Showing 3001 words to 6000 words out of 138779 words
Chapter 2 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
daka, da kyar ya iya furta, sorry Mami...
Jidda murmushi kawai tayi cikin tunanin hali irin na Aryan, bata san inda ya sami wannan halin ba.
Elmustapha ya maida kansa kirjinsa yana shafawa a hankali cikin shigar rarrashi, is ok kukan ya isa haka... dai dai lokacin uwani ta fito sanye da hijab har qasa sai qamshi take xubawa idanunta kyam akan sa kamar xata hadiyesa take ji saboda kauna.
Yaya sannu da xuwa, ya aiki, ta fada cikin muryarta mai Jan hankali, kallonta jidda tayi tana naxarinta,
Batare da ya kalle taba yace, yauwa uwani ga Aryan a canxa masu kaya xuwa na barci, akwai skul gobe.
Cikin rawar jiki uwani ta nufesa ta karbi Aryan, ba abinda take so kamar taji jikinta ya hadu danasa koda sau daya ne, kamar jidda tasani tayi qoqarin tsaidata ta amfani da karban Aryan hannunsa ta nufi uwani dashi wanda saura kadan ta kife qasa saboda baqin ciki.
Karo na farko kenan a xamantakewar su da ta soma jin haushin jidda, batare da ta bari jidda ta gane halin da take ciki ba ta saki murmushi mai cike da baqin ciki da haushi cunkude a xuciyarta kamar xata kifa ihu, haka ta karbi Aryan ta riqa hannu arham ta jasu badan ta so ba ta nufi dakin su jamila, banan ta miqawa su ta nufi dakinta a fusacce.
Da sassarfa jidda ta nufesa, rungumesa tayi hade da kai masa peck a kumatunsa, kallonsa take da murmushi a fuskarta,
All I have is you, ina matuqar son ka, bana fatan Allah ya kawo abinda xai rabani da kai koda kuwa mutuwace, nafison ta daukeni kafin kai,
Mutuwa xata daukeni ne kafin ke jiddana, duniyar nan idan babu ke am useless, ki daina maganar.
Taja dogon hancinsa tana murmushi, bana son kishiya elmustapha, I hate her, baxan iya rayuwa ina ganin ka da wata mace ba, baxan iya jure ganin ko wacce irin mace a kusa da kai ba koda a mafarki ne, ni dai bana sonta, bana sonta ba.... Yayi saurin rufe mata baki da nasa, sun dauki tsawon mintuna a hakan kafin ya dauke ta cak ya nufi dakin sa da ita.
Uwani dake bayan curtains tana kallonsu, jikinta ya fara rawa, hawaye take ba kakkautawa tare da ayyanawa a ranta wlhy sai dai jidda ta mutu amma sai ta auri elmustapha kuma sai ta raba sa da ita, sai ya sota fiye da yadda yake son jidda.
Bayan sun fito wanka wanka sun shirya cikin kayan barci, yaci abinci yayi abubuwansa da ya saba na aikinsa kafin ya kwanta, ya haye gado yayi kwanciya abinsa.
Hakan ba qaramin sosa xuciyar jidda yayi ba, domin ba abinda take buqata a yau kamar mijinta, tafi kowa sanin elmustapha yana daya daga cikin irin maxan nan da basu cika neman mace akai akai ba, sai sufi sati a haka bai damu ba amma romance tana samu sosai domin yafi sonshi sosai akan wancan, yau kam tana tsananin buqatar shi.
Gadon ta hau, yanda suka kwanta suna fuskantar juna sai dai shi idanunsa a lumshe suke, qirjinsa take kallo kafin ta dora hannu akai tana shafawa a hankali, bude idanuwansa yayi yana kallonta cikin yanayi na barci,
jiddana yau ban sami Hutu ba ko kadan, nagaji sosai, ban gayamaki ba har xaria naje yau.
Tayi shiru batare da tayi magana ba, amma yanda idanunta sukayi jaa kawai xai tabbatar maka na bacin rai ne, ta juya masa baya cikin fushi, hannu yasa ya juyo da ita hade da matse ta ajikinsa, hannunsa na yawo a doron bayanta,
'wannan kadai ya isa ki gane, ke kadaice macen dana keso, kin isheni a rayuwata, baxan iya lalurar wata macen ba, baxan iya son wata 'ya mace bayan jidda ba, bana son kina juyamin baya ko kadan.
Still bata tanka ba, banda sauke numfashi ba abinda take,
Ko baya buqata jidda ta nuna masa tata buqatar yana qoqarin sauke wannan nauyin just to make her happy and satisfied, baiga abinda jidda xata nema a gunshi ya hanata ba, ballantana karan kansa kacokan, ya sabule hannun rigar baccinta bayan ya hada bakinsa da nata.
Asuba ta gari *Jiddatulmusty*
*EL_MUSTAPHA*
HASKE WRITER'S ASSOCIATION
(home of experts and perfect writers)
Fertymerh Xarah 💞
11
'Washe garin ranar ga baki daya yinin ranar uwani bata fito ko falo ba tana can qunshe acikin daki.
Ganin shirun yayi yawa ne yasanya jidda xuwa ta dubata,
Kallo daya tayi wa uwani sai da hankalinta ya tashi, jikinta ya dauki rawa ta qarasa kusa da ita fuskarta dauke da mamaki take kallonta.
'meke damun ki uwani, meya same ki haka, idanunki sukayi jawur suka kumbura,
Uwani tayi qoqarin boye hawayen ta amma ina kamar kada ta tambayeta sai hawayen suka fara xarya, kukan me takeyi idan ba kukan so ba, rungumar da elmustapha yayi wa jidda jiya ba qaramin tarwatsa xuciyarta yayi ba, amma taya xata iya gayawa jidda saboda mijinta ne?
Ganin uwani tayi shiru batayi magana ba ya sanya hankalin jidda qara tashi, ta riqo kafadarta hannunta sai karkarwa yake kamar itama xatayi kukan haka take ji.
Uwani ki gayamin damuwar ki, a duniyar nan akwai wadda tafini muhimmanci a gurin kine kamar hajiya, ko kin sami matsala da Yusuf ne?
Uwani ta girgixa kanta cike da quncin jin ta ambaci wani Yusuf,
'ko matsala kika samu a makaranta? Nan ma ta girgixa kanta,
'to menene uwani, kiyi magana, ke ba arham bace da xan xauna rarrashin ki tun daxu jin matsalar ki, atleast ko menene ya kamata ki fara sanar dani kafin kixo kina kuka anan, kinga yanda idanunki sukayi kuwa?
'ba komai anty jidda, xaxxabi ke damuna kuma bayan wannan sai na tsinci kaina bana jin dadin rayuwata, I just feel like to cry.
'shine kuma baxaki gayamin ba, idan wani abu ya same ki am to hold responsible, dan Allah kidaina min haka bana so, idan abu na damunki let me know da wuri, kinsha magani ne?
'yanxu na sha,
'Abinci fa?
'A'ah
'bari na kawo maki ko tea ne kisha, ta tashi ta fita uwani ta bita da kallo tana jin wata qaunar sister din ta yanda take nuna damuwa akanta koda yaushe, amma ya xatayi da soyayyar mijinta da ta kanainaye xuciyarta, wannan abin kunyane a gurinta duk lokacin da jidda ta kamata dumu dumu cikin soyayyar mijinta, ta hada kanta da gwiwarta hade da sakin wani kuka mai narkar da xuciya.
Asalin labarin.......
Hajiya Zubaida itace mahaifiyar jidda, macece mai haquri da tawakkali, tana da riqon amana da rashin son abin duniya, Jiddah kadai ce ta mallaka tun bayan rasuwar mijinta,
Hajiya zubaida aminiya ce ga hajiya maimuna, xama suke na amana irin wanda yayi qaranci a wannan xamanin namu, xama suke batare da hassadar juna ba.
Suna rayuwa a gida daya ne, kasancewar mijin hajiya maimuna ba wani mai qarfi bane sosai yana xaune a gidan haya, wulaqanci iri iri yake gani sanadiyar hakan hajiya zubaida ta umurci da su dawo a gidan ta su xauna tunda bata da miji kuma gidan yana da girma sosai.
Yan uwan hajiya xubaida irin mutanen ne masu son cin dukiya hassada da kyashi ba abinda suke so daga gare ta kamar abin hannunta.
Sanda ta kwanta wani ciwo mai tsanani ta soma ganin take taken su tun tana da rai suke kissafa dukiyarta saboda sun dora mata mutuwa, tana tuna mahaifin Jiddah sanda yana raye shima haka sukayi saboda auren xumunci ne dama a tsakaninsu.
Dalilin haka hajiya zubaida ta tara su duka, ta basu wani abu cikin dukiyarta kada bayan mutuwarta su tayar da wata fitina, sauran kuwa ta damqawa hajiya maimuna tare da amanar jidda lokacin tana shekara goma a duniya, Uwani tana shekara biyar itace yar'hajiya maimuna.
Baa dauki wani dogon lokaci ba Allah ya yiwa hajiya xubaida cikawa, tashin hankalinsu a ranar bai misaltuwa, musamman jidda kusan sau biyu tana suma.
Jidda ta taso cikin maraici ba uwa ba uba, amma ta sami kulawa sosai a gurin hajiya maimuna tamkar yar'ta Uwani babu banbanci ko hantara tsakanin su, ta dauki jidda hannu biyu tana bata tarbiya gwargwadon iyawarta.
Ta hada kan ya'yanta, abu mai kyau da marar kyau duk tana nuna masu kuma tare da illar sa, duka family suna son junansu musamman jidda da bata da hayaniya, tana da sanyin hali da kauda ido akan komai, gata da girmama iyayenta sabanin uwani da ita a rayuwarta tana son ta ganta da manyan qawaye masu kudi, komai dai ayi qarya, kun dai gane😀
Sannu sannu har jidda ta kammala secondary School din ta, a lokacin ta hadu da elmustapha hajiya ta aike ta banki.
Daga yanayin tafiyarta xaka gane nutsuwarta da kamalarta, kai tsaye ta shiga bankin hannuwanta duka Acikin Jakarta da alama abu take nema tana tafe tana dubawa,
dai dai lokacin ya fito daga cikin bank din, sanye da baqaqen suit, hannuwansa wayar sa yana tafe shima yana latsa ta cikin sauri da alama wani yake son kira...
Kicibis sukayi karo da juna, wayar dake hannunsa ta subulce ta fadi qasa, ya daqo a fusacce ya dora idanuwansa akanta dai dai lokacin da ta sunkuya domin dauko masa waya.
Tun da taga wayar ta tarwatse hankalinta ya tashi, jikinta ya dauki rawa ta kasa daqowa illah hada kai da tayi da gwiwarta ta soma kuka cikin tashin hankali, abinda bata tabayi ba, yau tayi wa wani hasarar abu mai muhimmanci a garesa.
Turus yaja ya tsaya yana kallonta har lokacin baiga fuskarta ba, sai dai fuskarsa da xuciyarsa cike suke da tsananin mamakin yarinyar dake tsugunne a gabansa......
Vote me on wattpad phertymerh1
*EL_MUSTAPHA*
HASKE WRITER'S ASSOCIATION
(home of experts and perfect writers)
Fertymerh Xarah 💞
12
Hannu yasa ya xame wayarsa daga hannunta, kallo daya yayi wa wayar, hankalinsa ya qara tashi,
Daga yanayinsa xaka gane bai ji dadin hakan ba, ya juya da sauri ya bar gurin, yana gab da shiga motar sa yaji muryarta.
'Dan Allah kayi haquri ka yafemin kada ka tafi da fushina a xuciyarka.....
Juyowar da xaiyi ya ganta tsaye a bayansa ta harde hannuwanta duka biyu alamar tana roqansa, idanuwanta har sunyi ja, hakan da tayi yaji tausayinta matuqa.
'yace ba komai, kidaina kukan domin bai da amfani a yanxu.
'tace nagode, ta juya batare da taji amsar sa ba ta fice, kallonta yake yana observing akan ta har lokacin da ta shiga cikin bankin, ya jingina da motar sa yana kallon wayar,
Bude wayar yayi ya ciro sim din sa, kana ya bude motar ya dauko qaramar wayarsa ya bude da sauri ya sanya sim din.
Qoqarin kunna babbar wayar yake yagani ko xata tashi, cikin sa'a kuwa ta tashi, tunani yayi to kodai screen guard dinne ya tarwatse, da kuwa yayi murna sosai ya cilla wayar cikin mota.
Yana qoqarin shiga ya ganta ta fito, wannan karon waya take amsawa
Kallo ya bita dashi har sanda tayo gab dashi dai dai lokacin tana qoqarin mai da wayar a jaka, ko kadan batayi tunanin sake kallon sa ba saboda cike take da tsoronsa gani take kamar xai iya dukanta, meyiwuwa tsayuwar sa anan Ma ita yake jira,
Kamar ance ta dago, suna hada ido yayi mata alama da hannu taxo, sai da hantar cikinta ta motsa, ta juya tana kallon wani security tunani take ko xata hada shi da shine kada yayi mata wani abin, bata qara tsorata ba sai sanda ta gansa yana xuwa da kansa, ta riqe jakarta dam jikinta ya dauki rawa kamar ta xura da gudu take ji,
'amma ai nace kayi haquri ko, cikin rashin sani ne dan Allah kada ka cutar dani.... ta rumtse idanunta,
Idanu ya xura mata kallonta yake sama da qasa har xuwa lokacin da ta bude idanuwanta, irin kallon da yake mata ya qara ruda ta,
'your name? Shine abinda taji ya fada,
Tace ni.. ni... Hauwau Ahmed suna na am.. am.. Sai kuma ta kasa qarasawa,
'ki nutsu, ni ba mugu bane da xan cutar dake, ya nuna mata card dinsa, am a police, ko wani naga xai cuta maki xan kare ki.
Sai ta fara sauke numfashi ahankali ba dan ta nutsu dashi, ita kawai ya barta ta tafi xata fi samun nutsuwa fiye da tsayuwa dashi, ya nemi address nata ba gardama ta bashi, da sauri ta bar gurin yana ganin lokacin da ta shiga napep ta bar gurin.
Tana xuwa gida ta bawa hajiya labari, sosai sukayi dariyar ta bama kamar uwani,
'Anti Jiddah kin fiye tsoro ne meyasa xaki tsaya masa kuka,
Jidda ta tashi ta nufi dakin ta tana fadin ai kuma tunda ba ke bace ni sai ki barni.
*
El'Mustapha Maneer (CP) yana dawowa gida ba abinda ya fara sai maganar ya sami matar aure,
Jin kalmar matar aure a bakin el'mustapha ba qaramin mamaki ya sanya mahaifiyar sa ba, idan ta tuna shekarunsa da muqaminsa amma bashi da aure kuma baya da niyar yin auren sai a yau da taji mgnr a bakinsa.
'bana son kina min wannan kallon mama, I mean it nasami matar aure, very young, ina son mace mai nutsuwa da kunya, macen da xataji tsorona at anytime.
'kace qaramar yarinya ce, anya batayi Ma qanqanta ba, ba wannan bama ita tace tana son ka ne.
Ya tashi yana fadin koma menene mama ki shirya, very soon xaki sami in law, sai ki fara shirye shirye.
Ta bisa da kallo fuskarta dauke da murmushi, Allah ya karbi adduarta mustapha xaiyi aure, oh Allah ni har ina tunani ko aljana ta aure min shi, Allah ka nuna min ranar auren nan ka sanya alheri aciki.
Bayan kwana biyu....
Jiddah na kwance jikin hajiya tana tsifa sai ga Abban su ya shigo,
'ina jiddah?
'gani Abba ta fada bayan ta tashi tana kallon qofar shigowa,
'sanyo hijabinki ki sameni falo na yanxu,
Ta juya xuwa dakin ta, bata jima ba ta fito sanye da hijab din ta.
Tun da ta tunkari falon take jin bugun xuciyarta na qaruwa, da sallama ta shiga kanta a sunkuye, suka amsa mata sallamar.
Ta nemi guri ta xauna tana kallon abba,
'ga baqon ki, shi keson ganin ki.
'wata irin faduwar gaba ta dirar mata lokacin da sukayi four eyes da el'mustapha, jiki na rawa ta gaidashi kana ta juya tana kallon abba idanunta taf da hawaye.
'Abba wallahi na bashi haquri dan Allah kace yayi haquri idan yaqi ka siya masa wata wayar ni ya barni.
Murmushi ya subulcewa el'mustapha, yana kallonta qasa qasa yana jin wani abu game da ita a xuciyarsa mai girma da nauyi, tabbas yana son jidda yana son kasancewa da jidda tana matuqar birgeshi.
'ba maganar waya taxo dashi ba jidda, maganar aure taxo dashi amma xan barki dashi kiji da bakinsa, idan kin amince shikenan dan baxan maki dole ba, bai jira cewar ta ba ya tashi ya bar falon, tsananin mamaki ya sanya jidda binsa da idanuwa har sanda ya bar falon kafin ta juyo tana kallon el'mustapha cikin son gasgasta maganar mahaifinta.
Da sauri ta maida kanta ta sunkuyar, baxata jure kallon kwayar idanunsa ba, ya tashi ya dawo kujerar da take xaune, da sauri ta matsa cikin jin tsoron sa, bai damu da hakan ba fatan sa ta amince da shi a matsayin mijin aure.
'ina son ki jiddah, taji muryarsa tamkar saukar aradu a kunnuwanta,
'aure nake so muyi jidda, kamata baxan tsaya ina jeka ka dawo ba kamar yanda samari keyi idan suna neman budurwa, banxo rayuwar ki dan na cutar dake ba, ina son kasancewa dake ne jiddah amma idan kin amince kamar yanda mahaifinki ya fada a yanxu, ya gayamin wacece jiddah tun farkon rayuwarta har xuwa yanxu.
Jikinta yayi sanyi, qamshin turarensa ke sanyaya xuciyarta, baxata ce bata da samari as her age ba, akwai su kam har masu son auren ta Ma amma batasan meyasa xuciyarta tafi amincewa da el'mustapha ba, bata san meyasa take jin sa axuciyarta a yanxu ba, tunaninta idan matar sa bata son ta fa.
'kinyi shiru jiddah, ko nayi maki girma ne? ta girgixa kanta, yace to menene?
'ina jin tsoron matar ka ta ganni qarama ta riqa dukana, dariya yayi sosai yana kallonta.
Funny jiddah, saboda me xata dake ki, ballantana banda mata ban taba aure ba jiddah, ta dago tana kallonsa da mamaki, ya gyada kansa cikin tabbatar da xancen sa.
'ba wai na rasa matar aure bane, ina dasu har masu roqon mahaifiyata na aure su ko na auri ya'yan su, ban sami wadda nake so ta kwanta min a xuciya ba kamar jiddah, aure lokaci ne, nikam yanxu nawa lokacin yayi Allah yasa jiddah xata soni.
Kafin kace me jiddah ta saki jiki sosai tana kallon el'mustapha yanda yake bata labarinsa da yan'matansa sai dariya take tana kallonsa musamman da yace itama sai ta bashi labarin samarin ta.
Ta tambayi kanta shin ko mutane nawa ne a duniyar nan irin El'mustapha?
yana da wasu ilhamomi na musamman a tare da shi da bata taba ganin su a ďa namiji ba, ko yanda yake duban mutane daban ne da sauran maxa,
Tsarin maganarsa cikin seriousness shine babban abinda ke burgeta dashi, ga kamun kai da sanin mutuncin kai, hadi da rashin son wasa ta ko ina, amma yana da fara'a sosai.
My wattpad Phertymerh1
*EL_MUSTAPHA*
HASKE WRITER'S ASSOCIATION
(home of experts and perfect writers)
Fertymerh Xarah 💞
13
Suna tsaka da firar su sai ga Uwani taxo dauke da qaton tire a hannunta, dawowar ta daga School kenan lokacin tana S.s.2,
Har qasa ta gaida sa cikin satar kallon sa, tana yaba