Showing 117001 words to 120000 words out of 138779 words

Chapter 40 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

2002

matata ce, mahaifiyar ta tabar duniya tun jiddah bata da wayo haka ma mahaifinta, iyayen dake riqon ta a yanxu suna da tabbacin cewa iyayen jiddah sun dade da mutuwa, wace Zubaida kuma ake magana?

Kwantar da hankalin ka yaro na, ya sunan ka? Merah ya tambaya yana kallon sa.

Sunana El'mustapha,

Sarki yace Zubaida 'ya ta ce, ma'ana d'iyar qanina ce itace babbar yar'sa.

Zubaida yarinya ce mai nutsuwa da haquri duk gurinnan kowa yasan da haka, duk suka jinjina kai cikin gamsuwa.

Kowa yasan zubaida bata da hayaniya kuma bata da son abin duniya kamar sauran qanninta maxa domin ita kadai ce mace.

Zubaida ta fara canxa hali daga ranar da ta hadu da wani saurayi a makaranta can London.

Ta dawo wata irin yarinya da bata jin maganar kowa saboda yaron, shi kadai xai gaya mata taji ko ta bari, ta dauki soyayyar yaron ta saka a xuciyarta wanda ta kai ko karatu ta daina maida hankalinta akan sa.

Duk mutunci irin na family din merah sai ga zubaida ta dawo da wata dabi'a ta marassa mutunci, tana shan wannan abin da naga kwanaki sultan yana sha har na hanasa, menene shi ya tambayi umma yana kallonta.

Tace ranka ya dade bansan da wannan maganar ba, qila hajiya ce,

Ammi tace wannan abin mai fitar da hayaqi kake nufi, kamar shisha naji suna cewa.

Yace yauwa, ita, zubaida da shan wannan abin, hankalin mahaifin ta ya tashi ranar da kanshi yaxo ya sanar dani halin da ya sami zubaida, tana mace ta lalace ina ga sauran maxan.

Nasa aka kira min ita taqi xuwa, sai na aika mata Maina saboda shi nasan tana tsoron sa baya sake mata fuska.

A tare suka xo, kallo daya nayi wa yarinyar na gane bata cikin nutsuwarta kwata kwata kamar ba zubaida ta mu ba,

Fada da nasiha ba wanda ban mata ba anan, ta kuma nuna ta daina sha.

'Ashe a boye tana sha, ta girmi Maina sosai yana matsayin qanin ta amma shi xai iya mata magana taji, tun daga lokacin da ya mata magana kuwa ta daina sha.

Bayan wani lokaci ta koma makaranta, Allah ya sa a lokacin naje London yin wani abu, sai na kai mata ziyarar baxata kamar yanda nake kaiwa Maina da Afiya sanda suna makaranta.

'Na same ta da wannan yaron cikin gidanta, banda gansu suna wani abin Allah wadarai ba amma alamu sun nuna hakan daga yanda na same ta da wasu kaya a jikin ta shi kuma da gajeren wando.

Duk mutunci da tarbiya irin na zubaida har tasan ta kawo wani namiji ta xauna dashi a gidan ta ba mijin auren ta ba,

Ban mata komai ba amma raina ya baci sosai, na saka ta hada kayanta na dawo da ita Nigeria.

Duk kukan ta da magiyar ta bai sa na barta acan ba kuma na saka maina ya dake ta da bulala kafin iyayenta suji me ta aikata.

Dalilin wannan mahaifinta ya fitar mata da mijin aure, a lokacin ta nuna masa bata son xabin da yayi mata lallai ita tana da wanda take so suka yi alqawarin aure.

'Ko da na bincika na gane wannan yaron ne dana gansu tare acikin gida, sai na goyi bayan mahaifinta baxata taba auren wannan yaron ba.

Ana gobe auren ta tabar masarautar nan, ta gudu ta bar iyayenta cikin kunya da baqin ciki,

Bayan zubaida har yau babu wanda ya taba mana abinda tayi mana kaf a zuri'ar nan, amma ina ganin wannan yaron mai rawar kai sultan xai gwada, na gayawa mahaifin sa ya gargadi wannan yaron nasa baxai ji dadi ba idan na nuna masa halina.

Babu mai hawa mota ta a gidannan sai shi yana min ta'asa da ita, ya bige wannan yau ya bige wannan gobe ta kai har abokinsa yake bawa motata, ko danayi xamani na talakawa suna sona da mutunta ni bana kyamatar su ko kadan, haka mahaifin sa ma  amma shi na rasa dalilin da yasa baya son talaka ya rabe sa ko kadan, idan kun kasa yi matsa tsaye ni xan dawo dashi nan gidan baxan dauki wannan iskancin ba.

Rumaisa tace wai abba sultan naka kake yiwa haka, me yayi ma haka kwanakin nan baka da magana sai tasa.

Yace saboda ya bata min mota ne, falon suka yi dariya banda jiddah da el'mustapha.

Ammi tace kishi ne ke damun mai martaba banda haka banga abinda mijina yayi ba.

Rumaisa tace kyale shi ammi, yaya Bilal sai ya gyara masa motar ba shikenan ba, shi kuma sultan ya tsaya a tasa motar.

Sarki yace duk da haka sai sultan ya dawo xama gidannan idan har bai canxa ba.... Ya cigaba da fadin,

Mahaifiyar zubaida dama ta dade da rasuwa tun zubaida na nan gida, step mom din tace ke riqon ta dama, tafi kowa shiga damuwa saboda tana ganin tarbiyar yarinyar a hannunta yake kada a xargi itace ta bata yarinya.

Bata dade da guduwa ba ta turo mana saqon tayi aure, ta auri wanda take so sunan shi Ahmed.

Banda labarin zubaida ta dawo gida sai bayan tafiyar ta, ashe dangin mijin nata basa son ta ko kadan, sun adabi rayuwarta wanda dalilin haka zubaida ta dawo gida neman sulhu da iyayenta.

Sam mahaifin nata yaki karbanta har ya gargade ta da kada ta qara dawowa gidan tunda ita ta barshi da kanta kuma ta kunya tasa a idanun jama'a abinda ya'yan sa maxa basu masa ba sai ita da take mace.

Nayi masa fada sosai saboda babu wani cigaba ga korar 'ya mace baisan halin da xata je ta shiga ba, ya kamata a duba mata.

Zubaida bata yi qasa da gwiwa ba ta sake dawowa nan gidan amma tare da mijinta, tana kuka take roqon gafara a roqa mata mahaifinta ya yafe mata.

'Na lura mijin yana son ta gaskiya, tun daga lokacin da suka bar nan ban qara saka ta a idanuna ko labarinta ba kuma ba wanda ya taba cewa ya ganta a wani gu, na dai san mijin yace xai bar yan uwansa tun basa son zubaida kuma shi kansa saboda dukiyar sa suke tare dashi har suke son aura masa wata yar uwarsa.

Sai bayan wasu shekaru ne yan uwan mijin nata suka aiko mana saqon mutuwar zubaida, mijin ta ya rigata rasuwa kafin ita, amma bamu taba sani ba kuma bata neme mu ba, kuma basu taba gayamana cewa akwai rabo tsakanin su ba.

Da munsan da cewa ta bar 'ya da tuni mun dade da nemo ta ba sai anyi riqon ta a wani guri ba,

Zubaida ta saka maki Hauwa saboda sunan mahaifiyar ta ne, sai ta boye sunan tana kiran ki Jiddah.

Su waye suka riqe ki jiddah ko yan uwan baban ki ne.

Jiddah ta girgixa kanta a hankali, tana jin wata nutsuwa na shigo ta, ta ko ina, tana jin kanta kamar ba ita ba, idan mafarki take kada Allah ya tada ta a wannan barcin tafi so ta dauwama cikin mafarkin, ta rasa wane irin farin ciki xatayi, wace godiya xatayi wa Allah, amma ita a gurin ta abin kunyane ace yan uwan babanta sun kasa riqeta,  ta yarda lallai haqurin ta shi ya kawo ta ga hakan.

Ta kasa magana, jikinta rawa yake sai motsa baki take tana son magana,

Talk jiddah... taji muryar el'mustapha na mata magana, ta dago a hankali tana kallonsa, ya gyada mata kai alamar tayi magana.

Ta share wasu hawaye kafin ta hadiye yawu da kyar tana kallon Mai martaba.

Tace basu bane, aminiyar ummana ta riqeni, sanda na taso na fara wayo suka gayamin dalilin da yasa ummana ta bada ni a gurin su saboda dukiyar babana kawai yan uwan sa suke so, bayan mutuwar sa ba yanda basu yi ba dan su karbi dukiyar hannunta taqi badawa, sai da ta soma rashin lafiya ne sai ta raba dukiyar biyu ta raba masu kana ta bawa wadanda xasu riqeni sauran da cewa su kula dani da amana.

Amma ni nasan ummana, har yanxu ina ganinta a idanuna, nasan mutuwar ta amma bansan waye babana ba, tun banyi wayo sosai ba akace ya mutu.

Kuma wadanda suka riqe ni sun sha kaini dangin mahaifana suna min wulaqanci baxasu karbeni ba, tun daga lokacin hajiya da abba basu qara kaini ba har sanda na girma na mallaki hankalin kai na.

Amma yanxu alhamdulillah sun waiwaye ni kuma suna bani kulawa tun sanda na sami matsalar qafafu sunxo ganina kuma har Germany ma sun je.

'Na sami iyayen kirki masu amana sun riqeni da xuciya daya dai dai da minti daya basu taba min gorin rashin iyaye ko wani abu nasu ba, sun bani tarbiya da rayuwa mai kyau wadda har gobe da su nake taqama.

Sannan Allah yayi min kyauta ta biyu da Miji nagari, wanda yasan kansa da haqqin aure, wanda ya jajirce wajen nunawa duniya ni kadai ce tasa farin ciki na shine nashi, ya bani soyayya da kulawar sa tun ban fahimci menene auren ba, ya soni sanda ina mutum kuma ya soni sanda bani a mutum sanda na nakasa, ko sau d'aya bai taba nuna kyama ko son gujemin akan abinda ya same ni ba, shi ke rarrashi na yana kwantar min da hankali har xuwa sanda na sami qafafuna suka dawo min, ta sa hannu tana goge wasu kwallah shine farin cikina, farin cikin rayuwata da ya'ya na,.....

Su umma suka ce alhamdulillah tun da kin sami rayuwa mai kyau jiddah, babu abinda ya kai farin ciki a duniyar nan kamar samun iyaye na gari da miji nagari sune abokan rayuwa.

Afiya tace amma duk da haka umma na tausaya mata duk yanda wani xai riqe ka baxai kai na jinin ka ba, tsakanin harshe da haqori aka sami matsala ballantana mutum da mutum, ai ko yane sun taba bata maki ko jiddah, duk da sunyi qoqari amma baa rasa wani abin.

Jiddah tayi murmushi kawai ta sunkuyar da kanta,

Rumaisa tace ashe jiddah yar'mu ce, she is our daughter.

Mai martaba yace jiddah baki gayamin me ya sami qafar ki ba, kinyi accident ne?

Gabanta ya fadi ta dubi el'mustapha, budar bakinsa sai cewa yayi.

Just tell them jiddah, they are your family...

A hankali ta bayyane masu komai da ya faru da ita tun bayan auren ta har kawo yanxu da haduwar su da merah.

Wacece wannan uwanin? Afiya ta tambaya tana tasowa daga kinshingiden da tayi, wane mataki aka dauka akan ta?

Jiddah tayi caraf tace, el'mustapha ya yanke mata hukunci, kuma iyayen ta sun... Afiya ta katse ta,

'Wannan ba hujja bace, saboda mijinki yarinya ta cutar dake kice iyayen ta, meke damun ki, she is trying to kill your son in front of you har kike maganar an hukunta ta, wane hukuncine aka mata, qafarta aka cire ko hannun, ita wace irin xuciya ce da ita, har take iya fuskantar ki ta qara auren mijinki batare da kin cire mata kai ba, kinsan yanda nayi da nabila yarinyar da ta yaudari mijina da iyayena ta tarwatsa farin cikin gidanmu, lallai baki da xuciya irin tamu kamar ke ba jinin sarauta ba.

Afiya ho, why ol dis tace fa ta yafe mata beside ma ai mijinta ya hukunta ta akace,

Afiya ta tashi tana fadin ni wannan hukuncin bai min ba, sam baa ma jiddah adalci ba, abba kayi wani abu akai.

Jiddah tace nifa na yafe mata, dan Allah ku kyaleta komai ya wuce, iyayenta sun bada haquri sun nuna damuwa, yanxu idan nace yan uwana su ramamin abinda ta min xasu ga ban masu kara b.....

Shut up please, Afiya ta katse ta a fusacce, xatayi magana ammi ta katse ta ita,

Meke damunki afiya?

Amma ammi.... Sarki ya katse ta,

Ba ruwanki wadda aka ma laifi tace ta yafe, ba ruwanki.

Afiya tace Allah ni abba ko yanxu na ganta sai na kifa mata mari, na tsani yarinyar, ta fice ta bar falon.

Rumaisa ta soma dariya tana fadin kishi ke damun afiya kun sani, indai akan miji ne bata hada komai dashi ba.

Sarki yace ai magana ta qare yanxu, jiddah jikanya ta ce, ki aikawa iyayen naki gobe su xo ina son na gansu, kakan ki mahaifin zubaida baya qasar dama gobe yake dawo wa, ya dubi rumaisa yana fadin kira min maina yaxo gobe ina son ganinsa.

Xaa hada jiddah da dangin ta, tasan su suma sun Santa.

El'mustapha yayi godiya cikin farin ciki, haka yake ji kamar shine gaban iyayen sa, ashe jiddah yar dangi ce, yaji girma da matsayinta sun qaru a xuciyarsa.

Sarki yace amma jiddah baxata bi ka ba tukunna, a barta yau xuwa jibi acikin yan uwanta.

Farin cikin dake fuskar el'mustapha ya gushe, ya bata fuska, taya xai iya bar masu jiddah har tsawon kwana biyu, ina Ma laifin yaje da ita gobe ya dawo da ita ta yini tare da su.

Rumaisa ta tashi tana fadin xo muje daughter mu, ki saki jikinki damu kamar daman kinyi rayuwa damu, mu yan uwan kine.

Jikin jiddah yayi sanyi daga yanayin fuskar el'mustapha da take kallo,

Rumaisa taja twins suka fita tana kiran, I love them masu kyau kamar baban su.

El'mustapha ya fito dauke da airah, jiddah ta biyo bayansa suna fitowa ta dube sa,

Ka daina fushi abinda baka so bana so xan bika...

Tausayinta yaji yayi murmushi yana fadin ko bana so dole na haqura na barki kiga yan uwanki, I will miss you so much, ni kadai a wannan gidan yau, nima gidan mu xanje na kwana jiddah.

Ta fashe da dariya tana kallonsa, kaxo mu kwana anan jiddatulmusty, gidan xai maka girma yau.

Wallahi kuwa jiddah.

Ta riqo hannunsa tana fadin ai ba yanxu xaka je ba sai anjima, xo muje ka kira su abba a waya ka gaya masu saqon sarki.

Suna haka kiran merah ya shigo, el'mustapha ya dauka kafin yayi magana yaji merah na fadin,

Yanxu  ake min albishir jiddah yar anti zubaida ce, ina tayaku murna,

El'mustapha yayi dariya yana fadin ashe kai suruki ne,

Merah yace Allah kuwa girma ya qaru ta tashi daga qanwa ta dawo daughter so be careful in ba haka ba auren ma sai na raba shi.

El'mustapha yayi dariya yana fadin rufa min asiri, matata babbace jinin sarauta kada kamin baqin ciki.

Sukayi dariya lokaci daya, kafin su kashe wayar.

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

64

Jiddah ta dube shi tana fadin,

Kaima ka dauki wannan dabi'a ta uwani,

Aa amma gaskiya na fada, babu wata dabi'a ta uwani da mutum xai yi koyi da ita.

Tace haka ne kam, xo muce na nema maka abinda xaka ci, nasan kana jin yunwa a yanxu.

Da girman kujerar ki jiddatulmusty duk yanda kika ce haka xaa yi, yabi bayanta.

El'mustapha bai bar gidan ba sai dare shima sai da jiddah ta fara masa qorafi kada dare yayi.

Jiddah Kora ta kike yi?

Aa, ni na isa, bana so ne kayi dare.

Baiyi magana ba, ya tashi ya fito, da sauri jiddah tabi bayansa, tana kiran sunan sa yayi mata banxa alamar yayi fushi.

Ya shiga motarsa yana qoqarin tadawa tayi saurin shiga motar, key din ta riqe tana kallonsa,

A hakan kake so mu rabu, kaje kana fushi dani, laifin me nayi.

Baiyi magana ba,

Tace to shikenan fito mu koma kayi ta xama el'mustapha ni baxan hana ma, idan kuma xan bika ne muje gida ka gayamin naje na dauko airah.

Ya gyada mata kai alamar eh taxo su je.

Harta juya xata fita ya riqo ta,

Jiddah sarkin wayo, yanxu fisabilillah ni kadai xan kwana a wannan gidan.

Allah ya gafartawa mama, da nace yau kaje ka kwanta a bayanta.

Murmushi kawai yayi batare da yayi magana, ya sake ta yana fadin goodnight jiddah.

Itama murmushin tayi amma bata fita daga motar ba,

Ya kai bakinsa dai dai nata ya sumbata, yace xan kiraki anjima.

Batayi magana ba, ta fito daga motar tana kallonsa cikin murmushi.

Tana tsaye a gurin har ya fice, tana shigowa falo rumaisa tace,

Ke bakya gajiya da wannan mijin naki, yinin yau duk tare kuka yi, ina ji ma kin manta da twins dinki, ko da yake naki mai sauqi ne akan gimbiya afiya.

Afiya dake cin Apple ta dubi jiddah tana fadin,

Karki biyewa wannan matar, ki riqe mijinki gam ni a hakan ma naga kina sake dashi.

Jiddah murmushi kawai tayi ta xauna,

Rumaisa tace Allah Afiya   yarinyar nan ba sauqi,

Ke ni kimin shiru haka, cewar afiya tana kallon rumaisa idan bata riqe mijinta ta kula da shi ba wa kike so ta riqe, an gayamaki kowa ma irin kine, Allah idan kika yi wasa sai na nemowa yaya Aliyu mata ta biyu ya aura, classic baby, hot ones kinsan irin bebs dinnan dake bibiyarsa ai, wadanda xasu kula dashi s.... Rumaisa ta katse ta tana fadin,

Sai me, kinsani duk macen da xai so yanxu bayana take, wallahi sai naje na nemo nabila na dawo da ita a gidannan, dama ta fiki son yaya maina kowa tasa ta fiddashi.

Afiya ta jefar da Apple din dake hannunta tana kallon rumaisa,

Allah yau sai kin maimaita mgnr nan a gaban mai martaba, ina ji an miki magana akan hada ni da kike da wannan banxar ko.

Rumaisa tace ina ruwana ke waye yace kice xaki hada yaya Aliyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login