Showing 102001 words to 105000 words out of 138779 words

Chapter 35 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

1999



Kin yafe min dukan da na maki jiddah.

Ta daga kanta a hankali batare da ta kalle sa ba, ya jawota sosai ya rungumeta, lokaci daya suka sauke numfashi.

Al'amarin daya biyo baya baxai fadu ba🤧 da kyar ta janye bakinta daga nasa,

Yana kallonta yace bani abinci naci jiddah, yau komai ban ci ba tun safe.

Ta tashi a sanyaye ta fita batare da tayi magana ba, yabi bayanta da kallo kawai.

'Ko da ya gama cin abincin jiddah bata dakin tana falon ta, da alama har yanxu bata sauko daga fushin ba.

Shi yanxu damuwar sa hannunsa dake masa zugi tun daxu.

Da dare sai juyi yake akan gado ya kasa barci saboda xafin ciwon hannun, gashi ya kumbura, kallon jiddah yake barcin ta take cikin kwanciyar hankali.

Time ya duba, biyu na dare ya gota, ya sauko daga saman gadon ya fita daga dakin.

Sai safa da marwa yake tsakanin falon sa dana jiddah, yanda yake ji a hannunsa ya tilasta masa xuwa dakin da abba yake ba shiri.

A hankali yake buga qofar dakin,

'Abba ya tashi yana tambayar waye? Jin muryar el'mustapha ya taso da sauri ya bude dakin yana tambayar lafiya?

'Na kasa barci, hannuna ke ciwo sosai... El'mustapha ya fada yana nunawa abba hannun.

'Abba ya duba hannun yana fadin ai gocewar qashi ne el'mustapha me ya jima ka ciwo haka.

Ya yatsina fuska kafin yace na dan xame ne daxu a toilet na fadi, yanxu ya xanyi abba.

Daurewa xaka yi kayi haquri har xuwa gobe sai kaje asibiti ko kuma ayi maka aikin gida duk wanda kake so amma ni bani da sani akan irin wannan matsalar.

Shiru el'mustapha yayi kafin ya juya yana fadin Allah ya kaimu goben.

Xama yayi bakin gadon ya dafe kansa da hannunsa daya, dole ya sami gocewar hannu saboda girma da nauyin kujerar, inda ta sami uwani a kai kenan xaa sami matsala ba babba dan ya tabbata kwakwalwar ta gabaki daya xata juye.

Jiddah ta bude ido tana kallonsa, kallon agogon tayi kafin ta maida kallonta garesa cikin mamaki, meke damun el'mustapha, me ya hana masa barci a wannan lokacin yake xaune?

Ta matso a hankali xuwa inda yake, hannunta ta kai wuyansa ta taba tunanin ta ko xaxxabi ne,

Ya dago yana kallonta, ita ma shi take kallo

Tace meke damun ka?

Da kyar yace ba komai.

'amma naji jikinka da xafi ko baka da lafiya ne?

Ya girgixa kansa kafin yace ki kwanta jiddah ba abinda ke damuna.

Ta gyara xamanta sosai tana kallonsa,

'Na kwanta nayi barci kai kuma kana xaune, idan lafiyar ka qalau tunanin me kake yi el'mustapha?

Yayi shiru baiyi magana ba, ganin ta matsa da tambaya ya nuna mata hannun.

Tayi shiru gabanta na faduwa tana kallon yanda hannun ya kumbura, ta kasa daqowa ta kalle sa harda wani nauyin sa take ji.

Yaja numfashi kadan yana fadin kije ki kwanta tun kafin airah ta tashi gobe kixo kina complaining baki sami barci ba,

Ta girgixa kanta kafin tace kayi haquri n..... Shishsssss ya katseta ta hanyar dora yatsanta akan labbanta yana kallonta.

Kije ki kwanta bana son gardama,

Ta matsa kadan daga garesa amma taqi kwanciya, bata da wannan nutsuwar bata san yanda yake ji ba ta tabbata duk abinda xai hanawa el'mustapha barci ba qaramin abu bane.

Ganin taqi ta kwanta ya saka shi kwanciya yana fadin xo mu kwanta jiddah nima barci nake ji.

Ta matsa ta shiga cikin jikinsa, ya rungumeta yana lumshe idanuwansa ba dan ya daina jin xafin hannun ba.

'Washe gari ko da jiddah ta tashi el'mustapha baya gidan, tayi mamakin ina xaije da sassafe haka kuma tana da tabbacin ko wanka bai yi ba ya fita.

Ta shiga kitchen ta sami hajiya tana hada breakfast, gaidata tayi kafin ta soma taya ta suna yi suna fira jefi jefi cikin nishadi har suka kammala.

Goma na safiyar ranar el'mustapha ya shigo da alama gurin gyara ya tafi ganin yanda aka daure masa hannu.

Kai tsaye dakin sa ya nufa, jiddah tabi bayansa kallonsa take a sanyaye,

Sorry el'mustapha kayi haquri dan Allah,

Yace bani ruwa na sha magani, da sauri ta fita bata jima ba sai gata dauke da Swan da cup, da kanta take balla mashi maganin yana sha.

Ganin yana qoqarin cire rigar jikinsa ta taimaka mashi ta cire masa, ya kwanta yana fadin,

Kada ki tada ni jiddah, duk wanda yaxo bana nan,  na kashe wayar ma har yaranki kada ki bari su xo su dame ni.

Ta tashi tana fadin asha barci lafia, ya dan kalle ta yace lullubamin blanket sai ki kunna min AC.

'Ko da su abba suka gama shirin tafiya jiddah har tayi wanka, ta shirya twins ta bawa driver ya kaisu inda anty yusrah har anjima kada rigimarsu ta tada mahaifinsu daga barci.

'Abba yace ina el'mustapha da hannu, jiya bai sami barci ba ashe ya xame ya fadi ne yaji ciwo.

Jiddah tace bai jima da dawowa gurin gyara ba, ya sami barci yanxu.

Hajiya tace Allah ya bashi lfy idan ya tashi ina mishi ya jiki.

'Abba yace mu xamu tafi idan ya tashi ki gaidasa.

Suka firfito harabar gidan, jiddah dauke da airah sai wasa take mata tana dariya,

'Abba ya dubi uwani yana fadin ke kuma fa ina kayanki?

Uwani ta tunxure baki tana fadin ni xan raka ku ne ku tafi ba inda xanje ni.

Hajiya ta fito mota tana fadin baki isa ba, dole sai kin bar gidannan xaman me xaki masu.

Uwani ta juya tana fadin ance mijina bashi da lafiya sai naje na barshi saboda na xama sokuwa, idan ba baqin ciki ake min da ladar jinya da xan samu ba saboda me xaa tafi dani, ni ba inda xanje wallahi jinyar mijina xanyi.

'Abba xaiyi magana jiddah ta katse shi, shiga mota ku tafi abba Allah ya kiyaye ya kaiku lafia, cikin murmushi ta dubi driver da xai kaisu wani dan sanda ne, tace sai kayi a hankali da tsofaffin nan basu saba da gudun mota ba kamar el'mustapha,

Babu matsala madam, su abba suka shiga cikin motar, jiddah ta matsa lokacin da aka tayar da motar, tana tsaye gurin suka fice kafin ta koma cikin gida.

Tana tafe tana cira airah sama cikin mata wasa yarinyar sai dariya take, ta sami uwani xaune a falon ta kunna TV tana kallo, inda take Ma jiddah bata kalla ba tayi shigewarta dakin ta.

Da sauri ta qarasa gurin wayarta dake qara, New number ta gani hakan bai hanata daga wayar ba.

'Anty jiddah an tashi lafiya... taji muryar banan a daya bangaren.

Cikin murmushi jiddah tace amarya ce ke kira haka da sassafe,

Tace tun daxu nake kiraki baki daga ba,

Jiddah tace bana kusa ne, ya kwanan amarci.

Murmushi kawai banan tayi batace komai ba, dama jiddah tasan baxata amsa ta ba tasan banan da kunya jiddah ta cigaba da fadin, babu dai wata matsala ko banan?

Babu anti jiddah, na kira ne na gaidaki na qara maki godia akan hidimar da kika min, kin min gata inaji ko iyaye na keda rai iyakar abinda xasu min kenan, nayi kukan farin ciki anty jiddah idan na dubi irin kayan da kika min, ban san da wane baki xan gode maki ba illah nace Allah ya saka da alkhairi ya kuma kare ki daga sharrin maqiya, sannan anty jiddah nayi kukan baqin ciki idan na tuna na so mijinki kuma kinsan da haka, ina jin kunya da nauyin ki anti jiddah dan Allah ki yafe min.

Babu komai banan cewar jiddah, kidaina tuna duk abinda ya wuce, kuma duk abinda kike so ko akwai wata matsala duk ki gayamin.

Tau shikenan anty jiddah su kaka ma sunce xasu xo yi maki godia sannan anti jiddah wannan gas din bansan yanda ake amfani dashi ba, akwai abubuwa da yawa wadanda bansan kan su ba.

Oh oh... yanxu dai baxan sami xuwa ba sai an kwana biyu haka amma xan kira nabila na gayamata sai taje ta nuna maki komai ai baki fara girki ba ko.

Tace aa a gidansu aka aiko mana sai nan da sati daya yace kafin na fara girki.

Tau shikenan babu damuwa, ina gaida islam din.

Murmushi kawai banan tayi bata amsa ba kafin tace ina airah anty jiddah.

Gata nan tana ta missing din ki banan, nima kaina nayi kewarki abubuwa sun min yawa a yanxu dole dai sai na dauki wata mai aiki ko na dawo da Inna cikin gida tunda su suna da yawa acan.

Hakan yayi amma Inna xata bata maki falo da yawun goro kin santa fa yanda ake rigima da ita ko ina xubar da yawun goro take yi.

Jiddah tace sam na manta hakane fa, dole wata xan dauka.

'Anty jiddah ki kawomin twins na gansu...

Xasu xo banan idan xan xo, ki kula da kanki.

Nagode anti jiddah, ta tsinke wayar.

Jiddah ta xauna tana dialing number anty ikram, bata jima da ringing ba ta dauka, suna gama gaisawa jiddah ta soma yi mata bayanin komai akan rashin komawar uwani, anty ikram ta tsinke wayar tana fadin gani dama ina hanyar xuwa gidan el'mustapha ya fadamin bashi da lafia.

Batare da damuwa ba jiddah ta tashi ta goya airah, ta sami uwani ta qure volume tana kallo ta tuna el'mustapha barci yake, sai taje ta dauki remote ta rage volume din, tana ajiye remote din uwani ta dauka tana qara volume.

Gabaki daya jiddah ta kashe kallon tace kada ki qara kunna min komai anan.

Meyasa anti jiddah, inba neman fitina da baqin ciki ba saboda me ina kallo xaa xo a kashe min.

Saboda gida na ne kuma komai nawa ne kuma wallahi idan kika qara kunna min kaya sai kinyi mamakin abinda xan maki, tayi shigewar ta kitchen

Uwani ta tabe baki tana binta da kallo,

Kunji  wai gidanta dadin abin nima gidan mijina ne... bata gama maganar ba taji muryar ikram na sallama xumbur uwani ta tashi cikin rawar jiki ba shiri ta soma gyaran falon kamar wacce aka sata.

Gaisuwar da uwani tayi mata bata amsa ba, jiddah ta fito kitchen da wuqa a hannunta, cikin murmushi take gaidata.

'Anty ikram tace ina su hajiya ne naji gidan tsit.

Jiddah tace ai suna hanyar komawa,

Ikram ta dubi uwani fuska a daure tace to ke kuma xaman me kike da baki bisu kuka tafi ba.

Jiddah tayi caraf tace ta xauna tayi jinyar mijin tane wai a bata key na dakin ta.

Uwani tayi narai narai da ido tana fadin yaushe nace haka, kada kimin sharri.

'Anty ikram ta dubi jiddah tana fadin bani makullin dakin nata jiddah,

Jiddah ta maida wuqar ta ajiye kafin ta nufi dakin ta da sauri tana gyara goyon dake bayanta.

Uwani taja numfashi a hankali tana jin wani sanyi lallai matar nan tana sonta bata da baqin ciki tunda har xata maidata dakin ta.

Jiddah ta dawo ta miqawa ikram key din dakin, ta karba tana kallon uwani.

Ina kayan da kika xo dasu,

Cikin rawar jiki uwani tace suna wancan dakin bari na dauko, da sauri taje tana kwaso kayanta duka ta ajiye a tsakiyar falon,

Ikram ta soma tafiya tana fadin biyo ni a baya, uwani ta bita sai murmushi take harda kallon jiddah tana mata gwalo a fakaice tace yar baqin ciki sai dai ki mutu.

Murmushi kawai jiddah tayi batare da tayi magana ba tamkar bata ji me uwanin ke cewa ba.

Ikram ta bude dakin tana kallon uwani shiga ciki ki fito da duk kayanki da kike so aciki ki hada su cikin wadancan dake tsakiyar falon kana ki gyaran dakin tsab kafin naxo.

Farin ciki ya qara mamaye xuciyar uwani, ta juya dauko tsintsiya ta shiga dakin tana fito da kayanta, ba laifi dakin yayi qura amma haka uwani ta soma gyara batare da damuwa ba tunda dai xaa maidata dakin ta ko menene xatayi.

Jiddah taja tsaki tana sauke airah ta rasa dalilin da yasa yarinyar bata son goyo ko yaya ne xata fara mutsuniya har a sauke ta,

Ikram tace ina el'mustapha din,

Yana daki barci yake yi, ikram ta nufi dakin sa, jiddah tayi saurin kallonta tana fadin anty ikram yace kada a tashe sa fa.

Baxan tashe sa ba jiddah ai ya gayamin jiya bai sami barci ba hannun nasa kawai Zan duba.

Jiddah ta dauke kanta daga kallonta, ikram ta nufi dakin el'mustapha, bata jima ba ta fito tana fadin ya kanainaye cikin bargo haka taya xan iya ganin hannu, sai ya tashi tukunna.

Ta sami guri ta xauna nan falon tana kallon jiddah,

Gashi nan sai fama kike da yarinya babu mai riqa maki, gata da shegiyar fitina wannan da alama sai tayi quya.

Jiddah tayi murmushi tana kallonta,

Ke dai na gane kina son yarinyar nan sosai kike nuna mata halin ko in kula, kin ganta kyakkyawa da ita ba kamar twins din ki ba.

Me xanyi da wannan ajebo cewar ikram.... Uwani ta fito tana ajiyar xuciya da alama ta gaji sosai,

Tace na gama anty ikram cikin washe baki😁

Kallonta suka yi a tare sai xufa take kamar wacce tayi wani aikin axo a gani.

Ikram ta tashi tana fadin yauwa uwani, taje ta rufe dakin da key ta bawa jiddah.

Annurin dake fuskar uwani ya soma gushewa,

Tace saka hijab din ki ko gyale ki fito, yanxu xan saka a fito da kayan naki.

Jiddah da ikram suka fito, a sanyaye uwani ta yada gyale a kafadarta tana fadin to ko wancan part dinne xata kaini, ta fito tana kallo aka soma fito da kayanta ana sakawa a booth din anty ikram.

Uwani ta qara tsuke fuska, ni me xanyi a gidanta inba baqin ciki ba me xai sa ta rabani da gidan mijina.

Ana gama saka kayan a mota ikram ta dubi uwani tana fadin bismillah shiga mota,

A sanyaye uwani ta bude motar ta shiga, ikram ta dubi jiddah tana fadin je ki kula da mijinki idan ya tashi ki gayamasa na shigo.

Cikin farin ciki jiddah ta juya bayan ta fakaici idon ikram suna hada ido da uwani tayi mata gwalo irin mai cin rannan, ta juya cikin gida tana murmushi.

Uwani ta soma hawaye, anty ikram ko kallonta batayi ba taja motar suka bar gidan.

Kai tsaye tasha ta nufa da ita, sai da ta tabbatar uwani ta shiga mota har kayanta an gama sakawa, ta biya kudin motar kana ta sunkuya tana kallon uwani.

Idan kinje ina gaida hajiya da abba, naxo na masu bankwana ashe sun tafi, ke kuma kinxo ki xauna ki hana mata sakewa da mijinta, bayan ga gidan uban ki, ban gaya maki el'mustapha yafi qarfin ki ba kuma baxai taba maidaki ba, ki fitar da naki mijin mana idan babu ni baxan rasa wanda xan hadaki aure da shi ba amma a sakarwa baiwar Allah nan mijinta abarta haka taji dadin abinta yanda hankalin qanena xai sami kwanciya ya more tasa rayuwar.

Uwani ta hadiye wani qololon baqin ciki ta dauke kanta gefe tana hawaye,

A ranta tace idiot yar baqin ciki sai nadawo ba wanda xai rabani dashi kowa baqin ciki yake min da gidan mijina baa so na xauna.

Ikram bata bar tashar ba sai da motar su uwani na daga kana ta shiga ta ta motar tabar gurin.

(karki damu uwani qawarki Batul Mamman xata maidaki tunda ta xama UwanitulBatul tana maki Son So💖)

Bata jima da shiga gidan ba taji sallamar ibrahim, amsa sallamar tayi ta nufi dakin ta, hijab ta saka ta fito suka gaisa,

Tun safe nake kiran wayar Musty a kashe, office sai neman sa ake bai fita aiki ba shine naxo na duba ko lfy?

Bashi da lafiya ne ibrahim, kuma yana barci a yanxu.

Ibrahim ya xauna yana fadin Allah mai iko, naga lafiya lau muka rabu dashi jiya, meke damun sa.

Jiddah ta xauna tana kallonsa, yaji ciwo a hannunsa,

Oh yes nagani jiya sanda yace hannun na masa ciwo, na gayamasa lokacin yaji sosai yanda naga baya son riqa hannun ayi yace aa kumburi ne yayi da ya sha magani shikenan.

Tace ni bansan yaji ciwon ba sai da dare da ya kasa barci,

Kuma ke kika ji masa ciwon nan fa duk wajen rigimar kishi banda abin ki ina musty xai iya maida uwani a yanxu,

Ta tabe bakinta kafin tace ni baxan gane hakan ba,

Ya juya yana kallon dinning, dole Musty yaji ciwo waccan heavy chair, gsky yaji maxa tunda ba jikin qarfe ne da shi ba dole xai ji ciwo,  kuma da gaske xaki iya rotsa mata ita banda el'mustapha ya hana?

Wallahi kuwa, fashe mata kai duk mai sauqi ne  akan ni da taso kashewa, ta iya nakasa ni ballantana ni?

Yace haka ne, uwani ta bata mana jiddah,

Murmushi kawai tayi, ya soma qoqarin tashi yana fadin idan ya tashi ki fada masa naxo ina je office xan sanar dasu.

Taimako nake so ka min ibrahim.... ta katse, ya juya yana kallonta bayan ya xauna.

Taimakon me jiddah.

Ka taimakeni, bansan yanda xanyi ba, bani da wata mafita a yanxu bayan wannan dan Allah ka auri uwani...

Ya saki baki ya xuba mata idanu yana kallonta,

Ni na auri uwani, Allah ya sauwaqe min, matana biyu suna xaune lafiya shigar uwani a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login