Showing 99001 words to 102000 words out of 138779 words
Chapter 34 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
barci a xuciyarta.
*
Kuka take tana qarawa, lallai sai an maidata dakin ta.
Saboda baa sona ba wanda ke maganar yayi min aure a maidani dakin mijina abin sona, banan ma da take mai aiki anyi mata aure, ta auri miji mai kyau da kudi sai dan ni da ake ma baqin ciki anqi a maidani dakin mijina.
Sam hajiya bata kula ta ba, ta cigaba da hada kayanta saboda gobe xasu bar garin
Uwani ta tashi ta fito daga dakin taci sa'a kuwa el'mustapha ya fito xai je aiki,
Ta sunkuya tana fadin yaya an tashi lfy, yaya kayi haquri ka yafe min kuskuren da nayi a baya dan Allah ba danni ba ka yafe min, ka roqa min anti jiddah ta yafe min mu dawo tamkar da, dan Allah yaya ka taimakeni nima qanwar kace kuskuren da nayi a baya jarabawa ce da qaddara da bata wuce bawa.
Shikenan ki tashi komai ya wuce... yana maganar ne fuskarsa a daure,
Yaya a bani key din daki na xanje na gyara, yaushe xan fara karban girki.
Kafin yayi magana sai ga jiddah ta fito duk da bata ji me uwanin ke fada ba amma tayi mamakin samun uwani da el'mustapha a falon ta, gabanta ya tsananta bugawa.
Idan hauka ke damun ki uwani, na fiki hauka a yanxu indai akan el'mustapha ne, wallahi in baki barshi ba xan iya halaka ki ban damu ba.
Uwani ta tashi tana fadin haquri naxo na baki anty jiddah ki yafemin kuskuren da nayi a baya wallahi sharrin qawa ne, ni yanxu xuciyata a wanke take da alkhairi baxan cutar dake ba, ki qara roqon yaya ya aure ni ko baya da kudin sadaki ni xan iya ara masa, idan key din dakina yana hannunki ki bani naje na gyara.
Jiddah tace tau shikenan bari na baki, ta juya da sauri kamar mai neman wani abu
Ta rasa me xata dauka, kujerar dinning ta dauka tayi kan uwani a fusacce,
Uwani na ganin haka tayi bayan el'mustapha da gudu tana fadin,
Aa yaushe anti jiddah ta fara hauka kuma shine abba bai kaita itama a duba ta ayi mata aiki ba,
El'mustapha ya tare jiddah da sauri,
Me kike yi haka jiddah, kashe ta xakiyi?
Ko sauraren sa batayi ba tayi bayansa suka soma xagayen sa yana tsaye a tsakiyarsu, ya kalli wannan ya kalli waccan,
Lallai basu da hankali, wani abu ya taba kan jiddah indai ba gurin aikin bane aka taba kwakwalwarta,
Ya tsaida uwani cikin bacin rai yana kallon jiddah,
Yace xo gata ki dake ta jiddah, ga mamakinsa kuwa tayi kan uwani da gaske xata iya rotsa mata kujerar a kai,
Cikin fusata el'mustapha yasa hannu ya tare dukan da ta kaiwa uwani sai a hannunsa, yana juyowa ya dauke fuskarta da Mari karo na farko a xamantakewar auren su.
Falon ya dauki shiru na wani lokaci kafin jiddah ta saki abinda ke hannunta tana kallon el'mustapha.
Ita kanta uwani ta tsorata bata taba tunanin akwai ranar da el'mustapha xai iya dukan jiddah ba,
Ya yarfe hannunsa cikin jin ciwon dukan da jiddah ta kai masa, har lokacin fuskarsa ba walwala,
Yace na rasa gane meke damunki jiddah, yarinyar nan abba da kansa jiya yake gayamin hankali bai ishe ta ba, har aiki akayi mata amma babu wani cigaba, mutane nawa ne masu matsala irin ta uwani a duniya kuma aka xauna da su, saboda me xaki biye mata, shekaranjiya kin rotsa mata kai yau ma so kike ki rotsa mata kai ta qara samun wata matsalar akan wannan da take da, dan me baxaki kyaleta da haukanta ba is she not your sister?
Kallon uwani jiddah tayi kafin ta maida kallon ta ga el'mustapha,
Saboda uwani yau kake Mari na, saboda ina nemawa kaina yanci a yanxu shine nayi kuskure har ake kirana banda hankali, menene uwani batayi min ba nayi haquri, wace wahala ce ban sha akan uwani ba duk nayi haquri tun kafin na aure ka, wace yarda ce banyi wa uwani ba ta cuceni, na aura mata mijina tana son fiddani a gidana ta rabani da ya'ya na, tana son rabani da duniyar gabaki daya, wanda bashi da hankali yasan ya cutar da dan uwansa, bata da hankali tasan ta biya saboda a sace ni, a gabanta aka nakasa qafafuna, a gabanta aka dauke ni aka tafi dani duk cikin bata da hankali ne, ita uwani wace irin mutum ce, wace xuciya ce da ita marar tausayi da imani, taya xata xauna da mijina ni ta barni xaune a daji qarti suna gadina batare da tayi laakari da cikin dake jikina ba, a gabana uwani tasa a harbe min yarona, kishi ne ko hauka?
Wata na nawa kwance bana tafiya duk ta dalilin ta, bata xo neman gafara na tana nadama ba sai dan na qara aura mata mijina tun da na xama sakarai, amma yau jiddah ake ganin laifinta akan uwani, uwani ce mai gaskiya saboda bata da hankali, uwani ce yau ake tausayi saboda bata da hankali, duk haqurin da nayi yau baa ganin sa saboda uwani bata da hankali, duk jajircewata da tausayina akan ta a lokacin da kowa ya juya mata baya, yau kuma kowa uwani saboda ni bani da kowa da xai yi siding dina, iyayena basu da rai da xa suce suma yar'su tayi gaskiya, gaka ga uwani el'mustapha, ta juya da sauri tana goge hawaye da tafin hannunta.
El'mustapha yabi bayan ta a sanyaye, sai jin muryar uwani yayi tana fadin,
Ai da ka kyaleta tayi fushi ta tafi, ba gani ba, tunda kana dani ba damuwa, amma dai kaje ka rarrashe ta kaine baka kyauta ba da ka dake ta.
Ko kallonta bai yi ba yayi shigewar sa,
Uwani ta xauna tana fadin ta bani tausayi tana da gaskiyar ta wlhy, kuma ita taqi yarda na shiryu ba cutar da ita xanyi ba, gashi yau har tana tunanin ita marainiya ce amma ko jiddan bata ma abba da hajiya adalci ba su da suka raineta, bari ma nagayamasu butulcin da tayi masu, ta tashi ta nufi inda hajiya.
Hajiya kinji me jiddah ke fada,
'Naji komai uwani, xo ki hada kayanki ki bar gidannan, duk abinda jiddah ta fada gaskiya ne banga laifin ta ba, kece kika ja komai kuma jiddah tayi haquri dake.
Uwani ta tunxure baki, ni wlhy ba inda xanje, ba wanda ya isa ya rabani da gidan mijina, haka kawai ita anti jiddah ba tana da tausayi ba saboda me yanxu bata tausaya min ta aura min shi.
Uwani ki nutsu kisan me kike, ba kowace mace irin jiddah xata maki abinda ta maki a baya ba, ki tuna yarinyar nan fa dukiyar ta dake hannun mu ko sau daya bata taba mgn akai k...
Ke hajiya sai anyi magana kice dukiyarta, ai ba dukiyarta muke ci ba, abba yace ya ajiye mata komai nata yana juya mata dukiyarta idan an fitar da riba yana boye mata, ba ciki muke ci da sha ba, abbana yana da kudi kowa ya sani, idan dukiya kike so in kinyi haquri nima fa karatun nan xanyi nayi kudi kiyi alfahari dani ya'yana suyi alfahari dake kuma wlhy duk me min baqin ciki a rayuwa ko kwandala baxai ci ba.
Hajiya ta girgixa kanta, Allah ya shirye ki uwani, Allah ya shiryeki, Allah ya shiryeki.
Uwani ta muskuta tana fadin amin, addua ce kowa yana so, ni yanxu so nake ki saka baki a wannan maganar saboda da kinyi magana wallahi jiddah xata ji, na lura tana maki biyayya tana son ki kuma tana jin maganar ki, kice ta bari a maidani dakin mijina indai ba baqin ciki xaa min ba, kowace mace na gidan aure sai ni, wai ace harda mai aikin da nafi matsayi da gata tayi aure ta barni.
Nan ma hajiya batayi magana ba, so take taje ta rarrashi jiddah kuma kada ta qara jin ta kira kanta da marainiya.
Yana shiga ya sameta tana hada kayanta cikin jaka kuka take sosai airah na kuka,
Hankalinsa in yayi dubu ya tashi, me jiddah ke nufi xata tafi ta barshi ne ko me.
Sai ya nufi airah dake kuka sosai amma uwar taqi ta kulata, ya rasa yanda xaiyi da ita sai ya dauki sucker ya saka mata a baki ta fara tsotsa.
Ya juya yana kallon yanda jiddah ke ta xuba kayan ta a jaka tana kuka, ya qarasa gurin ta a hankali jikinsa na rawa gashi yayi latti sosai gurin aiki,
Am so sorry jiddah, idan Marin da na miki ne yayi maki xafi xo ki rama,
Ko kallonsa bata yi ba, ta rufe jakar, ta dauki hijab ta saka, hankalinsa ya qara tashi,
Ina xaki je jiddah? taqi sauraronsa, tana qoqarin ficewa ya riqota, cikin daga murya yace ina xaki je nake tambayarki,
'Wannan ba damuwar ka bane ta fada cikin muryar kuka,
Ya gane Marin da yayi mata sam bai kyauta ba kuma yasan ba yanda xaa yi ta fahimce sa duk da yana ji kamar ta ji masa ciwo a hannu sai yaje an duba,
Sai ya tsinci kansa da janyota xuwa jikinsa ya rungumeta sosai, duk da suna cikin bacin rai sai da suka ji wani irin yanayi,
Cikin sanyin murya yace, yaji xakiyi jiddah, dan Allah karki fara wannan, kada kiyi yaji pls jiddah, kiyi min duk hukuncin da kike ganin ya dace amma banda yaji,
Ya sake kwantar da murya yana rarrashin ta, yasan halin ta sarai baxata saurare sa ba in ma ta sauraresa xatayi ta qalubantar shine, shi baiga laifinsa anan ba laifinsa daya na daga hannu ya mare ta,
Sai ya fita daga dakin hajiya yaje ya kira ya gayamata yana ganin ta nufi dakin jiddah sai ya dauki wayarsa ya fice,
Jiddah fushin ma har da yar ki!kina ji tana kuka ki rasa kama ta, waya ce maki laifin wani yana shafar d'a ko kin manta wahalar da kika yi akan ta.
Shiru jiddah bata yi magana ba, hajiya ta dauki airah ta kawo mata,
Karbe ta ki bata tasha kada fushina ya sauka akan ki yanxu,
Ba musu jiddah ta karbe ta, hajiya ta xauna tana fadin duk wannan matsalar duk akan uwani ne jiddah, ki kwantar da hankali uwani baxata taba auren el'mustapha ba, idan mukayi haka ai mun so kanmu da yawa.
Kuma da kike hada kaya kibar gidan kije ina jiddah?akwai inda yafi maki gidan mijinki kuma da ya'yan ki.
Cikin kuka jiddah tace da ace ina da iyaye a yanxu babu gidan da xai fiye min gidan uba na, gidan miji ai ba gidana bane,
Me kike nufi jiddah, mu ba iyayen ki bane, su waye iyayen ki bayan mu, kada bacin ran uwani ya fitar dake daga hayyacinki, idan abban ku yaji kina wannan maganar a tunaninki xaiji dadi jiddah?
Ni kaina banji dadin wannan maganar ba jiddah,
Jiddah bata yi magana ba, ta cigaba da shayar da airah tana kuka sosai, hajiya tasa hannu tana share mata hawayen, kafin ta janyota xuwa kafadarta,
Kowa yasan jiddah mai kirkice da haquri amma bansan me ya canxa jiddah yanxu ba, ki cire mgnr uwani a ranki, qanwar ki ce laifin da tayi maki a baya ki yafe mata kiyi haquri ki daina tunawa, maganar komawarta dakin ta babu ta ba wanda ya isa ya maidata, ki kwantar da hankalinki, kiyi rayuwa mai kyau da mijinki, el'mustapha yana son ki jiddah kidaina masa duk wani abu da xai daga hankalinsa, kukan nan kibarshi haka babu mgnr fushi dashi kin ji ko?
Jiddah ta gyada kai a hankali,
Maxa tashi ki maida kayanki yanda suke, bari naje da airah, ko da kike maganar baki son mai raino dole xaa dauko maki ita, ai ba duka aka taru aka xama daya ba, ZUCIYA kowa da irin tasa.
*
El'mustapha kuwa ya rasa sukuni ranar ko aiki da yaje ya kasa aiwatar da komai, tunanin sa kada ya dawo ya sami jiddah ta bar gidan, ya tashi aiki ya nufi gidan anty ikram ya gayamata komai.
Ita may tayi masa fada sosai na ganin laifinsa akan hukuncin da ya yankewa jiddah gaban uwani, wannan yarinyar ma har kuke barin ta xauna a gidanku, banda darajar iyayen ta da tuni banyi maganin ta ba.
Tare suka xo gidan shi da anti ikram.
Dai dai wannan lokacin hajiya ta tursasawa jiddah yiwa el'mustapha girki, ta gama hada komai ta fito ta sami uwani xaune a falon ta taci uban kwalliya tana xaune jiran el'mustapha ya dawo shi aka yiwa kwalliyar.
Ko kallonta jiddah batayi ba ta shigewar ta, toilet ta nufa wanka tayi ta fito daure da towel dai dai lokacin da taji muryar anti ikram a falonta tana sallama.
El'mustapha na bayan ta suka shigo, lokaci daya suka kalli uwani, el'mustapha ya nufi dakin sa batare da yayi magana ba,
'Anty ikram tace, ke xaman me kike anan?
Uwani ta tashi tana inda inda dama tana tsoron anty ikram sosai bata taba sake mata fuska ba,
Anti ikram tace karna qara xuwa na same ki xaune a falon nan dai dai lokacin da mai gidan xai dawo, idan inda jiddah kika xo ki same ta a ciki kiyi abinda xakiyi ki fice bawai ki xauna mata ba,
Uwani ta gyada kai tana kallonta, ita kadai ce xata iya gayawa uwani magana ta kyale ta batare da ta maida martani ba, ita kanta uwani ta rasa meyasa take tsoron matar nan haka, shiyasa anti ikram ke daukar duk abinda uwani keyi iskanci ne ba wani hauka dake damun ta.
Fita daga falon nan kuma karna qara jin kin tsaya da el'mustapha idan bada amincewar jiddah ba, maganar a baki key kidawo dakin ki babu ta, jiddah bata so kuma el'mustapha ma baya so to xaman me xaki xo ki masu, idan aure kike so kije ki sami naki mijin a waje ko dole sai el'mustapha ne?
Uwani batayi magana ba ta juya tana kuka, ikram taja tsaki ta nufi dakin jiddah ta same ta xaune akan stool tana shafa mai.
Ta cikin madubi jiddah ke kallonta kafin ta gaida ta,
Ikram ta xauna dai dai lokacin el'mustapha ya shigo idanun sa akan jiddah.
Jiddah xo xauna nan magana xamuyi cewar ikram,
Ba musu jiddah ta tashi ta nufi inda take nuna mata ta xauna, idanunta na kallon kasa.
El'mustapha ya gayamin abinda ya faru tsakanin ku, duk irin mgnr da mukayi dake kin manta kenan, me na gayamaki idan el'mustapha ya bata maki.
Jiddah ta daqo tana kallonta idanunta taf da hawaye, ta kasa magana sai motsa bakin take,
Kiyi magana jiddah,
Da kyar cikin rawar murya tace, cewa ki.. kayi na kira ki na fada maki.
To meyasa baki kirani ba jiddah, amma shi gashi kinga ya kirani, ko dan ni ba yayar ki bace yayar el'mustapha ce kawai.
Jiddah ta girgixa kanta tana share hawaye,
Me yayi xafi haka har kike neman yaji, menene amfanin yaji ga mace, idan kika je kika barshi farin cikin yaran ki fa, sannan shi bakya tunanin halin da xaki saka shi, kenan el'mustapha idan ya maki magana ba kya bi, ba kya bin umarnin sa?
Jiddah ta girgixa kanta batare da tayi magana ba,
Ikram tace to meyasa idan ya maki magana bakya ji, yayi ta baki haquri kinqi.
A sanyaye tace ina bin maganar sa.... yimin shiru ikram ta katse ta cikin daure fuska,
Magana xan gayamaki kada ki koyawa mijinki qin jin rarrashi, ina nufin idan ya rarrashe ki to ki haqura,
Idan kika bari ya saba da idan ya rarrasheki kinka qi ji kika kangare wai ke Jan aji ko taurin kai daina rarrashinki xai yi yana tunanin ko yayi baxaki ji ba, kinga daga nan kin dauko hanyar da xai daina jin tausayin ki, ina gayamaki ne ba dan yana qanina bane kema qanwatace shiyasa na fada maki duk abinda yayi maki na bacin rai just take your phone and call me kigani idan ban xo na kwatar maki yancin ki ba.
Amma anty ikram meyasa xai nuna yafi tausayin uwani akaina, meyasa xai tsawa tamin akan ta har yana kirana marar hankali dalilin ta, kenan uwani ta fini a gurinsa.
Sosai anty ikram ta hau sa da fada da nuna masa rashin kyautawarsa, jiddah matar sace saboda me xai fifita uwani akanta, meyasa xaifi tausayawa uwani akan halin da ta saka jiddah a baya.
Ya sosa kansa, ya lura fushin na jiddah ba akan Marin da yayi mata bane tunda har batayi magana ba,
Yace sister ayi haquri
Kuma maganar duka kada ka qara El'mustapha sam banji dadi ba, ka hukuntata dai dai laifinta amma banda maganar duka, ko kadan bana son namiji mai dukan mace ko yane...
Yace kuskure ne na karbi laifina,
Jiddah bata ce komai ba, el'mustapha ya tashi ya fita,
Ikram ta soma bata baki tana rarrashin ta banda wauta irin ta jiddah saboda me xata damar da kanta akan uwani, ko mutuwa xatayi baxata auri Musty ba, ki kwantar da hankalin ki, mijinki shine farincikin ki, ki bi duk abinda yake so ki gujewa wanda baya so xakiji dadi, yanxu idan kina haka amira tayi kice mata me? Da yayi maki wani misbehaving da bakya so dauki waya kirani kigani, idan naxo idan ban mashi hukunci ba,.
Bata bar gidan ba har sai da ta saka jiddah dariya, ikram na barin dakin ya dawo kusa da ita ya xauna, tafin hannunta ya riqo ya hada da nashi yana murxawa a hankali.
Wani irin yanayi da take ji ne ya tilasta mata lumshe idanuwanta,