Showing 120001 words to 123000 words out of 138779 words

Chapter 41 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

2012

da wata beb, kece bakyaso sai ni kenan idan nabila ce bakyaso sai a canxa maki mana mata nawa ne kika sani masu son yayana, amma ke yayan naki in ba ni ba waye ke so, nima dai dan yana d'an uwa na ne.

Afiya ta qara bata fuska tana fadin qarya kike wallahi, yayana yafi yayan ki komai ni da aka ma dole ga auren sa ai da kinsan nafi ajin sa, banda sarauta ma me kuke dashi, Mulki shi ke tafiyar da komai harda sarautar ma.

I see cewar rumaisa tana kallonta, naga mulkin ma a qarqashin sarauta yake, da ke da mulkin duk kuna tafin hannun mu ne, naku shine ku mana biyayya, dan kinsan yaya yafi son sarautar sa dake😏

A kufule afiya ta janyo wayarta, number merah ta soma kira bayan ta saka hands free, bata jima da ringing ba ya dauka yana fadin da girman kujerar ki, ta turo baki kamar yana kallonta,

Tace ni da kai waye mai son wani? Yace ni ne,

Tace ni da sarauta wa kake so? Yace gimbiya,

Tace shine wannan yarinyar ke cewa kafi son sarauta dani, wai baa sona nice na liqe mata.

Tunda yaji tana wannan tambayoyin ya saka a ransa ita da rumaisa ne, su har yanxu basu daina wannan fadan ba, kusan kullum sai an kira sa a waya an masa wannan tambayar yafi a qirga, da kyar yace

Kice mata nine na liqe maki shikenan, tayi dariya tana kallon rumaisa harda mata gwalo, ta tsinke wayar tana fadin kin daiji da kunnenki yafi sona akan sarauta saboda bai dauke ta da muhimmanci ba amma yaya baxai xabe ki ba akan mulkinsa.

Rumaisa ta tabe baki tana dialing number Aliyu,

Gimbiya kamar kinsan ke nake tunani a yanxu,

Rumaisa ta yatsina fuska tana kallon Afiya,

'Wannan yarinyar ke maganar kafi son mulki akaina,

Yace ba dai Afiya ba, ki gayamata mijinki ba irin mijin ta bane da yafi baiwa sarautar sa muhimmanci akan matar sa, mijinki yafi son ki akan mulkinsa,

Afiya ta matso tana fadin, Allah yaya ba gaskiya bane kana fada ne dan taji dadi,

Rumaisa ta tsinke wayar tana kallonta,

Ki jiki sanda kina wayar ki na saka baki na ne, saboda me miji da mata suna  hira xaki sako bakinki a ciki.

Afiya tace ai naji xai fara maki dadin baki irin nasu kafin kan naki ya fara girma,

Idan dadin baki yake min kema shi yaya maina ya gama maki a yanxu,

Jiddah dai sai kallon su take, ta rasa gane kansu duk suka hadu sai sunyi fada, tana kirga fadan su na uku kenan bayan taxo gidan, kuma duk akayi fadan sai sun kira maxajensu.

*

'Washe gari da sassafe sai ga el'mustapha a gidan,

'Na kasa haqura jiddah, jiya da kyar nayi barci gani nake kamar an kwace min ke,

Taja dogon hancinsa tana murmushi, bari na kawo maka breakfast nasan baka ci komai ba,

Yace ina twins ne,

Nima tun jiya rabona da su,

Ya kwanta yana fadin ni fa harda tsoro na riqa ji a gidan,

Komai ma ji xaka yi hardai yau dinnan, dan baxan bika ba sai gobe.

Kallonta kawai yayi baiyi magana ba, jiddah ta fita.

Kakan jiddah, mahaifin zubaida shine mutum na farko da ya fara dira a gidan, tun da yaji labarin anga yar zubaida ya kasa sukuni.

Yana shigowa da Afiya yaci karo dauke da Cup din tea a hannunta, ta saki cup din gurin ya tarwatse bata damu ba ta nufe sa da gudu ta qanqame shi,

Uncle B is back yeeeh, kan kace me sai ga qananan yara yan jikoki suna fitowa da gudu, suka qanqame shi kamar xasu kada shi a gurin.

Uncle B yana da farin jini a gidan sosai,

Waye ya xubar da tea anan, umma ta tambaya tana kallonsa.

Uncle B yace nine Matar yayan mu,

Dariya kawai umma tayi.

Kai tsaye falon sarki ya nufa, ya jima sosai acan kafin a kira masa jiddah, yana ganinta ya fashe da kuka tabbas wannan jikar sa ce yar zubaida ce daga yanayin kamannin da suka yi.

Ya rungume jiddah tsam a jikinsa, haka jiddah ke jin wani sanyi a xuciyarta kamar a jikin mahaifin ta take, wai wannan ne kakanta, sai ta soma godewa Allah a xuciyarta.

Ya saki jiddah yana kallon sarki cikin share hawayen fuskarta,

Aiman ya kyauta daya gano min jiddah, xan masa babbar kyauta.

Sarki yayi dariya yana fadin ni kuma da nayi albishir din fa.

Uncle B yace xan baka yar budurwa ka aura.

Suka sa dariya lokaci d'aya,

Goma na safe abba da su hajiya suka iso abuja, tun jiya da el'mustapha ya kira su anga yan uwan jiddah suke cikin farin ciki musamman da suka ji ta fito daga jinin sarauta,

El'mustapha yaje da kansa yaxo dasu gidan, tun da suka shigo uwani ke kallon gidan ta kasa gasgastawa har sai da ta bude baki ta tambayi abbanta,

'Abba amma nayi barci a mota ne har muka shigo jirgi muka xo qasarnan bani da labari.

'Abba komai baice ba, ta juya tana kallon el'mustapha da niyar tambayarsa, fuskarsa daure cikin baqin glass, taji wani tsoron sa ya taso mata, ta hade yawu da kyar hade da Jan bakinta tayi shiru.

Bata qara tsorata ba sai da suka shigo cikin gidan, ta saki baki da hanci tana kalle kalle, bama ita kadai ba har su abba din ma, hajiya ta kasa haqura,

Tace el'mustapha ina ne kake shirin kaimu haka,

Ya cire glass din idonsa yana kallonta cikin murmushi,

Hajiya ai kinsan baxan cutar daku ba, dogari nawa kika gani a waje wannan kadai xai tabbatar maki gidan sarauta muka shigo, baki ga kalar ginin su bane irin na sarauta.

Tace kuma sune yan uwan jiddah?

Yace insha Allah.

Allah mai iko, lallai a duniya baka debe tsammani daga rahamar ubangiji, shi kadai yasan abinda ke boye da bayyyane, kuma shine mai badawa da hanawa a duk sanda yaso, nayi wa jiddah murna sosai.

Suka isa falon sarki, lokaci daya suka xube suna gaidashi.

Jiddah bata san da xuwan su ba tana can tare da kakanta, ko motsi tayi sai ya tambaya me take so, su Afiya sun xageyasa, Uncle B Uncle B, suna taya sa kula da jiddan sa, saboda shi mutum ne daya san kansa sosai a gidan, yana sake masu fuska da hannu, haka kuma wasa da raha a gurin sa baa magana, kowa nasa ne shi na kowa ne, shi kadai a gidan ke iya saka sarki abu ko hanasa, akwai soyayya ta yan uwanta ka sosai tsakanin sa da sarki da yaran gida, shiyasa suke sonsa yaro da babba.

Mai martaba sosai ya nuna wa su abba karamci kuma yayi masu godia da amana da suka riqe ta jiddah har yayi masu kyauta mai girma, sai godiya suke suna qarawa.

'Abba yace dukiyar jiddah xan maido mata ne,

Sarki yace aa, ai kaine mahaifin jiddah kuma kaine mahaifiyar jiddah ta bawa amanar dukiyarta a hannunka, mu baxamu karba ba illah ka cigaba da kula mata ita kamar yanda kake yi, Allah shi sanya mata albarka.

Duk maganar nan da ake uwani idanunta na kan sarki, kallonsa take babu ko kyaftawa, ita tun da take a rayuwarta, tun da take ganin sarakuna a tv ko hoto bata taba ganin wanda sarauta tayi masa kyau ba kamar Sarki merah, yanda yake magana ma birgeta yake, qasaitar sa na rudata.

Sarki ya tsargu da kallon da uwani ke masa ko baa fada ba yasan wannan ce uwani da jiddah ta basu labari daga ganin rashin nutsuwar ta,

Ya kira jakadiya yayi mata umarni da ta basu masauki har xuwa gobe su koma gida.

'Abba yayi godiya kana suka tashi suka bi bayanta.

Bayan an kaisu masaukin su suka nemi ixinin a hada su da jiddah suna son su ganta.

Jakadiya tace, jiddah tana tare da kakanta a yanxu a wancan bangaren, nan bada jimawa ba xaku ganta taxo dan naji sarki ya aika mata da cewa kun xo.

Uwani ta dubi iyayen nata tana fadin,

Hajiya dan Allah ni ba qanwar jiddah bace, kin tabbata ba maman mu bace ta mutu ta barmu hannunka, nifa ina ji a jikina nima jinin sarauta ce.

'Abba yace kidaina ji a jikinki, kece uwar jiddah ma.

Ta xauna tana kallon cimar da aka kawo masu, wani abin Ma bata taba ganin sa ba, taci wannan taci wancan, haka take ji AC gidan daban ne da wanda ta saba ji a kullum, taji haushin da bata xo da kaya masu yawa ba, ita da barin gidan har abada.

'Abba dan Allah ku gayamin gaskiya su waye iyayena, ina dangina suke?

'Abba yace a bola aka tsince ki, mu din da kika bakyaso mune iyayen ki kuma a hakan xaki xauna damu ko kina so ko bakyaso.

'Abba karka min baqin ciki da samun arxiki, ka hadani da iyayena na a...... Bata qarasa ba hajiya ta kifa mata mari, kafin ta dawo hayyacinta ta qara mata wani.

Wayyo Allah na, na tuba hajiya kiyi haquri wallahi ina son ku kune iyayena dan Allah kiyi haquri.

Suna haka sai ga jiddah ta shigo dakin sanye cikin alkyabba, sosai tayi mata kyau ba kadan ba,  sallama tayi ta shiga dakin.

Kallon ta suke cikin farinciki da kulawa, yayin da uwani ke mata kallon mamaki kamar wata yar sarki.

Ta qarasa jikin hajiya ta rungumeta cikin farin ciki, abba sai dariya yake.

Jiddah ta gaidasu tana fadin, yanxu ake gayamin kunxo ashe tun daxu kuka xo.

'Abba yace eh mun jima gaskiya muna inda sarki, nayi maki murna jiddah, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.

Hajiya tace nima ina maki murna jiddah.

Murmushi kawai jiddah tayi, ko kallon inda uwani take batayi ba, kamar yanda bata mata magana ba tana matsayin babba ba yanda xaa yi ta kada girmanta gurin mata magana, suka cigaba da hira abin su.

Jiddah ta dade sosai a gurin kafin ta fito, uwani tabiyo bayanta dan taga yanda gidan yake.

Falon da tabar mutanen gidan can ta nufa, inda kakanta taje ta xauna tana cigaba da ja masa yatsun kafa kamar yanda ya saka ta a daxu.

Haka uwani taji ta muxanta a falo ganin yanda ake kallonta cikin rashin sanin ita wacece.

Uwani kuwa haka ta xubawa afiya ido da sam bata Ma lura da shigowar ta ba, taga tana kama da wannan baturen da ya mata baqin ciki, uwani ta tsargu ta fita daga falon.

Rumaisa ta dubi jiddah tana fadin idan na canka da kyau wannan ce uwani.

Jiddah ta gyada kai, rumaisa ta sunkuya tana fadin kada ki gayawa afiya kinsan bata son yarinyar.

Uncle B yace wacece uwani?

Jin an ambaci uwani ya saka afiya dagowa tana kallonsu kafin tayi magana suka ji sautin busa na sarewa, ko baa fada ba sun san Maina ne ya sauka domin shi kadai akewa busar duk gidan.

Afiya ta tashi tayi sashen ta da sauri tana cire alkyabba jikinta, ko ya gayamata xai sauka da tuni ta dade da shiryawa.

Rumaisa da sauran yaran suka nufi falon sarki sun san acan xai sauka.

Aka bar jiddah da uncle B, ta dube sa cikin murmushi tana fadin.

Ance ummana nada qanni maxa amma ni ban gansu ba,

Yace maxa biyu ne ai, Murdasi wanda yake binta sai qaramin Ibrahim, Murdasi yayi aure yana da yara biyu yana xaune a kaduna, xaki ganshi yaxo insha Allah, sai Ibeey shi yana karatu Phoenix makaranta daya da sultan yaron Afiya, amma ibeey ya girmi sultan sosai ba ajin su d'aya ba, shima da ya dawo xaki ganshi.

Sauran dangi ma xuwa gobe duk xaa kaiki kafin ki koma gidan mijinki, munyi maganar da sarki.

Tayi murmushi tana kallonsa, shima kallonta yake yanayin ta da sanyinta duk irin na zubaida, haka yake jin son jiddah a xuciyarshi kamar itace zubaida.

Aikin me mijinki yake yi jiddah.

AIG ne na yan sanda,

Yace iyyeh ashe dai jikanyar nan tawa yar gata ce, auren babban dan sanda haka, no wonder banji sarki yana mgnr aikin mijin ki ba, daga yau xan fara Jan fada a gari ina da mai tare min.

Tayi dariya tana fadin idan kaja wani fadan duka xaa yi ma, mu namu muyi ma sannu ne.

Yanda jiddah ta saki jiki dashi kamar sun saba yaji yana qara son ta, har wata nutsuwa yake ji duk wani bacin rai na zubaida ya neme sa ya rasa dalilin jiddah da ya'yan ta daya ke kallo.

*

Da dare tana xaune da twins dakin da aka bata uwani ta shigo, harda sallama.

Jiddah ta amsa tana kallonta, uwani ta koma gefe ta xauna tana kallon jiddah.

'Anty jiddah naxo na qara roqon ki dan Allah ki yafe min abinda na miki a baya, tuni na gane kuskure na tun xamana a prison, wallahi babu wani niya ta cutar wa tare dani game da ke.

Murmushi jiddah tayi tana fadin ba komai, Allah ya yafe mana gabaki daya, ta dubi twins kuje daddy yana jiran ku xai ganku kafin ya tafi, suka fita da gudu suna tsalle.

Uwani ta cigaba da fadin ni dai ban taba maki gorin iyaye ba, duk na tuna hakan sai naji dadi wlhy, sau daya ne nasan nayi kuskure da nace baki ma su abba adalci ba, shima kiyi haquri kinji anty jiddah.

Tace ba komai,

Yanxu anti jiddah shikenan xaki daina xuwa gidan mu.

Jiddah tace saboda me, karkiyi wannan tunanin har gobe sune iyayena kuma xan cigaba da masu biyayya.

Uwani ta gyara xama tana fadin, ni kuma ina nan qanwarki, duk inda naje xan buga qirji ni qanwar jikanyar merah ce, ai nima na xama jikar sa ko.

Jiddah tace haka ne,

Uwani tace shiyasa nake ganin baxan koma gida ba xan cigaba da xamana anan gidan wallahi.

Hmmm kawai jiddah tace batare da tayi magana ba,

Cikin farin ciki uwani na soma fadin ashe wannan baturen ya xama baban ki ai na ganshi daxu, ina jin tsoronsa ban barshi ya ganni ba kada ya min baqin ciki ya koreni a gidan nan tsab xai iya wallahi shiyasa bana so na hadu da shi,

Kuma anti jiddah..... tayi shiru jin afiya ta shigo dauke da airah tana kuka,

Wai ina jiddah ne, wannan yarinyar sai shegen kukan tsiya, duk tabi ta dami mutanen gida da baqar fitinar ta, ta hana mata da miji ma su sake.

Uwani ta taso da sauri xata karbe ta, afiya ta dube ta a wulaqance tana fadin,

Ke kuma fa? Wacece ke?

Uwani ta washe baki tana fadin nice qanwar anty jiddah, sunana Aisha ana ce min Uwani, iyayena ne suka r...... bata qarasa ba Afiya ta wanke fuskarta da kyawawan mari guda biyu masu kyau, jiddah ta tashi tana kallon ta cikin mamaki.

Afiya tace bana son shishigi, ina ruwana da ke ko matsayin ki, anti jiddar ubanki kin cutar da yarinya sannan kixo kina mata dadin baki, hala me ma kike gayamata haka, saboda kinga ta xama mutum a yanxu har kike wani rawar kai wai qanwar jiddah, kece anty zubaida gabaki daya, banda darajar iyayen ki da tuni na saka ancire maki wannan shegiyar qafa mai kama da maburgi, gobe idan kika ganni a hanya ki nuna kin sanni kiga yanda xan wulaqantaki.

Afiya ta dubi jiddah cikin takaici, har kike iya xama da wannan yarinyar kina saurarenta, ku biyu acikin daki bakya ko tsoron ta cutar da ke, wanda duk xai iya kashe jinin ka a gabanka tsab xai iya rabaka da duniya, kuma irin su abin gudu ne musamman kema din an so a kashe ki Allah bai nufa ba.

Ni bana son yarinyar nan, ina gayamaki gaskiyar abinda ke xuciya ta ne, ta juya ta fice bayan ta ajiye airah a saman gado.

Uwani ta fashe da kuka tana fadin wallahi anty jiddah baxan iya maki komai a yanxu ba, dan Allah ki yafe min ki yarda dani.

Jiddah tabe baki kawai tayi ta xauna tana qoqarin shayar da airah sai ga el'mustapha ya shigo, uwani na ganin haka ta fice da sauri ta bar dakin, tana fitowa taci karo da maina xaune a falon.

Ta rude har ta rasa hanyar fita, kyawun sa na qara ruda ta, ashe dan sarki ne shiyasa ganin farko ta ganshi yana ji da kansa sai qasaita yake xubawa, yanxu wannan shima dan uwan jiddah ne, ita kam jiddah taji dadi, ita kam tana son shi.

Jin muryar afiya na tun karo falon ya saka uwani qara rudewa, ta rasa hanyar da ta shigo, sam baxata manta muryar afiya ba.

What? You again, uban me ya shigo dake ne, kada kice maina kike kallo anan.

Sai a lokacin maina ya daqo yana kallon afiya kafin ya dubi uwani, ya qara bude idanunsa yana kallon ta cikin mamaki.

Cikin rawar murya uwani tace na manta hanyar fita ne, bansan na shigo nan ba,

A fusacce afiya ta nufe ta, tsananin tsoro da faduwar gaba ya saka uwani xubewa gurin a sume.

Afiya taja tsaki tana fadin shegia matsoraciya ko ta dauka dukan ta xanyi ne?

Ta juya tana kallon merah,

Kana nufin kace baka san da shigowar ta ba?

Yace gsky I don't know,

Tace amma ai kai naga tana kallo duk baka san da wannan ba.

Shigowar ta ma ban sani ba ballantana nasan da tsayuwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login