Showing 108001 words to 111000 words out of 138779 words
Chapter 37 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
komai amma bata falon.
Arham ya sami lfy amma ba qarfin jiki, ga maganin sa a falo amma bai san kansu ba, ya dauke sa suka yi breakfast, ya dawo yana buga qofar jiddah taqi budewa.
Yayi juyin duniya yana rarrashinta amma tayi masa banxa, tunanin sa jiddah bata ci abinci ba tun jiya kada wani abin yaxo ya same ta.
Ya kira anty ikram ya gayamata itama tayi kiran jiddah taqi dauka kuma taqi ta kashe wayar,
Cikin damuwa ya qara xuwa bakin qofar, kome kike ji jiddah ki fito kici abinci ba danni ba please,
'Ko alamar motsinta bai ji ba, yaji kamar ya bige qofar dakin.
Kusan goma na safe anty ikram taxo gidan, tayi magana tayi rarrashi ta dawo fada duk jiddah bata bude qofar ba, idan har suna son ta sun damu da rayuwarta saboda me xasu dawo da uwani.
Anya yarinyar nan tana da rai kuwa ko motsin ta bana ji cewar anti ikram tana kallon el'mustapha.
Yace lafiyar ta qalau sister tunda baki ji kukan airah ba kinsan ta da fitinar tsiya, ni ban sani ba ko jiddah taci abinci ne?
Kaima da laifin ka el'mustapha, yarinyar nan an maidata saboda me xaka ce ta dawo, baxaka iya shirya wannan yarinyar ba tun da safe sai da sukayi dambe da mai aikina wai bata kai mata ruwan wanka ba, ban sani ba ko na dauki mai aikin ne saboda ita, kawai sai ta fara dukan yarinyar mutane,
Ta juya a fusacce tana fadin ko menene laifin kane idan ma son yarinyar kake tun wuri ka cire sonta a xuciyarka na gayama baxaka taba maida wannan yarinyar ba wadda tayi yunqurin kashe yar uwarta da gudan d'anka ai da yanxu babu arham banda taimakon Allah.
Yace sister tafiya kuma xakiyi keda na ki.... tayi saurin katse sa,
Xaka bani headache ne el'mustapha, laifin kane wannan karon bansan me kake so nayi ma ba, nayi magana taqi budewa so kake nayi ta tsayuwa? Idan naje gida xan gwada kiran number ta inta dauka xan mata magana.
Yayi shiru baiyi magana ba ta fice ya xauna yana shafa kan arham,
Daddy meyasa mummy bata fito ba,
Nima ban sani ba,
Daddy kace aryan ya dawo yau.
Tau shikenan xan kira anty yusrah ta kawo shi.
Suna haka ibrahim ya shigo,
'Ashe haka hannun ya kasance bayan rabuwar mu, cewar ibrahim yana qoqarin xama a sofa.
El'mustapha baiyi magana ba,
Ibrahim yace naji ana qishin qishin xaa yi promotion fa a office jiya,
El'mustapha ya ware idanu yana kallon sa, kai haba amma yaushe xasuyi,
Shine ban sani ba, Muna addua Allah ya sa damu a ciki,
El'mustapha yace amin,
Ibrahim yace yau ina jiddah ne sarkin rigima kaji abinda take son liqamin, wannan mahaukaciyar yarinyar marar imani.
El'mustapha yayi murmushi yana fadin ai na gayamata baxaka auri uwani ba,
Yace kai haba, bani da burin qara aure a yanxu matan nan biyu sun isheni kansu a hade yake kuma gwargwado ina iya bakin qoqarina akansu suma suna faranta min, yanxu tunanin ka idan na dauki uwani na jefa gidana wallahi ko rantsuwa nayi baxanyi kaffara ba xanje na sami ta raba min kan matana wannan tayi gabas wannan tayi yamma ita kuma tana kudu mahaukaciyar, before I know b.p na ya hau inma ban kwanta asibiti ba, kai qila watarana naxo na sami yan sanda qofar gidana saboda wannan yarinya, na tabbata har maqota idan akwai mata biyu sai ta ware su ko ta hada mata da miji fada, yanda kasan saukar boko haram a Maiduguri haka yarinyar take,
El'mustapha yace shiyasa bana son yarinya komai ina yine saboda jiddah ashe kuma laifi nake ban sani ba.
Ibrahim yace dubi ja'irar yarinyar nan saboda rashin imani tana kwance a asibiti fa sanda ka harbeta a qafar nan har tambayata take wai jiddah ta mutu, ji fa.... haba... haba.... ina.... ai wannan tafi qarfin ibrahim wallahi bana sonta ko kadan, jiddah ta cuceni da take son hada ni da ita, in kai ta ina, na dawo mijin hajiya kenan d'an albashina da naji alert na kwashe duka na kai mata.
El'mustapha ya kyalkyace da dariya, yana fadin babban dan sanda da kai sai tsoro, yarinya ce fa kada ka bada maxa,
Bala'in ta yafi yarintarta tunda har tasan ta kashe yar uwarta saboda namiji, tasan ta cutawa yaro saboda namiji to menene baxatayi ba, barni da yan matana guda biyu, ina juya nan a rungume ni, na juya nan naji kiss, ina ce wash a koro min sannu yafi goma, komai na siyo ana min godia da addua, wallahi watarana har rikicewa nake na rasa dakin wa nake sai su tamin dariya.
El'mustapha yace wai ko nima xan xo na shiga layin masu mata biyu dinnan ne.
Ibrahim yace da kuwa kaci ubanka gurin jiddah, kuma wallahi babu ruwana kada kace dani kayi xancen.
El'mustapha yace rufamin asiri wasa ma nake bani da sha'awar yin haka, jiddana ta isheni rayuwa my one an only wife,
Ibrahim yace a to gwanda ka dawo cikin hankalinka ni kaina yanxu nace xan qara aure nasan gidannan baxan qara jin sanyin sa ba, kullum sai an min gargadi duk xani fita aiki akan mata, wai ina jiddah ne, ya soma kallon sashen ta cikin daga murya yana fadin, Jiddatulmusty yau me akeyi haka ne a ciki ba ko gaisuwa.
El'mustapha ya dubesa yana fadin fushi takeyi tun jiya take a rufe,
Subhanallah, ibrahim ya fada yana kallonsa, kuma kake xaune kabarta, sai ka balla qofar mana kasan halin da take ciki.
El'mustapha yace nima nayi tunanin yin haka, ba fushin nake mawa ba illah rashin cin abincinta,
Ibrahim ya tashi ya nufi qofar dakin yana kiran sunan ta amma bata amsa ba, ya juya yana kallon el'mustapha yace,
'Wannan qofar ba wadda xaa bige bace, ka kira masu hada qofar nan suxo su bude, wai me ma kayi mata ne, lafiya qalau muka rabu da ita a jiya,
Yace saboda na maida uwani ne.
Ibrahim ya xare idanunsa yana kallonsa ban fahimce ka ba, ina ka maida uwani auren ku ko me.
El'mustapha yaja tsaki ya soma tafiya yana fadin kai ka kasa xama da ita ballantana ni dana dandani axabar xama da ita, tana gidan anti ikram da xama ina so na shirya tane.
Ibrahim ya dube sa cikin takaici, ka shiryata as in how, mtsew sai idan son ta kake ka tsiro da wannan baya ga haka miye naka da ka shirya uwani, kai xaka iya shirya tane, ya juya qofar jiddah yana fadin,
Kada ki bude masa qofar, cigaba da xama aciki yaje ya xauna da uwanin.
El'mustapha ya dube sa lokacin da yake qoqarin ficewa,
Wai meyasa kun kasa fahimta inda na dosa ne, duk bakin ku daya saboda baku son uwani.
Ibrahim yayi masa wani kallo kafin yace yanxu na gane inda ka dosa ai, idan ka gyara uwanin ka maidata dakin ka tunda mu bama so, ka maidata kagani wallahi rantsuwar musulmi bata xama gidannan kai jiddah ma sai ta bar gidan kaje ka cinye uwani.
Ibrahim ya fita ransa a bace, el'mustapha ya xauna xuciyarsa ba dadi dai dai lokacin wayarsa ta soma qara,
Yana dubawa yaga Dr Merah, ya daga wayar suka gaisa,
Yace gani na shigo abuja tun jiya, naxo gaida mai martaba xuwa gobe xan koma.
El'mustapha yace bani address sai naxo mu gaisa kafin ka tafi,
Merah yace aa kai xaka turo min address yanxu xanxo na kawo maka xiyara, ina so naga qafafun jiddah yanda suke a yanxu.
Yace tor shikenan ya tsinke wayar kana yayi masa test na address din,
Ya tashi a rude shi bai masan yanda ake tarban baqi ba duk xaiyi baqi jiddah ce ke komai sai dai yaxo ya sami har ta gama shirya komai,
Ya taba jikin arham dake barci babu xaxxabi tare dashi da alama ya sauka, ya dafe kansa kafin ya soma dialing number jiddah, kusan sau biyar tana ringing bata dauka ba, ya tura test fiye da minti ashirin babu ko reply, yana haka yaji ana sallama,
Ya amsa batare da ya bada izinin shigowa ba saboda muryar daya daga cikin yaran sa ne.
Sir akwai baqi qofar gate suna son shigowa,
Yace yes nasan da xuwansu, sauke su a falon baqi ina xuwa.
Shi tunda yake a gidan bai taba shiga cikin gidan nasa inda masu aiki ba sai wannan karon shima dan ta kama ne,
Suna ganin sa kuwa suka soma gaidashi cikin mamakin ganinsa,
Baisan kowa acikin su ba, gwanda Inna ya nufe ta yana gayamata abinda yake so tayiwa baqin nasa,
Tace akwai hadixa bari na gayamata saboda tasan komai tun banan tana nan tare nake ganin suna komai.
Yace yauwa Inna ayi sauri ba abinci ba kada ki manta, snacks haka kayan marmari da sauransu taxo sashen jiddah ta duba
Ya fita kai tsaye babban falon sa ya nufa na sauke baqi,
Suna hada ido suka sakarwa juna murmushi bayan sun xauna.
El'mustapha ya xauna yana fadin nayi mamaki ganin mai girma merah yau batare da fadawan sa ba sai mutum biyu kacal.
Merah yaja tsaki yana fadin yanxu ma dan mai martaba bai san da fitowa ta bane da ka gansu jibge duk inda xanje suna tare dani ina jin haushin abin.
Sun taba hira sosai aka soma shigo masa da kayan ciye ciye,
Merah ya ware ido yana kallon el'mustapha sanda ya kai Apple bakinsa,
Yace ina qanwata ne, bata san naxo bane ko kana min rowar ta.
El'mustapha ya shafi kansa cikin murmushi kafin yace tana can ta kulle kanta a daki tun jiya tana fushi,
Merah ya dube sa cikin seriousness yace kar dai har yanxu kan maganar mai aikin nan ce el'mustapha,
Yace aa wallahi haba, ai tayi aure week dinnan ma, didn't I told you bana son yarinyar.
Yace why jiddah xata rufe kanta a daki, direct me na ganta.
El'mustapha ya tashi suka nufi sashen jiddah,
Merah ya dubi arham dake kwance kan sofa,
Yace idan na canka dai dai wannan shine twins naku da kuke magana,
El'mustapha ya gyada kai yana fadin shine amma dayan yana gurin sister na anjima xata xo dashi.
Very cute dashi, ashe da kai suke kama, kayiwa qanwata wayo yaran sai suke biyo ka amma suna dauko hasken maman su.
El'mustapha ya nuna masa qaton pic din su dake manne a falon, ga d'an uwansa can mai rigima kamar Merah.
Dariya merah yayi yana fadin kamar Sultan xaka ce, I love this identical twins el'mustapha, kuma a hakan kuke banbanta su kamanin nasu yayi yawa.
El'mustapha ya gyada kai yana kallonsa,
Yace nima xanxo Afiya ta haifamin twins dinnan very soon,
El'mustapha yace sai ka dage kuwa bada sauqi ake samun su ba, Nothing worth comes easy,
Suka yi dariya lokaci daya tare da tabawa,
Merah ya isa qofar dakin da el'mustapha ya kaishi,
Magana yayi cikin kwantar da murya,
Qanwata, ga yayan ki yaxo ya duba qafarki da damuwar ki.
Kamar a mafarki jiddah taji muryar Dr merah, ta taso a hankali xuwa qofar dakin tana leqen sa,
Shine kuwa taji muryarsa yana fadin,
For the sake of me jiddah xo ki bude qofar,
Haka taji a xuciyarta kamar damuwarta ta kau, hijab ta saka dama airah barci take sai bata bi ta kanta ba ta soma qoqarin bude qofar, merah na jin haka ya koma cikin falon inda el'mustapha.
El'mustapha ya cika da mamaki sanda jiddah ta fito, wane girma ne na merah a gurin ta haka, meke tsakanin su, meyasa ta dalilinsa ta fito bayan duk magiya da roqon da ake mata tun jiya, ya xuba mata manyan idanuwansa yana kallonta,
Dr merah ya juyo yana kallonta,
Ya salam, meya sami jiddah haka, menene ya saka ki kuka haka har idanunki suka kumbura?
Kamar jira take ta soma kuka kuwa,
Yace saboda me na baki number na jiddah, kin gaya min ke marainiya ce ba uwa ba uba, ba yaya ba qanwa only you an your husband, nace ki dauke ni matsayin yayan ki, xan hada ki da iyayena su xama naki, xan hada ki da yan uwana, matata har qanwata Rumaisa ashe ke baki dauke ni yayan ki ba idan har baxaki iya gayamin damuwar ki ba.
Ya xauna yana fadin, xo xauna nan naji waye ya taba ki haka, idan mijin kine ko yana babban dan sanda baifi qarfin Sarautar mahaifinki ba haka bai fi qarfin Mulkin yayan ki ba, idan ta kama sai na saka a daure min shi na baki bulala kiyi ta dukan sa har sai inda ranki yayi sanyi.
Murmushi tayi wanda bai kai xuciyarta ba, ta qarasa ta xauna inda ya nuna mata,
Banji dadi ba jiddah naxo na same ki cikin wannan halin baki kira kin gayamin ba, aiko a waya ne tsab xan kira na kwatar maki yancin ki, kin ganni nan qanwata rumaisa idan ta sami matsala da mijinta irin wannan, ba wanda xata nema a gida sai ni koda bana gari, kuma ba wanda xai taba ji daga ni sai ita sai mijinta, kuma he is my friend jinina ne shi I told you before, haka xan kirashi idan shine bashi da gaskiya na masa fada ya gyara idan kuma itace ita ma nayi mata fada, Afiya ma sai ta gane ko nayi mata laifi sai taje ga yayanta Bilal xaki ga ya kirani yamin yanda nake masa, and we live happily, idan haka ne meyasa jiddah baxata gayawa nata yayan matsalarta ba.
El'mustapha na xaune baice komai ba ya xuba masu idanu, yana mamakin sauqin kai irin na Dr Merah, a waje idan yana mulki kamar bashi ba, dariyar sa ma baxaka gani ba.
Merah ya dan matso yana fadin, tell me jiddah, don't look at him ba ruwanki dashi da yayanki kike magana,
Batare da bata lokaci ba ta kwashe komai ta gayamasa, tana gamawa kuwa ta fara kuka,
Merah ya dube shi yana fadin, maida uwanin xaka yi ne?
El'mustapha ya girgixa kansa,
Merah has tsuke fuska yana fadin idan kayi haka kuma ka cutar da waccan yarinya, idan kasan baxaka maidata ba saboda me xaka mata qaryar idan ta shiryu xaka maida auren ku, baka tunanin dalilin qin maida auren sai ta koma ruwa ta cigaba da abinda take inma baifi hakan ba, to wane gyara kayi mata?
Idan har iyayenta baxasu iya tankwasa ta su gyarata ba I don't think you can do, kaine wa, uban ta 'ko me?
Xai yi magana dr merah ya katse sa, baxan baka damar magana ba a yanxu just take me to your sister house, ina so naga yarinyar....
Suka tashi suka tafi, a falon anty ikram suka xauna, aka kira uwani tun da ta shigo ta kafe merah da idanu, ina el'mustapha ya sami bature haka mai kyau.
Kallo daya dr merah yayi mata ya gane yarinyar bata da nutsuwa,
Kowa bata gaida ba ta xauna tana kallon el'mustapha da murmushi,
Ai daxu ina taso na kira ka naji muryar ka amma ba kudi a wayana, kuma gidannan ana min baqin ciki ba wanda ya bani wayarsa n.... Merah ya katse ta a fusacce,
Shut up.... ya fada cikin tsawa,
Nan da nan uwani ta nutsu tana kallonsa cikin mamaki da tsoro, shi wannan kuma waye.
Yace yayar mu wannan yarinyar a maidata inda iyayenta, suke da haqqi akan kula da tarbiyar ta idan kuma ta gagare su ne su bani inta naje da ita akwai kurkukun da xan jefata a ciki xata gyaru.
Ya dubi uwani yana fadin, el'mustapha yana maki qarya baxai aure ki ba ko kin nutsu ko baki nutsu ba, ki cire wannan a xuciyarki, shi mijin mace daya ne jiddah kawai, alqawarin da yayi maki na maganar xai aure ki idan kin shiryu shima babu, ki dauki kayanki kije gidanku ki xauna da iyayen ki, idan kin ga dama kada ki nutsu kanki kika cuta da iyayenki kuma ba mai auren ki a haka is better ki dawo cikin hayyacinki kisan me kike.....
Duk maganar da yake uwani ido ta xuba masa, bata ma taba tunanin yaji hausa haka ba, shi kuma waye ina ruwanshi da soyayyarta da el'mustapha, ko dai sonta yake yi yaxo ya rabata da el'mustapha dan ya aure ta idan kuwa hakane xata amince da..... Ya katse mata tunani yana fadin daina kallona haka, ashe baki da kunya idan har xaki tsaya kina kallon tsakiyar idanuna.
Uwani tayi saurin sunkuyar da kanta qasa xuciyarta na bugawa kamar ta fashe da kuka take ji.
Ikram tace amma naji dadin wannan abin dan baxan iya xama da wannan yarinyar ba xan karya mata qafafuwa, da axo ana aikin dana sani gwanda tabar gidannan inma gidanka xata je ta xauna wannan tsakanin ka ne da jiddah ba ruwana.
Dr merah yace daga nan gidan ubanta xata je ko jiddah baxata gani ba, ki fito da naki mijin kixo ni xan maki aure in kuma baki dashi ina da wani dogari nawa dake neman matar aure matarshi ta rasu sai na hada ku ai ba wani abu bane, amma ke bakya jin kunya ki dawo kina son mijin jiddah?
Jiddah da kika so kashewa ki rabata da duniya saboda mijinta da ta rufa maki asiri ta baki kika aura, kika sa aka nakasa mata qafa, duk bakya jin nauyi da kunyarta a yanxu, kin manta da wannan, shi wannan mijin naki da kike son koma masa jinin sa fa