Showing 114001 words to 117000 words out of 138779 words
Chapter 39 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
ba, tsab xata kashe ni, tun a yanxu ta hanamin sukuni tana bibiyata a barcina.
Yace kin dai saka abin a xuciyarki ne, kiyi addua ki kwanta.
'Washe gari ya nufi jiddah da mgnr,
Kallon sa tayi da murmushi a fuskarta,
Baxan ce komai ba a yanxu yusuf sanda na nema mata auren ibrahim akace na so kaina, ina mata baqin ciki da komawar ta dakin el'mustapha, ni kuma bana daya daga cikin masu yiwa uwani baqin ciki kamar yanda take fada, ba abinda xance illah addua Allah ya xaba mata mafi alkhairi.
Yace aa anty jiddah kinsan yanda xaki taimaka min, yayana bashi da matsala kamar yayar mijinki, yanxu da ta furta baa yi tabbas yayana xai dauki maganar tane saboda yana ganin tafi shi sanin wacece uwani tunda ta auri qanin ta dan haka baxai amince da ni na aure ta ba.
Idan ta wannan ne duk mai sauqi ce yusuf xan Ma el'mustapha magana ya yi wa anty ikram magana, amma surry tasan da maganar kuwa.
Yace wlhy tasani kuma bata amince ba, ina sha'awar auren uwani ne saboda ina tausayinta a yanxu amma nafi son surayya da uwani ina fada maki gsky ne ba dan cin fuska ba.
Allah sarki surry, yarinya mai hankali xaa hada ta kishi da mahaukaciya, Allah ya basu xaman lafiya.
Yace amin...
Baban twins, yusuf yana neman alfarma ka saka bakin ka a neman auren sa da uwani... Jiddah ta fada lokacin da take qoqarin xama a kusa da shi.
Kallon ta yayi bayan ya cire watch din dake hannunsa, ya tashi yana fadin.
Babu wani hannuna da xan qara sakawa a al'amarin uwani again kafin axo ana kuka da qananun maganganu cewar ina son uwani.
Murmushi tayi tana kallon sa bayan ta tashi,
Haba Musty na, ina ji ko kai xaka iya bada auren uwani a yanxu, mgn kawai muke so kama anty ikram ta saka baki a ciki.
Believe me jiddah ba wani baki da xan saka a lamarinta, na cire hannuna akan komai nata, amma na amince maki ke kije da kanki ki mata magana
Ta saka hannunta ta xagayo dasu a qugunsa tana kallonsa cikin langabar da kanta.
Fushi kayi el'mustapha saboda na nuna kishina a soyayyar ka akan abinda ni kuma xai cutar dani.
Yace ba fushi nayi ba jiddah,
Idan ba fushi kayi ba meyasa xaka ce ka cire hannunka akan komai nata.,
Saboda jiddana ta yarda dani, ta yarda farin cikin ta kawai nake so,
Tace ba wani ni na gane kana kishin uwani ne saboda ta sami wani mijin.
'Wannan yarinyar ko.... yaja dogon hancinta yana fadin watarana sai nayi kullin kubura dake.
Tayi dariya tana qanqameshi a jikinta.
A gurguje pls😏
Bayan an gama solving komai aka tunkari abba da maganar.
Sanda uwani taga baqi sunxo inda abbanta har da el'mustapha ta fara tsalle tana murna, xaa fitar da ita daga gidan ta huta da axabar da ake mata, dama tasan wannan baturen yana son ta dole ne ma yaxo neman auren ta, ashe shiyasa jiya ta ganshi a mafarkinta bawan Allah ashe auren ta xai xo nema.
Su el'mustapha na barin gidan taje inda abbanta tun bai dawo rakiyar su ba ballantana ta jira har a kirata,
'Abba wannan baturen suke magana kenan,dama nasan sona yake ashe ba baqin ciki yake min ba da ya rabani da El..... bata qarasa ba ya wanke fuskar ta da mari.
'Ashe baki da kunya uwani.
Nan da nan ta shiga cikin nutsuwar ta, ta tuna yanxu fa ba irin da bane da ake kyaleta kuskure daya tayi jikinta sai ya gayamata, da sauri ta soma bashi haquri.
'Ko da taji yana fadawa hajiya yusuf ne xai aure ta harda kukan ta, bashi take so ba abokin el'mustapha take so, ita baxata aure sa ba.
'Abba yace to shikenan xan kira el'mustapha in basu haquri su haqura dama jiya Malam guzuma yayi min mgnr yana so ya aure ki tunda ya dauko hanyar shiryaki.
Ta ware idanunta sosai tana kallonsa, Malam guzuma wannan mugun malamin fa mai dukanta da abba ya hada ta dashi, ai da ta aure sa gwanda ta mutu,
'Abba kayi haquri kada ka kira ina son yusuf dina, shine masoyina na gaske dan Allah abba.......
Yusuf kuwa tunda yaga ya sami uwani hankalinsa ya dan kwanta, yana xuwa gida ya rungume surry yana fadin ya biya masu umara xasu je tare, sosai tayi murna sai kiss take ta xuba mashi...
Yace kuma xan canxa maki wannan gidan, ke xan saka a wancan sabon.
Tayi tsalle ta dira daga jikinsa tana kallonsa,
Bangane ba duk wannan kyauta haka ta mecece, meyasa xaka canxa min gida, shi wannan fa.
Gabansa ya fadi, yace aa da wancan da wannan duk nawa ne surry, xamu koma wancan ne na saka yan haya anan kingane.
Sai a lokacin ta saki fuskarta.
*
Yau ya akayi haka ka dawo da wuri baban twins,
Ya soma qoqarin cire rigar jikinsa yana fadin, tashi ki shirya, ki shirya airah ni xan ma su twins wanka na shirya su fita xamuyi,
Ta tashi da airah a jikinta tana fadin ai nayi masu wanka sai idan wasu kaya xaka canxa masu.
Yace to shikenan jiddatulmusty, bara na shiryasu, ya nufi dakin su suka nishi da gudu suna tsalle.
Daddy ina xamu je?
Daddy xamu je shan ice cream ne?
Duk bai amsa su ba, ya jima sosai kafin ya gama shirin su, sunyi kyau sosai har ya dauke su pic,
Daddy muje cikin garden kayi mana mai kyau, bama son dakin mu.
Yace tor shikenan wait at the falo kafin na gama nawa shirin.
Suka fito da gudu shi kuma ya nufi nashi dakin, bai jima ba ya fito cikin tsadaddiyar shaddar sa, yayi matuqar kyau sosai sai kace ango, inama uwani xata ganshi😉.
Suka nufi garden sai pics suke dauka.

har lokacin jiddah bata fito ba.
Meya tsaida jiddah haka, el'mustapha ya tambaya lokacin da yake qoqarin shiga dakin.
Jiddah taja tsaki, kasan shirin wannan yarinyar aiki ne.
El'mustapha ya qarasa yana fadin sai kukan tsiya tun daxu muryanta kadai ake ji a gidannan, ki xauna ki bata tasha da kyau kar muje gidan mutane ta nuna halinta.
Jiddah ta xauna da kyau tana kallonsa bayan ta sakawa airah mamma a baki.
'Wannan kwalliya haka el'mustapha duk ta mecece, wai ina xamu je?
Ya tashi ya qarasa bakin mirror yana gyara xaman hularsa,
'Ashe ko dana ji twins na fadin daddy is looking beautiful dai gaskiya suka fada min tunda gashi jiddah ta yaba.
Ni bance kayi kyau ba fa, kasan na fika kyau ai.
Wasa kike jiddah, ai inaji airah kawai xakice kin fi kyau na yarda ke ita ma din ban yarda ba.
Ba wani, nasan na fika kyau.
Dariya yayi ya juyo yana kallonta, El'mustapha yafi jiddah kyau ta sani kishi ke hana mata fadin gsky.
Ta tunxuro baki batayi magana ba.
Yace neman aure fa xanje jiddah kece xaki rakani.
Ta tashi tana fadin, baka da jarumtar da xaka tsaya gabana kana gayamin wannan mgn indai da gaske ne, ta bashi airah tana fadin riqe min ita na shirya.
Yayi murmushi ya karbe ta yana fadin, wai wannan yarinyar ba tayi 4 months ba,
Tace tayi mana,
Amma shine har yanxu bata iya xama ba, sai fitinar tsiya, ko dai baki koya mata xama ne.
Tace ina fa ajiye ta bata dai gwane ba tukunna, me kake ci na baka na xuba, nan da qanqanin lokaci xaka ganta tana maka oyoyo.
Yace bana so, na twins dina kawai nake so, na gaji da riqon ta xo ki karbi kayanki.
Ta cigaba da kwalliyar ta kafin ta juyo tana kallonsa,
Allah mijin jiddah kayi kyau sosai, wai miye sirrin?
Yaja hancinta yana murmushi, kema kinyi kyau jiddana, xo muje yanxu ne yayanki xai soma damu na da kira.
Tace wai da gaske can xamu je.
Ya gyada kai yana fadin tun daxu ya kirani su Afiya sun sauka naje dake.
Tare suka fito, el'mustapha da kansa ya tuqa motar suka tafi.
Sanda suka iso gidan abin ya daure masu kai da aka tsaida su ana masu tambayoyi kafin a barsu su shiga.
Basu fito motar ba suna xaune a ciki suka tsurawa qaton gidan kallo,
Ta ina ma xasu fara shiga, su ce gurin wa suka xo.
'Ko xamu koma ne jiddah,
Aa wlhy ai sai naga yanda cikin gidannan yake tun da har muka shigo,
Mata kenan da ganin kwab,, ta ina xaki shiga, bari na kira merah tukunna, wannan gida haka sai kace Palace ai mutum ma sai ya bata acikin sa.
El'mustapha ya soma kiran merah, jiddah ta juya tana kallon twins ashe sun yi barci ne shiyasa suka ji shiru.
El'mustapha na gama wayar baa jima ba sai ga wasu mata kuyangu sun fito,
Suka gaidasu a natse suna fadin gimbiya Afiya tace a shiga da ku.
El'mustapha ya dubi jiddah yana fadin kije xan jiraki anan saboda twins dake barci kada a barsu su kadai.
Tace to shikenan, ta balle murfin motar ta fita airah ta kwantar da ita a seat, tana biye dasu har suka shiga.
Jiddah ta shagalta da kallon cikin gidan tamkar a wata qasa ba cikin abuja ba, haka ta dawo kamar wata baqauya musamman da suka shiga dakin da Afiya take.
Kallon kallon suka shiga yiwa juna, ta yarda Afiya yar uwar merah ce suna da kamanni sosai, kyakkyawa da ita.
Afiya kuwa kallon jiddah take a matsayin yarinya dan baxaka taba kallonta kace ta haihu ba ballantana ta fitar da ya'ya uku a jikinta, hasken fatar ta mai kyau, haka kawai taji tana kishin jiddah, meyasa merah ke son hada ta da wannan yarinyar har yake damun ta da xancen ta.
Da kyar tayi wa jiddah dake tsaye tana kallonta nuni da hannu akan ta xauna batare da tayi magana ba.
Jiddah ta xauna a hankali a ranta tana cewa lallai ga inda mulki da sarauta suke ba gurin merah ba.
Sai dawainiya ake da ita ta fannin ciye ciye, jiddah bata ci komai ba kamar yanda Afiya bata mata magana ba.
Sai jiddah ta tsinci kanta cikin jin haushin kanta, me ya kawo ta, shishigi ko neman cusa kai, taya ma xata iya qulla alaqa da ita alhali ita ba jinin sarauta ba.
Afiya.. Afiya.. suka ji daya bangaren ana kiranta, suka juya suna kallon mai shigowa.
Matashiyar macece mai ji da qasaita kallo daya xaka mata ka gane hakan, sai dai da alama tana da fara'a da sakin fuska ba kamar Afiya ba.
Tace yaya maina ya kira fa wai baqin sun xo.
Afiya tace yes she is with me,
Sai a lokacin ta juya tana kallon ta,
Oh baquwar mu ashe kin xo ta fada cikin murmushi tana qoqarin xama kusa da jiddah.
Tace kin ganta Afiya very cute da ita wlhy, sunan ki jiddah ko?
Jiddah ta gyada kai tana kallonta ko baa fada ba tasan wannan itace Rumaisa.
Rumaisa tace sannu da xuwa masarautar mu jiddah, Muna miki barka da xuwa, yaya maina ya fada mana yayi mana qawa mai kirki sai dai bai mana bayanin ta ba.
Afiya ta kasa sukuni, sam taji bata yarda da merah ba saboda me xai turo masu wata mace yace wai xasu yi qawance da ita, she is part of the family, ta tashi ta nufi wani dakin cikin tafiyar ta, ta kasaita.
Kiran sa ta soma yi, ringing d'aya ya dauka yana fadin,
Kin ganta...
Eh na ganta amma meke tsakanin ku.
She is my new sister.... ta katse sa,
Nooo saboda me, ta ina bayan she is not part of our family, just tell me Aiman ita wacece.
Ji wata magana da kike yi, idan budurwa tace xan turo ta nan gidan ne,
Eh mana ai xaka iya, ko kamanta sanda kaxo da nabila ne.
Murmushi yayi yana fadin ko sultan baxai yi wannan ba ballantana ni Afiya, go back to her ki kalle ta a natse kigani yarinyar da wa take maki kama, tun sanda na fara ganin ta Germany da nayi mata aiki naga she looks familiar amma ban gane ba dalilin haka ne da naxo gida Nigeria har na xiyarci gidansu still ban gane ba, dalilin hakan ne nace ta dauke ni matsayin yayanta har na bata labarin family din mu thinking she knows something about us, amma na lura she don't.
Kema kin san ba kai tsaye nake yarda da mutane har na saki jikina dasu ba, yarinyar nan look familiar ku je da ita mai martaba ya ganta, ko me ake ciki you let me know sarauniyar Aiman.
Tace naji amma bata da aure ne,
Tana fa dashi Afiya baki ga mijin ta bane.
Tace ni ban gani ba ita kadai nagani shiyasa hankali na ya tashi.
Yaran ta fa, baki gansu ba, akwai yarinyar da take shayarwa ai.
Tace wallahi duk ban gani ba, shiyasa na kasa sakin jiki da ita,
Yayi dariya sosai kafin yace ina son ki Afiya, ya tsinke wayar, kallon wayar tayi tana murmushi kafin taji wata nutsuwa tana saukar mata, ina xata yarda ayi mata irin na nabila, ta koma falon ta sami rumaisa da jiddah sai hira suke suna dariya.
Jiddah tayi mamakin ganin wannan karon afiya ta saki fuska tana mata magana.
A dan xaman da suka yi a gurin sai ta fahimci afiya mai sauqin kai ce sosai sai ka xauna da ita xaka fahimci hakan ba daga kallo daya ba.
Rumaisa yayan ki yace jiddah tana kama da wani a gidannan, wai waye ni ban gane ba.
Rumaisa a kalli jiddah tana fadin nima ban sani ba gaskiya.
Sultan ya dame ni fa afiya wai nayi wa yaya magana kan maganar wata fauzy da yake son hada shi da ita baya son ta.
Afiya tace kyaleshi, maina baxai saurara masa ba kinsan tsakanin sa da dr iman, alqawari yayi mata kuma ni banga laifin sa ba ina son yarinya.
Babbage ko qarama rumaisa ta tambaya,
Qarama ce fa,
Sultan din ma ai bai isa aure ba,
Afiya ta tashi tana fadin hakane kam, muje inda mai martaba kada mu tsaida baquwar mu tabar mijinta a waje.
Suka tashi suka nufi falon sarki, kusan faduwa jiddah ta tashi yi, yanxu ta daina mamaki da komai na gidan sai dai ta xuba idanu tana kallo,
Ganin yanda suka yi suna gaida sarki itama jiddah ta bisu da sauri suna gaidashi.
Wacece wannan ya tambaya yana kallon rumaisa.
Abba ai yaya yace a xo da ita xata gaida ka.
Sarki ya qara tambayar shi yariman.
Ta gyada kai tana kallonsa bayan ta gyara xamanta.
Jiddah jikinta sai rawa yake rashin sabo yau gata a gaban sarki merah cikin sauqi.
Ya juya yana kallon jiddah, ya sunan ki?
Cikin rawar jiki tace Hauwa,
Mahaifin ki fa?
Tace sunan sa Ahmed Rufa'i,
Yace a ina yake?
Idanunta suka kawo kwallah,
Ya rasu....
Ina kika san yarima?
Tace nayi fama da rashin lafiyar qafafu shine ya min aiki.
'Wannan dalili baxai saka yarima turo ki inda nake ba, patient nawa yayi wa aiki?
Hawaye suka xubowa jiddah hankalin ta ya tashi da kyar tace nima ban sami ba, amma yace ya xama yayana.
Sarki yace ina mahaifiyar ki da yan uwanki?
Mahaifiyata ta rasu ita ma, amma ina da wasu iyayen da suka yi riqo na tun ina qarama.
Baki da aure ne?
Ina da yana waje tare da ya'ya na.
Ya dubi rumaisa yana fadin, kira min mijinta, kana ya dubi afiya yana fadin kiramin mahaifiyar ku.
Duk suka tashi suka fita jiki a sanyaye, jiddah Ma hankalinta ya tashi musamman daga kallon da sarki ke mata.
Suna haka iyayen mata suka shigo, jiddah ta kasa gaida kowa acikinsu ta sunkuyar da kanta, sai kawai ta tsinci kanta cikin tashin hankali sosai, ta hada kai da gwiwa tana kuka sosai wannan taron me aka mata haka, da tasan abinda xai faru da bata xo ba.
Twins suka fara shigowa da gudu kafin el'mustapha dauke da airah.
Ganin falon cike ga kukan jiddah na tashi hankalinsa yayi matuqar tashi, ya nufi inda jiddah da sauri,
Duk falon aka xuba masu idanu sai a lokacin afiya tace ashe itama mijinta classic ne,
'Ko me el'mustapha ya tuna sai kuma ya fasa xuwa inda jiddah ya xauna kawai ya tankwashe qafafuwansa yana gaida mai martaba cikin jijjiga airah.
Twins kwantawa sukayi a jikinta,
Waya dake ki mummy?
Mai martaba yace, ku dubi yarinyar nan me kuka fahimta a tare da ita.
Duk falon aka juya ana kallon jiddah, nan ta qara tsarguwa, ta juya tana kallon el'mustapha,
Ammi tace tana kama da ZUBAIDA fa...
Jiddah ta dube ta da sauri, el'mustapha ma kallonta yake, a ina tasan sunan mahaifiyar jiddah?
Mamaki qarara a fuskar jiddah, ta kalli wannan ta kalli waccan.
'Exactly....
Rumaisa ta fada tana kallon Ammi,
Wallahi ammi sai da kika fada naga hakan,
Afiya tace yeah is true tana kama da Anty Zubaida, but ita wannan jiddah who is she?
Umman tace nima tun da na ganta naga tana kama da Zubaida, wannan kuma bamu santa ba.
El'mustapha ya dubi sarki,
Ranka ya dade, wacece zubaida da kuke magana, jiddah