Showing 27001 words to 30000 words out of 138779 words

Chapter 10 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

1990

Xarah💞

_dis page is 4 u pherty novels and musha karatu, I heart u ol❤_

27

Jin motsin fitowar el'mustapha ya sakata juyawa tana kallonsa, shima kallonta yake,

'keda waye naji a dakin nan kuna magana,

'amarya ce, ina ji kai take nema bata jima ba ta fita.

Ya tabe bakinsa, ya qaraso yana kallon takardar dake hannun jiddah,

'Wannan takardar mecece?

'nima yanxu na ganta bansan ko ta mecece ba, ta soma warwarewa, el'mustapha ya karbi takardar da sauri yana fadin.

Jiddah kira min uwani yanxu.

Me ya faru,

Just call her.

Bata qara mgn ba ta fita, bata jima ba sai gata ta dawo tare da uwani a bayanta, wannan karon ma da carbin ta a hannu.

Yanda uwani ta gansa yayi matuqar bata tsoro, fuskarsa a daure, bama wannan ba ita kam duk iskancinta bata taba ganin namiji haka a gabanta ba, sai ta buya bayan jiddah,

Fito nan, ya nuna mata gabanshi,

Wayyo Allah, anty jiddah ki bashi haquri, kice ya saka rigar shi.

Jiddah ta dan dubeshi cikin marairaice fuska, sai kuma taje ta dauko masa doguwar riga, kamar baxai saka ba ya xura yana kallon uwani.

Takardar da na baki saboda kin rainani, sai kika kawowa matata ko?

Kayi haquri baxan qara ba,

A tunaninki menene acikin takardar?

'Na dauka saki ne aciki,

Kin dauka saki ne aciki shiyasa kika kawowa jiddah,

Aa bahaka bane,

To meyasa kika kawo takardar, saboda kin rainani ko, ba laifin ki bane, fara yimin tsallen kwado anan kafin na hau kanki da duka.

Da sauri ta fara hade da riqe kunnuwanta,

Wayyo Allah hajiya, an taru anci amanar aure saboda an ganeni qaramar yarinya.

El'mustapha bai kula taba xama yayi yana shafawa jikinsa mai, jiddah kuwa jikinta yayi sanyi saboda tausayin uwani, duk ta wani koma kalar tausayi kamar xatayi kuka itama takeji ganin uwani nayi.

Hajiya... Hajiya.... Kixo karsu kashe maki ni, wayyo ni Allah maqiya sun sakani a gaba xasu ga bayana, saboda baa sona anga bani da kowa.

Murmushi el'mustapha yayi yana kallon uwani, kuka take idanunta a rumtse take maganar.

'Dan Allah el'mustapha ka kyaleta,

Kallon mamaki yakewa jiddah, lallai har yanxu jiddah bata san kanta ba, yarinyar da ke neman fidda ta a gidan take tausayi yaga alamar Sam bata damu da abinda uwani tayi ba, yana so yasani shin har yanxu jiddah bata san kanta bane ko me?

Bata san halin da take ciki bane game da uwani, xaiyi magananin ta ya gani ko ina hankalin ta ya tafi.

Ya dubi uwani,

Xo nan uwani,

Da sauri taxo gabansa tana fadin kayi haquri.

Karbi takarda hannun jiddah taki ce kuma ba saki bane aciki, takardar yarjejeniyar auren muce idan kikayi wasa da ita tamkar kinyi wasa da auren kine kin fahimceni.

Ta gyada kai gwani tausayi tana kallonsa, tashi ki bace min da gani,

Ta tashi sai da ta kai bakin qofar ta juyo, Allah ya isa kuma human rights xanje yanxu abimin haqqina... ta fita da gudu, murmushi kawai el'mustapha yayi shi yanxu uwanin Ma ta fara birgesa, abubuwanta akwai nishadi aciki.

'Dan Allah el'mustapha ka daina yiwa uwani I........ Enough ya katse ta, ta hanyar daga mata hannu

Uwani matata ce right, ta gyada kai tana kallonsa,

Ki samin ido akanta, ba ruwanki, ya juya ya fice.

Ta bisa da idanu har ya fice, menene laifinta saboda ta bashi haquri, sai ta tabe bakinta tayi kwanciyarta.

Yana fitowa dakin ta yaci karo da uwani ta fito tana kuka, sanye da hijab din ta, yarinyar nan da gaske take yi kenan.

Da sauri ya nufe ta, hannunta ya riqa ya nufi dakinsa da ita, tun da ya riqa hannun uwani take kallon sa cikin wani shauqi na soyayyarsa, bai taba riqa hannunta ba ballantana tasa ranar da xata shigo dakin sa, koda wasa jiddah bata taba aikota dakin el'mustapha ba, yau gashi da kansa ya kawo ta, xuciyarta fal da farin ciki harta manta damuwar da take ciki,

Juyowa yayi yana kallonta yaga shi take kallo, ya daure fuska nan da nan tasha jinin jikinta,

Kika ce Allah ya saka maki ko?

Ni bada kai nake ba,

Dawa kike yi ai ba jiddah ta saka ki ba,

Ni wlhy da qafafuna nakeyi, sune suke min ciwo,

Yace sune xaki kai human rights kenan? ta gyada kai da sauri tana kallonsa.

Yanxu xamu fara shiri dake saboda wani dalili nawa, amma kada hakan yasa ki rainani ki kuma raina matata ta.

Shiru tayi tana kallonsa, a xuciyarta tace ni daman nasan sai ka soni dan Ma ban fara yi maka kwalliya ba ina matsewa tunda anti jiddah batayi.

Jiddah tace kin daina karatu bautar aure kike yi, gayamin abinda kika sani acikin bautar aure?ta washe baki tana kallonsa,

Bautar aure duk baxai wuce na kula da kaina, na kula da abincin da nake so naci nasha, na nemawa kaina tsari ga mahassadan aure na, na kuma yi maka girki.

'Ashe ma komai baki sani ba akan aure uwani, yayi maganar cikin dariya, itama dariya take cikin nishadi gani take kamar tana aljannah ne tare da el'mustapha,

'Na raba maku girki daga yau keda jiddah kowacce kwana biyu biyu ne, girkin jiddah xai fara daga yau saboda itace babba, bayan kwana biyu naki ne, tunda sassafe xaki tashi kimin breakfast kin dai san yanda jiddah keyi ko?ta gyada kanta, yace yauwa kuma xaki riqa xuwa kina gyaramin sashe na duka babu mai aiki acikin wannan, idan naga kina bin jiddah sau da qafa xan bude maki dayan sashena ki koma da xama, in kuma naga sabanin haka xaki cigaba da xama a wannan dakin.

Yanxu kaji kana sona ne?ta tambaya tana kallonsa da murmushi a fuskarta,

Aa jiddah kadai nake so ai kinsani, bana so nashiga haqqinki ya saka na baki damar yin duk abinda kike so a gidannan tunda akwai auren ki akaina, ki kiyaye.

Ta bata fuska, dama ina so kabani kudi na fara Sana'a kuma nima ina so abani mota.

Ya dube ta da mamaki, yanda ta daure take maganar sai kace uwarsa.

Ki bari xanyi tunani nagani keda jiddah, kowacce ku xan bata jari.

Har da anty jiddah xaka ba, amma ai ni na tambaya.

Duk abinda xan bawa jiddah sai na baki, haka itama duk abinda xan baki sai na bata shine adalci.

Amma ai ita tana da kudin ta kuma tana da mota,

Yace uwani idan na baki mota sai na canxawa jiddah sabuwa amma fa ba iri daya ba, jiddah dabance a xuciyata, kiso jiddah idan kina so mu xauna dake lafia a gidannan kafin wa'adin auren mu ya cika.

To nagode ta fada tana qara kallon dakin, yanxu bayan kwana biyu inxo in kwanta anan dakin?

Baiyi magana ba, ya maida kallonsa ga wayar da yake dannawa,

Uwani ta juya ta fice farin ciki fal a xuciyarta ji take tafi jiddah yanxu Ma a gidan,

'Washe garin ranar iskanci Kala Kala take mawa jiddah harda su habaici ai itama xata karbi miji ta fara kwana a dakin sa, xata fara masa girki, yace yanxu yana sonta, harda yan waqe waqen ta.

Tun kafin ranar taxo har an fitar dasu Maggi, da sauran kayan da xaa yi amfani dasu an ajiye, arish Ma an diba an ajiye a gefe, kwai ma haka, har plate da cup duk an tana da an kai daki an ajiye.

Jiddah na kallonta bata tanka mata ba duk wannan habaicin da ake mata.

Ana gobe xata karbi girki ta sami jiddah a falonta, harda russunawa cikin ladabi.

'Anty jiddah naxo abani kudi na fara Sana'a in sami kudin kaina ina debewa kaina takaici indai na gani ga kishiyoyi, mutane suna min kallon na auri mai kudi ina cikin qaton gida ina auren babban dan sanda sai a dauka nima kudin nake da.

Ni kam banda kudin da xan baki kiyi Sana'a uwani tunda bani ke auren ki ba,

Tau shikenan, daman nasan baxaa bani ba na bata lokacina da yawuna wurin fallasawa kishiya sirrina, to wallahi xan bawa mutum mamaki, yau xan fara Sana'a kuma ko wacce iri naga dama ita xanyi wacce xata kawomin kasuwa na sami kudi, kuma kar naga mutum yaxo siya, ta fice a fusacce.

Jiddah kallonta kawai take da mamaki har lokacin da ta fito ta nufi harabar gidan,

dan aikensu ta kira, kudi ta bashi je ka siyomin buhun masara wadda ake gasawa nima Sana'a xan fara kayi sauri ina jiranka.

Ta dawo tana cigaba da fada, nace abani jari anqi abani, shi yana min maganar jiddah, ke naxo kina min maganarshi tuni nagane manufar ku baa son bani ne anfiso aganni talauci na qullin kubura dani, to wallahi gasasshiyar masara xan fara saidawa a qofar gidan nan ba ruwana.

Xumbur jiddah ta miqe tana kallonta,

Masara kuma uwani, keda kanki?

'au ashe ma kinji kenan, kudina ne ehe, ni na nemawa kaina jari na tallafi kaina da ya'yana masu xuwa nan da lokaci qanqani dan xan fara kwana da miji gobe, kada suxo yayan kishiya suna masu gorin maman su bata da kudi.

Kin tambayi el'mustapha ya baki jari ne bai bada ba, kina so ki xubar da mutuncin gidan nan uwani ki bata mana suna, dan Allah kada ki fara wannan Sana'a, shiyasa akace ai ki tsaya kiyi karatu.

Karatun ne dai baxanyi ba, wasa wasa jiddah ta kasa hanata barin sana'ar amma tasan idan el'mustapha yaxo baxaiji dadi ba.

Tana ji tana gani uwani ta yasa banan suka fita tare da aka kawo masarar .

'Ashe uwani da gaske take cewar banan lokacin da taga uwani ta fara gyaran masara, har garwashin ta ya kama.

Yan sandan dake qofar gidan suna gadi cike suke da al'ajab, amma sanin halin uwani da kasancewarta matar mai gidan ya saka suka ja bakinsu sukayi shiru, sai Ma suka fara siye suna ci, mutanen unguwa sun fara garxayowa wasu kuma tsegumi ke kawo su suganewa idanunsu.

Banan kam harda hawayen ta.

Bayan wani lokaci sai ga motocin el'mustapha sun shigo layin, baiyi mamakin mutanen da yagani qofar gidansa ba dan a tunaninsa yara sukayi fada yan sandar ke sasantasu kamar ko yaushe,

An bude masu gate, gab da xasu shiga gidan idanunsa na sauka akan uwani dake firfitar gawayi.

Ya kasa gasgasta abinda idanuwansa na hangowa masa, tun kafin motar ta gama Parking  ya fito da sauri batare da ya jira an bude masa motar ba,

Wajen gidan ya nufa, yana leqawa kuwa sukayi ido biyu da uwani.

My wattpad Pherty-xarah

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

28

Ko kadan uwani bata ji tsoron ganin sa ba ko alamar firgita a tare da ita,

'Na nawa xaa baka? Shine abinda ya fito bakin uwani lokacin da take kallonsa.

Murmushi el'mustapha yayi a ganinsa girmansa ya fadi ya tsaya cece kuce da uwani a waje,

Ya ciro dubu daya yana fadin, bani ta dubu daya ina jiranki yanxu.

Uwani ta washe baki, Banan bude masara ga costumer na kwarai wanda ba baqin ciki a tare dashi, kinji har ta dubu xai siya.... Uwani ta fada tana bude masarar🌽🌽🌽

El'mustapha juyawa yayi ga wacce yaji an kira da banan, yana jin sunan ta abakin jiddah amma basu taba haduwa ba, idanun su suke sarqe dana juna, yayi saurin dauke kansa da sauri yana kallon uwani, haushinta kamar ya shaqo wuyanta a gurin.

Banan kuwa tuni jikinta yayi sanyi, yau tayi ido da ido da el'mustapha, ashe haka yake, dole uwani xata kamu da ciwon xuciya dalilinsa, ba kowacce mace xatayi masa kallo daya ba batare da taji wani abu a xuciyarsa ba.

Uwani dauko wadannan haka sai ki cikamin sauran daga baya ina sauri,

Banan cigaba da gasawa bari na kai masa acikin gida,

Tana gaba dauke da masara yana bayanta, suna shiga harabar gidan ya kira wani dan sanda gefe,

Ka watse min wannan taron, duk abinda ke gaban gidan ka jefar dashi cikin bola duk ka watsar da komai bana son ganin ko tsinke a wajen ko naga an dawo dashi gidannan.

Suna shiga falon suka tarar da jiddah xaune tana yiwa twins lesson,

Kafin uwani tayi wani yunquri el'mustapha ya dauke ta da wani wawan Mari a kuncinta,

Shiru ya biyo baya falon har wace aka Mara saboda rudewa, twins kuma tuni sunyi bayan jiddah saboda tsoro abinda basu taba gani a gurin baban su ba,

Tsawon second talatin uwani ta dauka kafin ta dawo hayyacinta, sai a lokacin ta fashe da kuka ta dafe kuncinta tana qoqarin barin falon a rude bata ma sani ba,

Fincikota yayi ya dawo da ita tsakiyar falon ya jefar, qoqarin xare belt din sa yake, tana ganin haka ta rarrafo da sauri ta riqe qafafunsa, duk da haka el'mustapha bai fasa yi mata biyar masu kyau a bayanta ba,

Jiddah ta dauki twins ta fita dasu daga falon itama a tsorace take da el'mustapha, ita kam tunda take tare dashi bai taba sa hannu a jikinta da sunan duka ba abinda tangujewa uwani kenan tun farko.

Sanda ta dawo ne taji uwani na fadin,

'Dan Allah kayi haquri baxan koma ba, anty jiddah ce tace nayi wlhy itace tasa nayi,

Cak jiddah ta tsaya hade da dora hannunta a qirjinta, ta xare idanu tana kallon el'mustapha cikin girgixa kanta,

Ni? Wlhy qarya take min sai dana hanata taqi, uwani na kuka tayi caraf tace

Wlhy kece Ma kika bani kudin, ashe sharri ne kika min k..... El'mustapha ya bige mata baki, jiddah na ganin haka ta xura da gudu dakinta, rufewa tayi hade da sanya key cikin tsoron el'mustapha.

what a disgrace uwani, kamar ki, ki dora sana'ar masara a qofar gidana inama laifin a qofar gidanku ne tunda dama can kinyi kama da masu gashin masara.

'Dan Allah kayi haquri sharrin shaidan ne da aljannu, sune suka sani, ka tambayi anti jiddah tasan ina da aljannu kuma suna sani yin abu ban ma sani ba.

Ai gobe idan suka saki nasan da gudu xakiyi tunda baki san kina yi ba,

Wallahi ko sun sakani baxan yi ba, dan Allah kayi haquri.

Juyawa kawai yayi ya barta gurin, anan tsakiyar falon ta kwanta tana kuka bataso ta daga murya sosai yanda yan aikin xasu jita su rainata shiyasa takeyi kadan kadan.

Har akayi magrib uwani na gurin kwance, jiddah kuwa tunda ta shiga bata fito ba, el'mustapha na fitowa cikin shirin xuwa masallaci ya ganta a gurin.

'xaman me kikeyi anan tun daxu?

Ta tashi tana share hawayen fuskarta,

'gobe tafiya xanyi, xanje Lagos, idan na dawo na tarar da kin kafa rumfa a qofar gidannan kina siyarda abinci ki xama maman iyabo kinji.

Ko qala batace ba ta ficewarta,

Tana gama sallah taji sallamar jamila qawarta, ai kuwa da murna ta tare ta, dauko wannan dauko wancan, ta hada mata kayan maqulashe abinda bata yiwa hajiya ba kenan.

Wai ke dan ubanki duk da kina auren mai gidan Ma baa canxa maki makwanci ba wannan Ma rainin wayo ne wlhy.

Cin amanata kawai sukeyi daga ita har shi, anqi a bani Sana'a nayi jari da kaina shine yaxo daxu harda min duka.

Duka uwani? Kuma kika kyale, amma kekam anyi sakarya daya dake ki yana fita ki daki matar shi mana,  har yaushe xan xauna mace da mijinta su rainani acikin gida, ke dan ubanki sai kace ba qawar jamcy bace ke danme baxaki kirani mu hadu muci u... a gidannan ba.

Ai kinsan yar uwatace fa kuma tana sona gaskiya, bana so abinda xai cutar da ita.

Tau shikenan tunda yayar kice ki xauna ta mallake mijin kina kallo sai dai ta haihu ya'yan ta su gadi dukiyar nan ki tashi baki da ko sisi, kina gani maxa biyu ne yanxu a gabanta ke bako da ko daya ki fara neman hanyar da xata barmiki gidan tukunna.

Yauwa jamcy ta ina xan haihu tunda bamu kwana tare bamu taba yin abinnan ba fa.

Ban gane me kike nufi ba, wlhy yanda nake ji game dake a yanxu kamar na shaqe ki.

Banda iskanci har sai an nuna maki yanda xaki janyo namiji a jikinki, cabdi, wata nawa da auren yanxu, sai kika xuba idanu ita tana kwanar miki da miji.

Ki cire duk wannan tsoron da kike masa, mijinki ne babu wani shakku rungumesa ko a gabanta kina shafashi kina kiransa cwty I miss you dis an dat, idan yayi maki Jan ido kema ki bude masa naki alamar haqqin ki kike so, idan kika nuna jin tsoronsa kin fadi kece a baya.

Kuma kinsan fa xan iya, dama nice da girki gobe.

'Yauwa uwani, gobe ki matse a gidannan, da dare kada kiji kunya kisaka nighty wacce xata firgitashi, idan yaqi ina da pills acikin jakata na shaawa yanxu xan baki ki saka masa wlhy da ya ganki xai rude dolensa ya nemi ki, ta ciro taba uwani, ta karba tana kallonta,

Amma gobe yace wai xaije Lagos fa, saboda cin amana sai ranar girkina xaiyi tafiya.

Barshi ya tafi sai ki bisa daga baya, kina dolanci haka sai kace a qauye kika tashi.

Ban taba xuwa Lagos ba fa,

Acikin yaransa baxaki rasa wanda bai sani ba har masaukinsa kuwa, ki biyasa ya kaiki ni xan baki kudi domin ki kwato yancin ki,

Aikuwa nagoda xan hada kayana wlhy baxanji tsoron sa ba kin sanni ai,

Wace Sana'a ce kika fara ya dake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login