Showing 87001 words to 90000 words out of 138779 words
Chapter 30 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
right? Duk qoqarin yarinyar nan akan ki, meyasa kike tunanin abinda baxai taba yiwuwa ba, idan saboda wannan ne banan baxata bar garin nan ba, you are talking rubbish babu wata soyayya tsakanina da yarinyar nan.
Ta tsura masa ido cikin mamaki baki a sake,
Tace yanxu na gane hasashena ya xama gsky, tabbas ka nuna min kana son banan, ka damu da banan, idan hakane baka min adalci ba el'mustapha..... Sai ta fashe da kuka,
Ya tsura mata ido cikin mamaki ga wani haushi da yake ji a xuciyarsa, yana ji tuntuni sun gama magana da ita akan babu soyayya tsakanin sa da banan amma me ya dawo da maganar? Dan ya qara kufular da ita yace,
Eh naji, koma menene haka ne, kuma aure kece kika buda min hanyar yin sa, banan din Ma amanata kika bata so banga abinda xai saka ki tada hankalin ki ba, idan Allah ya nufa xan aure ta auren ta xanyi.....
Wallahi baka isa ba, ta fada tana kallonsa da jajjayen idanuwanta, kuma banan sai ta bar garin nan gobe ko ni na barshi, sai ku xauna tare.
Oho dai koma menene ke kika sani, ya tabe bakin sa alamar ko a jikinsa,
Ka fita bana son ganin ka el'mustapha, ashe qaryar so kake min, you can't be with me a duk yanayin da nake as you say, kana tunanin baxan qara tashi bane kake son qara aure, auren Ma da banan,
Fassarar da tayi mashi baiji dadi ba ko kadan, xai yi magana ta katse sa,
Karkace komai ka fita please, dan Allah ka tafi ta fada tana kuka...
Duk abinnan da suke hajiya ta shigo dakin tana ji, ranta ya baci ta hau jiddah da fada sosai,
El'mustapha bai qara magana ba amma yayi fushi sosai har sai yaushe jiddah xata gane ita kadai ce a xuciyarsa babu wata, shi feelings din da Ma yake ji akan banan before yanxu duk ya daina ji tun lokacin da yaji an bada ta ga Islam, banda kallon qanwa babu abinda yake wa banan yanxu.
Hajiya tace ashe baki da wayo jiddah ban sani ba, ban gaya maki ba saboda ki bata da mijinki ko ki kori banan illah ki dauki mataki mai sauqi akan ta da mijinki.
Waya ce maki haka ake yi?
Wallahi hajiya banan tana son el'mustapha, naga kallon da take mashi yanxu a gabana, kina ji fa abinda el'mustapha ke fadi kamar shima din fa yana son ta, da wannan baqin cikin gwanda na mutu hajiya.
Tace subhanallah... Kar na qara jin wannan mgnr a bakin ki, indai banan ce xata koma Nigeria amma ki bawa el'mustapha haquri ransa ya baci sosai kuma Sam baki kyau ta ba, bai kamata kifito fili ki nuna kinsan komai akan su ba, kuma ni bana jin ta el'mustapha ko yana son banan ita kadai ke haukanta.
Shiru kawai jiddah tayi batayi magana ba ama xuciyarta sai xafi take yi.
*
K'eeeeeeeeeeeey kake ji uwani ta janyo qatuwar jaka ta fito falon cikin shirinta sai taunar cingam take a hankali.
'Abba naxo muyi ban kwana ni xan bar garin,
Ya dube ta ya dubi jakar yana fadin xuwa ina haka kuma uwani?
Kudin jirgi xaka bani nima xanje Germany nayi jinya daga nan xan roqi anti jiddah gafara,
Yayi shiru yana kallonta kafin yace,
Waya gayamaki shiga jirgi daya yake da shiga motar kasuwa, me kikayi na fita waje, tukunna Ma idan kinje Germany ta ina xaki same su.
Tambaya xanyi abba, duk wanda xan Ma misalin hajiya da El'mustapha tsab xai gane su, ina ji acan ai basu da yawa kamar mu nan ko abba,
Da wannan jakar xaki je kenan, ta gyada kai tana kallonsa,
Yace tor shikenan Allah ya kaiki lfy, ina gaida su.
Kudin jirgin fa?
Yace banda su, ta saki baki tana kallonsa,
Haba abba wallahi kana da su, kowa yasan akwai su sai idan baqin ciki xaa min ga wannan tafiyar kada na shiga jirgi, amma qiri qiri ace ba kudi bayan nasan akwai.
Baiyi magana ba, ta xauna dirshan gurin tana miqe qafafu bayan ta xare takalmin qafafunta,
'Abba dan Allah ka kaini Germany, ka kaini na shiga jirgi dan Allah abba ba danni ba.
Yace naji idan xanje duba ta xanje dake,
Ta washe baki, Allah ya sada mu aljanna abba, shiyasa nidai ina sonka saboda a rayuwarka baka da baqin ciki kuma kana sona, nagode abba.
Tashi kije ki maida jakar kixo xamu fita, ki sauya wannan gyalen ki saka hijab din da ya sauko maki a gwiwa.
Abbana Abbana, Abbana Abbana, fita xamuyi kenan, na rasa Ma me xance maka sai nayi tunani abba saboda kai din rayuwarka mai kyau ce baka da baqin ciki wlhy, ynxu da hajiya fa nan taji xamu fita haushi xataji ta hana dan kawai kar ka siyamin ice cream, amma abba harda shopping xamuyi ko.
Yace eh,
Ta tashi tana murna ta fita, shikam so yake ya kai uwani a duba masa kwakwalwarta yana son sanin matakin da take xaune akai, tun tana qarama ya kamata suyi wanna binciken tunanin su yarinta da quruciya ce amma gashi har ta girma bata daina ba.
EL'MUSTAPHA
Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers
Fertymerh Xarah💞
53
Bata jima da shiga ba ta fito sanye da hijab din ta, abba ya tashi suka fita sai kirari take masa tana take masa baya.
Acikin mota ne suna tafiya take bashi labarin qawayenta na prison, ai abba xaka fitar da ladidi ko, ina tausayinta sosai amma kaga anty aj da runkes sunci amanata.
Kuma fa abba ita ladidi tana sona tana kareni idan xasu dake ni ita a rayuwarta bata da baqin ciki shiyasa nake son taimaka mata na roqi mijin anti jiddah ya fiddata.
Kuma abba naje na hadu da wata hajiya Mariya ita wannan yar iska ce har dani tace muyi iskanci fa (abba ya kalleta kafin ya maida kallonsa ga tuqin da yake)
Kunyi iskancin kenan..
Kai haba ai ina da wayo kuma ni ba yar iska bace da naqi amincewa ne ta fara axabtar dani aikin gidan duka nike mata harda cewa ina yarda xata siya min mota ta kaini waje nayi karatu, shiyasa Ma ni abba kaji nace ka kaini waje nayi karatu na bata mamaki dan tasan Abbana mai kirki ne kuma shi a rayuwarshi bashi da baqin ciki, ko abba? ya gyada kansa baiyi magana ba,
Ta cigaba da bashi labari har suka iso asibitin.
Kai tsaye yayiwa likitan bayanin halin da uwani take ciki aka shiga a dubata.
Sun dade asibitin sosai kafi result din ta ya fito,
Likitan ya dubi abba yana masa bayani, abinda nake tunani ba shi bane, nayi tunanin ko congenital disorder wanda ake haihuwar mutum da shi (presence since birth) kamar hydrocephalus water (fluid) on the brain, ko mutum yaji sauqi bayan yi masa aiki idan bai cigaba da shan magani ba xai iya xama wani psy.
Sai na gane lalurar ta bayan haihuwa ne, she has traumatic problem, (an emotional wound leading to psychological injury) me yiwuwa kun taba accident ta bugu da kan, baku dauki serious action akan abin ba har girman ta a yanxu.
'Abba yayi shiru yana kallonsa kafin yace, bamu taba accident ba, sai dai ta taba faduwa tana koyon tafiya a saman bene baxan manta ba, kuma mun kawo ta asibiti suka nuna mana ba komai a lokacin,
Sai bayan ta fara girma ta fara magana take wasu abubuwa masu ban mamaki, xata gayawa babba maganar da duk ta fito bakinta babu ruwanta kuma idan kashe ta xakayi bakin baxai taba shiru ba har sai ta fada, a lokacin sai muka dauka kurciya ce da yarinta muka kyaleta saboda muna son ta bamu da wata 'ya bayan ita, bayan girmanta ne muka fahimci cewa abin ya qaru duk abinda take so kai tsaye xata fada kuma bata boye abinda ke xuciyarta, daga nan ne muka fara tunanin sakacin mu ne da tun muna qarama muka barta take yanda take so har ta lalace haka?
Likitan yace aa ba daga gareku bane laifin ku daya na rashin bincike a kanta tun tana qarama sai a ynxu wannan lokacin da abin ya dadi sosai a kanta, baka observing nata sometimes xaka ganta kamar normal tana abubuwa kamar na masu hankali wani sa'in kuma sai abin ya rikice, ynxu ma qarin abin yayi yawa ta shiga damuwa ne a baya, sannan mai irin wannan cutar ta ta, baa masu fada dan su gyara sam, rarrashi da ban baki cikin tausayi shi xai saka sannu sannu ta daina abin da take, idan tayi ba dai dai ba kada ku mata fada shi ke qara tunxurata ga maida maku magana, kuyi mata ta rarrashi yanda xata fahimta ku nuna mata bai dace ba, sannan kuriqa bata labari mai ban tausayi da shiga rai shi xai saka ta tunani in tayi ba dai dai ba.
Yanxu likita wane taimako xaka mana ina son uwani ta gyaru ta dawo cikin nutsuwar ta, ko nawa ne kudin aikin nata ka gayamin xan iya biya idan dai xata dawo normal kamar kowa.
Likitan yace ka kwantar da hankalinka, insha Allah xan qara bincike akan ciwon nata daga nan xuwa wani sati mai xuwa kadawo.
'Abba yayi godia sosai yana fitowa ya sami uwani sai kumburi take kamar xata fashe,
Tana ganin sa ta nufe sa,
'Abba tun daxu ka shige ka xauna ka barni anan sai kallona ake, shi wancan harda cewa yana sona ya dauka baxan koma gidan mijina ba.
Baiyi magana ba yace bani kudin da na baki riqo,
Tace lah abba ai tuni na bada su aro,
Aro? Ya tambayeta cike da mamaki,
Tace eh wallahi ai wani ne yaxo siyan magani anan baida kudi shine na ara masa nayi masa kwatancen gidan mu gobe xai kawo mana, iyakar gaskiyarta take magani babu damuwa a tare da ita.
Yace kin sanshi ne,
Tace aa
Yace shikenan Allah ya bada ladan sadaka da kika min da kudin dole na yafe,
Tabi bayansa tana fadin yanxu abba saura shopping din ko,
Yace bayan kin kyautar da kudin,
Haba abba ai yace xai maida fa...
Bayan sun dawo shopping ajiye ta gida yayi ya nufi masallaci.
Tan gama ciye ciyenta ta dauki qatuwar jakar da ta shirya kayanta daxu tana fadin na lura abba baqin ciki yake min da shiga jirgin nan shiyasa yace na jira muje tare alhali ba inda xaije shi kullum yana hanyar xuwa masallaci gashi anqi a bashi ko limamin masallacin duk wannan gemun da ya ajiye a fuskarsa.
Nasan dubu biyar goma xasu kaini Germany tunda ance da tsada ake shiga, el'mustapha ko jiddah xasu min na dawowa.
Taja jakar ta fito, napep ta shiga ya kaita airport.

Ga jirgi kam uwani tana gani amma an hana mata shiga, tayi fada harda xage xage wanda ya janyo da yawa mutane a gurin suna mata kallon tababba in ba haka ba taya xata xo da kudi dubu goma tace na shiga jirgine kuma wai Germany xata je kamar mai shiga mota xuwa wani gari, har fadi take tana so taga driver jirgin taji dalilin sa na yi mata baqin ciki da karban kudin ta.
Tana tsaye jirgin ya daga, gurin ta xube tana kuka sosai kamar ranta, da farko kafin ya tashi sama har da binsa tayi da gudu tana ihu bata bar wurin ba har dare.

Haka ta tattara ta dawo gida, abba ya fito neman inda taje ya ganta da jaka shabe shabe da hawaye.
*
Dr Merah ya shigo dakin da sassafe, ward round kamar yanda yake yi kowace Safiya kafin ya isa office din shi.
Yayi mamakin samun jiddah ita kadai a dakin tunda yake xuwa ita da el'mustapha yake samun ta ko wace Safiya kuma ai yaga el'mustapha xaune a waje me ya hanasa shigowa, tabbas akwai matsala,
duk da halin-sa-ido ba halinsa bane amma wannan dai confrontation ne like a chase game da yakeson ganin yanda xai qare, el'mustapha a waje ba walwala, jiddah a ciki cikin damuwa.
dan haka yake ganin bai kamata ya kira sa-idon nasa da sunan sa-ido ba sai dai ya kirashi curiosty wanda haline na kowane dan adam akan abinda ya bashi mamaki musamman shi da yake ganin el'mustapha yanxu abokin sa ne, jiddah kuma patient din sa ce.
Bayan ya gama duba ta, kallonta yayi yana fadin lailah ina majnun ya akayi na same ki ke kadai yau,
Murmushi kawai tayi tana kallonsa,
As a professional medical doctor a take dr.merah ya gano cewa akwai damuwa a tare da ita daga yanayin ta, yanda ya san ta da fara'a.
Kujera ya janyo ya xauna yana fuskantarta,
Akwai damuwa jiddan musty ne ko ya kuke cewa, nagano patient dita tana cikin damuwa ni kuma bana son ganin ta cikin damuwa, kullum naxo xan same ki tare da mijin ki, yau kuma meyasa?
Tayi rau rau da idanunta kafin tace ba komai, ya dan fita ne.
Aa jiddah, your eyes shows akwai matsala, idan akwai abinda xan iya taimaka maki just take me as your brother ki gayamin,
Ta bude baki da kyar tana kallonsa, aure yake so ya qara...
Aure? Dr merah ya tambaya cikin tsananin mamaki, meyasa yake son qara auren?
Tace saboda na nakasa yake son qara aure bayan ya manta dalilin sa na fada wannan halin, saboda son da ake mashi aka nemi kasheni a rabani da duniyar..... ta soma kuka sosai har ranta.
Shiru dr merah yayi amma jikinsa yayi sanyi sosai, kuma el'mustapha ya bashi mamaki, kukan jiddah na qara tayar mashi da hankali.
Yace kibar kukan jiddah, nasan el'mustapha yana matuqar son ki, bana jin saboda kin nakasa xai qara wani auren ballantana Ma baki nakasa ba jiddah, xaki tashi aikin da aka maki is successful, nan da wata daya xuwa biyu xaki fara taka qafar.
Ta dubesa idanunta jawur, yana sona ne baxai xauna dani hakan ba.... Ya katse ta,
Ni nasan el'mustapha baxai qara aure ba ki kwantar da hankalin ki, kidaina saka damuwa a xuciyarki kinga baki da lafia, idan har el'mustapha xai qara aure baxai gayamaki a wannan halin da kike ciki ba domin yafi kowa sanin condition din ki, el'mustapha yasan *Labari na* dana gidana, haka shima ya bani nashi har dalilin wannan ciwon naki amma bai taba gayamin yana son wata ko niyar aure ba.
Xai iya gaya maka komai amma baxai taba gayamaka yana cin amanata da mai aikina ba, ita yake so a yanxu kuma ita yake son aure, ka gayamin ina adalci anan, ina son da yake ikirarin yana min idan har xai iya auren yarinyar dana raina a hannuna?
Dr merah ya bata fuska alamar fushi mai tsanani a tare dashi, idan har da gaske kike abinda kika fada el'mustapha bai kyauta ba kuma baxai taba auren yarinyar da kika rena ba sai dai ya auri wata can d..... Jiddah ta katse sa,
Wata din Ma baxai aura ba, a hakan xai xauna dani ko yana so ko baya so, idan har dole sai ya auri wata ni baxan xauna dashi ba, baxan yarda na qara cutar da rayuwata ba duk da na farkon nice sanadi ni na jawa kaina.
Murmushi merah yayi ganin yanda take magana cikin seriousness, ya tashi yana fadin xan turo maki el'mustapha, baxan lamunta da wannan fushin da kuke da juna ba, kuma ina goyon bayanki karki yarda ya qara auro maki wata, idan yace xai qara aure xan gayamaki wani sirri da Afiya ke min barazana dashi a duk lokacin da na kalli wata ko nace xan qara aure koda da wasa ne.
Tayi murmushi cikin jin dadi tana kallonsa tana mamakin girman qasaitarsa tana mamakin yanda yake furta mgn da kyar, duk mgnr da ke fitowa bakinsa idanunsa akan wayarsa wanda idan bata manta lbrn Yarima maina ba da Sarautarsa data qaryata qasaitarsa(masu yawan tambayata labarin dr Merah kuduba littafin mulki ko sarauta a wattpad)
Ya dago yana kallonta,
El'mustapha baxai qara aure ba jiddah, yanxu na xama yayanki baxan bari a qara cutar da ke kamar a baya ba, kema sai kin dage damtse wajen saurin yarda da mutum da bashi amanarki.
Tace nagode... Ya juya ya fice cikin tafiyar sa ta qasaita, yana fitowa ya hadu dasu yusrah sun shigo suka gaisa kana ya dubi el'mustapha yaja hannunsa suka nufi office din sa.
Aure kake son qarawa el'mustapha meyasa? Dr merah ya tambayesa idanunsa akan laptop kamar ba shi bane ke tambayar.
El'mustapha ya qara bata fuska, wato jiddah tana gayawa mutane aure xai qara... Jin shiru ya saka merah kallonsa,
As a friend, ban boye maka kaina ba kai kana boye min, banyi mamaki ba tunda har xaka iya cutar da innocent girl like jiddah ka munafunceta kana tare da mai aikinta, dan me ni baxaka munafurceni ba nida haduwar asibiti ce?
Murmushi ya subulcewa el'mustapha, yanxu abin ya daina bashi haushi,
Yace a tunanin ka saboda me xan qara aure saboda me xanci amanar jiddah?
Yace saboda kana ganin ta nakasa....
'Ashe bakin ku daya da jiddah cewar El'mustapha, ban sani ba ko kai ke shirya mata wannan saboda nasan halin jiddah bata da wannan xafin dana gani a tare da ita jiya.
Dr merah ya dube sa, yace eh nine ke shirya mata me xaka iya yi, idan kai mijinta ne ni kuma qanwata ce kuma patient dita baxan so naga an cutar da ita ba.
El'mustapha yayi murmushi yana fadin ba abinda xan iya yi amma komai mulkin mutum da sarauta baifi qarfin Shari'a ba