Showing 129001 words to 132000 words out of 138779 words
Chapter 44 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
sakata shirin tafiya, ga mamakin ta sai ji tayi uwani na fadin.
Yanxu anty jiddah shima yusuf xamuyi irin wannan abin da mukayi da yaya el'mustapha kenan,
Cikin rashin fahimta jiddah tace menene uwani.
Tace ai kinsan da mukaje Lagos har jamcy ta bani pills na saka masa a juice, ai sau daya mukayi bamu qara ba, amma yusuf shima sai na saka masa pills dinne?
Subhanallah uwani, wannan abin sirri ne da baa so kowa yaji, tsakanin ki ne da mijin ki, ki riqe sirrin auren ki karki qara fadawa kowa, maganar ki saka masa pills kada na qara jin wannan, kin manta kece mace, shi xai neme ki ai.
Uwani ta washe baki tana fadin, ai anty jiddah hajiya ta bani wani abu nasha, shikenan inajin jikina ba dadi, ya xanyi yanxu.
Jiddah xata yi magana kiran el'mustapha ya shigo, tana dauka ya soma fada,
Ina hanya mijin jiddah, yanxu xan qaraso, baiyi magana ba ya tsinke wayar, sam bata bi ta kan uwani ba ta fice da sauri, a ranta tana tsoro kada su yi wani abu da yusuf uwani taje tana fadawa mutane.
Bayan fitar jiddah uwani taje tana qara duba gidan, taji dadin gidan sosai, taji ta qara son yusuf tunda bai hada ta xama da surayya ba, lallai el'mustapha bai son ta yana mata baqin ciki tunda ya hada ta xama da jiddah.
Tana xaune a falo ta tura masa test,
_cwt ni bana son wannan kaza da ake siyowa amarya, kifi nake so babba mai nama, ko daxu naci naman kaxa a gida bana so, ina ta jiranka tun daxu kayi sauri._
Yusuf ya jima yana karanta message din yana nanatawa, kuma ya kasa nuna wa wani abokin sa saboda nauyi da baqin ciki, kazar ma har sun siye haka ya qara siyen wani kifin daban.
Tana xaune a falo suka shigo tare da abokansa masu rakiyar ango, ba xato yaji uwani ta rungumesa,
Oyoyo mai sona,
Cak ya tsaya, numfashinsa na neman daukewa saboda irin rungumar da tayi masa, abokansa suka bisu da kallo.
Cikin wayancewa suka soma dariya, amma gobe su hadu majalisa akwai tsiya.
Da kyar ya janye ta daga jikinsa, cikin bacin rai yace miye haka? Ganin abokansa sun juya sun fita.
'Anty jiddah tace idan xaka fita na raka ka ina maka addua, idan ka dawo na tarbe ma ina maka oyoyo xaka ji dadi.
Yace haka ta gayamaki tace kiyi a yau a gaban abokaina, ba ko alkunya uwani?
Ka siyo min kifin?
Cikin takaici yace ban siyo ba, yayi shigewarsa, ta bisa da kallon mamaki,
Inba baqin ciki ba miye laifinta dan ta nuna tana son sa agaban qawayenta?
EL'MUSTAPHA
Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers
Fertymerh Xarah๐
68_69
'Ta bi bayansa tana tunxuro baki,
Kai tsaye dakinta ta nufa a tunanin ta nan ya shiga, wayam babu shi, batare da tunanin komai ba ta nufi toilet din ta wai neman sa take.
Fitowa tayi tana kiran sunan sa,
Yusuf.. Yusuf, ina ka boye ne, meyasa kake guduna?
Bata ji ya amsa ba, sai ta nufi dakin dake kusa da nata, da alama nan ne dakin nasa.
Yana tsaka da cire dogon wandon shaddar sa ta shigo, xuba masa idanu tayi ganin babu riga a jikinsa.
Ya rage daga shi sai gajeran wando a jikinsa, ya juyo yana kallonta cikin mamaki sam bai san da shigowar ta ba, yanda ta xuba masa idanu ya saka shi jin kunya, sai ya soma kokarin kare jikinsa cikin mamaki wace irin macece wannan yarinyar.
Uwani kuwa tana kallon sa ne tana tuna El'mustapha, sai take ganin yusuf yaro ne akan el'mustapha, bata manta fadin qirjinsa dan bata iya tsayuwa ma ta kalle sa kamar yanda take kallon yusuf a yanxu.
Ta sami guri ta xauna tana cigaba da kallonsa,
Yana qoqarin saka doguwar riga ya kare jikinsa sai wani tunani yaxo masa, idan ita bataji kunyar kallonsa ba saboda me xaiji kunyar rufe mata jikinsa, sai ya cire rigar ya ajiye, da gangan ya soma qoqarin cire gajeren wandon dake jikinsa ya gani xata dauke kai ko me.
Uwani na ganin yana qoqarin cirewa ta qara tsura masa ido, idanunta na kan yanda xata ga abin nashi so take ta gani ko irin ta el'mustapha ce, har wani murxa ido take yanda xata gani da kyau.
Gabansa ya tsananta bugawa, ko surayya da suka haihu da ita bata taba qoqarin gwada hakan tare da shi ba, ya kasa cire wando yayi tsaye kamar statue yana kallonta cikin tsananin mamaki.
Uwani ta dube sa tana murmushi bata yi magana ba, shima juyawa kawai yayi ya nufi toilet.
Har ya fito wanka uwani na xaune gurin,
Tace wanka kayi, Allah yasa kayi alwallah muyi sallah, na qagara naci kifina na kwanta tun daxu shi nake jira.
Baiyi magana ba, uwani ta cigaba da fadin,
Baka kyauta min ba kayi wanka kai kadai bada ni ba, Anty jiddah ai tare take yi da mijinta, ko xamanin su abba tare yake yi da hajiya nasani sai ni da kake wa baqin ciki da samun lada, ba komai na yafe ma haqqina amma gobe ni xan ma.
Wani tunani yusuf yayi kafin ya juyo yana kallonta,
Je kiyi wanka kixo ina jiranki magana xamuyi.
Ta tashi tana murmushi, ai nasan ka matsu dani kai dai kace kana so mu kwanta ba wata magana da xamuyi, ta fita da sauri ya bita da kallo baki a bude.
Bata jima da fita ba ta dawo da kayan barci a hannunta kusan Kala uku ta xube a gabansa.
Nifa baxanyi wani wanka ba, ai kafin muxo nayi wanka ka kira gida ka tambaya kowa yasan ni ba qaxama bace, xaba min kayan da kake so nayi ma kwalliya da su saboda na faranta ma, ance farin cikin ka shine nawa, baqin cikin ka naka ne kai kadai danni bana son abin baqin ciki.
Kallonta yayi kafin ya maida kallonsa ga kayan da ta xube a gabansa, hannu yasa yana daga kayan d'aya bayan d'aya, wata riga ya dauka qarama mai kyau iyakar ta cibiya, sai qaramin wandon ta iyaka cinya,
Ta yatsina fuska tana kallon kayan, su kake so?
Ya gyada kai yana kallonta tunaninsa ko xatace baxata iya sakawa ba sai ganin yayi ta soma qoqarin cire kayan dake jikinta anan gabansa,
Da gaske baxakiyi wankan ba?
Nifa baxan yi ba, sai kace wata agwagwa, idan nayi yanxu fa sai nayi da safe, so kake fatar jikina ta kode a banxa ta fara warin ruwa, shiyasa ai kaga anty jiddah bata qiba kullum take ramewa yawan wanka ne da takeyi ruwan ke cin jikinta ita tana so ta birge miji kullum cikin wanka sai kace yar ruwa.
Yaja numfashi yana fadin, tunani na uwani a yanda abba yace lamarin naki yayi sauqi ban dauka haka xan same ki ba, xaman da mukayi dake a farko nayi haquri dake sosai kowa ya sani daga baya kika guje ni...... ta katse sa,
Kace gori kake min saboda ka aure ni yanxu, ni dama na dade da sanin ka aure ni saboda ka ci mutuncina na yaudare ka a baya, amma baka min adalci ba wannan ba so bane.
Yace if I can't control you tabbas baxan iya xama da ke ba uwani idan har baxan iya saka ki kiyi ki bari ba, ko na fada maki kiji kiqi ji ba, idan babu biyayya a auren mu babu amfanin xaman mu tare, bana jin ta halin ki saboda tun farko na sanki haka da abin ki, na dauka abin naki yayi sauqi ashe babu wani sauqi a tare da ke, baxan iya xaman aure dake a hakan ba uwani idan har baxaki nutsu ki dawo cikin hayyacin ki ba.
Hankalinta ya tashi sosai, tace kada kamin baqin ciki yusuf kasan ina son ka, bana so na rabu da kai, yanxu idan ka sake ni anty jiddah xataji dadi qila harda Party xatayi, baka san akwai yan baqin ciki a auren nan namu ba, kamar su Sumee, Serdia, Ummy fingers, Ayusher, habeeba,ย da Ummy koko ba, ka barsu da baqin cikin su, tunda kace nayi wanka xanyi kome kake so xan maka kada ka rabu dani kaji mijina.
Bai yi magana ba illah idanu da ya xuba mata, ta tashi da sauri ta dauki kayan ta fice tana fadin bari naje nayi wanka, ni ko a tsakiyar dare ne ka tadani xan maka girki dan na maka biyayya, ni bana maka baqin ciki da jin dadi a rayuwarka.
Tana fita yaja numfashi tare da girgixa kansa, wayarsa ya dauka ya kira surry, tunanin sa baxata daga ba, yanda yaji muryarsa ya tabbatar masa da tayi kuka.
Kin qara yin wani kuka ne surayya?
Da kyar tace aa,
Amma muryanki ya nuna hakan, why? Kin manta maganar da muka yi dake.
Tace yanxu yusuf uwani ce matarka, kana tare da uwani, kuma tare xaku kwana a yau ka barni ni kadai, kace mafarki nake yi dan Allah yusuf, sai ta fashe masa da kuka.
Jikinsa yayi matuqar sanyi sosai kafin yayi magana ta kashe wayar, ya kira wayar taqi ta dauka har ta tsinke, ya sake gwada kira yaji ta switch off.
Shigowar uwani ta katse masa tunanin da yake, tana sanye da hijab, ya tashi ya xura doguwar jallabiyar sa, ya ja su sallah.
Bayan sun kammala komai ya dauki ledar kifin ta ya bata yana fadin kije falo kici kifin bana son warin sa.
Ta tashi ta fita da sauri yawunta sai tsinkewa suke saboda kwadayi da ganin kifin.
Haka yabi lafiyar gadon ya kwanta cike da kewar sahibar sa surayya,
Uwani kuwa taci kifi iya cinta komai bata rage ba, kaf ta cinye, ta Kora da ruwan lemu, sai da tayi gyatsa kana ta tashi tana fadin, Alhamdulillahi Allah nagode maka da ka rabani da gidan baqin ciki ka kawo ni gidan mijina na gaskiya, komai nace yayi min yana min, Allah ya kare shi daga idon maqiya su ummy fingers da aysher barmo, Allah ya kare shi daga sharrin masu sharri da masu baqin cikin auren nan, kasa duk wacce taxo tamin snatching din sa bakinta ya koma kamar na karya, ta riqa magana kamar kukan jaki, ka maida idon ta daya a rufe irin na munafukai, amin summa amin, ta tofa addu'ar a tafin hannunta ta shafe fuskarta.
Taje ta wanke hannunta sosai yanda baxaiji warin ba, tayi brush ta qara nufar dakin sa, (wai ni inda amarya ke bin ango dakin sa daren farko๐ค)
'Ashe har ka kwanta shine baxaka jira ni ba, yayi mata banxa.
Ta kwanta bayansa tana shige masa a jiki sai washe haqora take yau gata kwance da mijinta itama.
Yayi shiru yana sauraren ta, sai ji yayi ta rungumosa tana fadin, ni ina so kayi min wannan abun ne.
Da kyar yace wani abu kuma,
Tace in baka iya ba, ka kira el'mustapha ya koya maka shi kam ya iya sosai.
Yaji wani haushi, ya dube ta yana fadin idan muna tare dake kada na qara jin kin kiramin tsohon mijinki, ya soma qoqarin janye ta, ta qanqame shi tana fadin, ni sai kayi min xan kyale ka๐จ.
Yusuf tashi yayi yana cire kayan jikinsa, duk da acikin duhu ne bai hana masa hango yanda take wiqi wiqi da idanu ba, da alama a tsorace take cika baki ne kawai ai kuwa xaiyi maganinta.
Tana ji ya soma cire kayan jikinta, har tana taya sa ma ๐คฃ,
๐๐ปโโ๐๐ปโโ๐๐ปโโ
Yusuf ya kasa yardarwa kansa cewa uwani ba budurwa bace, har ya kasa haqura a karo na biyu ya sake yi, uwani ta tsine masa harda sakin sa๐, wani abin ma idan ya tuna dariya yake basa, yanda itace ta far nemansa da abin tun baa je ko ina ba ta soma bashi haquri tana kuka, uwani a wannan fannin bata da jarumta kamar surryn sa.
Tun bayan sallah asuba bnda barcin wahala ba abinda take, harda su minshari da alama harda gajiya a tare da ita.
Murmushi kawai yayi yana kallonta, ashe akwai ranar da xai mallaki uwani da komai nata, tabbas matar mutum kabarin sa ya yarda da wannan.
Ji yayi ana buqa qofar falon nasu, da sauri ya fita gudun kada a tada masa ita daga barci๐ฏ,
Yaro ne surayya ta aiko da breakfast ya kawo masu, yusuf ya karba yana murmushi,
Ka gaida ta kayi mata godia, Allah yayi mata albarka.
Yaron yace amin ya fice.
Tun bayan tashin uwani take tunani, yanda yusuf ke ta rawar kai da ita abinda el'mustapha bai mata ba, lallai ta yarda baya son ta baya qaunarta, ta tuna wahala da axabar da el'mustapha ya bata a sau daya da yayi amma yusuf ko kwatan kwancin wahalar bai bata ba duk da sau biyu yayi mata, ita yanxu baxata manta ba sau uku akayi mata amma na el'mustapha yafi xafi, lallai anty jiddah tana qoqari da shi.
Yusuf ya tambayeta xamantakewar ta da el'mustapha hala bai taba kasancewa da ita ba.
Tace yayi min sau d'aya ku.... ya katse ta, shikenan basai kin qara ba, xo ga breakfast surayya ta aiko mana.
Ta yatsina fuska, tace ni baxan ci abin hannun kishiya ba, waya sani ko ta saka min magani a ciki dan ta rabani da kai.
Ya bata fuska sosai, surayya matata ce, ina sonta sosai bana son na qara jin kin jefeta da wata kalma marar dadi, ki girmamata ki so ta idan har kina so xaman mu dake yayi kyau, maxa matso kici abinci.
Ta matsa tana tunxure baki.
Sanda yaxo fita taxo raka sa ta tsinkayo vespa dinta a kusa da motar sa,
'Yauwa kabari naje na kaika da vespa dina, ai na iya tuqashi tuntuni.
Ni na hau wannan vespa din, Allah ya sauwaqe min, kuma kada ki kuskura ki hau sa ki fita wlhy.
To miye amfanin siyen sa idan bana fita dashi, ko xan ajiye sa ne ina ta kallonsa haka, kasan yanda nake son abu na kuwa.
Yace duk yanda kike son sa bai kai son da nake maki da kare mutuncin ki ba, kudin da kika says vespa din ki gayamin ni xan siye na baki kudin amma bana son ganin ki dashi.
Kai haba, bana saidawa bane, idan kana so ka siya kaje kasuwa, amma wannan ina son abuna, har training nayi masa fa.
Ya tabe bakin sa ya nufi motar sa, taje taja vespa din gefe har masa kiss kafin ta nufi inda yusuf yake,
Cwty Allah ya kaika lafia, kayi min addua Allah ya rabani da yan baqin ciki.
Murmushi kawai yayi yana tada mota, uwani kayan Allah ya lura bata da magana sai ta baqin ciki a rayuwarta.
Bayan wasu awanni jiddah taxo gidan da kuyangunta as usual kun san su๐คช
Uwani ta rungumeta cikin farin ciki,
'Anty jiddah ai naji dadi da kika xo da har xanxo fa akan vespa dina idan nayi wanka xuwa anjima,
Kinga yusuf jiya da dare sau biyu yayi min fa, abinda ake sau d'aya, kuma yanda yaya el'mustapha yayi min ba haka yayi min ba, yaya el'mustapha ya taba min nan ya taba min nan naji dadi amma shi bai min ba, kuma yaya el'mustapha y..... tayi shiru sakamakon bige mata baki da jiddah tayi iya qarfinta cikin bacin rai, sai ga jini a bakin uwani.
Ban gaya maki jiya sirrin ki da mijin ki kada ki bari kowa ya ji ba,
Cikin kuka tace amma ke ai yar uwata ce kakan mu daya fa saboda me xan boye maki.
Tace ko ni uwarkice bai kamata ki gayamin ba, har kina nuna kinfi jin dadin el'mustapha da yusuf ko, ashe baki da hankali uwani, da wani ne yaxo bani ba shima duk xaki gaya masa wannan labari.
Amma anty j..... Yimin shiru shashasha, dama abba ya bani saqo wlhy duk baki gyara rayuwarki da wannan shegen bakin naki ba xai xo ya dauke kine ya raba ki da yusuf ya hada ki aure da malamin ku dama shine dai dai ke.
'Anty jiddah kiyi haquri baxan qara ba kada ki gayamasa.
Kuma dama Malam guzuma abba yayi magana da yusuf xai xo yacigaba da karantar dake anan yana kula da takunki duk kika yi ba dai dai ba ya hukunta ki kamar da, yanxu haka xaa nema masa islamiya anan garin saboda ke.
'Na shiga uku ni uwani jikar sarki merah, wallahi xan nutsu anti jiddah, komai bakuso xan daina harda magana Ma amma kada ku kawo shi nan gidan dukana xaiyi.
'Wannan ya rage naki, harda fadin ana maki baqin ciki duk baki daina fada ba an bashi dama ya daki wannan bakin, da maidawa mutane magana, da rashin tarbiya duk xaiyi maganin ki.
Ki xauna ki kula da mijinki kinga kina da kishiya, ki kyautata masa ki masa abinda xaiji dadi wanda xai saka shi son kasancewa dake sannan ki boye sirrin ku kowa kada ki fadawa, in ba haka na Allah xai yi fushi dake sosai.
Sannan dan Allah uwani ina roqon ki kada ki maimaita abin da kika yi a baya kiji tsoron Allah kiji tsoron Mahaliccinki, ki tuna akwai mutuwa akwai hisabi, ki tuna akwai kwanciyar qabari ki tuna baxaa tabbata a duniya ba jin dadin ta kadan ne xai xo ya wuce, kada kiyi wa surayya abinda kika min, ki riqe ta da hannu biyu ki sota ki mata biyayya kada ki cutar da ita saboda bata da niyar cutar dake uwani dan Allah.
Cikin kuka uwani ta riqo hannunta, tana fadin baxan yi ba anty jiddah, babu