Showing 24001 words to 27000 words out of 138779 words

Chapter 9 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

1984

/>
Yanxu sai dai ki juyawa iska baya, uwani ta daina shiga aji ni bautar aure nake yanxu, wannan casbi da kika ga ina ja kariya ce daga sharrin aljannu ko wani sihiri da kishiya ke aikowa amarya dan ta hana mata xaman gidan miji.

Lallai uwani, ai kowa yasan xuciyar jiddah abinda kike fada baxata iya aikata maki ba kuma insha Allah xan sanar da ita yanxu cewa kindaina xuwa makaranta.

Kifi ruwa gudu, kada ta barni da rai tunda tasan gaibu kotasan dalilin qin xuwana.

'Surry ta tabe baki, idan kika ce kina bautar aure dariya Ma kike bani, keda miji baya kulawa bai masan da xamanki a gidan ba, is better ki koma makaranta ko kin sami abinda xaki taimaki kanki watarana, kafin uwani tayi magana ta ciro mata katunan auren ta ta miqa mata,

Ina miki albishir aure na da Yusuf wani sati.

Wane Yusuf din?uwani ta tambaya tana kallon katuna,

Yusuf dai wanda kika sani..... Ashar din da uwani ta dura ya katse surry,

'Dan kaza kaza...... Ni xaki ci amana ki yaudara, saurayina xaki aura.

Auren soyayya kuwa xamuyi, ba auren ina so baya so ba, saurayine kuma ni kadai a gurin sa mu murji quciyarmu da soyayyar mu son ranmu.

'ashe dama ke macuciya ce, ina tare dake kina cin amana ta kina soyayya da saurayina, wlhy sai na rama.

Da auren naki xaki rama, kinji haushi kenan, ashe ba dadi kika Ma anty jiddah, abinda kika ji a xuciyarki yanxu shi itama taji, abinda kikayi aka maki Allah baxai kamani da laifin cin amanarki ba domin har Yusuf din hana sona.

Wlhy sai kin san kinyi dani daga ke har shi sai na wulaqantaku a garinnan, sai na nuna maki A. I. G na dan sanda nake aure.

'Surry ta dauki jakarta tana fadin, to matar A. I. G idan kin tashi wulaqantamu kisa yasa bindiga ya harbe mu duka, mtsewwwww banxa da bata san ciwon kanta ba ta fice ta bar uwani na kumfar baki sai ashar take durawa.

Jiddah taje ta gayawa halin da ake ciki tunda tace bata san gaibu ba, kafin ta bar gidan, haka jiddah ta aika aka Kira  mata uwani, sai da taga dama taje kiran da qaton casbin ta a hannu tana ja.

'Na kiraki ne inji yanda akayi kikasan gaibu tunda ni ban sani ba uwani,

Tsaki taja a ranta, ta xata wani abin kirkine ashe mgnr da sukayi da surry ce, ta bata fuska,

Ban gane nasan gaibu ba, a ina nayi mgnr,

Inaji surry baxata maki qarya ba, haka kika gayamata, uwani ta dube ta,

Dana gayamata ce mata nayi gobe xaa tashi qiyama ne, karatu ne nace na bari kuma ba shegen da ya isa ya sani?

Nice shegiyar kenan? Jiddah ta tambayeta tana kallonta da mamaki a fuskarta.

Da munafukar da taxo ta gayamiki nake nace ba wanda ya isa yasani karatu bautar aure nakeyi,

Oh shiyasa na ganki da carbi a hannu kina neman gafarar ubangiji,

Takaici ya kama uwani na ganin an canxa mata ma'anar wuridi,

'to ni ba istigfari nake yi ba, jiddah tace hailala kikeyi kenan tunda kince gobe tashin qiyama,

Uwani ta muskuna tana cigaba da Jan carbinta bakinta na mus mus, kafin tace, neman tsari nake daga sharrin mahassada kada a jefeni da wani mugun abin a hanamin xaman aure.

Sarai jiddah tasan da ita take sai ta maida martani da cewa musamman da maqiya sukayi yawa akan auren gashi kuma har da iyayen tunda suma ance harda su suna baqin ciki, Allah yasa kin saka dasu suma ki nemi tsarin su.

Uwani ta dan kalleta, tace ni ban cire kowa ba, kowa da kowa nace.

Shiyasa nima ai nace harda su hajiya ai, kuma miye dalilinki na daina karatu bayan kin fara, ni na dauka ai hutun amarcine kike shiyasa bakya fita.

Tunda ance ni daqiqiya ce ban iya karatu shiyasa na kalli kwanyata da rayuwata nagane Sam babu amfanin karatun a gurina gwanda na tsaya nayi bautar aure na kula da mijina abin sona.

Hakane kam kinyi dabara kuma kinyi rashin wayo na karatunki, da nice keda damarki ba abinda xai hanamin karatun, kuma ba gori nake maki ba duk kudin dana kashe akan karatunki yanxu kina nufin sun tafi a banxa.

Kimin Bill in biyaki in huta da gorin kishiya, kada ya'yana su taso a goranta masu an tallafi mahaifiyarsu, dadin abin nima mijina mai kudi ne xan iya biya.

Jiddah tace ba sai nayi Bill ba ko nawa ne kinfi kowa sani, sai ki biyani idan mijin kuma bashi da kudi sai ki ranta kibani tunda naga mijin naki kullum a rance yake qarewa.

Shiru uwani bata qara magana ba, cika baki ne ba kudin tasan baxata iya biyan jiddah ba, sai ta cigaba da Jan carbin.

Jiddah bata qara bi ta kanta ba ta tashi ta soma gyaran gadon ta, uwani na ganin haka ta marairaice fuska,

'Na ce ba anty jiddah.... Sai tayi shiru, jiddah tayi shiru tana kallon ta yanda taga uwani ta marairaice fuska tasan akwai abinda take nema,

Ina jin ki.

'Dan Allah kima mijin ki magana, ki roqeshi koda baxai kwana a saman gado na ba, ya roqa sake min fuska yana min murmushi, wlhy anty jiddah ko dakina bai taba kwana ba, kuma dai kowa yasan nima fa ina da haqqi akan sa.

*

Pherty....... ✍🏻

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

_ina matuqar qaunarku, haske writers Association._

26

Ke da mijin ki abin son ki har sai kin nemi alfarma gurin masu baqin cikin auren ki?

Ban kawo kuka na dan ayimin fade ba, indai mutum yaci amanata Allah yana gani.

Jiddah ta juya ta cigaba da abinda take tana murmushi, uwani kuwa cigaba da Jan carbin ta tayi tana mus mus mus da baki.

'Angon uwani ashe matar taka ta ijiye karatu saboda bautar aure, ko da yake amaryar Ma tace baka shiga dakin ta ballantana tayi tunanin kwanciyarka akan gadonta, jiddah ta fada tana qoqarin sakawa arham riga, el'mustapha na gefen su.

Kallon ta yayi, Uwanin ce ta gaya maki haka?, ta gyada kai tana kallonsa.

Ina guje maka axabar Allah, domin baka adalci a tsakanin mu, ya kamata ko menene a xuciyarka game da uwani kacire sa daga yanxu, kabata haqqinta tunda har ta fara magana akai.

Kin sani baxan iya rabar wata mace a duniyar nan bayan ke ba, bayan wannan ina matuqar jin nauyi da kunyar na kwana da mace a gidannan kina cikin sa jiddah, ballantana bana son uwani ko kadan, I can't make love with her.

Idan hakane ka sauyamata wani gidan mana, ni dama nagaji da xamanta tare dani.

Xama yanxu kuka fara jiddah tunda kikaji xaki iya, baxan sauya mata wurin kwana ba, amma tunda kin matsa na bata haqqinta xanyi qoqarin cusa soyayyar uwani a xuciyata saboda nayi adalci tsakanin ku.

Idanun jiddah sukayi rau rau, ta dubesa, ka manta a alqawarin mu kace baxaka taba son uwani ba.

Ban manta ba amma ke kike son sakani na karya, maganar karatun uwani babu ruwana aciki adaina sakoni, wait uwani bataga tsakona bane har take mgnr bana shiga dakin ta.

Wane saqo? Jiddah ta tambaya tana kallonsa.

Ina xuwa ya fada a hankali bayan ya diro daga saman gadon, fita yayi aryan yabi bayansa.

Waya take yi lokacin da ya shigo dakin, sakin wayar tayi saboda rudewa kamar ta xura da gudu take ji.

'Ashe idan naxo na kwanta a dakin ki saman gadonki xaki tafi ki fadawa duniya tunda har xaki iya fadawa matata ban taba kwanciya a dakin ki ba.

Kunya da tsoro suka dabaibaye ta,

Look uwani, idan kina shirmenki kidaina sako ni aciki, ni ba sa'ar kibane, saboda na aure ki bashi xai saka kiraina ni ba, idan kika qara min wannan iskanci, bindiga xan sa na dauke kanki naga qaryar ciwon da kike yaudaran jiddah dashi.

Sai a lokacin ta daqo tana kallonsa cikin mamaki,

Ko qarya xan maki, ko kin manta ni dan sanda ne ina da ikon bincike akan komai likitan da kika hada kai dashi shine ya gayamin komai, nayi shiru na kyaleki ban gayawa jiddah ba saboda ina son ta gano kuskuren da ta tabka na yarda dake da baki amanarta harta amince ki auri mijinta, koma menene so nake ta gano da kanta kuma tayi nadamar abinda ta aikatawa kanta.

Shiru uwani ba bakin magana jiki sai rawa yake, iskanci Ma guri gare sa.

Yace inajin takardar dana baki, kin ajiye tane baki duba ba ko?

Tayi xuru tana kallonsa, a ransa yace shegiya mayya sai dai kici kanki, bai qara mgn ba yasa kai ya fice.

Ta soma safa da Marwa a dakin, lallai jiddah ni xata wulaqanta tasa mijinta yaci xarafina, wlhy sai nayi maganin su, kuma baxan karanta takardar ba, bari na kira jamila ita kadai xata warware min yanda xanyi dama itace mai sona.

*

Bayan kwana biyu tunda sassafe sai ga uwani ta fito daure da towel tana gwale qafafuwanta tana yatsina fuska,

Kallonta jiddah tayi a tunanin ko uwani ciwo taji bata sani ba,

Meya same ki haka uwani?

Uwani ta xauna tana yarfe hannuwanta,

Anti jiddah ba ruwan xafi ne na gasa jikina, ciwo yake min, musamman qasan cinyoyina.

Me ya sami cinyoyin suke ciwo?

Sukuwa akayi a samansu, tunda shi kike son ji, in fada kuma kice banda kunya ko kuma kije ki gayamashi, nima yanxu na wuce gorin kishiya da miji nake kwana a daina min kallon bora acikin gida.

Duk da jiddah taji wani abu a xuciyarta bata nuna ba, murmushi kawai tayi tana fadin,

Kina so ki nuna min mijin bai dauke ki da daraja ba tunda baxai iya taimakamiki da ruwan xafi har sai kin fito nema, duniya ta shaida anyi sukuwa akanki.

'Wannan dai bashine na farko ba na talatin ne karki dauka dama baya barci a dakina.

Ai naga alama, jiddah ta fada hade da gyara kwanciyarta, kallonta uwani tayi,

Kada kishi yasa aje a gayawa miji, yaxo yana min muxurai a daki na ko yi maganin mutum a gidannan ehe..... Uwani ta fada cikin jin tsoron kada el'mustapha yaji tunda tasan ko takalminsa bai taba kwana a dakinta ba ballantana shi kansa.

Jiddah shiru tayi mata, uwani ta raina mata hankali, jiya ta kwana da el'mustapha kuma yanxu taxo mata da xancen dakin ta ya kwana har sunyi wani abin, bata san sanda dariya ta subulce mata ba wanda ya sanya uwani yi mata kallon mamaki.

Banan ta shigo da sallamarta, dauke da aryan yana kuka,

Anti jiddah dubi wannan yaron goyonsa yake son nayi, jiddah ta dubeta,

Saboda me baxaki Goya sa ba, banan

'Wannan ai sai ya karyamin baya dama dama arham dai,

'Dan Allah ki goyasa kona minti talatin ne, dauko xani daki na kixo, bana son kina masa wulaqanci banan.

Uwani ta tabe baki Sam ta daina kula yaran, suma sun daina xuwa gurinta tunda take dukansu a boye, ta tashi tayi shigewarta.

Suna tsaka da goyon sukaji sallamar hajiya, ai kuwa da gudu ya diro yayi kanta har arham, jiddah tayi mamakin ganinta.

Hajiya ashe kina hanya ko ki sanar dani, banan kawo mata abinci da lemu.

Hajiya ta xauna tana murmushi,

Munxo gaisuwa da abbanku ne, shine nace bari na biyo naga yanda kuke xaune da yar uwar taki ince dai lafiya,

Wlhy lafiya lau hajiya ba wata matsala.

Ki qara haquri jiddah ki kuma yi haquri tunda ke kikaji kika gani, Allah ya gani banso auren ba kuma bana so har yanxu haka ma abbanku dalilin dayasa yaqi xuwa gidannan kenan saboda kada yaga uwani.

Jiddah murmushi kawai tayi, tace hajiya kayan menene haka,

Tsumi ne na kawo maku keda uwani, ki dauki daya ki bata daya,

Jiddah tace mungode hajiya bari na kira uwani,

Aa barta inje inganta xamuyi mgn ne dama, jiddah ta koma ta xauna, hajiya kuwa ta nufi dakin uwani.

Ko maraba batayi da ganin hajiya ba, tea din ta take sha hankalinta a kwance, hajiya ta xauna tana kallonta.

Uwani baki ganni bane ba gaisuwa.

'Na ganki mana bangama mamakin ganin ki gidan aure na bane?

Da kika ganni gidan auren ki ai ba wani abu naxo nema a gurinki ba, ashe laifi ne uwani dan naxo na duba lafiyarki.

Jikin uwani yayi sanyi, tace kiyi haquri hajiya ni yunwa nake ji shiyasa kika ganni ina shan tea.

Yunwa kuma, ba abinci a gidanne? Uwani ta tabe baki,

Waccan banxar matar ce ta xuba min abinci kadan, hajiya sai ki rantse ita ke siyen sa ba mijinmu ke nemowa ba.

Da dai kina da mutunci ko cokali guda ta baki na abinci sai inga kamar tafi qarfin xagi a wajen ki, ai ko buga baici arxikin komai ba yakamata ya ci na igiya bugu da qari kuma ba Karen kane ya nemo ba.

Wai hajiya tsakanin nida jiddah wa kika Haifa?

Kai tsaye ta amsa mata cikin nuna da gaske take,

Ke na haifa, amma ita riqonta kawai nayi amma ta daukeni kamar wacce ta kawo ta duniya, tana mutuntani da girmama ni.

Uwani tace shiyasa ta sami lasisisin rainani saboda an nuna anfi son ta dani.

An fi sonta din, kuma ana kan son ta bama ni ba har abbanki yafi sonta akan ki, wanda xai iya baki mijinsa ki aura shine xai hana maki abinci, tunda can da kike xaune a gidan bata hana ki abinci ba sai yanxu, maaikatan gidan suka sami wadataccen abinci sai ke matar gida, to uban waye ya hana ki shiga kitchen din ki girka da kanki.

Ni daman nasan gori kika xo kimin kuma kinyi, tunda na auri mijin jiddah duk nayi motsi sai an goranta min itace mai gaskiya, muje xuwa.

Hajiya ta kawar da xancen ta hanyar fadin,  koma dai menene ke kika sani, jiddah ta kirani a waya cewa kin aje boko bautar aure kike ko meyasa.

Eh ai idan an hana ihu baa hana aha, nace ni baxan yi karatu ba, bautar aure xanyi, duk wanda ya dage sai nayi  to kamar ya dage yin asarar yawun bakin sane, lokacinsa da kuma kudin sa, tunda nike karatun ba wani ba, banda munafurci irin na kishiya har an daga waya an kiraki an gayamaki.

Saboda tana sonki da karatun ne ya saka ta kira ga wadanda suka isa dake ashe muma bamu isa ba?

Ni nagane dalilin dayasa matar nan ta dage nayi karatu saboda idan na xama wani abu agaba lokacin ta mutu ya'yanta suci moriyata.

Dukiyar Uban su fa? Ko bakiga a daular da kike xaune ciki bane, kada kiyi karatun kanki xakiyi nadama.

Ba nadamar da xanyi hajiya kune Ma xakuyi nadamar tursasani karatun saboda kudin ku xaku kashe.

Allah ya kyauta, ya kuma shirye ki, ki dawo cikin hayyacinki.

Amin, uwani ta fada tana kumbure kumbure,

Ga tsumi na kawo maki keda jiddah, amma ta dauki nata wannan naki ne.

Kallon tsumin tayi kafin ta dubi hajiya baki a bude cikin mamaki,

Idan ba wani abun ake son hadamin ba saboda me xaa banbance nawa dana jiddah, idan gaskiya ne a hade musha tare mana.

Yaushe kikaji nace kowa nasa daban, guda biyu ne ta dauki daya ta baki daya shine abin cutarwa, taya xaita cutar da abinda na haifa da kaina uwani.

Sau nawa akayi hajiya, idan iyaye xasu iya maka baqin ciki a auren ka menene baxasu iyaba, nikam ban yarda da wannan tsumin ba anga na soma jiki nayi fresh na fara jin dadin gidan mijina yana sona sosai yanxu ake son rabani dashi.

Hajiya bata qara magana ba ta tashi ta fice saboda wasu hawaye da suka xo mata, dakin jiddah ta nufa, kallo daya tayi mata ta gane akwai matsala,

Hajiya dan Allah kiyi haquri indai akan uwani ne, kada kisa xuciyarki cikin bacin rai, kisa abin a ranki yaxo yana damunki, jiddah ta fada tana qoqarin share mata hawaye.

Allah shi maki albarka jiddah, dan Allah ki qara haquri akan uwani idan kika ga abin yafi qarfinki kada kiji komai ki saka el'mustapha ya sake ta ta dawo gida.

Uwani kuwa hajiya na fita ta dauki tsumin ta xuba a pith tayi flushing,

Kar nake kallonku nasan abinda nake ba wanda xai iya cutar dani acikin ku, xama a gidan mijina daram kuma karatu baxan yi ba bautar aure xanyi.

*

After 2 days...

Uwani daukar takardar da el'mustapha ya bata tayi, sai juya ta take amma ta kasa budewa.

Nikam ko menene aciki matarka xan baiwa ita, sai dai ta bar gidan wlhy, Allah kasa saki uku ne aciki da nayi rawar one corner a gidannan.

Kafin ya dawo bari na kaimata takardar, tayi ta bar mana gidan, ta fita da sauri.

'Anty jiddah hutawa ake haka,

Ina hutu ga mai iyali, uwani.

Motsi taji a cikin toilet ta juya tana kallonta,

Waye a toilet din ki anty jiddah,

El'mustapha ne,

'Ashe ya dawo uwani ta fada tana qoqarin tashi cikin dabara ta ajiye farar takardar.

Ki xauna mana,

Aa bari dai na tafi, ta fice da sauri,

Jiddah ta gyara kwanciyarta sai kuma tayi toxali da farar takardar.

Takardar mecece wannan? Ta fada tana qoqarin budewa dai dai lokacin da el'mustapha ya fito toilet daure da towel a qugunsa.

*

Pherty....... ✍🏻

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login