Showing 18001 words to 21000 words out of 138779 words

Chapter 7 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

1989

riqo qafafunsa tana kuka.

Fincike qafafunsa yayi daga gareta, haushinta yake ji sosai, abinta ya xama rainin wayo, taya xata xo masa da maganar ya auri uwani, wai uwani ya qara nanatawa a xuciyarsa yana mata wani irin duba mai cike da dimbin mamaki, tayi saurin sunkuyar da kanta baxata jure kallon kwayar idanun sa ba a yau.

Doguwar jallabiya ya xura ya fita daga dakin gabaki daya, sosai jiddah ta shiga damuwa.

A daren ranar yini tayi sukuku ba walwala a tare da ita, da kyar ta iya yin wanka, binni binni tana kallon agogo dare ya tsala sosai amma el'mustapha bai dawo ba, bai xo yaci abinsa ba ita Ma ta kasa cin abincin, ta kira wayarsa tana ringing bai dauka ba.

A falonsa ta xauna xaman jiransa, barci ya soma fisgarta, sanda ya dawo kallo daya yayi mata ya dauke dubansa daga gareta, motsin dawowar sa ya farkar da ita, tabi bayansa da sauri lokacin da yake qoqarin cire jallabiyarsa.

'Dan Allah ko menene ka ajiye shi a gefe kayi haquri kaxo kaci abinci, dan Allah mijina kada kamin wannan horon, lets save a soul, tana buqatar taimakon mu, ya kake so tayi da rayuwarta Allah ne ya dora mata.

let her die, sai me? Ina ruwan wani, idan ke damuwarta damuwarkice sai akace harda el'mustapha? Duk garinnan ba namiji ne sai ni, ya nuna ta da yatsa cikin matuqar bacin rai,

Look jiddah, I can't take it anymore, kada ki qara xomin da magana irin wannan.

Kwanciya yayi akan gado bayan ya rage hasken dakin, jiki a sanyaye ta hau gadon matsawa tayi sosai xuwa ga jikinsa, dogon tsaki yaja bayan ya janyeta daga jikinsa, juya mata baya yayi hade da Jan blanket ya rufe jikinsa har kansa.

Bata iya daukar wannan fushin ko kadan, xuciyarta ta karaya, ta soma hawaye sosai hade dasa hannu ta toshe bakinta kada sautin kukan ya fito,

Kadan kadan yake jin sautin kukanta, yana jinsa har cikin ransa, he can't take it anymore, ya juyo a fusacce hade da kunna bedside lamb,

Ban nemeki ba kece kika kawo kanki baxaki xo kidameni da sheshshekar kuka anan ba ki hanamin barci You can leave pls, ya fada lokacin da yake qoqarin hada ido da ita.

Haduwar idanuwansu ya sanya xukatansu bugawa lokaci daya, akwai soyayya mai tsanani tare da wadannan masoyan, bacin rai ke dawainiya dasu, yanda idanunta sukayi luhu luhu ya sanyashi weakness, bai qara magana ba ya juya ya kwanta abinsa, ganin haka ya sanya ta rungumosa ta baya, daga shi har ita suka sauke numfashi lokaci daya ba kamar ita kamar wacce tayi gudun fanfalaqi.

*

Kusan sati daya babu canji daga el'mustapha, tun da safe xai fice ya barta baxai dawo gidan ba sai tayi barci, sosai ta shiga damuwa, ga uwani tunda ta fuskanci akwai matsala ta kwanta ciwon qarya bata cin komai sai Lipton, daga ita har jiddah sukayi wata irin rama,

Ana haka mama taxo gidan, yanda taga jiddah sai da hankalinta ya tashi,

jiddah ko dai ciki ne dake kikayi wannan ramar?

Ta girgixa kanta cikin jin nauyin ta,

'ki gayamin damuwar ki, idan el'mustapha ne inji, kinga yanda kika lalace kuwa?

Shiru kawai jiddah tayi batare da tayi magana ba, sosai mama ta matsa da sai taji damuwar jiddah har lokacin da tagayamata komai tana kuka.

'Wannan mgnr babu dadin ji Sam jiddah, el'mustapha baxai auri uwani ba ni kaina bana son yarinyar.

Mama ki duba halin da take ciki, tana axabtuwa da qaunarsa, dalilinsa ta kamu da ciwon xuciya, kije kiga yanda uwani ta koma a yanxu, baxan iya samun nutsuwa a yanxu ba har sai uwani ta sami abinda take so, dan Allah ki saka baki ya amince da mgnr mama, ta soma kuka sosai,

Mama taji tausayin jiddah, ke kam rayuwarki dabance jiddah, kowace mace tana gudun kishiya ke kina roqo da kukan ki, kuma yar uwarki kike so a aura, ina ma laifin wata qawar kice daban amma Sam rayuwar uwani bata dace da 'dana ba.

Uwani ta canxa daga yanda kika Santa mama, xo kiga yanda ta dawo, sukaje dakin uwani na kwance tsakiyar dakin tana jin motsin shigowa dakin ta soma wani irin numfashi gwani ban tausayi.

Mama ta riqe haba cikin salallami da mamakin yanda uwani ta dawo,

Yanxu saboda el'mustapha ne yarinyar nan ta dawo haka, lallai abin a duba mata ne.

Suka koma falo suka bar uwani na murmushi, sosai mama ta tausayawa halin da ta tsinci uwani akai tana tunanin idan yar'ta ce a haka ya xataji.

Bayan kwana biyu sai ga el'mustapha ya shigo dakin jiddah tana xaune tana tana duba wayarta, yanda ta ganshi sai da ta tsorata.

'lallai ashe da gaske kike, kinfison farin cikin uwani akan farincikin ki da nawa, har xaki iya gayawa mama ta tursasani akan uwani batare da kinyi tunanin ni kin cutar da tawa rayuwar ba, kinyi nasarar aure na da uwani amma abinda xai biyo baya daga ranar da aka daura auren ki kuka da kanki....

Ya watsa mata wata harara yana mata wani duba kafin yaja dogon tsaki ya bar dakin.

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

23

Dogon Numfashi taja tana kallon bayansa har lokacin da ya fice,

Tana ganin Allah baxai kamata da laifin komai ba tunda alheri tayi niyar aikata, bata ga laifinta anan ba illah son xuciyarta da tagani, yes da gaskiyar el'mustapha da yace ta shiga haqqinsa ta tursasa xuciyarsa auren abinda baya so, insha Allah komai xai wuce kamar baa yi wannan rigimar ba, ta cigaba da duba wayar amma hankalinta baya jikinta.

*

Uwani ki shirya kije gida inda su hajiya ki roqi gafarar su, su sanyawa auren ki albarka domin kina buqatar hakan saboda babu mai goyon wannan auren naki.

'ni har sai naje na roqesu gafara sai kace mutuwa anti.

'baxakije ba kenan?

'A'ah ni bance haka ba,

'ki shirya yau kitafi, driver xai kaiki ya dawo shi kadai, kwana biyu xakiyi acan har dangi Ma kije, rayuwar aure da kike gani ba abin wasa bane.

Uwani bata qara mgn ba amma xuciyarta har wani tuqiqi take, haka taje ta hada kayan tana qunquni ko sallama batayi da jiddah ba ta fice,

'au inda ban fito ba ashe baxaki sanarda ni kin tafi ba, kina min wannan abin uwani kuma kike son mu xauna lafiya dake uwani? Tana jin haka tayi saurin russunawa,

Kiyi haquri anty jiddah, yanayin jikina ne kesani kuya akan komai amma xan kiyaye.

Ga wannan ki baiwa hajiya kuma ina gaida abba, uwani ta karbi saqon hade da jefawa cikin handbag din ta, murmushin yaqe tayi tana kallon jiddah.

'Anty jiddah na tafi kimin addua,

Allah ya kiyaye hanya ya kaiku lafiya,

Amin ta juya ta fice.

*

Sanda uwani ta iso gidan taga canji sosai wanda yayi matuqar bata mamaki daga iyayenta, ashe da gaske jiddah take mata basu farinciki da auren ta?

'Abba har da kai baka son auren ne? Ta tambaya tana kallonsa,

'tunda ke kina so kije kiyi, duniya ce uwani kije gaki gata wanda bai xo cikinta ba Ma jiransa take, duk kika cutar da rayuwar jiddah Allah baxai barki ba kuma xaki gani, Allah ya gani bana son auren nan bana farinciki dashi kuma baxan taba xama waliyyin daura shi ba, tunda bamu isa mu hanaki ba kije kiyi duk yanda kike so da rayuwarki, ya tashi ya fice ta bisa da kallon mamaki a xuciyarta tace banda abin abba shi kadai ne datijjo a duniya da xai xama waliyina, ko dashi ko ba dashi ba ai dama auren xanyi, a fili kuwa tabe bakinta tayi ta juya tana kallon hajiya tana cewa,

Iyayen yanxu idan baka nuna ka isa da kanka ba kwarar ka suke suci amanar rayuwar ka.

Kika ce me? Hajiya ta tambaya tana kallonta,

Uwani ta washe baki hade da gyara xamanta, aa hajiya wace ni d'iyar Malam Adamu addua ce kawai nake masa.

Addua indai daga gare kice bama buqata domin ba karbabbiya bace,

'hajiya kinsan gaibu kenan, gayamin dalilin da yasa baxata karbu ba tunda nidai musulmace, sallah biyar kike yi nima ita nake yi.

Jikin hajiya yayi sanyi, abin uwani ya soma bata tsoro da mamaki, a da uwani xata maida mata magana amma cikin qunquni ynxu kuma abin yayi tsauri ta kai ido da ido uwani xata iya gaya mata magana.

Ni dai kam uwani lafiya na gama rayuwata da iyayena har suka mutu kuwa,

'nima lafiya qalau xan gama daku, Allah ya nuna mana lokacin.

😳Xuru hajiya tayi tana kallonta, sai kuma taja bakinta tayi shiru, Allah ya gani sun baiwa uwani tarbiya kamar yanda suka baiwa jiddah, itace ta banxar tar da tarbiya insha Allah, Allah baxai kamasu da laifi ba.

Xuge jakarta tayi ta dauko saqon jiddah ta miqa mata, gashi hajiya abokiyar xamana tace in kawo maki.

Ki maida mata indai ta hannunki saqon xai xomin wallahi na yafe,

Qas... Qas.. Qas... Uwani ta tauna cingam din ta tana maida saqon cikin jakarta,

Hajiya fushi kike dan xan auri mijin jiddah, ai abin farin cikine, kuma ni bana tunanin cin amanar jiddah a rayuwata saboda tamin halaccin auren mijinta na har abada, ashe da gaske ne wadanda suka haifeka suna maka baqin ciki idan sunga cigaba ya same ka.

Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un shine abinda hajiya ta fada lokacin da hawaye ke fitowa a idanuwanta.

Ni uwani, ni ke maki baqin ciki, ni kike gayawa magana haka?

'ga wani baqin ciki na biyu nan kina min, saboda kar naji qamshin aljanna kike min hawaye hajiya, to dan Allah kiyi haquri ki gafarceni ki barni na shiga aljanna lafiya qalau tare da el'mustapha, dan Allah ki yafemin.

Alherin da kike cewa ina maki baqin ciki akansa kije kigani insha Allah baxaki taba ganin alherinnan acikin rayuwar auren ki ba, Allah ya albarkaci jiddah da ya'yan ta, fuuu hajiya ta fice a fusacce.

Kwanan ta biyu ta tattara inata inata tabar gidan.

Ana gobe saura kwana biyu auren, suna xaune da uwani a falo suna tattaunawa akan bikin, el'mustapha ya shigo.

Kallo daya uwani tayi masa ta soma neman nutsuwarta saboda kwarjini da sonsa dake qara linkuwa a xuciyarta ta xuba masa idanu tana kallonsa,

Idanunsa kyam akan na jiddah yana murmushi cikin boye damuwarsa kada uwani ta gano akwai yar tsama tsakanin sa da jiddah.

Ya xauna yana fadin jiddatulmusty me akeyi hakane aka manta dani.

Cikin yanayin ta mai sanyi take kallonsa,

'abubuwan biki muke hadawa mijina kai kuma nasan ba abinda xakayi dasu.

Murmushin dake fuskarsa ya kau har lokacin bai kalli sashen da uwani take xaune ba, ta kuwa tsura masa ido ba kakkautawa kamar ta hadiye sa take ji.

'Na manta ban sanar da ke ba, kada naga kowacce mace ta tako gidannan da sunan taxo biki na rigada na gayawa securities kada su bude mini qofar gidana mata su shigomin.

Sannan baxaa amin taron biki ko a ina bane ke koda walima ce ban amince ba,

Hankalin uwani ya tashi bata da ikon magana domin bataga fuskar hakan a tare dashi ba tana matuqar tsoronsa.

Amma meyasa, jiddah ta tambaya cikin damuwa, kasan auren farko ne yana buqatar koda walima ce.

Kin dai ji abinda na fada an I mean it, a wannan auren banda waliyi sai ibrahim ne xai xama waliyina dan haka kema ki nemo nata waliyin saboda mahaifinta ya rantse, dama ke kikaji xaki iya kuma nagayamaki kome xai biyo baya ki kuka da kanki.

Sosai jikin jiddah yayi sanyi, meyasa xakamin haka el'mustapha, bar maganar waliyi naji ko acikin securities din nan ne xan samu, banji kana maganar gidan da xata xauna ba.

Har akwai wani gida da xan bata ta xauna ya wuce wannan da take xaune a yanxu, ai amaryarkice ko kin manta, uwani ce da kika xaba akaina, har akwai wani gata da xan mata da ya wuce ta xauna a gidan kuma a dakin da take xaune anan xata cigaba da xama shine mallakinta.

Ban fahimce ka ba el'mustapha, wannan dakin da take xaune wai xata cigaba da xama?

kwarai da gaske,

Itama fa matar kace, kabata ko wancan bangare ne idan har baxaka iya bata gida daban ba.

Nafiso na saka yan haya aciki, bana son musu.

Haba mijina dan Allah ka sassauta haka kasani kayan dakin tama baxasu ishi wannan dakin ba, yayi qarami.

'Wannan kuma ya rage naki, ai nasan kina son ta kuma damuwar uwani damuwar kice, nafi kowa sanin jiddah uwar tausayice da karamci nasan xaki iya bar mata sashenki ta xauna ke sai ki dawo nan dakin saboda tausayawa.

Jiddah tayi shiru ta juya tana kallon uwani sai ta ganta tana kuka, to ni ya xanyi, wannan karon banda mafita banda kibi umarnin mai gidan.

Kudi ya ciro daga cikin aljihunsa ya qirga dubu goma cif ya bawa jiddah, ta karba tana kallonsa da son sanin kudin menene.

Idan kin sami waliyin nata kibata yaje da kudin masallacin bayan gidannan ina jiransa, kudin sadakin tane, banda kudi wannan Ma ranto su nayi.

Ba jiddah kadai ba wannan karon Ma uwani ta firgita da jin wulaqancin da el'mustapha ke qoqarin yi mata, wannan wane irin toxarci ne haka.

Dubu goma sadakin budurwa el'mustapha?

Banyi qoqari ba kike nufi, a maimakon ki gode min, kin manta wani nauyi kika doramin, cin ta shan ta da suturar ta duk sun dawo kaina, a da kudi na dagani sai jiddana da twins dina tayi mana karambanin kawo mana bare ta shiga cikin mu,

Ya soma laluben aljihunsa, dubu biyu ya ciro ya miqawa jiddah, kinsan kowane aure da yanda arxikinsa ke xuwa inaji wannan kam babu kanta dan ba wanda ya bani gudumuwa sai ibrahim shima dubu biyu ne kacal yace a siye goron daurin aure.

Ya juya batare da ya saurare su ba yace qarfe biyu ne bayan sallah xaa daura, idan waliyin ya bata lokaci kuma xan fasa auren dan baxan xauna xaman jiran sa ba, ya fice.

Shiru ya biyo baya tsakanin jiddah da uwani,

'nikam uwani da kin haqura da auren el'mustapha kinga tun baki aure sa ba kenan,

'Anty jiddah karki damu, abinda kake so shike wahalarda kai, nasan watarana har gida xai bani, kuma na haqura da bikin, ni yanxu damuwata daya ce.

Mecece kuma uwani.

Ni yanxu banda gata irin wanda amare suke samu ga iyayensu kowa baya sona a yanxu, shine nace nikam naji shiru baa fara min gyara ba.

Cikin rashin fahimta jiddah ke kallonta, gyaran me uwani?

Karki ce banda kunya anti jiddah kema nasan lokacin da hajiya ta miki gyara na kayan mata, nima ayimin ko kaza ce kuma abani nasha dana matsawa duka inyi inma akwai na turare duka inaso.

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

_Oh ni Bintu ashe haka Uwani keda masoya all over, sai xancen ta kuke yi, to kubarta haka kada ku cinyeta ku hana mata qiba a gidan mijinta_🤤

24

Tun da kina ganin ban miki gata bane uwani kije ki hada da kanki, ta wannan fannin banda kwari akai, ta fada cikin takaici da kishin uwani, lallai yarinyar nan bata da kunya.

Uwani ta dafe qirjinta tana fadin ni xuciyata ke min xafi anti jiddah duk na nemi abu ban samu ba sai ta dinga min xafi.

Ina ji wannan karon kam idan kika fadi anan, nan xaki cigaba da kwanciya ba wanda xan saka ya kaiki asibiti, abin naki ya xama rainin wayo tunda baki da kunya, ta tashi ta fice fuuu, uwani ta bita da kallo to ko anty jiddah ta fara kishine, bari na lallaba matar nan har a daura auren kada ta bore ta fasa.

El'mustapha yana dakin sa kwance, komai na jiddah mamaki yake basa yanda ta jajirce ga wannan auren, shi kansa yasan qarfin hali take yi amma yasan jiddah sa game dashi bata da haquri akan kowace mace, lallai uwani ta taki sa'an auren el'mustapha sai dai kam xaman ne bamusan yanda xata kaya ba.

El'mustapha shiru kawai yayi a saman gado idanunsa a lumshe har lokacin da jiddah ta shigo dakin,

Kallon sa take tana jin wani sonsa da kishinsa, wai yau el'mustapha ta xai xama mijin wata, watan Ma uwani, batare da tayi magana ba ta juya ta nufi kitchen domin hada breakfast, duk abinda take el'mustapha na kallon ta, yasan kishine ke dawainiya da ita, da shine ya bijiro da aure nan da yanxu yasan babu xaman lafia a tare da jiddah sa.

Dakin dasu banan suke a bayan gidan ta nufa, maaikatan sai gaidata suke cikin girmamawa yara da manya, cikin sakin fuska take amsa masu kamar yanda ta saba, tsofaffin Dany take barkwanci da su kuwa suna tabawa suna dariya kamar wacce bata da damuwa a tare da ita.

Ni kam tun jiya banga banan ba, lafiya dai ko.

Ai banan bata lafiya hajiya tun jiya tana fama da xaxxabi.

Subhanallah amma shine ba wanda ya sanar dani, ta shiga dakin tana fadin tasha magani kuwa.

Banan na kwance xaxxabi take, tun lokacin da taji ana maganar uwani xata auri el'mustapha, ta riqo hannu jiddah jikinta yayi xafi rau sai makyarkyata take,

'Anty jiddah wai da gaske uwani xata auri Alhaji?

Eh mana yau ake daurawa Ma, me akayi.

Banan ta fara hawaye sosai, anty jiddah kar ki barta ta aure sa dan Allah.

Meyasa banan

Saboda ita muguwa ce, bata da tausayi bata dace dashi ba.

Jiddah ta share mata hawaye,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login