Showing 84001 words to 87000 words out of 138779 words

Chapter 29 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

2015

kayi haquri na tuba na bi Allah, ka yafe min kabarni na shigo naji dadin da kowace d'iya keji a gidan ubanta dan Allah abba kayi haquri.

Bai saurare ta ba ya shige hade da rufe gate din,

Tayi shiru tana kallon sama yanda ake ta xuba walqiya, ta xauna tana dafe cikinta, yunwa take ji amma ya ake so tayi tunda ba sata xata je tayi ba ko bata.

Tana xaune a gurin ruwa masu qarfi na fara saukowa, ta rakube guri daya da alama harda sanyi tana ji sai sharar kwallah take, wata wahalar ni najawa kaina ko yanxu na gane kuskure na, da ynxu ina can tare da anti jiddah ina cin dadi na kwanta cikin AC Allah sai ya sakamin baxan taba yafewa jamcy ba.

Ance d'a da mahaifi sai Allah, ya kasa samun nutsuwa sai tunanin uwani yake da halin da take ciki,

Abinda tayi kuskure ne ta riga ta aikata idan yayi laakari da shekarun ta kuma qaddara tana kan kowa, musamman idan yayi dubi da kowacece uwani kamar hankali bai ishe ta ba.

Tana aikata komai nata batare da tunani ko neman shawara ba kawai abinda yaxo ranta shi xatayi ba ruwanta ko xai baci ko xai gyaru burinta kawai ta biya buqatar ta.

Idan ya Kora ta tabi duniyar alhakinta na kansa kuma yana da kamashon lalacewar ta saboda macece kuma qarama mai rauni, ba abinda uwani ta cancanta kamar addua shiriya kuma yana qara roqon Allah ya shiryeta ya gyara ta yasa tuban da tayi har acikin xuciyar tane.

Umbrella ya dauko ya fito sosai ake ruwa, yana bude gate din ya ganta tsugunne a gurin ta rakube sai makyarkyata sanyi take,

Jin alamar bude gate din ya saka ta dagowa tunanin ta mai gadin ne ke leqenta tayi masa rashin mutunci, suna hada ido ta tashi da sauri,

Tausayin ta yaji, yar'su kwaya dal a duniya haka Allah ya rubuto da tata rayuwar, Sam uwani bata da nutsuwa, baiyi magana ba ya juya tana ganin haka ta shiga gidan harda rufe gate din,

Bayansa tabi tana fadin,

'Ashe dai abba kana sona, ai nayi tunanin xaka barni acan ne ruwan ya kashe ni, irin kune ake gani a aljanna ayi mamaki baa san tausayi ne da ku ba.

Kyaleta yayi baiyi magana ba, yana ganin sai an kai uwani asibiti an duba masa kwakwalwar ta.

Ta tsaya tana matsar kayanta har lokacin jikinta bai daina rawar sanyi ba,

Ta shiga falon tana kallonsa,

'Abba yanxu dai ka yafe min saura hajiya da anti jiddah, shi el'mustapha baxan roqe sa ba saboda yaci amanata ya kulleni a prison kuma ya harbeni a qafa banda ibrahim da yanxu ta fara wari ancire.

Shiru baice komai ba, sai kallonta yake cikin jimami,

Wayarsa ta dauka tana fadin abba bari nayi selfie da wannan kayan da datti saboda daga yau baxan qara xama acikin su ba, hassalima kayan meenah parrot xan baiwa su ko khadija candy.

Yana kallo ta fara daukar pic harda bashi wai ya dauke ta....

Tana gamawa dakinta ta nufa, ta jima sosai a ciki ta fito sanye da kayan barci bayan tayi wanka,

Yana xaune yana kallon news,

'Abba ni inajin yunwa kamar xan mutu, hanjina sai xafi suke suna bugun juna tun daxu.

Yace ai kinsan hanyar kitchen bana tunanin kin manta,

Har xata je sai kuma ta dawo tana kallonsa,

Wai ina hajiya ne abba hala dai bata ji dadin dawowa ta ba shiyasa Ma ta kasa fitowa?

Hajiya taje Germany,

Uwani ta xube qasa cikin firgici,

Germany abba, waye ya kaita?

El'mustapha ya bata amsa yana kallonta, sun je ayiwa jiddah aiki a qafar da kika nakasa.

Ta hadiye wasu yawu, wannan ba shine damuwar taba,

Tace yanxu abba kana nufin hajiya ta shiga jirgi kenan, innalillahi amma meyasa xaa min haka, ni nafi cancanta aje dani meyasa ake min baqin ciki ne, ta soma kuka kamar ranta ana mata baqin ciki da shiga jirgi banda haka meyasa baa jira ta ba ko anje an nemo ta.

Shiru yayi yana kallonta, shi dai yasan ba wannan ne karon farko da hajiya ta shiga jirgi ba ballantana uwani ta tada hankali, sunje Makkah sunje umrah to kwadayin me hajiya xatayi wa jirgi banda fitina ta uwani da rashin kunya har tana cewa aje da ita jinyar jiddah.

Shikenan abba babu komai tunda na gyaru, ina so a maidani makaranta, Cairo ko London ko sudan.

Yace ke me xakiyi da karatu keda babu abincinki aciki kuma kwakwalwarki baxata dauki karatu ba.

'Abba ka daina tuna baya wannan duk baqin cikin shaidan ne da sharrin xuciya, tuni na hango akwai abincina a karatu, akwai arxikina a ciki, nifa abba ina ji a jikina nan gaba first lady xan xama shiyasa har islamiya nake so ka sakani ko a aji daya ne xan xauna, ina so nayi ilimi saboda ya'yana kuma xa kuyi alfahari duk inda kuka shiga ana nuna ku ana ga iyayen uwani first lady 😊.... Bai bari ta qarasa ba ya tashi ya bar falon cike da haushi.

Ta bisa da kallo kafin ta tabe baki, wato har yanxu baa daina mata baqin ciki ba, ina laifin ta xama first lady ai abin alfaharin su ne.

Ta tashi ta nufi kitchen tana yan surutai, cornflakes ta gani babu batun cin abinci an dade baa hadu ba,

Qaton Cup ta dauko da spoon ta shiga neman inda aka ajiye madara.

*

Kallonsa dr merah keyi yana observing din sa, halayen el'mustapha suna burgesa sosai, akwai soyayya mai tsanani tsakanin sa da jiddah ba sai an baka labari ba kaida kanka xaka gano hakan.

Ya dafe kansa da duk hannayensa biyu cikin damuwa, meya hanata farfadowa, why ya fada a hankali yana Jan numfashi.

El'mustapha ya dago yana kallonsa daga cika wata takarda da yake, ya ajiye biron yana fadin.

Thanks once again Dr Aiman Merah,

Dr merah yayi murmushi yana miqa masa hannu,

Can we be friends?

El'mustapha bai bashi hannu ba kallonsa yayi yana fadin,

Xaka iya abota da d'an sanda ba jinin Mulki ko Sarauta ba?

Of course ya fada yana kallonsa, I have alot of friends like you,

Murmushi el'mustapha yayi kafin ya bashi hannu,

El'mustapha ya juya ya fita yana fadin ina jiran ka insha Allah yau xamu koma qasar mu da gawar jiddah.

Jiddah na kwance har lokacin idanunta a lumshe, jin alamar bude qofar ya sakata bude idanuwanta a hankali carab suka hada ido,

Kusan rudewa ko ince gigicewa yayi, ya rasa ina xai nufa ciki ko waje, jiddah ce ko dai fatalwarta ke mata gizo, shi ko fatalwarta jiddah ce yana so xai iya xama da ita, koda babu jiddah ya xamto ruhinta yana tare dashi,

Da sassarfa ya isa ciki har lokacin bai dauke idanunsa akan taba, sai kallo jiddah ke binsa da shi na mamaki.

Hannu yasa ya taba ta baiyi magana ba, ya qara riqo hannunta ya kai bakinsa ya ciza don son gasgasta jiddah din ce ko fatalwa.

'Wash Allah ta fada a hankali tana qoqarin xame hannun ta,

Ya rasa me xaiyi saboda tsananin farin ciki, sai kawai ya sami kansa da yin sujjada a gurin yana qara godewa Allah kafin ya taso ya rungumeta tsam a jikinsa yana sauke numfashi da sauri da sauri,

Jiddah is back, jiddana bata mutu ba I know, ya fara sumbatarta ta ko ina cikin rudewa kamar wanda xai maida ta ciki.

Shiru tayi tana sauraren wannan sabon al'amari daga el'mustapha, tasa hannu da kyar ta riqo fuskarsa tana kallonsa dai dai lokacin dr merah ya shigo tare da su yusrah da hajiya da nurses a bayansa.

Cak suka tsaya suna kallon ikon Allah cikin tsananin mamaki, jiddah ta janye jikinta tana qoqarin kwanciya el'mustapha sai qara rungumarta yake,

Dr merah da mutanen sa suka koma baya, anty yusrah sai washe baki take cikin tsananin farin ciki ita da su hajiya.

Qafata ciwo take el'mustapha ka barni haka,

Ya bude idanunsa a hankali yana kallon qafar, kafin ya dubeta,

Ina son ki jiddah cikin kowane hali, ko da qafar ko babu, ki rayu tare dani jiddana.

Murmushi tayi tana fadin, nima ina son el'mustapha cikin ko wane hali, son da ban taba yiwa kowa ne mutum a duniya ba bayan ummata.

Ya gyara xamansa, hannunsa na cikin nata  sai murmushi yake kamar wanda akayi wa albishir da gidan aljanna,

'Me na haifa el'mustapha?

'Har kin manta kenan, bayan kin bar yarinya sai kuka take tana son jin dumin mahaifiyarta.

'karbo min ita na ganta....

'ba yanxu ba kiji dani tukunna, nafi ta buqatar ki jiddah.

Taja hancinsa tana murmushi,

Yanda kace haka xaa yi mijin jiddah,

Yace yauwa jiddatulmusty, sai kuma yayi murmushi ya tashi yana fadin bari na karbota jiddah nasan kinfi buqatar ta dani a yanxu.

Ta bisa da kallo tana murmushi....

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

52

Bayan kwana biyu, jiddah ta warware sosai sai dai rashin kuxarin jiki,

'Anty ikram Ma sunxo tare da wani kawun jiddah.

Sosai dr merah ke kula da jiddah musamman qafarta, sun xama friends da el'mustapha ko da yaushe suna tare a office, har yake baiwa el'mustapha labarin sa da Afiya.

Hajiya bani ruwan tea na sha, cewar jiddah tana kallon ta,

Hajiya ta tashi goye da jaririyar ta hada mata bayan ta xauna kusa da ita,

Magana xamu yi jiddah ta fahimta, bana so naga abinda xai cutar dake ko kadan.

Jiddah ta tattara hankalinta da nutsuwar ta tana kallonta,

Hajiya tace meke tsakanin wannan yar aikin taki da mijinki?

Jiddah ta qara kallonta cikin faduwar gaba tana bude idanuwanta, ta ajiye Cup din tea tana fadin, me kika gani hajiya?

Tambayar ki nake yi kibani amsa,

Cikin rawar murya  jiddah tace nima ban sani ba hajiya,

Ba ina gayamaki bane dan ki tada hankali ki, amma kisani wannan karon ko mutuwa xakiyi baxan taba yarda ki aurawa wata mijinki ba, tun da na lura ke Sam baki san ciwon kanki ba sai haquri, ina ji ranar da xaa shiga dake aiki har kina bata amanar ya'yan ki da mijinki, meke damun kine jiddah.

Jiddah tace hajiya banan tana da kirki bana xaton xata cutar dani ko wani nawa shine dalilina na bata amanar yarana, amma maganar el'mustapha cikin xafin ciwo ne ban san na nata amanar sa ba kuma ba wai ina nufin ta so shi ba hajiya.

Koma dai menene na riga na gano banan tana son mijinki, kuma kinji na gayamaki wannan karon baki isa ba, kuka taso da uwani tun kuna yara ta cutar dake ballantana wata bare,

Jiddah taja numfashi a ranta tana cewa hajiya baxata gane ba wani bare yafi dan uwa kuma ba duka aka taru aka xama daya ba.

Amma hajiya meyasa kika ce tana son el'mustapha, ni na dauka shine kadai ke son ta.

Hajiya ta xare ido cikin mamaki, tace kina nufin wai el'mustapha yana son banan? Ya akayi kika yi wannan saken jiddah, taya xaki reni yarinya da hannunki ta aure maki miji, wai ke meke damun ki ne, wace irin mutum ce ke, ban taba sanin wata mace mai hali irin naki ba jiddah, kin fiye tausayi da sanyin xuciya wanda shine ke cutar dake kuma shine ya kawo ki matsayin da kike a yanxu.

Jiddah ta soma kuka tana fadin, ba laifina bane hajiya, bansan yaushe ya fara son ta ba, nagano hakan bayan dawowa ta daga batan da nayi kuma el'mustapha ya rantse min babu soyayyarta a xuciyarsa sai dai ban sani ba akan ita banan.

Hajiya tace to bari kiji ban san komai akan gidan ki ba amma a waya da naji banan nayi na fahimci komai, kin bata auren qanin aminiyar ki, tana waya naji tana bashi haquri akwai wanda take so tuntuni kuma yanxu tana da tabbacin xata same shi amma ya rufa mata asiri kada ya gayamaki dan bata son fushin ki ko kadan.

Bansan me yace da ita ba naji tana roqonsa da magiya cewa xai iya haqura da ita har ya sami wacce ta fita.

Ban taba kawo el'mustapha take so ba sai a jiya da dare, ta kwana kiran el'mustapha a barcinta wataqila ma yusrah ta ji ta ban sani ba, yau da safe ban mata mgn ba amma daga irin kallon da take wa el'mustapha daban ne da wanda take mana, na lura duk inda yayi idanunta na kansa bai Ma san tana yi ba.

Jiddah ta dafe kanta, innalillahi ta fada a hankali, sai ga hawaye, ta dubi hajiya cikin kuka,

Meyasa suke son el'mustapha, meyasa suke son mijina, menayi masu suke son raba ni dashi?

Taya xanyi na sani jiddah, bansan mu'amalar ki dasu da shi a gida ba, uwani bata bani mamaki ba kamar banan saboda uwani tun kafin ki auri el'mustapha ta furta tana son sa, amma banan taya xata so mijinki bayan kece kika riqeta kuma yar aikin ki, ya akayi ta sami kusanci haka da el'mustapha, kina sakaci da gidanki da mijinki jiddah, samun miji a wannan xamanin kamar el'mustapha sai an tona, bako wane namiji xai iya maki halacci irin wanda el'mustapha yayi maki ba, ki so shi da xuciya daya kuma ki rungumeshi da hannu biyu ban isa na hana mashi qara aure ba amma kam ba banan ba na gayamaki gsky tun yanxu, idan uwani ta maki ciwon qarya ta ci galaba akan ki wannan karon ko ciwon mutuwa banan xatayi a gabanki baxata taba auren el'mustapha ba.

Ta tashi a fusacce xata fice, jiddah tayi saurin tsaidata

Hajiya laifina kike gani, Wlhy ko a mafarki baxan bar el'mustapha ya auri banan ba ballantana a xahiri, idan banan tace tana son el'mustapha taci amanar yarda da ita da nayi, na bata amanar ya'ya na bawai ina nufin ta auri el'mustapha ba, ko da nace mata el'mustapha ko Islam Allah kadai yasan mijin auren ta saboda a lokacin inajin kamar baxan rayu ba amma ban taba kawo banan xata so mijina ba, hajiya ya xanyi ba banan ba ni bana son kowace mace ta kusanci el'mustapha koda da murmushi ne.

Hajiya tace kisha tea din tukunna har ki sami lafia xamuyi maganar,

'Na kasa sha hajiya, hankalina ya tashi yanxu ina banan din da el'mustapha..... Bata rufe bakinta ba el'mustapha ya shigo, bayansa banan ce da anty ikram.

Ta xare idanu tana kallonsu cikin faduwar gaba, el'mustapha kuwa kallon hajiya yayi yana kallon jiddah cikin mamakin kukan me jiddah keyi.

Kafin yayi magana anti ikram ta xauna tana fadin,

Jiddah xuwa gobe da safe xamu koma tare da yusrah da yayan ki, tun da jiki alhamdulillah kin sami sauqi sai fatan Allah ya tada ki lfy.

Abinda ya fito bakin jiddah ya bawa kowa mamaki ba ma kamar banan.

Tace anti ikram idan xaki koma kuje da banan, hajiya xata kula dani.

'Anty jiddah me..... Wani kallo da jiddah tayi mata ya saka ta rufe bakin ta ba shiri abinda bata taba yi mata ba, kada dai jiddah ta gano tana son mijinta da ta shiga uku.

Hajiya tace aa jiddah baxaa yi haka ba, kibar banan ta.... ta katse ta,

Banan xatabi su anty ikram Nigeria, umarni ne ba shawara ba.

El'mustapha na tsaye baice komai ba sai kallon jiddah yake yanda ta sauya lokaci daya,

'Anty ikram tace banan tayi maki wani laifine jiddah? Duk suka xuba mata ido,

Tace aa ta koma saboda su twins, bama haka ba ta dai koma hajiya is ok.

Banan taji kamar ta rusa ihu a gurin, har wani xufa take, meyasa jiddah xatayi mata haka na nisanta ta da el'mustapha, karo na farko da ta soma jin haushin jiddah a xuciyarta tun xaman su.

Hajiya bata qara magana ba ta juya ta fita, ikram Ma fita tayi tana amsa waya,

Banan ta dubi el'mustapha dai dai lokacin shima ya dago yana kallonta,  jiddah na kallonsu, bugun xuciyarta ya tsananta,

El'mustapha ya xauna baiyi magana ba amma yana son sanin dalilin jiddah na cewa banan ta koma bayan tana qoqari sosai akan ta.

'Anty jiddah idan laifi nayi d...... ta katse ta a fusacce,

Get out pls kuma kisani ko kinqi ko kin so Islam ne mijinki idan har baxaki aure shi kafin nadawo kibarmin gidana.

Banan ta soma kuka a rikice, ni anty jiddah yaushe nace bana son sa wlhy qarya yake min idan shine ya gayamaki hakan, dan Allah kiyi haquri kada ki maidani, ina son xama dake bani da xabi sai naki ki yarda dani.

Jiddah tace na riga na gama magana kije kawai, idan kina ganin auren ki da Islam na cutar dake ne Allah ya na gani, kuma wanda kike so a yanxu baxaki taba samun sa ba gwanda ki rungumi Islam shine kyautar da Allah yayi maki ko banxa Islam ba ajinki bane kima godewa Allah.

Banan bata qara magana ba, amma kalaman jiddah na nuni da kamar ta gano tana son El'mustapha, idan kuwa hakane dole ta nisanta kanta da jiddah kamar yanda ta buqata harta sauko, ta fita da sauri tana kuka.

Shikam el'mustapha na xaune baice komai ba amma ya rasa wannan xafin da jiddah ta dauka akan banan, yayi shiru,

Dole xakayi shiru ka shiga damuwa saboda na Kore abinda kake so, na riga na gama fahimtar ku, kuna munafuntata a bayan idona..... Shut up jiddah, ya katse ta cikin tsawa,

Ok... Ok saboda wannan dalilin you are sending banan away from you

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login