Showing 111001 words to 114000 words out of 138779 words
Chapter 38 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx
kika so kashewa a gaban mahaifiyarsa, kinsan xafi da radadin da uwa keji a xuciyarta a duk lokacin da wani abu ya sami dan cikin ta, idan har bakyason jinin el'mustapha qarya kike kice kina sonsa.
Inaji jiddah tare aka raineku kuka taso cikin gida daya qarqashin iyaye daya ta riqe ki da amana tana xaune dake da xuciya daya amma kika iya mata wannan ballantana el'mustapha da baki hada komai dashi ba, kenan shima idan ya bata maki rai watarana xaki iya saka a kashe shi.
Kuma saboda Allah dan baki da kunya da imani ki dawo kina son mijinta, hala ita bata da xuciya a jikine ko an gayamaki dutse ce bata son mijinta, kinxo kina saka damuwa a tsakanin su kina son raba mata da miji kina so ki raba farin ciki da soyayya saboda wata buqata taki ta banxa, to baxaki aure sa ba, kuma el'mustapha baxai aure ki ba.
Duk abinda kika ga kin ma iyayenki sun xuba maki ido kina ganin kamar sun kyaleki ne to akwai wannan baqin cikin a xuciyarsu naki wanda ko basu fito sun gayamaki ba yana damun su a xuciya saboda ke jinin su ba yanda xasu iya dake, dan haka kije ki nemesu gafara ki kuma je ki nemi gafarar jiddah, domin mace ce mai haquri, da ace kin tsaya kin nutsu tun farko wallahi xaki ji dadin xama da ita kuma el'mustapha har yanxu yana mijinki, amma kinyi sake da wannan damar kuma baxaki taba samun sa ba.
Kuka sosai uwani keyi tamkar ranta, sam bata da nutsuwa a tare da ita, hankalinta ya tashi sosai tana ji tana gani anti ikram taje ta fito da kayanta.
Suka fito da ita, sai ga yusuf qanin mijin anty ikram,
'Yauwa yusuf xo ka kai uwani gida,
Yace aa anty ikram ina da wani uxuri baxan iya xuwa har wani gari yanxu ba ki hadata da driver, ya gaisa dasu merah yayi ciki abinsa,
Uwani ta bisa da kallo.
Merah ya dubi el'mustapha kai kuma muje gida inda qanwata nayi maka hukunci a gabanta in ta kama ta dake ka da kanta....
Uwani ta tsurawa yusuf ido cikin mamaki, yusuf din ta ne fa, yusuf din da qawarta surry tayi snatching ta aura, ashe qanin mijin anty ikram ne amma bai taba gayamata shiyasa tayi mamakin yanda akayi jiddah tasan yusuf, bai gane ta bane kome?
Tayi saurin shan gabansa tana kallonsa,
Haba yusuf baka gane ni ba, nice fa uwani masoyiyar ka ko ka manta, dan Allah kayi haquri ka yafe min, ni dama kai nake so wlhy.
Duk gurin suka xuba masu idanu,
Merah yace wannan bata san wanda take so ba kenan, Mijin qanwata shiga mota muje kafin mai martaba ya ankara da bana gidan.
Suka ma anti ikram sallama suka fice,
Yusuf ya dube ta, idan yace baya son uwani ya yaudari xuciyarsa, cos itace first love din sa, sun fara soyayya da ita a skul har jiddah tasan da soyayyar su amma bai taba gayawa anty ikram a lokacin ba saboda yasan yanda basu qaunar yarinyar, uwani ta cuce sa ta guje sa saboda el'mustapha shine yau take dawo masa saboda auren ta ya mutu, yaja dogon tsaki cikin takaici ya raba ta gefenta yayi shigewar sa.
'Anty ikram ta shige tana fadin idan kin tashi ga driver nan ya kaiki in kuma xaki tsaya kwadayin maxa ne to, tunda ke kowa ma so kike, banxa tayi shigewarta.
A sanyaye uwani ta shiga motar jikinta ba kwari, haka take jin wata nadama na ratsa xuciya da gangar jikinta, sau biyu tana samun dama tana kubce mata, meyasa hakan, tabbas harda haqqin iyayenta.
Tasan bata cancanci jiddah ta yafe mata ba, ta aikata babban kuskure a rayuwarta, inama hannu agogo xai dawo baya da ta canxa rayuwarta da xamantakewar xamanta da jiddah, amma ta sani a yanxu abu ne mai wuya jiddah ta qara yarda da ita, lallai el'mustapha ya mata nisa kuma baxata taba samun irin sa ba.
Sanda suka iso gida driver yana ajiyeta ya juya, ta dauki kayanta ta shiga cikin gida,
Kuka take sosai sanda tayi toxali da iyayen nata xaune a falo,
Ta xauna tana kallonsu, hajiya da abba ku yafe min, nidai naga ta kaina ko yanxu naga rayuwa kowa baya sona a duniyar nan kowa baqin ciki yake min, suna ta cewa na canxa halina, ya xanyi na canxa abba.
Duk suka mata shiru musamman ma hajiya da har yanxu bata huce haushin ta ba,
Uwani ta cigaba da fadin, shine suka kirani naje aka hadani da wani bature dan baqin ciki wai el'mustapha baxai aure ni ba sai dai ya hada ni da dogarin sa kuma shima din idan aka bincika sona yake kawai dai yana min baqin ciki ne.
Ta matso kadan kusa da abba,
'Dan Allah abba ku yafe min ko naga haske a rayuwata, duk nasa buri a abu baya kasancewa sai dai ya lalace, bana ganin haske a duk al'amari na, ni na gane harda haqqin ku dana anty jiddah, ku yafe min abba.
Hajiya dai bata ce komai ba, abba yace Allah ya shiryaki yasa kigane abinda kike kina quntatawa iyayenki.
Uwani ta dubi hajiya tana fadin, hajiya kinyi shiru har yanxu kina min baqi..... bata qarasa ba taji saukar Mari a kuncin ta,
'Ashe baki da mutunci ban sani ba cewar abba yana kallonta a fusacce, iskancin ya kai har ki kalli mahaifiyar ki kice tana maki baqin ciki, baqin ciki yafi duk wanda ta kawo ki duniyar kika bijire mata, ya janyo wayar cable a fusacce,
Uwani na ganin haka ta soma roqonsa tana bashi haquri, abba ya soma dukanta yana fadin, dama ba na barki bane jira nake har mahaifiyar ki ta dawo na yanke maki hukunci a gabanta akan rashin kunyar da kike ma mutane tuni na gane iskancine ke damunki, anci kudina kawai a asibiti ba wata lalura dake kanki.
Ya soma dukanta sosai baji ba gani, hajiya na xaune har wani sanyi take ji yau anyi mata maganin uwani.
Gskyr abba abin na uwani iskancine tunda har tasan ta rufe bakinta da hannun kada ta fadi abin da xai qara tunxurasa,
Banda gurnanin kukan ta ba abinda kake ji a falon,
Hajiya tashi ma tayi ta bar falon, abba kuwa sai da ya gaji dan karan kansa, lokacin uwani ko kwakkwaron motsi ta kasa yi, kukan ta kuwa har qofar gate ana jiyo ihun ta, duk jikinta yayi tsamin duka, tana kwance tana maida numfashi.
*
Yanda suka bar jiddah haka suka dawo suka same ta xaune a falon, wannan karon arham na kwance a jikinta yana cin pringles din sa.
Merah ya xauna yana kallon el'mustapha, wannan hannun da kake maqalewa haka meya same sa,
El'mustapha yace qanwar kace ta min wannan raunin wajen kishi.
Amma fa ta kyauta, muga hannun, El'mustapha yaqi bada hannun yana fadin an riga an duba min kabarshi hakan.
Ya dubi jiddah yana fadin very soon Afiya da Rumaisa xasu shigo Abuja biki, idan sunxo El'mustapha please take her to them, olready xan masu mgn akanta xasu kaita inda ammi da mai martaba,
Idan yaqi, ki kirani jiddah serious baxaka ji dadi na ba,
El'mustapha yace to yayan jiddah sai me kuma,
Sai maganar wannan yarinyar kuma, ba dan na isa ba amma ina roqon ka, ka fita hanyar yarinyar tun da ba auren ta xaka yi ba, inma taimaka mata xakayi jiddah should be the first person da xaka fara gayawa, idan bata amince ba ka barta in kuma ta amince mai sauqi ne, she is your wife, your life partner, share your secret with her nasan tana da sauqin kai xata fahimce ka.
Jiddah idan ta xauna da Afiya ta gayamata wasu sirruka believe sai ka raina kanka, ni kaina mulkina da sarauta ta a waje take kawai amma da xaran na shiga gida munyi two eyes da Afiya to itace sarkin, sai kayi mamaki duk ranar da ka ganmu tare.
El'mustapha ya tabe bakinsa baice komai ba,
Jiddah kema You have to be respectful to your husband, duk abinda yayi maki ku xauna ku fahimci juna, idan shine bashi da gaskiya you let him know ba sai wani ya ji a waje ba sirrin ku ne, idan kuma kece baki da gaskiya kiyi gaggawar bashi haquri, mijin kine, aljannar ki tana gurin sa, kiyi masa biyayya, idan ya bada haquri ayi haqurin dan xama yayi dadi, na tuna sanda mai martaba ya aura min Afiya ba abinda yake ce min a koda yaushe, na riqe ta hannu biyu, nayi haquri, nayi haquri, ban gane haqurin da yake mgn ba sai bayan tafiyar Afiya wanda a lokacin ganewar bata da amfani a gurina.
Ki daina rufe kanki a daki, akwai irin fushin da mace ke yiwa namiji wanda ke daga hankalinsa ya kuma ruda sa ba sai ta hanyar rufe qofa kawai ba, domin xaki iya cutar da kanki a ciki baki sani ba.
So, on behalf of El'mustapha ina bada haquri, a yafe masa kuskuren da yayi baxai qara ba, please qanwar merah.
Murmushi tayi ta sunkuyar da kanta qasa batare da tayi magana ba,
Kai kuma idan ka qara maimaita irin wannan xan dauke kane na kaiwa mai martaba, ni naga kamar ma jiddan bata haqura ba, in kuwa haka ne gaskiya dundu xan tayi maka har sai ta bude baki tace ta haqura.
Dariya ta subulcewa El'mustapha yana kallonsa,
Yace jikin mu ba daya ba, sai dai kajiwa hannunka ciwo.
Dr merah ya tashi cikin wasa yana fadin bari a gwada a gani, idan na fara baxan bari ba har sai jiddah tace ta haqura.
El'mustapha yace to shikenan indai akan jiddah ne xan jure komai idan har xata saki fuska ta daina fushi dani.
Ganin fa da gaske merah dukan el'mustapha xaiyi a baya, tayi caraf tace,
Yayan mu ai na haqura fa,
Cikin dariya yace ai da kin barni nayi masa ko daya ne, ashe dai kina son sa haka.
Merah bai bar gidan ba sai da yaga ma'auratan sun saki jiki da junan su sosai kamar ba abinda ya hada su, har jiddah tayi masa abubuwa sosai naci sai murna yake domin wani abin ma bai san dashi ba, ya saki jiki sosai dasu kamar daman sun saba da juna,
Sanda xai tafi el'mustapha tsadaddiyar shadda guda biyu ya bashi ya kaiwa mai martaba, sosai merah ya nuna farin cikin sa yayi masa godia.
Har merah ya shiga mota el'mustapha ya sunkuya yana kallonsa da murmushi,
Karka manta idan har kana son twins ka dage, kace Afiya ta dage nothing worth comes easy mu ma sai da muka dage,
Merah dariya yayi yana fadin, xan baka mamaki kuwa, triplet xamuyi nida Afiya insha Allah.
Allah ya kawo masu albarka cewar el'mustapha,
Ameen merah ya amsa cikin murmushi,
Shiru el'mustapha yayi yana kallon yanda merah ya hade fuska tun bayan fitowarsa inda masu tsaronsa, kamar bashi bane suke dariya dashi a daxu, ya daga masa hannu sanda suka fice.
Yana shiga falon ya rungume jiddah sosai yana sauke numfashi,
For only yesterday jiddah, kinsan yanda naji?
Ta janye jikinta tana murmushi,
Arham is watching us,
Ya juya yana kallon arham, yaron kuwa yayi masu qur da ido kamar na Serdia.
El'mustapha ya nufe sa yana fadin, I hug mum let me hug my arham too,
Arham ya soma dariya sosai lokacin da el'mustapha ya cira sa sama,
Daddy saura aryan shima,
Yace baya nan sai ya dawo tukunna,
Airah fa, arham ya fada yana kallonsa.
El'mustapha ya xauna yana fadin tana barci sai ta tashi.
Yaran xamani kenan duk abinda kake idanun su yana kanka, iyaye sai an dage an kauda ido.
*
A gurguje😏
Acikin wata biyu abubuwa sun gudana ko ince sun faru, ciki kuwa harda engagement din uwani, ku tambayeni da waye, baxa kuji a bakina ynxu ba🏃🏻♀
Amma fa ba laifi tun dukan da abba yayi mata abubuwa sun ragu sosai daga uwani, kullum abba yana hukuntata, acikin gidan komai ita keyi ya sallami mai aikin su, ta dawo wata iri sai kunyi mamaki duk da ba duka aka nutsu ba akwai dan rawar kai tukunna.
Haka ya dauke ta ya kaita islamiya ya hada ta da wani malami duk ranar da bata je ba ko tayi wani abin Allah wadarai acikin makarantar ya mata duka sosai kada yayi Dublin girmanta,
Uwani bata dauki xancen da gaske ba sai ranar da tayi fada da wata a aji akan biro kuma itace beta da gaskiya saboda anqi aramata ta karbi biron ta karya tana fadin idan akwai uban da ya tsaya maki yaxo yace na biya.
Aikuwa a ranar ta daku, ko da taje gida tana kuka ba wanda ya kula ta illa girki da aka ce ta dora.
Tun daga lokacin take tsoron ta nemi wani da fada, kuma ganin yanda yake takura mata akan karatunta ya saka ta maida hankali,
Dalilin haka abba har kyauta yayiwa malamin domin ya qara jin dadin kula masa da uwani.
Bari mu leqa amaryar mu banan😊
Banan anyi kyau ta kwantar da hankalin ta sosai ta rungumi mijinta da hannu biyu, kulawa da soyayyar da take masa bata son ko kadan mace ta rabe sa.
Shi kansa yaji dadi sosai samun soyayyar banan, tana da hali mai kyau kuma tana da biyayya akan duk abinda ya umurceta dashi, bugu da qari tana girmama yan uwansa sosai, ya yarda banan rainon jiddah ce kuma yana roqon Allah yasa ta dore a hakan.
Akai akai take xiyarta jiddah, ita ma jiddah tana xuwa ba laifi, suna xumunci sosai duk abinda ya shige mata duhu tana gayawa jiddah ta wayar mata da kai.
Waye wannan mijin uwani🤔
Ku biyo ni🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀
EL'MUSTAPHA
Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers
Fertymerh Xarah💞
62
_Flash Back_
Yusuf tun da ya ga uwani a ranar ya rikice dama tuni ya dade da sanin tabar gidan el'mustapha, yana da labarin duk katobar da ta aikata.
Ranar surry ta kasa gane kansa har ta shiga damuwa,
Uwani nake so na aura surayya.
Wace uwanin ta tambaya cikin tsananin mamaki.
Yace uwani qawar ki mana,
Kai haba, chabdi, wallahi baka isa ba, da kasan kana sonta tun farko meyasa ka aure ni, ka tuna fa kaine na roqeni na aure ka saboda cin amanar da uwani tayi maka, na amince na aure ka saboda kyawawan halin ka da kuma haushin abinda uwani ta maka, amma meyasa xaka min haka, shekara biyu da watanni da auren mu xaka ce xaka min kishiya, kishiyar ma irin uwani ballagaza, me nayi maka yusuf?
Hankalinsa ya tashi sosai, ya matso kusa da ita da sauri ganin yanda take kuka,
Yace wallahi surayya idan nace maki bana son uwani na maki qarya, itace mace ta farko dana fara so, duk haukan ta haka nake son ta tunani watarana Allah xai shiryata idan muka yi aure, sai nagane daga baya uwani el'mustapha take so qanin matar yayana, ban gasgasta ba sai bayan ta aure sa, na shiga damuwa da tashin hankali sosai lokacin shine dalilin da yasa na aure ki saboda nima na baqantawa uwani, kuma ke da kanki kin gayamin yanda kuka yi dalilin haka har kuka sami sabani, amma wallahi ina son ki surry, ba dadin baki ba kuma ba ina gayamaki ne dan ki yarda dani ba, har acikin xuciyata a yanxu nafi son ki akan son da nayi wa uwani a baya, ni kawai dai ina so na aure tane.
Ta share hawayen ta, ta tashi tana fadin,
Shikenan baxan hana maka auren first love din ka ba, sai dai ni baxan xauna da kai ba, baxan xauna nayi kishi da wannan mahaukaciyar ba, indai har uwani ta iya cutar da anty jiddah saboda el'mustapha tabbas ni qona ni xatayi saboda kai, dama tana jin haushina tsab xata iya saka a kashe ni, baxan xauna ba sai ka sake ni.
Ya tashi ya riqo ta, haba surry idan kika tafi kika barni ya kike so nayi ne, idan ba kyason xama da uwani a gida daya ne wallahi xan ware maku pls surry,
Lallai yusuf ashe abin naka da gaske ne, Uwani kake so, wallahi baxan yarda ba ko ni ko ita.
Yace wallahi na xabe ki na gayamaki ke nake so surayya, ina jin tausayin uwani ne kowa baya sonta ya guje ta saboda halinta.
Ina ruwanka dole sai kai xaka aure ta, maxa nawa ne a duniya, bana son wannan maganar kada ka qara tada min xancen uwani a gidannan idan ba haka ba xan barshi.
Ya xauna yana fadin shikenan ba damuwa na amince.
Taja qaramin tsaki cike da haushi ta bar dakin.
Ranar barci sai dai barawo a idanunta, har mafarki tayi uwani ta biyo ta da wuqa xata kashe ta, ta xabura tana addua, yusuf ya bude idanuwansa yana kallonta,
Me ya faru surayya?
Wallahi mafarki nayi uwani tana bibiyata da wuqa xata kashe ni,
Yayi shiru yana kallonta ta cigaba da fadin wallahi uwani annobace baxaka gane ba yusuf, qawatace na fika sanin wacece ita.
Yace Allah ya kyauta ya gyara kwanciyar sa.
Ta koma ta kwanta cike da tunani iri iri, wani mafarkin tayi wannan karon uwani ta biyo ta da qatuwar tabarya tana faduwa ta fara dukanta da ita har sai da ta daina numfashi.
A xabure ta tashi tana kyalla ihu, yusuf Ma ya tashi a firgice yana kallonta,
Ta fashe da kuka tana kiran, ina wallahi uwani baxata shigo gidan nan