Showing 135001 words to 138000 words out of 138779 words
Chapter 46 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
keken koyon tafiya duk ta siyo masa.
Haka yusuf ke xaune da uwani yana son ta yana kula da ita kuma yana biye mata duk da tayi sanyi sosai akan da.
'Abba kullum cikin sakawa yusuf albarka yake duk wanda xai iya xama da uwani tabbas abin a jinjina masa ne.
Cikin uwani ya shiga watan haihuwa.....
El'mustapha ina so na yaye airah na gaji da wannan tsotson nata shi ke hana min jiki,
Ya xauna yana fadin shekara daya da wata biyar fa jiddah, ina laifin ki barta tayi two to three months ta qara sha, haba jiddatulmusty me kike son taci.
Tace tana cin abinci sosai fa You know, dana yaye ta yanxu ne xaka ga na maida jikina sai kayi mamaki.
Yayi murmushi hade da Jan dogon hancinta yana fadin a qara mata two months ta kai da wata bakwai pls jiddah.
Xatayi magana wayar sa ta dauki qara yana dubawa yaja tsaki hade da ajiye wayar,
Waye yake kiran ka kake bata fuska haka musty,
Xaiyi magana ta qara ringing karo na biyu, ya dauka cikin bacin rai yana fadin didn't I warned you not to call me again, bai jira amsarta ba ya tsinke wayar.
Murmushi jiddah tayi tana fadin el'mustapha mai yan mata, ya kai mata dukan wasa ta goce tana dariya, suna haka wayarta ta dauki qara tana dubawa sunan banan tagani, ta dauka.
'Anty jiddah na haihu yanxu,
Masha Allah banan, me aka samu,
'Na sami baby girl,
Allah ya raya gida ko asibiti?
Yanxu haka ma muna asibiti baa sallame mu ba,
Tau shikenan gani nan xuwa, el'mustapha yana maki barka,
Banan tayi murmushi ta tsinke wayar batare da tayi magana ba.
Jiddah ya dube sa tana fadin banan ta haifi baby girl yanxu.
Yace Allah ya raya mata shine naji kina fadin xakije,
Eh mana idan banje ba wa take dashi ai nice komai nata dole tana buqatata a gurin, nice uwa ko ka manta, ai munyi mgn da kakarta idan ta haihu xata xo taje da ita acan xatayi wankan gida.
Ya tashi yana fadin shikenan sai muje tare dan baxaki barni ni kadai ba bayan kinsan yau ba inda xanje muna tare,
Murmushi kawai tayi....
Bayan sati biyu da haihuwar banan..
Tun da uwani ta tashi take jin ciwon Mara, ta dauka period ne xai xo mata taje ta saka pad ta dawo tana fadin wannan shegen abun na daina yinsa ynxu xai dawo bayan ance idan kana da ciki baka yinsa to me ya kawo sa yanxu idan ba baqin ciki xai min cikin ya xube ba.
Kodai breakfast din da yusuf ya hada nata ya saka mata maganin xubar da cikine ai kuwa da yaci amanarta ya cuce ta.
Marar ta tsananta ciwo wanda ya saka uwani ta kasa gane ciwon Mara take ko ciwon ciki, a nata tunanin qila baby ke ciwon ciki shiyasa har take jin ciwo, ta tuna ai ta siyo gripe water bari taje ta sha yanda yaron xai sami sauqi.
Ta dauki gripe water ta shanye gaba d'aya,
Ciwon ya tsananta sai cizon yatsa take, ta dauki waya ta kira hajiya tana kuka,
Hajiya kixo cikina xai xube sai ciwo yake min kixo ki kaini asibiti,
'Ko baa fada ba hajiya tasan haihuwa ce uwani bata sani ba, tuntuni akayi da uwani taxo gida a kula da ita taqi wai xaa rabata da mijinta, akace a kawo wata ta xauna da ita taqi wai xata amshe mata miji.
ta tsinke wayar ta kira jiddah ta gayamata kafin ta kira abba akan yaxo suje abuja yau uwani xata xama mama😃,
Uwani xama ya gagareta sai yawo take tsakiyar falon ciwon na tsanantawa,
Tana jin wasu ruwa na fito mata suna bin qafafunta, wayyo Allah cikina ya xube gashinan yana fitowa, ta durqushe tana jin alamar fitowar wani abu ta duqa tana dubawa, kan baby ne xai xo, tasa hannu tana maidawa tana ihu tana kuka sai matsar qafa take ga cikin nan yaxo xai xube, iya gigicewa ta gigice dai dai lokacin jiddah da yusuf suna shigo kisan tare suka xo abba ya kira sa a waya.
Yusuf baiyi wata wata ba ya dauke ta sai mota suka nufi asibiti sai kira take a rufe mata qasan kar cikin ya xube.
Nurses suka karbeta, suna qoqarin fito da baby tana qoqarin saka hannu ta maida xasu cire mata ciki saboda suna mata baqin ciki da xata haihu, nan take gurin uwani ta suma.
Baby boy aka samu, tun da aka bawa uwani yaron taqi ta baiwa kowa ya gani ta riqe abinta gam sai runguma take, ga jariri da shiga rai haka uwani kejin qaunar yaron har cikin ranta.
Duk da yusuf taqi ta bashi yaron ya gani, gasu jiddah tsaye, su abba ma sun iso da hajiya uwani taqi ta bada jariri duk wanda xai gansa sai dai ya gani a hannunta.
Mamaki ya hana su magana sai idanu suka xuba mata ganin yanda take ta sumbatar yaron tana masa wasa,
El'mustapha na xuwa tun bai nemi a bashi ba ta dube sa da murmushi,
Xo ka ganshi yaya, mai kyau ne kamar abbana shine yaqi ya biyoni nida na haifesa sai ya biyo abba saboda yana min baqin ciki, xo ka ganshi ta miqawa el'mustapha shi.
Duk gurin aka cika da mamaki aka hana uban d'a aka baiwa wani😨, El'mustapha wani jigo ne na rayuwar uwani da take matuqar gani qima da girmansa,
El'mustapha ya karbi yaron cikin murmushi lallai uwani tayi gasky yaron duk abba ne, a hannunsa suka samu suka karbi yaron suka gani.
Ta nace baxata bi su hajiya wankan gida ba, a gidan jiddah xata xauna haka suka haqura suka je da ita can gidan,
Yan barka masu ganin jariri da yawa idan sunxo sai dai suga jariri a hannun uwarsu bata yarda ta basu ba yanda take ganin sa fari haka kada a sama sa datti yayi baqi, tayi ta tabin fatar jikinsa tana jin dadi, sai ta hanawa yaron ya samu yayi barci saboda taba nan taba can.
'Ko barci yake sai an tada shi yasha nono kada ya xauna da yunwa, idan wanka aka je yi mata da taji kukan sa xata fito toilet da gudu ta dauki abinta.
Idan yana kuka uwani tana kuka, idan yana barci tana yi idan ya tashi ita ma ta tashi.
Mutanen gidan suna ganin ikon Allah.
Yusuf bawan Allah, yaxo yana tambayar uwani wane suna take son a sakawa yaron?
Kai tsaye tace a saka masa *EL'MUSTAPHA* saboda ya biyo hali, haxaqa, da kwarjinin mai sunan, tana son El'mustapha, yusuf yasa hannu ya bige bakinta yana fadin,
Kada na qara jin kalmar uwani, Allah ya raya el'mustapha.
Ranar suna fa an cashe babu laifi anyi taro lfy an watse lfy.
El'mustapha yayi namijin qoqari ga takwaran nasa, bayan suna uwani ta tada masa fitinar sai ya bata vespa din ta xata baiwa yaron ta Affan dama shi ta siyawa, da kyar el'mustapha ya kashe wutar vespa din.
Wata daya da haihuwar uwani har lokacin bata koma gidan yusuf ba jiddah taqi ta bari ta koma har sai ta gama yarda da nutsuwarta tukunna.
A dai dai wannan lokacin el'mustapha ya sami qarin girma daga A. I. G xuwa D. I. G, farin cikin su baxai misaltu ba,
Ibrahim yana daya daga cikin mutanen da suka sami promotion din,
Dr.Merah da kansa yayo tattaki har Nigeria dan taya El'mustapha qarin girman da ya samu.
Yusuf yana buqatar matarsa ta koma duk da anty ikram tayi wa jiddah mgnr komawar uwani dan yanxu suna shiri sosai da uwani ta nutsu ba kamar da ba, haka Ma anty yusrah.
Yan uwan yusuf a yanxu sun dan ko waye uwani haka suke xaune da ita ana haquri,
Akwai ranar da jiddah ta risketa da bindigar el'mustapha lokacin tana shayar da jaririn, kai tsaye ta cewa uwani kashe yaron xatayi.
Saboda tsoro da raxana uwani harda sakin fitsari ganin lallai jiddah da gaske take xata kashe mata yaro tunda har ta saita ta da bindiga,
'Anty jiddah ki kashe ni kibarmin shi ya rayu, dan Allah ki yafe min kada ki kashe min yaro ina son sa, idan kika harbesa nima mutuwa xanyi.
Cikin daure fuska jiddah tace sai dai ki mutu amma sai na harbesa kamar yanda kika harbi arham, ta qara saita bindigar akan yaron, nan take uwani ta xube gurin a sume.
Jiddah ta dauki yaron tana fadin ko ba komai kinji radadin da naji lokacin da aka harbi 'dana aka bani shi rai a hannun Allah, baki dubi halin da nake ciki a lokacin da nake da juna biyu ba, jiddah ta fita da yaron tana jijjigashi.
Bayan farfadowar uwani sai kuka take tana qara roqon jiddah gafara, tana jin nadama mai tsanani a tare da ita a duk lokacin da ta tuna sanda tace a harbe arham har ya fadi hannun jidda, ashe abinda jiddah taji kenan amma shine bata suma ba har ta iya riqe sa tana kuka, lallai jiddah tayi namijin qoqari Allah ya yafe mata.
Yau kam yusuf yaxo yana so matar sa ta koma ya gaji da kawaicin da yakewa jiddah, ya sami uwani a dakin ta, ya san ta da jaraba.
Uwani yaushe xaki koma ne, nayi missing din ki kinsan bana gajiya dake.
Tace ai kaine da kaqi gayawa anty jiddah har yau fa mu ango da amarya ne maso son junan mu bama gajiya da wannan abun.
Murmushi yayi yana kallonta darun uwani na birgeshi, yana son matarsa a hakan, yace ban taba fada mata ba ina jin nauyinta kin sani.
Uwani tace haba shiyasa ta qudundune mu a wannan gidan nata take gasa mana aya a hannu, idan kana jin nauyin ta ni xanje na gayamata daukar haqqin da take yayi yawa.
Rufamin asiri uwani, ai baxan iya ba,
Ta soma qoqarin tashi tana fadin ni bari naje na fada mata saboda ina son wannan abun dai dai lokacin jiddah ta shigo, yusuf ya gaida ta,
Uwani ta dube ta tana fadin, anty jiddah ko xaki yiwa yaya El'mustapha magana ne a bude mana wancan part din nida yusuf da affan mu dawo da xama a cikinsa,
Jiddah tace ban gane ba, naki gidan fa?
To ai naga kin tsare mu a wannan gidan naki bayan kinsan muna da namu, tuntuni nake son maki magana ana kwaba ta kuma ke kinqi ki gane kina daukar haqqi, ke kullum kina tare da mijinki amma ni ana min baqin ciki da nawa mijin.
Mamakin uwani ya hana shi motsi daga inda yake xaune,
Jiddah da ta saba da halin uwani murmushi kawai tayi tana fadin, Uwani will never change, Uwanitilyusuf kayan Allah, Allah ya baku xaman lafiya ya qarawa yusuf haquri da ke.
*
El'mustapha ya siyowa jiddah form na jamb ta cika yana so ya maida ta makaranta tayi karatu kamar yanda mahaifin jiddah Uncle B ya bashi shawara,
Jiddah ta kwashe yanda suka yi da uwani ta fadawa el'mustapha sai dariya yake,
Jiddah yarinyar nan baxata kashe ni ba, she is olways funny katobarar tace kawai bana so.
Jiddah ma cikin dariya tace like serious El'mustapha, Uwanin ka ce fa, Uwanitilmusty wanda mutuwa kadai xata raba ku duk mai mata baqin cikin xama da kai bata son shi.
Taja hancinsa tana murmushi, Matar El'mustapha before mai neman takara ta fito yar siyasa bayan ta gama gashin masara a qofar gidansa, Uwanitilmusty mai xubawa mijinta pills,
El'mustapha ya matse ta sosai a jikinsa yana fadin, uwani ta yusuf ce a yanxu kada ki mata baqin ciki da mijinta Uwanitilyusuf, El'mustapha kuwa na jiddah ne ita kadai har qarshen rayuwarsa Jiddatulmusty,
Suka kyalkyace da dariya cikin rungume junan su......
A'UZU BILLAH MIN AZABIN NARI WA AZABIL KABRI WA FITINATIL MAHYA WAL MAMATI WA FITINATIL MASIHID DAJJAL (AMEEN)
ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI (kuskuren dake ciki Allah ya yafe mana)
BISSALAM.
*EL-MUSTAPHA*
17th Nov,2018
HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of Experts and Perfect Writers)
Fertymerh Xarah💞
*SHARHI*
daga
kungiyar
*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*
( Home of perfect and expert writters)
El'mustapha labari ne daya qunshi abubuwa da dama way'anda suke faruwa awannan zamanin namu,
Abubuwa ne da suke faruwa a rayuwarmu ta yau da kullum."
El'mustapha ya kunshii jarumai irinsu JIDDAH da kuma UWANI, dashi kanshi adon tafiyar EL'MUSTAPHA, sannan kuma aka sakayo mana BANAN aciki."
El'mustapha labari ne daya kunshi
#k'addara."
#cin amana."
#ilimantarwa."
#fad'akarwa."
#yadda zakayii tarbiyar yaranka."
#wa'zantarwa."
#Dakuma nishad'antarwa."
#hakurii."
#Tausayi."
*El'mustapha*= hak'ik'a el'mustapha shine jigon wannan labari, El'mustapha ya kasance mutum mai sanin darajar iyalinsa, hankalii, hakurii, martaba dakuma mutunta iyalinsa, matashine mai ji da kud'i, Mulkii, dakuma ilimi, ga kuma uwa uba kuma mutum ne shi mai addini."
El'mustapha yakasance mutum mai kwarjini da shiga zuciya, ga kuma kyau, El'mustapha yana kula da matarsa sosaii, wanda hakan yajawo y'ar uwarta da kuma mai aikinta fad'awa soyayyarsa, dan suma sunason samun kwatan kwacin farincikin dayake baiwa matarsa."
*JIDDAH* hakika samun mace mai zuciya dauriya hakurii, juriya, tausayii rigon amana yayi wuya awannan zamanin namu, Amma kuma Allah sai ya had'awa wannan duka abubuwan, majidda mata awajen El'mustapha."
JIDDA macecce mai matuqar son mijinta sosai, Tanayi masa biyayya bata d'aga muryarta akan mijinta, a kullum ba tada buri daya wuce taga y'ay'anta da mijinta cikin farinciki,
JIDDAH tana da qoqari wajen farantawa duk wani wanda yake tare da ita.
" JIDDAH marainiyace bata da uwa kuma bata da uba, Allah ya bata marik'anta wanda suka riketa tsakanii da Allah suka bata tarbiya, suka raineta kamar yanda sukayi wa y'arda suka haifa acikinsu, Allah ya dubii maraicin JIDDAH ya bata miji mai mugun son ta da kuma kula da ita wanda ko wace mace zatayi sha'awar samu."
*UWANI*" uwani itace musabbabin sanya y'ar uwarta jidda cikin wani hali, uwanii ta kasance maiciya amana, kuma cin amanar ma way'ar uwarta, kwata-kwata batad'auki tarbiyar da mahaifanta sukayi mata ba, kai halin uwani dai ba'acewa komai, sai dai Allah yaraba mu da hali irin nata."
*BANAN*" banan takasance y'ar aiki awajan JIDDAH yayin da taraineta tun tana qarama bata kyamarta, ta sanyata a makaranta, amma kuma daga baya tazo ta nuna tanason mijinta."
*K'ADDARA* Hak'ika jiddah taga kaddori da dama, jiddah ta kasance mace mai kishin mijinta, tana son mijinta fiye da komai a fad'in duniya tana kishinsa sosai bata jin zata iya had'ashi da kowace irin mace a duniya amma kuma Da kaddara ta tashi fad'a mata sai ya juye ita da kanta take roqonsa yaqara aure, ya aurii y'ar uwarta dan batason rasa y'ar uwarta."
*CIN AMANA* mijin yar uwata nakeso, farin cikin dayake baiwa y'ar uwata nake son samu fiye da hakan, koda wannan kalamai da uwanii tayii ya kasance cin amana, tabbas uwani taci amanar y'ar uwarta, ta yaudare ta ta hanyoyi da dama domin ta cimma burin ta na ganin ta raba wadannan masoyan, bayan wannan kuma take qoqarin kashe yar uwarta da yaronta duk saboda mijinta duk da tayi sanadiyar nakasa mata qafa.
BANAN" banan bata kyauta ba na son mijin jiddah duk da halacci da kyautatawar da tayi mata a rayuwa.
*ILIMANTARWA*" hakika wannan littafi ya ilimantar damu kuma ya nuna mana muhimmancin haquri da yarda da qaddarar da Allah ke dorawa bawansa domin ya jarabcesa.
*FADKARWA*" tabbas wannan littafii yafad'akar ta hanyoyi da dama, tabbas idan ka karanta wannan littafi sai ka samu hanya da yawa wanda zakayiwa rayuwar ka gyara."
*WA'ZANTARWA*" lallai wannna littafii ya wa'azantar damu ta fannonii da dama."
*TARBIYAR YARA*" lallai JIDDAH tayi qoqarii sosai wajan kula da tarbiyar yaranta, duk da kasacewar yanda uwani takecin zalin yaran sannan kuma take musguna musu, JIDDA bata ta6a sanyawa sunyi mata rashin kunya ba, aa sai dai ma ta sanya su bata haquri."
*NISHAD'I*" tabbas wannan littafi yayi mugun sanya makarantashii nisahd'i, uwani ta taka rawar gani wajan nishad'antarwa cikin wannna littafi itace jibin nishadin komai sanadiyar hakan take da masoya kuma take nishadantar dasu.
*HAKURI*, hak'ika jiddah tayi hakuri wajan zama uwani a gidanta, tayi hakuri nabarin y'ar uwarta ta auri mijinta, tayi hakuri data zauna day'ar uwarta cikin inuwa d'aya na auran mutum da take matuqar so da qauna, tayi hakuri a lokaci da uwani keyi mata izgilancii bastard a tad'auki mataki ba, Jiddah tayi haquri a wannan littafi wanda ba kowace mace xata iya irin sa ba.
*KORAFE-KORAFE*
Qorafin da marubuciyar ta samu a littafin lokacin da jiddah ta tashi mutuwa yanda mutane ke kirana wasu suna min message cewa na bata littafin, wasu har da cewa baxasu qara karanta littafin ba, kai tsaye sun yanke hukunci batare da sun san inda littafin ya dosa ba, da yawa ana samun readers haka masu canxawa writers ra'ayi akan abinda suka yi niyar rubutawa daga farko, ni bana haka yanda na tsara littafina tun farko haka nake tafiyar da shi.
Qorafi na biyu meyasa uwani bata koma gidan el'mustapha ba, meyasa idan baxai auri uwani ba ya auri banan saboda jiddah ta gane kuskuren ta, sun manta haquri da halacci irin na jiddah wanda ba kowace mace a irin wannan yanayin xatayi abinda jiddah tayi ba, idan har el'mustapha ya auri uwani ko banan kenan babu riba ga duk haqurin da jiddah tayi a baya, yanda ta wahala a littafin yaci ace ta ji dadin auren ta, ta more mijinta batare da mahaukaciya uwani ba, duk wannan qorafin yana fitowa ne daga masoyan Uwanitilmusty yan baqin ciki da jiddah.
Allah yasa mu