Showing 105001 words to 108000 words out of 138779 words

Chapter 36 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

2014

gidana tamkar tashin bomb ne a Maiduguri.

Believe me ibrahim, ina so ka auri uwani saboda kasan halinta kasan wacece ita xaka iya xama da ita, ina so ka aure tane saboda nasan baxaka cutar da ita ba, ba kowane namiji ne a duniyar nan xai iya xama da uwani a hakan ba, dan Allah ka aure ta ka koya mata sonka wallahi xata so ka xata nutsu, ina sa rai uwani xata gyaru amma ni baxan taba iya gyara ta ba saboda ta rainani.

Ya tashi yana fadin matar abokina kike so na aura, yarinyar da bata da tarbiya ba wanda ya isa ya fada mata ta ji, so kike nima ta saka matana acikin wani hali ta tarwatsa xaman su.

Jiddah ta tashi tana kallonsa El'mustapha bashi da matsala ibrahim, shima xaiyi farin ciki da hakan, iyayen mu xasu ji dadi ace yau uwani tayi aure ta nutsu ka taimakeni ka taimaki soyayyata da el'mustapha.

Ibrahim ya tabe bakin sa ya juya yana fadin we talk later jiddah idan nayi tunani.

Tace tau shikenan, ta nufi cikin gida, tayi mamakin sunyi saurin gama abincin rana haka har suna rabawa maaikatan gida, gashi ita yanxu take shirin dorawa, sha biyu har ta gota.

Hadixa ga airah ayi mata wasa, idan tayi kuka ki goyata in taqi sai ki kawo min ita.

Ta dawo cikin gidan a hanxarce, dakin el'mustapha ta fara nufa ta duba shi kafin ta dora girkin.

Xaune ta same sa bakin gado ya dafe kansa da hannunsa daya, ta qarasa gurin sa da sauri ta dafa sa tana fadin,

Ya jikin, har yanxu hannun yana ciwo ne?

Ya girgixa kansa a hankali,

Get me something to eat,

Sai a lokacin ta tuna ko breakfast bai yi ba, ya tashi ya nufi toilet, ta fita........

Su abba sun tafi ne, ya fada yana kallonta bayan ya xauna a dining,

Sun jima da tafiya sunce a gaida ka da jiki.

Ya gyada kansa kawai batare da yayi magana ba.

Ta cigaba da ciyar dashi......

El'mustapha ya tsayar da cin abincin da yake ya xuba mata narkakkun idanuwansa cikin mamakin jin abinda take koro masa,

'meyasa ibrahim xai auri Uwani, ke kina gudun ta kuma kike liqawa wani, wanda ya riga ya san halinta?

Amma El.... yayi saurin katseta, ibrahim baxai taba iya auren uwani ba, ya bani lbr tsanar da yayi wa yarinya, bayan wannan Ma meyasa xaki kira anty ikram ta fitar da uwani a gidannan, idan a gaban iyayen ta kin amince ta xauna sun tafi sun bar ta saboda me xaki tura ta daga baya, why jiddah?

Meyasa uwani xata cigaba da xama a gidannan, tana xama gidannan before saboda karatu da aure yanxu kuma babu xaman me xata min a gida.

Mtsew yaja tsaki hade da ture plate din arish dake gabansa, tashi yayi ta biyo bayan sa tana fadin,

Breakfast din fa, nasan baka qoshi ba, baiyi mgn ba dakin sa ya nufa, wayarsa ya kunna kafin ya xauna bakin gado yana dialing number Abba, bata jima da fara ringing ba ya dauka.

'Abba ya hanya,

'Alhamdulillah mun iso tun daxu, ya jikin naka,

'Jiki 'Alhamdulillah, Uwani ta iso kuwa?

'Abba yace aa tana hanya ne?

El'mustapha yace tana hanya, idan ta iso ta huta xuwa gobe ka turo min ita,

'Abba yace ba dai wani abin tayi ba ko?

Yace aa,

Tau shikenan abba ya fada yana tsinke wayar.

Jiddah ta tsura masa idanu, xuciyarta na bugawa me el'mustapha ke nufi da uwani ta dawo, yana son xama da ita ne kada dai el'mustapha yana son uwani ne a yanxu, indai har uwani xata dawo ta cigaba da xama a gidan tabbas xata barshi kuwa.

Meyasa uwani xata dawo el'mustapha? Ta tambaya tana kallonsa idanunta cike da kwallah.

Fada ko bacin rai bashi xai gyara uwani ba, rarrashi da tausayi shine xai gyarata, ni xan iya xama da uwani na gyara ta.

Xaka iya xama da uwani ka gyarata bafa matar ka bace You know it, ko dai kana son ta ne kana son maida auren ku kake min yawo da hankali, da can da take matar ka baka gyara ta ba sai yanxu da ba aure tsakanin ku.

Kallonta yake cikin ido, yace duk yanda kika dauka hakane, in ma son ta nake in ma auren ta xanyi, I have the right.

Tace hakane nasani kana da iko el'mustapha bayan uwani ma xaka iya auro wasu biyun ka aje, ta juya ta bar dakin da sauri, kitchen ta nufa duk da xuciyarta ba dadi bai hana mata dora girki ba sai dai tana yin komai ne tana sharar kwallah cikin damuwa.

*

Hajiya sun koro ni, hajiya xo kiga yanda suka koro ni da komai nawa saboda ana min baqin ciki xan xauna da el'mustapha ko tsinke nawa baa bari a gidan ba, harda cewa naje na auri nawa mijin.... Shine abinda uwani ke fada lokacin da ta shigo harabar gidan kusan magrib kenan, abba na shirye shiryen xuwa masallaci.

Ya tsaida idanunsa akanta yanda ta xube gurin tana kuka kamar qaramar yarinya,

Yace uwani sai yaushe xakiyi hankali kisan kin girma ne, menene amfanin wannan abin da kike,

'Abba koro ni sukayi, dubi kayana gabaki daya na dawo dasu, jiddah tace na xauna amma ita wannan yayar tana xuwa ta fito dani da qarfi, sai kaga yanda take turoni na fito gidan kamar gidan ubanta, ni ba wannan ne damuwa ta ba yanda ta saka ni gyaran gidan gabaki daya na share nayi mopping, nayi wanke wanke har da wanki ta sakani abba bayan ga masu yi ga washing machine amma tace lallai sai ni, uwani ta cigaba da kuka.

Yace to menene dan kinyi ai yar uwarki kika yimawa, qila taga bakyason aiki ne ta saka ki ko kin mata rashin kunya ta koro ki, banda haka ni ban yarda xaa iya koro ki gidan a gaban jiddah ba kuma ta kyale.

Wlhy koro ni suka yi abba, wai inje in nemi mijina harda cewa idan naqi xasu saka bindiga su harbeni na mutu kowa ya huta dama babu mai sona.

Yace amma el'mustapha ya kira idan kika huta xuwa gobe kije yana neman ki,

Tayi wuf ta tashi tana kallonsa cikin bude ido.

Yaushe ya gayamaka hakan, ya kira ka ne, amma shine abba ka barni tin daxu ina surutu kaqi gayamin ai da yanxu na dade da kai.

Yace kije ina yanxu uwani ai kin bari har gobe idan kin huta yanxu dare yayi.

Wallahi abba yanxu xanje ai baxan iya barci ba, ni ba sai na huta ba.

Yace to baxakije a yau ba sai gobe ynxu dare yayi har yaushe kika je.

'Abba dan Allah ka barni kaida baka min baqin ciki kuma kake hanani komawa, haba abba daxu ina barci a mota har mafarki nayi muna aljanna banda yan baqin ciki.

Ki xauna ba inda xakije, ya fita da sauri xuwa masallaci.

Uwani bata may shiga cikin gidan ba ta bude katuwar jakarta ta dibi wasu kaya ta saka a qaramar jaka ta fice tana murna, el'mustapha yana son ta yana son xama da ita amma ana mata baqin ciki dashi sai ta koma.

Fitowar jiddah daga daki yayi dai dai da dawowar el'mustapha daga masallaci, ta gabatar mashi da abinci fuskarta ba annuri, ta qarasa tsakiyar falon ta xauna tana duba arham da aka maido mata saboda xaxxabin da yake.

Xaka ci abinci naxo na baka, ya girgixa kansa yana kwantawa cikin jikinta,

Mummy kibani magani,

Ba yanda xaa yi kasha magani babu abinci a cikin ka, bari na kawo maka ko yoghurt ne kasha, ya qanqameta yana kuka,

Ni bana so kibani magani nasha,

Ba wani magani da xan baka yanxu arham, paracetamol na airah I don't think xai maka aiki, ko xamuje asibiti ne?

Ya girgixa kansa yana qara shigewa jikinta, jikinsa yayi xafi sosai har bata son yana shiga jikinta,

Duk abinda suke el'mustapha na sauraren su yana cin abincinsa, yana gamawa ya tashi ya bar falon, arham kuwa ya soma amai sosai hankalin ta ya tashi.

Hadixa taje ta kira ta gyara gurin kana ta dauke shi ta nufi toilet dashi, wanka tayi masa ta shiryasa ko ta kan airah bata bi ba ballantana el'mustapha ta dauki key din mota ta fita.

Har goma na dare bata dawo ba tana xaman jiran likita, dai dai wannan lokacin uwani taxo gidan, tana shiga falon idanunta na sauka akan dining, ta jefar da jakarta da gudu ta nufi dining da alama yunwa take ji sosai.

Shiru shiru el'mustapha baiji motsin jiddah ba tun yana wasa da airah da ta tashi tun daxu har ya soma gajiya da alama yarinyar kuka take son farawa yanda yaga tana mutsuniya.

Ya dauko ta ya fito da ita anan yaci karo da uwani xaune sai loda abinci take a cikinta,

Ita wannan yaushe taxo gidan? Xaiyi amfani da son da take masa da kuma tsoron anti ikram da take wajen ganin ya gyara rayuwarta.

Yaushe kika xo gidan waye ya baki ixinin ki xauna kici wannan abincin?

Ta xuba masa idanu bayan ta dago tana kallonsa, nan take taji gabanta ya fadi wani tsoron sa ya risketa lokaci daya,

Tace kayi haquri,

Ya tako a hankali har xuwa inda take, ya xauna yana fuskantarta cikin jijjiga airah,

Ke da nace sai gobe ya akayi kika dawo cikin wannan daren,

'Na kasa haquri ne nasan xaka maidani dakina kada kamin baqin ciki kasan ina son ka.

Yace kinyi sallah kuwa?

Tayi caraf tace ai banayi tun jiya bana yi, kwana hudu nake yi na ga.... yayi saurin katse ta,

Kin san meyasa nace kixo?

Ta girgixa kanta da sauri tana sud'e yatsun hannun ta,

Ai nasan kina sona ko uwani,

Sosai ma wlhy har mafarkin ka nake yi, kullum ina tunanin ka, ina son ka sosai dan Allah kayi haquri ka taimaka ka maidani dakina kada kamin baqin ciki, ko barci nake kai nake gani, idan naji muryar wani namiji kai nake tunawa, ko dan sanda nagani birgeni yake yi saboda kai.

Tau shikenan naji uwani idan kina so na yarda kina sona kuma kina so na maidaki dakin ki sai kin nutsu, duk wannan shashancin ki daina, girmama iyayen ki da duk wanda ya girmeki, banda maidawa mutum magana idan ana maki fada, banda tsokanar mutaneย  musamman maxa, ki riqa girmama duk wanda ya girmeki, wawancin da kike da rashin ji duk ki daina, ina ga kin xama mutum irin jiddah nan da wata biyu kacal na miki alqawari xan maidaki dakin ki.

Ta langabar da kanta, ai kasan ina son ka kome kake so xanyi, ni yanxu ba ruwana ma da kowa baxan qara kula kowa ba koda xagina aka yi, idan na nutsu xaka aure ni ko,

Ya gyada kansa yana kallonta,

Tace kuma xaka riqa kirana Uwanitilmusty ko?

Nan ma ya gyada kansa, tayi murmushi tana kallonsa,

Yace yanxu xamuje dake driver ya kaimu inda anty ikram dan baxan iya driving ba,

Xumbur ta miqe tana fiddo idanuwa,

'Wannan matar ai wallahi baxan je ba, ai itace ma ta koreni a gidannan saboda tana min baqin ciki da xamana a gidan mijina.

Yace ashe baki sona uwani tunda har bakyason abinda nake so, idan nace ina son abu baxaki iya yi min ba kenan, banda wannan ma yanxu na gama yi maki mgnr girmama wanda ya girmeki amma yaya ta kike cewa tana maki baqin ciki.

Kayi haquri sweet baxan qara ba, ai xanje wasa nake ma, kuma nasan dama bata min baqin ciki tana sona.

'Yauwa gurin ta xaki xauna duk yanda tayi dake haka xaki bi, idan kika nutsu kika gyaru ita ce ma xata maidaki dakin ki.

Allah ko?ta xauna cike da farin ciki dai dai lokacin jiddah ta shigo dauke da arham a kafadarta, duk suka juya suna kallonta, cak ta tsaya qofar falon tana kallonsu cikin faduwar gaba, haka taji kamar falon yana juyawa da ita, da kyar ta iya daga qafafunta ta qarasa cikin falon.

'Anty jiddah kin dawo, kinga nima na dawo ai yaya ne yace na dawo xai maidani dakina.

'Ko kallonta jiddah batayi ba ballantana tasa ran xata amsa ta,

Uwani xata yi magana el'mustapha yasa qafa ya bigi qafarta, ta juyo da sauri tana kallonsa, harararta yayi yana fadin tashi marar sirri.

Ta tashi da sauri, shima ya taso da airah, ya shimfide ta akan sofa kana ya nufi arham yana taba jikinsa, har lokacin akwai xafi.

Arham ya dube sa yana fadin, mummy ta kaini anyi min allura asibiti,

Ya shafa kansa yana fadin sorry, kaci abinci kasha magani yanxu xanxo maka da ice cream ka ji.

Arham ya gyada kai yana fadin harda Pringles daddy,

Yace to shikenan, ya dubi jiddah a hankali yace xamu fita da uwani.

Komai bata ce ba amma gabanta na tsananta bugawa, ya juya ya fita uwani tabi bayansa da jakarta tana waiwayen jiddah.

Wa nake gani kamar uwani cewar anty ikram tana kallonsa da mamaki a fuskarta,

Uwani ta qara matse jakarta tana boyewa bayan el'mustapha,

Ikram tace kada dai uwani bakije gida ba kika dawo?

El'mustapha yace ni na dawo da ita sister?

Meyasa ta tambaya tana kallonsa da tsananin mamaki,

Ya riqa hannun uwani ya xaunar da ita kana ya dubi ikram yana fadin, xo muyi magana sister.

Ikram tabi bayansa, suka fita ya koro mata bayanin komai da dalilinsa na son uwani ta xauna a gidan.

'Naji banqi maganar ka ba, duk wanda ya gyara d'an wani tamkar ya gyara nashi ne, kuma ga lada amma kasani el'mustapha ko ta nutsu ta shiryu baxaka taba auren uwani ba.

Ya sauke numfashi yana fadin na sani sister, kina son jiddah ta barni kenan yanxu haka ma fushi take tun da na kira nace uwani taxo, ko abinci bata ci ba, arham ma bashi da lfy da kanta ta kaishi asibiti duk saboda tana fushi uwani xata dawo.

Banga laifinta ba saboda abinda aka mata da farko bata ji dadi ba kuma baxata qara yarda da uwani ba ballantana ta dawo gidanta.

Nifa ba wai ina son maida uwani bane, kawai ina so nayi amfani da son da take min naga na shiryata da taimakon ke da take tsoro, amma idan nace na barta gida tare da jiddah kishi baxai saka jiddah taya ni gyaran uwani ba.

Uwani tayi mamakin ganin anty ikram ta dawo har tana murmushi, ta kira mai aikinta cewa ta shigar da uwani dakin su amira.

Uwani taji dadi anty ikram ta daina mata baqin ciki.

El'mustapha yayi masu sallama ya tafi, bai manta da saqon arham ba sai da ya saka driver ya biya dashi ya siya masa kafin su dawo gida.

A wannan lokacin tasha kuka sosai kamar ranta, idanunta sunyi jawur tana tuna wahala da tasha a baya saboda uwani amma el'mustapha keson maidata, wannan ke qara tada hankalin jiddah dan batasan plan din uwani na biyu akanta ba duk ranar da ta qara auren el'mustapha, ba wai son xamane bata yi da uwanin ba illah tsoron rashin imanin ta da take.

Kallonta el'mustapha yayi sai da gabansa na fadi saboda ganin yanda idanunta suka yi jawur,

Kuka kika yi jiddah, kukan me?

Tayi masa banxa, ya matso yana tambayar kinci abinci kuwa, nan ma shiru tayi masa,

Yana qoqarin xama kusa da ita, ta tashi xumbur ta dauki airah ta nufi dakin ta, ya bita da kallo har ta shige kafin ya maida kallonsa ga arham dake kwance yana lumshe idanunsa yana bude wa.

Mummy taci abinci kuwa?

No, tun daxu take kuka.

Xo ga ice cream din kasha sai muje mu kwanta dare yayi,

Daddy ni bana jin barci yanxu.

Yace aa, sha ice cream din tukunna kafin naxo, ya tashi ya nufi dakin jiddah, ga mamakinsa jiddah ta rufe qofar da key, hankalinsa ya qara tashi, jiddah bata taba rufe masa qofa ba, meyasa take tsiro da abubuwan da bata saba yi masa ba a xamantakewar auren su?

Saboda tana xargin ka da son abinda take gudu take ganin kamar cutar wane yanxu a gare ta, yaji xuciyar sa ta bashi amsa.

Ya soma buga qofar a hankali yana kiran sunan ta amma tayi masa biris.

Daddy ni baxan sha ice cream din ba sai gobe, idan nasha amai xanyi.

El'mustapha ya juya yana kallon yaron a sanyaye.

On your birthday, I wish you a year with loads of fun, excitement and beautiful memories. Happy birthday Girlfriend Baby Bello๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚

60

Pringles din fa?

El'mustapha ya tambaya yana kallonsa,

Baxan ci ba sai gobe,

Yace tor shikenan, ya riqa hannunsa suka nufi dakin sa,

Daddy yau tare xamu kwanta ne?

Ya gyada kai yana kallon yaron,

Ya xauna yana dialing number jiddah, tana fara ringing yaji an kashe gabaki daya, ya dafe kansa, arham ya kwanta jikinsa yana fadin,

Daddy baka sakamin kayan barci ba, kullum momy sai ta sakamin kafin na kwanta.

El'mustapha ya tashi cike da damuwa yace cire kayan kafin na dauko ma kayan barcin naka,

Bai jima da fita ba ya dawo yana fadin,

Meyasa baka cire kayan ba arham,

Daddy ni bana iya cirewa,ย  el'mustapha ya xauna yana cire masa kayan, ya saka masa na barci ya dubesa har yanxu jikinsa akwai xafi, suka kwanta.

*

'Washe garin ranar koda suka tashi jiddah ta gama komai na breakfast ta ajiye masu, ta shigewar ta dakin ta rufe., koda suka yi wanka suka fito ta gama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login