Showing 132001 words to 135000 words out of 138779 words
Chapter 45 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
wannan a xuciyata *Nayi Nadama*, ki yafe min abinda na miki sharrin jamcy ne wlhy itace ta tsaramin komai.
'Na dade da yafe maki uwani sai dai ki kula kuma ki kiyaye,
Tace insha Allah anty jiddah sai na baki mamaki xan xauna gidan aure na da amana saboda nasan masu baqin ciki da auren yawa ne dasu.
Jiddah tace baxaki daina kiran baqin cikin ba kenan.
Murmushi uwani tayi tana kallon ta kawai.
EL'MUSTAPHA
Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers
Fertymerh Xarah💞
70
Yes, today is my birthday, Therefore I will be treated like a Queen..💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻🎂
*Just want to THANK ALL OF YOU for making me feel special on my Birthday, Love You Guys!*
Jiddah bata bar gidan ba sai kusan magrib, sunyi girki tare da uwani, ta qara koya mata wasu abubuwan sosai dama uwani ba girki aka iya ba.
Bayan ta gama sallah tayi wankan ta, ta shirya cikin kayan barci sai qamshi take xubawa tana jiran angon nata.
Yana shigowa da sallama ta amsa tana masa sannu da xuwa.
Abinda ya fito bakin ta ya bashi mamaki,
Tun safe ka fita ka barni sai yanxu kake dawowa, hala kana gurin matar ka kuna yin wannan abin ne? Idan mutum yaci amanata Allah baxai barshi ba.
Yace uwani baxaki bari ko xama nayi ba, kinsan gajiyar da naxo da ita kuwa?
Tace ai nayi maka sannu da xuwa kuma na amsa sallamar ka, banda anti jiddah tace na riqa welcoming dinka xaka ji dadi Allah baxan yi ba tunda kana can kana wannan abun da matar ka.
Wane abu?ya tambaya yana kallonta,
'Wannan abun da kayi min jiya, ya dube ta da kyau yana fadin,
Ni bani da abin yi ne sai hawan mace ko kuma babu abinda mata da miji xasuyi sai wannan abin kadai?
Ta fara kuka yaci amanarta yaje ya barta, haka yusuf ya soma rarrashinta akan baxai qara yin dare haka, dama ya barta ne saboda yan xuwa dubin amarya.
Ta share hawayen tana fadin xo kaci abinci sai muje ka min, ni naji ina son wannan abin kuma.
Baisan meyasa yarinyar bata boye feelings din ta ba, ko kunya da nauyin fada bata ji Allah ya sa uwani ba irin jarababbun matan nan bane.
Batare da ya kalle taba yace ba yau ba, sai gobe yau na gaji.
Tayi shiru batayi magana ba, xuciyarta kamar xata fashe saboda bacin rai, yana kallo ta tashi taje ta dauko paracetamol, ya dauka ko ita ce xata sha sai yaga tana xuba masa a juice din da xai sha,
Miye haka uwani, meyasa kika saka min aciki.
Ai kace baka son wannan abun ni kuma ina so shiyasa na saka ma idan kasha kamin wannan abun.
Yace an gayamaki paracetamol d.. ta katse sa tana fadin ai shima kwayoyin magani ne kuma su ake sakawa mutum.
Yace gayamin a ina kika san ana sakawa namiji kwayoyin sha'awa uwani.
Ta tsura masa ido, ganin yanda ya kafe ta da idanuwa ya saka duk taji hankalinta ya tashi,
Tace ai nima ban sani ba,
Yace qarya kike, gayamin ina kika san wannan, kuma wa kika taba sakawa.
Ita kam tana jin kunya ta fada masa itace ta jawo el'mustapha gare ta, ai wannan abin kunya ne a gareta, (su uwani ansan kunya) ta tunxuro baki tana fadin ai a film nagani an saka wa wani tun a gida Ma na kalla, kuma da yasha yayi mata, akwai dadi kuma akwai ciwo.
Taya kika san akwai dadi da ciwo, kai tsaye tace ai kayi min jiya naji.
Mtsew yaja tsaki, ya cigaba da cin abinsa batare da ya kula ta ba, yana gamawa kuwa wanka yaje yayi, uwani har ta isa dakin nasa ta haye gado tana jiransa.
Shi kansa yana da buqata da uwani sosai sai ya bada kai bori ya hau😂
*
'Washe gari yana shirin fita sai ga uwani ta shigo da alama daga kitchen take, (uwani an san ayiwa miji breakfast)
Tace kafin kayi breakfast xaka qara yi min wannan abin ne naji kuma ina so,
What? ya fada yana kallonta cikin fito da idonsa alamar mamaki, yana tuna jiya bata barshi barci ba da ta motsa sai tace ya mata, shi yanxu tsoro ma take bashi.
Ke bakya gajiya ne?
Ni ban gaji ba, muje,
Yace muje ina, You are not serious, gwanda ki rage son wannan abun cos tafiya xanyi na barki, nan da two wks umrah xamu je da surayya.
Ta xaro idanu waje, ni fa baxaka je dani ba, me nayi maka a rayuwa yusuf kake min baqin ciki.
Ya fita yana fadin tun kafin na aure ki na biya mana, kema wani lokacin xaa je dake.
Wallahi baxan yarda ba, nima sai kaje dani, ta soma kuka sosai, haka ya gama breakfast dinsa ya fice bai qara kula ta ba, tana ganin ya fice ta dauki hijab ta saka da key din vespa din ta, ta fito.
Gidan su jiddah ta nufa,
El'mustapha na daure da towel a qugunsa da alama fitowar sa wanka kenan yaji alamar bude gate din gidan nasa,
Waye haka da sassafe da securities xasu budewa gida, ya qarasa bakin window yana daga labule,
Kamar mace ya gani akan vespa ta shigo gidan, wacece wannan, ya qara bude idanunsa sosai yana kallonta lokacin da take shigowa harabar gidan.
Uwani ya fada da qarfi cikin mamaki, jiddah dake fito masa da kayansa ta juya tana kallonsa jin ya ambaci uwani, da sauri ta nufi inda yake tsaye tana kallon window, dai dai lokacin uwani tayi parking din vespa din ta sauko, ta cire hijab din ta daure a qugunta, sannan ta fashe da kuka tayo cikin gida tana kiran anty jiddah.
Jiddah da el'mustapha tare suka dubi juna cikin mamaki, ko me ya fito da uwani yanxu, a tarihin sa bai taba ganin mace Bafillatana mai asali da tushe irin uwani akan vespa ba sai dai qabila,
Ihun da take tana kiran anty jiddah ya saka el'mustapha fadin je ki same ta jiddah kinsan xata iya shigowa,
Jiddah ta fita, uwani na ganinta ta qara sautin kukan ta,
'Anty jiddah yusuf baya sona yana min baqin ciki xasu je umrah da matar sa su barni😭
Jiddah ta bata fuska tana kallon ta, saboda wannan kike wannan haukan, bashi iko yaje da matar sa duk inda yaga dama ne, idan bashi da halin biya maku ku biyu ba sai ki haqura ya fara xuwa da surayya ba ai itace babba ke kuma daga baya sai aje da ke.
Uwani ta share hawaye tana fadin kema kina bin bayan sa kenan, mijina xaije da wata umrah kice na haqura na xauna gida suje can suna soyayya suna wannan abin ni ina nan ina gadin gida, sun shiga jirgi ni ina nan akan vespa, suna bauta ni ina nan ina barci lallai anti jiddah har yanxu kina min baqin ciki a rayuwa.
Fitowar el'mustapha cikin uniform ya hana jiddah magana, uwani na ganin sa ta kafe sa da idanu kamar mayya, harara ya jefe ta dashi cikin daure fuska, ta hade yawu da kyar Allah ya gani har yanxu tana son el'mustapha a rayuwarta, ta qarasa a hankali inda yake,
Cikin hawaye ta soma fadin yaya kaga xasu je umrah su barni shi da matarsa saboda baya sona yana min baqin ciki da na sami rahamar ubangiji.
Yace to miye aciki dan yaje da matar sa ta farko ya barki, ke ba daga baya kika shiga gidan ba.
Tace amma inda so da qauna ko yanxu na shiga xaije dani, ai kaima nasan xaka je da anti jiddah shikenan ni sai a barni, ta fashe da kuka.
Kowa baya sona, ina son kowa bana ma kowa baqin ciki amma ni ake min, kuka take sosai wanda ke nuni har cikin xuciyarta take yin sa babu alamar wasa.
El'mustapha yaja numfashi yana fadin shikenan share hawayen ki daina kuka, ni xan biya maki kudin sai muje tare, baqin ciki ya qare.
Fuska cike da hawaye take masa godia tana murmushi, shiyasa ta kasa cire sa a xuciyarta, lallai shine babban masoyin ta na haqiqa wanda baya mata baqin ciki,
Yace amma uwani meyasa kike hawan vespa kuma ki tuqa da kanki, kina matar aure.
Murmushi tayi tana fadin ai ni na says vespa din da kudina saboda na debewa kaina takaici duk inda xanje da abuna, yanxu da babu shi dame kake tunanin xanxo akan qafa ko me, ai ni bana daukar wulaqanci a yanxu.
Yace kuma gashi ni naga vespa din ina so uwani xaki bani?
Tace aa, kasan yanda nayi hustling na sami kudin ne, ai ko mijina ya roqe ni na saida masa naqi ina son kayana, ta bata fuska.
Yace shikenan uwani ashe akwai ranar da xan nemi abu a hannunki ki hanamin, (yana so ya rabata da vespa din)
Tayi shiru tana kallonsa ga mamakin sa shida jiddah sai yaga ta miqa masa key din vespa din tana fadin,
Gashi amma kada ka 'dana kowa akan sa, kuma kada ka arawa kowa, idan na haihu ya'yana sunxo duniya xan xo na karbar masu dukiyar maman su ce,
Ya karba yana fadin idan anyi kyauta baa dawowa a karba uwani, kyauta kika min kuma nagode, ya juya yana kallon jiddah dauko mata key din motar ta ki bata, dama tun farko na bata,
Uwani tayi murmushi tana fadin, jamcy ta cuce ni, ashe haka kake amma yaushe ka fara sona haka, kodai kana tausayi nane saboda ina jikar merah kana so kakana yayi maka kyauta.
El'mustapha bai yi magana ba, ya soma tafiya a hankali, uwani tabi bayansa,
Yaya dan Allah kayi min alfarma ka fitar da qawata ladidi daga prison, ita mai sona ce, kuma fa bata da laifi.
Wacece ladidi me tayi aka kaita prison,
Tace ladidi qawa tace ai acan muka hadu, itace wacce akawa qaxafin kissa akan ta kashe wadda ta riqe ta bayan mijin ne ya kashe matar sa da hannunsa.
Yace au na tuna, yanxu ake shari'a din ta, insha Allah xata kubuta dan ankama mijin ma, duk sanda xaa yi sharia xanxo naje dake ki ganta.
Taji dadi sosai, bayan jiddah ta baa key din motar ta fito sai kallon vespa din ta take tama fi sonsa akan motar, lallai da ba el'mustapha bane ba wanda ya isa ya raba ta dashi.
Bayan tafiyar uwani el'mustapha ya saka driver dinsa ya dauki vespa din ya kaiwa abba akan kada a sake bata shi ta hau.
Uwani saboda murna xata je umrah ta soma yawo ma'aikata ma'aikata tana neman inda yusuf ke aiki ta gayamasa, taji baxata iya haqura har ya dawo ba, sannan bafa aikinsa ta sani ba ballantana tasan inda xataje ta gansa, har wurin masu wanki da guga take xuwa neman sa😂
Ta kasa samun sa ta gaji sai ta nufi asibiti, tana so a duba ta ko tana da ciki idan baxata manta ba yau kwananta biyu da aure kuma yayi mata ya kai sau biyar dole kuwa tana da ciki.
Abinda likitan ya fara tambayar ta tana da aure?
Tace eh yau kwanan ta biyu da aure, ya dube ta sosai kwana biyu da aure kike maganar kina da ciki.
Ta gyara xamanta tana fadin saboda sau biyar yayi min, kuma na fara jin motsi a cikina ina so a dubamin mace ne ko namiji yaushe xan haihu.
Likitan ya xuba mata idanu nan take ya tuna ta, ta taba xuwa da irin wannan magana haka watannin baya ne ko anyi shekara ma.
Dabara ta fado masa, yace kije nan da wata hudu ki dawo a lokacin ake duba ciki agani mace ko namiji ne sannan kada ki fadawa kowa ki boye abin har mijinki kada ki gayawa.
Wani jin dadi da farinciki suka xiyarce ta, tace ai likita baxan gayama kowa ba har hajiya ta kada amin baqin ciki aje a xubar da cikin ina barci, da anyi wata hudu ko uku inxo kenan, bayan wata tara sai na haihu, likita gayamin nawa kudin kane.
Cikin murmushi aa kyauta na miki ai kin xama qanwata,
Au kaima dan gidan sarki merah ne?
Ya girgixa kansa,
Tace to ni ba qanwar ka bace, ni jikanyar sarki merah ce, anty jiddah yaya tace.
Baiyi magana ba shiru kawai yayi yana kallonta har ta fice,
Tana xuwa gida babu mgnr girki aka xauna ana list din wadanda xaa yiwa tsarabar umrah,
Xan bawa xoxo amma baxan baiwa Sally ba, Qaumi da mom sadeeq xasu samu amma sumayya da Serdia komai baxan basu ba, yan baqin ciki ne.
'Yauwa xan baiwa hajja, saina da Maman 4h amma baxan bawa ummy da aysher ba, kuma baxan bawa shafa ba, suma suna min baqin ciki,
'Abba xan siya masa praying mat da casbi kadai tunda su yafi baiwa muhimmanci a rayuwarsa, idan kudi na ya isa xan qara masa da qur'ani ko jallabiya.
Ita hajiya qila goron umrah xan siyo mata sai na hada mata da hijab tunda ita matar ustax ce.
Yusuf ma komai baxan siyo masa ba, ko sisi baxan kashe masa ba tunda yake min baqin ciki,
Shi wannan likitan da yace ina da ciki xan siyo masa biro tunda naga rubutu kullum ya keyi.
El'mustapha kuma xan siyo masa wani sabon vespa, da jallabiya goma, harda kayan yan sanda idan na gani xan siyo masa tare da xobe na gwal tunda baya min baqin ciki yana sona.
Ita anti jiddah komai baxan siya mata ba, amma xan siyawa twins kayan wasa,
In siyawa kakana merah alkyabba ta umrah amma wannan afiya da baturen ko sisi baxan kashe masu ba😏
Ya'ya na xan siyo masu kaya masu kyau da tsada, harda kayan wasa ma,
Ni kuma xan siyowa kaina sabon vespa, qatuwar sarqa ta zinari, takalmi masu kyau, dogayen riguna, nasa haqorin zinari idan nayi dariya kowa ya gani, amma pherty komai baxan siya mata ba taje jiddah ta siya mata.
Haka ta gama rubuce rubucen ta, ta ajiye har yusuf ya dawo.
Labari ta soma bashi akan komai da ya faru.
Shidai shiru kawai yayi yana kallonta, Allah ya shirya uwani.
A gurguje pls😏
7 months😃
Ina ce maku a wannan lokacin uwani nada ciki You ppl will not be surprised saboda kowa yasan jarababbiya ce bata da haquri🤣
Yanda uwani ke kula da cikin tana riritashi xakuyi mamaki, uwani bata yarda tayi wanka ta wanke cikin ba kada jaririn ya kamu da sanyi, ta fiso ta jiqa towel ta goge cikin dashi.
Bata cin abinci mai xafi kada jaririn ta ya qone,
Game da kayan dadi ba abinda bata ci koda ita bata so xataci wai saboda yaron yaji dadi, idan cikin ya fara motsi ta xuba ido tana murna tana daukar cikin vedio, da yusuf yaxo a nuna masa.
Bata yarda yusuf ya dora hannunsa akan cikin ta kada nauyin hannunsa ya jiwa yaron ciwo, kiss kawai take bari ya masa shima da kyar idan ya nace wai bata so ya lalata mata yaro.
Ta daina kwanciya da yusuf kada yaxo yana magagin barci ya shure mata ciki😨, uwani masu ciki.
Duk wannan abin da uwani keyi akan cikinta tana yine iyakar gskyr ta, kuma gwargwado uwani ta nutsu daga yanda kuka santa yanxu komai tana yinsa cikin nutsuwa ta daina maida magana tun bayan dawowar ta umrah.
Da kace hajiya uwani xata washe bakin nan dan kawai kaga haqorin da ta saka, ko baka mata mgn ba kuka hadu a hanya xata yi ma dan kawai kaga abinda ke cikin bakinta.
Tare suke xuwa kullum da yusuf asibiti a duk sanda xata je ganin likita, wani xuwa ne da suka yi uwani ta hadu da hajiya Mariya da kyar ta gane ta saboda yanda matar ta rame tayi baqi ta lalace.
Da tsinin cikin uwani ta bi bayanta tana fadin kamar Mariya nake ganin wannan tambadadiyar,
Hajiya Mariya ta dubi uwani, bata manta da fuskar uwani ba,
Tace Allah sarki uwani kinyi aure kenan ashe xan qara ganin ki.
Uwani tace me ya same ki haka kika lalace.
Tace wlhy rashin lafia nake fama da ita kullum ina hanyar asibiti kan wannan abun da nake na kamu da lalura.
Uwani ta tabe baki ta fice ta barta bako Allah ya bata lfy, Mariya ta bita da kallo cikin mamaki.
A kasuwa sunje siyayyar kaya ita da yusuf suka hadu da mahaifiyar jamcy inda take gayamata ai sai daga baya ta sami labarin jamcy taje America, har an kama ta ita da saurayin anyi hanging din su, uwani tayi wa matar alheri suka tafi,
Sai take qara jin wata nadama da nutsuwa a tare da ita, lallai ba qaramin cutar da jiddah tayi ba, haka ta shirya taje tana qara roqon jiddah akan ta yafe mata.
Uwani bata cin wani abinci mai nauyi, daga kifi, sai indomie da kwai, sai bread, sai apple, wai kada taci wani abinci yaron ta ya fito da qaton ciki ko kuma ya kasa tafiya,
'Ko turare xata sakawa jikinta sai ta shafawa cikin, yaron ta ya fito mai qamshi.
Bata aikin komai har mai aiki ta saka aka nemo mata ummi fingers, ita ke kula da gidan da komai.
Sun shirya da surayya suna xama na mutunci a yanxu a duk sanda suka hadu, babu wannan kishin sai dai wanda baa rasa ba.
Kullum xancen uwani baya wuce da ta haihu bayan biki xata fara koyawa yaron tafiya yaje makaranta da wuri ya gama saboda yan baqin ciki, har