayi kuskuren yarda da uwani"
*NASARORI*. tabbas ansamu nasarorii cikin wannan littafii ko daga yanda ya karbuu wajan makaranta, sak'onnii dakuma waya akaii akaii marubuciyar ta ringa samu na yabo da kuma jinjina."
*SAKO*, wannan littafii ya kunshii saqonni da yawa, yadda zaka kula da gidanka, yanda zaka zauna da mutane, yadda zaka kula da mijinka, kai hatta ladabin da zakayiwa mijinka magana, tabbas el'mustapha ya kushi sakonii dayawa ya yafadar ya wa'azantar sannan ilimantar."
SHARHI
ZAYNAB BAWA
*'