Showing 57001 words to 60000 words out of 138779 words
Chapter 20 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
xuba mashi,
An tashi lafia, ya jikin uwani.
Ta tabe baki tana yatsina fuska,
Ina so na tambayeka jiddah tana da rai kuwa?
Baiyi mamakin tambayar ba idan da sabo ya saba da wannan tambayar a duk lokacin da ya xiyarci uwani, yana tuna shine ya dauki nauyin kula da ita maganin ta da komai na asibitin duk cikin aljihunsa ne amma yarinyar ko godiya baxata iya masa ba hassalima kallon kirki baya samu daga gareta ballantana yayi darajar da xaa gaidashi, ita bata da damuwa sai ta jiddah.
Bata san cewa albarkacin jiddah da iyayenta ya saka ya taimaketa ba da kasancewar ta musulma.
Dama hausawa na fadin duk inda musulmi yake dan uwan musulmi ne kuma xuciyarshi tasha banbam da ta Arne ko ya take, dama Allah ya halicci musulmi dan xumunci da qauna ga dan uwansa musulmi,
Koda basu hada jini ko yan uwanta ka ba, ko da kuwa haduwar hanyace, amma uwani ta kasa gane darajan mutanen da taci.
Ya dubeta fuskarsa a daure, naxo na duba jikin kine xuwa gobe xaa wuce dake a rufe ki kamar yanda el'mustapha ya bada umarni.
Ta fiddo idanuwanta tana kallonsa cikin tsoro,
Ni xaa rufe? Me nayi, jiddah ce kuma ya ganta saboda me xaa rufe ni, laifin me nayi, saboda mugunta da cin amana ana baqin cikin ganina a raye ake son kulle ni a hana min walwala da jin dadin rayuwata.
Ke har kina da bakin da xaki kira wani mugu ne, akwai wanda ya kaiki mugunta a duniya ne, ki shiga taitayinki uwani kisan me kike, wlhy idan baki roqi gafarar jiddah da iyayenki ba alhakin su baxai bar ki ba.
To naji ban warware ba, kuma baxan warware ba dan har yanxu ina jin xaxxabi.
Ya fiddo mata ankwa ya nuna mata kin ganta anan tuntuni ya bada ita kuma ya rantse sai ya rufe ki gobe ko dani ko ba dani ba, naso na taimakeki amma nagane ke wawiya ce bakida hankali gwanda ya rufe ki din ya axabtar dake kamar yanda kika sa aka axabtar da jiddah, wannan qafar taki Ma naso ta lalace ta rube acire a yarda kowa Ma ya huta da baqin halinki.
Uwani ta fusata tace idan remote din duniya a hannunka yake ka maidoshi baya ka barni inda ka ganni ba sai ka taimakeni ba, waya sani Ma ko sona kake shiyasa ka nace min kai baxaka yi xuciya ka barni ba, baka ganin kowa ya gujeni ba mai xuwa inda nake harda wadanda suka kawoni duniyar saboda suna min baqin cikin rayuwa ta, nidai baxan soka ba mata biyu ne dakai baxan je a ta uku ba, el'mustapha nake so kuma sai na mallakesa.
Murmushi yayi mai cike da takaici,
Yace uwani ana maganar ki gyara rayuwarki waya kawo maganar so anan? Wace alama kika gani ta so a tare dani, daga taimako? Ko mace na rasa a duniyar nan baxan iya auren mai mummunan hali irin naki ba, mata biyu nake dasu kuma alhamdulillah basu samin damuwa ba kamar yanda kika sawa el'mustapha da yan uwansa, Kuma ina so kisani burin ki baxai taba cika na mallakar el'mustapha ba qarya kike ba sonsa kike ba, ban taba ganin irin wannan son naki ba.
Tayi shiru ba dan bata da abin cewa ba sai dan tunanin yanda xaa rufe ta a gobe, ibrahim ya juya ya fice.
*
El'mustapha tare da Dr Bakori a asibiti,
'Mun kasa gano wannan matsalar ta qafafun matarka, but I have called my friend he was a consultant also but orthopedic,
what do you mean Dr its about my wife explain it to me, cewar el'mustapha yana kallonsa,
Dr bakori yace ohhh AIG don't hesitate kasan ko wane irin ciwo akwai wadanda suka shahara akan shi,so da na duba qafar ne naga I can't do anything bcos its not my specialities, daz why I called him,
Knocking suka ji tare da sallama, suka amsa, Dr Hafix ya shigo, cikin sakin fuska suka soma gaisawa,
ya kai dubanshi ga El'mustapha gaba daya ba ya cikin nutsuwa,
Yace wai dama matar AIG ce d patient ur telling me,?
Yah she's, cewar Bakori
ohhh sorry pls AIG take it easy u know we care but Allah heals,where is d ex-ray, dr hafix ya tambaya yana kallon bakori
ga sunan Dr ammafa ahotunnan
da akayi mata sun nuna babu wata matsala bayan wannan kumburin,
Yace no! dere most kai dai baka gani ba muje office pls induba da kaina,
Dr Bakori ya juyo yabawa el'mustapha hannu, AIG bari muje ya duba pls kajiramu,
suka juwa su ka nufi office dinshi suna shiga yafara duba ex ray din.
Ya kai tsawon 30mnt yana duba wa den ya dago da kanshi
kasan me friend da kabari anyi report da ka fahimci matsalar kafar zo ka gani yana nunamai yadda veins din suke da kashin,what i concludes is dat rheumatism arthritis ne amma insha Allah zanyi iya koqarina akai ,I will prescribe the drugs,harda wanda za'a riqa shafamata a qafar,now where's she,
tana ICU,amma nasan yanzu anyi transfer din ta zuwa obstetric ward dan ta farfado
ok muje can din,
Suna fitowa su kaga el'mustapha tare da Abba a gurin, suka hada baki wurin cewa muje ko,
sun dauki hanya sai ward,
please AIG let's see her first, cewar dr hafix yana qoqarin maida glass din idonsa,
suka Shiga ya ganta sasai yaqara examine din qafar ya tabbata abinda ya ke tunani ne harma yaso yafi hakan OK muje my frnd suna fitowa ya taresu,
meke damun jiddana,me ya hana mata tashi, el'mustapha ya tambaya yana kallonsu
dr bakori yayimai bayanin da ya kamata and last am not sure ko xata tashi da qafar ko baxata tashi ba wannan ne ban sani ba amma munyi iya yin mu, is like ta rasa wannan qafar sai dai a siyamata wheelchair kuma asiyo drugs din da na rubuta after 1wk za'a kaita physiotherapy afara mata exercise kuma a gasa kafar dan jijiyoyin su saki.
El'mustapha ya dubesa a fusacce,
Yace ban san cewa baka san aikin ka ba sai yau, a hakan kake consultant ?kumburin qafa shi xai hana mata tafiya har kake cewa baxata tashi ba, ko kaine ka halicce ta, Uwarka ce baxata qara tafiya ba amma ba jiddana ba, ba kai kadai bane likita a duniyar nan.
Dr bakori baiyi mamaki ko jin xafin xagin da el'mustapha yayi masa ba domin bashine mutum na farko ba, ya lura jikin el'mustapha har rawa yake yana magana tamkar baa hayyacin sa ba yanda idanunsa suka juye, shi tausayi Ma el'mustapha ke bashi halin da yake ciki.
'Abba ya dafa kafadarshi shima yana sharar kwallah,
El'mustapha kamar ba namiji ba, namijin Ma dan sanda, baka yi kuka dan ganin al'ummar da ake kashewa ba sai dan matarka, mu godewa Allah jiddah tana raye muna ganin ta ba mutuwa tayi ba, Allah da yafi mu sonta haka yake son ganinta, ka xamo mai haquri da tawakkali, yau idan jiddah ta same ka a wannan halin waye xai rarrashi wani waye xai qarfafa wani?
El'mustapha yayi shiru ya kifa kai cikin cinyoyinsa, ya kasa yarda da abinda kunnuwansa suke jiyo masa jiddah baxata qara tafiya ba, saboda me xasu yanke wannan hukuncin bayan ba sune Allah ba.
Abba ya miqar da el'mustapha, hannu yasa yana share masa hawaye, ya soma tausar el'mustapha da kalami masu dadi da sanyin imani tare da tuna masa muhimmanci yarda da qaddara, dr bakori Ma ya saka baki gurin rarrashin sa tare da nuna masa baa debe tsammani ga rahamar ubangiji.
Xaku iya xuwa ku ganta tun daxu ta farfado.
'Abba yaja hannu el'mustapha kamar qaramin yaro suka nufi dakin da aka kwantar da jiddah,
A bayan kofa ya tsaya ya rabe, ya kasa qarasawa yana leqenta, idanu ya qura mata yana kallon yanda take kallon dr bakori da abba,
ji yayi antaba shoulder dinshi Dr Hafix ne yace hey be a man please, focus on what's important shine your wife ta samu lfya,capture the good times,develop from negatives, I know move on is never easy,you must fight to hold on,you fight to letgo please gather your strength before you enter, yayi masa sallama ya fice yana tausayawa mashi.
Abba, Arham fa? Shine abinda ya fito bakin jiddah tana kallon sa.
Yace arham ya sami sauqi jiddah yana tare da hajiya tana kula dashi tace a gaidaki kafin taxo.
Tayi shiru hade da shafa cikinta,
Dr bakori yace yaron ki kawai kike tambaya shi kadai kike son gani?
Tayi murmushi cikin jin kunya da nauyin abba, ta dauke kanta gefe, shima abba murmushi yayi cikin tausayawa ya fito yana kallon inda el'mustapha ke rakube.
Dr bakori yace, ki gayamin abinda kike son gani bayan arham, farin cikin ki nake so tare da kwanciyar hankalin ki, bana son abinda xai saka jinin ki ya qara hawa saboda abinda ke jikinki.
Ta juyo tana kallonsa idanunta sunyi rau rau,
Tace dr mijina nake son gani,
Murmushi kawai bakori yayi sanda el'mustapha ya shigo dakin,
A hankali ya soma taku ya isa ga gadon da take kwance, yaja kujera ya xauna dai dai da fuskarta yana fuskantarta, dr na ganin haka ya fita ya ja masu qofa.
Hannun ta tasa tana taba ciwon dake kansa, cikin murmushi tace sorry mustyna.
Ya riqe hannunta ya sumbata yana kallonta, ya kasa furta kowace kalma a gareta, baisan yanda xai fuskance ta da maganar ba, shikam a wannan fannin ya kasa juriya ya kasa samun nutsuwa a duk lokacin da ya tuna jiddah baxata qara tafiya ba, Uwani ta cutar dashi a rayuwa.
El'mustapha are you not happy with me, meke damun ka, meyasa ka canxa lokaci daya?
Ya tashi daga kujerar gadon ya hau yana kallonta har lokacin baiyi magana ba, sai ya shafa cikinta,
Ta tsura masa idanu tana kallonsa, akwai abinda ke damunsa yake boye mata, yanayin sa kadai ya nuna hakan, kada dai ta rasa arham ne, gabanta ya tsananta bugawa, ta dora hannunta akan hannunsa dake cikinta tana kallonsa shima kallonta yake,
Arham ya mutu ne?ta jefa masa tambayar, ya girgixa kansa,
Talk to me el'mustapha, meke damun ka?
Yaja dogon hancinta yana murmushi a karo na farko, yace ba komai jiddah, ta soma qoqarin tashi yayi saurin riqeta yana tambayar,
Kiyi a hankali saboda drip din dake hannunki, me xakiyi idan kika tashi,
Inyi ta kallon ka el'mustapha tunda baxaka gayamin damuwar ka ba,
'Wannan karon Ma murmushi yayi yana jin wani sanyi da nutsuwa a xuciyarshi abinda ya dade bai samu a tare dashi ba, yasa pillow a bayanta da kanshi ya gyara mata ta kishingida, ta dan dubi qafar ta kamar xatayi magana kuma sai tayi shiru jin el'mustapha na fadin,
'ni jiddah yaushe kika fara fita batare da sani na ba, meyasa da uwani ta kiraki baki kirani first kin gayamin ba, kuma meyasa kika hana dan sanda ko daya yaje dake.
Jikinta ya dauki rawa, idanunta suka kawo kwallah,
Nayi kuskure kayi haquri ka yafe min na fita bada ixinin kaba, ya dora yatsansa akan labbanta yana kallonta ido cikin ido,
Ba sai kince in yafe maki ba jiddah, tuntuni na yafe maki but tell me har yanxu kina son uwani?
Jiddah ta lumshe idanuwanta sai ga hawaye shaaa, da kyar ta bude su tana kallon kyakkyawar fuskarsa,
Ka daina tunamin da wata uwani a rayuwata, na fiddata a xuciyata da rayuwata, I don't know her and I dont want to, yarda da qaunar da na nuna mata a baya taci amanata Allah xai saka min, bana jin xan iya yafewa uwani, ka sake ta tabar mana gida bana so na sake dora idanuna akan ta.
Ita uwanin? El'mustapha ya tambaya cikin shigar tsokana,
Ta daure fuska tana kallonsa,
Xaiyi magana tayi saurin dakatar dashi hade da rufe kunnuwanta da tafin hannayenta,
Bana so kadaina el'mustapha, I don't want her in my life ko sunan ta bana son ji.
Abin ya bashi dariya sosai, ya sumbaci bakinta a hankali,
Sauke hannayen jiddah nima bana so tunda jiddatulmusty bata so.
Ina so nayi wanka, jikina ba dadi kaje ka dauko min kayana kaxo min da aryan please, ta langabe kai tana kallonsa.
Ai bama sai naje gida ba, komai naki naxo dasu suna gurin hajiya bari na karbo, ya tashi yana qoqarin fita,
Ba yanda xaa yi naga arham?
'Na gaya maki arham yaji sauqi baa bashi damar fita ko ina bane kamar yanda kema baa baki ba, kiyi haquri har lokaci yayi da kaina xan kawo maki shi, bai jira cewarta ba ya fice da sauri.
Ta bisa da kallo har ya fice kafin ta maida kallonta ga qafar tana taba kumburin, bata ji el'mustapha yayi maganar qafar ta ba kodai likitocin basu duba qafar bane, sai ya dawo xata tambayesa.
Bai jima da fita ba sai gashi ya dawo dauke da kaya jikinsa na rawa ya ajiye, ya kunna wayar sa ya bata yana nuna mata wani vedio.
Arham ne xaune a gadon asibiti yana cin burger, dariya yake da alama yana cikin farin ciki el'mustapha yayi masa vedio ya kawo mata,
Mummy I miss you ya soma kissing wayar, itama kiss tayi Ma wayar tayi murmushi tana kallon el'mustapha,
Sai ki daina damuna da arham ki kwantar da hankalin ki tunda kin ganshi a raye,
70% of my damuwa ya ragu Mustyna sauran kuma na barwa xuciyata.
Meya hana sauran damuwar su wuce, ya tambayeta yana kallonta, yanxu mecece damuwarki, gaya min naji jiddah na.
Ka saki wannan matar ta fita daga gidan mu da rayuwar mu, I don't want to see her again.
Murmushi el'mustapha yayi yana matsa MacLean akan brush din ta,
Saboda me xan xauna da igiyar aurenta akaina bayan babu jiddah a tare dani, tuntuni na sauwaqe mata ina jin kece kika matsa da auren ta saboda ke nake xaune da ita kuma babu ke meyasa xan cigaba da xama da ita?
*NAYI NADAMA* El'mustapha, bansan yanda xan gayama baqin ciki da dana sanin dake xuciyata ba, amma ina roqon ka yafe min kuskuren danayi a baya da tilasta ma danayi akan sai ka aure ta, nayi ne saboda tausayin ta da kuma iyayen mu.
Ya ja kunnenta cikin xolaya gobe Ma sai ki roqeni na auri banan tunda kin xama sarkin tausayi.
Ta bata fuska tana kallonsa,
Kace Allah ka tuba el'mustapha, da ina da iko dana bige bakin da yayi wannan furucin a yanxu, nayi hankali a yanxu wanda ka saka a inuwa shi yake saka ka a rana, ko da ina da qanwa baxan barta ta auri mijina ba ballantana wata banan, ta turo baki cikin jin haushi meyasa Ma kake mgnr banan a yanxu?
Ya kawar da mgnr ta hanyar sunkuyowa, bakinsa ya turo yana fadin kina da iko jiddah ki bige bakin idan hakan xai sanyaya xuciyarki.
Ta kai bakinta dai dai nasa ta sumbata, ya xauna yana kallonta.
Gobe ma jiddah idan iyayenki basu baki goyon baya kiyi abu ba ki qara kinji xaki ga abinda rashin bin maganar su xai janyo maki, keda Ma ba haihuwarki sukayi ba kenan ina ga alhakin su dake kan uwani.
Uwani ta cuce ki babu wata cuta a tare da ita ta ciwon xuciya, she is pretending, jiddah ta fiddo idanu tana kallonsa,
Taya akayi ka sani.
Nima ban sani ba, dan sanda ne nifa jiddah kuma ba qaramin dan sanda ba, na saba yin bincike Kala Kala kuma ina nasara, ban taba xuwa asibiti na bincika halin da take ciki ba ko kuma tambaya amma dan na gwada ta nace mata naje asibitin na bincika a gurin likitan da ta hada kai, wallahi ban sani ba I just say it, daga yanayinta da amsar da ta bada nagano hasashena gaskiya ne amma baxan gaya maki ba har sai kin gano da kanki kuma kika kasa.
Jiddah tayi shiru ta dubesa, uwani ta cuceni, dubi qafana el'mustapha, uwani har take cewa a kashe arham a gabana, a kuma kasheni, ta dauki kudin ka dasu ta biya kudin aikin mu, tsohuwar dake kula dani saboda sunji xata taimakeni suka kashe ta a gabana, kasan yanda nayi rayuwa tare da su kuwa, kasan yanda nake kwana na yini tare dasu, kasan irin abinda suke bani naci wai a matsayin abinci batare da sun duba abinda ke ciki na ba, babu tausayawa ko jinkai a tare dasu sai wani mutum daya suna kiransa goga,
El'mustapha ya rufe mata baki da tafin hannunsa yana kallon yanda take xubar da hawaye, haka yake ji kamar shima ya tayata kukan saboda tausayinta,
Ba sai kin gayamin ba jiddana, nagani da idanuna daga yanda kika dawo kamanin ki suna neman sauyawa, uwani Ma xatayi xaman prison ta dandana abinda kika ji.
Ta soma share hawayenta, ya tashi yana fadin bari na kira wata nurse ta cire drip dinnan jiddana tayi wanka tacire wannan dattin dake jikinta.
Tayi dariya tana fadin, kada kace kaji warin dattin ni bana son sharri,
Wari kam jiddana baa magana idan na cigaba da jinsa tabbas xaa bani gado a asibitin nan,
Ta janyo cup dake kusa da ita ta jefeshi a bayansa ya fice yana dariya, itama dariyar take.
Wayar sa dake ajiye a gefenta ta soma qara, idanu ta tsura tana kallon mai kira, number ce akai ba suna, bata da niyar dauka saboda bata taba masa haka ba, har wayar ta tsinke bata dauka ba,
Da wata nurse ya shigo tana bayansa, bama musulma bace ta cire drip din, bayan ta fita ya dauki jiddah sai toilet.
Yana ajiye ta