Showing 33001 words to 36000 words out of 138779 words

Chapter 12 - El-mustapha Complete Hausa Novels By Fertymerh Xarah.docx

09 Oct 2025

2020

an gurxu idanu har sun kumbura saboda kuka, da kyar ta samu barci ya kwashe el'mustapha gurin saboda gajiya.

Da rarrafe tabar dakin ta nufi falo, wayarta ta dauka ta kira jamcy ai kuwa tana dauka ta fara dura mata ashar kafin ta gayamata komai.

Dariya jamcy tayi tana fadin, ashe kin sha dadi uwani kin shigo layin manya, to ai shine auren, xafin da kike ji xai bari kuma inaji kinsa masa maganin da yawa ne.

Biyu nasa masa, gaskiya baxan qara yarda ba ni kin cuceni.

Keda nace ki saka masa daya, yanxu dai ba matsala kin xama mace abinda jiddah ke taqamar  dashi yanxu kema sai ki fara ki nuna mata kema fa duk daya kuke, sannan abinda el'mustapha yayi maki a yanxu ai kinga ba laifinsa bane naki ne so kada ki nuna masa damuwa ki ta masa shagwaba ki nuna masa babu wani a xuciyarki sai shi, ki daina gudunsa ki daure komai xafi xaki daina ji.

Anya xan iya kuwa jamcy kinji yanda abin yake kuwa baya tausayina.

To ai kinga laifinkine, idan kikace xaki riqa hana masa to taya xaki haihu ko kin manta, sannan fa da wannan abin xaki siye xuciyarsa, ki daure qawata.

Uwani ta sauke ajiyar xuciya kafin tace to shikenan xan qoqarta.

Yanxu ina el'mustapha din,

Yana daki yana barci.

Ki koma ki kwanta dashi, gobe kada ki nuna masa damuwa kuma ki tabbatar kin shiga ruwan xafi sosai kin gasa jikinki.

Uwani ta ajiye wayar tana tunani.

'Washe gari da matsinancin ciwon kai el'mustapha ya tashi, ya dafe goshinsa yana kallon gefen da uwani take kwance,

Gabaki daya komai na dawo masa tiryan tiryan, ya soma tunani meya hau kansa ne har ya kwanta da uwani bai sani ba, shikenan yaci amanar jiddah, da wane ido xai kalli jiddah duk ranar da tasan wannan.

Allah ya gani bada nufi ya aukawa uwani ba, bai san ya akayi ba sai dai kukan uwani yake ji, sai kuma ya tausayawa uwani, da kyar ya tashi ya nufi toilet.

Alwallah yayi ya fito a gurguje ganin ya makara sallah yau.

Har ya gama shirinsa da komai uwani bata tashi ba, ya bar gidan da sauri, koda uwani ta tashi bata damu da rashin ganin saba, ita yanxu Ma ta qarajin tana sonsa sosai.

Jiddah kuwa xaxxabi ya rufe ta, banan ta damu sosai ganin yanda jiddah ke ta xuba amai gashi sai kuka take har lokacin,

Itama banan din kuka take tana roqar jiddah suje asibiti, da kyar jiddah ta amince, banan ta kama mata ta shirya suka fito.

Gwajin farko a asibiti suka tabbatar tana dauke da ciki wata biyu, banan ta rungumeta cikin farin ciki,

'Anty jiddah xata haifa mana baby, Allah yasa twins ne mata.

Duk da halin da jiddah take ciki bai hana mata godewa Allah da kyautar da yayi mata ba, sai kallon banan take da murmushi yanda yarinyar ke nuna damuwarta akanta.

El'mustapha ya damu sosai na ganin yaqi samun wayar jiddah, da kyar ya kammala abinda ya kawo sa garin amma duk jikinsa ba kuzari, bai koma gidan ba sai dare.

Inda uwani ma bai kalla ba, yayi shirinsa na barci ya kwanta, uwani bata damu ba ta kwanta bayansa hade da dora hannunta a qirjinsa tana shafa.

Shiru yayi yana sauraren rashin ido na uwani, ya janye hannunta yasa blanket ya rufe jikinsa hade da lumshe idanuwansa.

Ranar jiddah taga kulawa gun banan, kayan kwadayi irin na masu ciki banan ke mata, sosai damuwar jiddah ta rage kasancewar banan na qoqari akanta na ganin ta hanata shiga damuwa.

'Washe garin ranar da xasu dawo kamar jiddah baxata je tarbar shi ba amma tunawa da tayi shi ya bata umarni akan haka yasa ta shirya suka tafi tare da driver.

Sun jima suna jiransu kafin jirgin ya sauka, su uwani a jirgi?

Daga can ta hangi fitowar el'mustapha, uwani na bayansa sai kalle kalle take abinka da baa saba ba.

Babu xato el'mustapha yayi toxali da jiddah tsaye, nan yasha jinin jikinsa, gwiwowinsa suka yi sanyi,  gaban sa ya fadi, ya rasa wace irin fara'a xai mata, dariya ko murmushi? Kamar qasar gurin ta tsage ya shiga yake ji saboda kunyar jiddah.

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association

Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

30

Uwani na ganin jiddah ta saki wani malalacin murmushi,

'Anty jiddah ashe kece kika xo daukar mu, ya gida.

Murmushin itama jiddah ta maida mata,

'dole nake xuwa daukar amarya da ango, ya amarci.

'amarci alhamdulillah mu ma mun xama manyan mata.

Jiddah bata kula ta ba ta dubi el'mustapha dake tsaye yana kallonta sororo, duk da abinda take ji a xuciyarta game dashi bai hana mata qarasawa gurin sa cikin murmushi ta rungumeshi hade da sumbatar kumatunsa tana kallon idanuwansa.

'Barka da xuwa mijina, ya amarci, da kyar ya amsa mata bayan ya qago murmushin yaqe yana kallonta,

Lafiya lau jiddana, ta dauke dubanta daga garesa, wai jiddansa bayan ya munafurceni yake kirana da jiddansa, sai kace ni kadai ya ajiye, ya dauki uwani sun tafi amarcin su harda kiran ta a waya dan taji idan haushi xai kashe ta sai ai kashe ta ai kuwa baxata nuna masu hakan dan suji dadi ba, ta yarda namiji bashi da ta ido el'mustapha ya raina mata wayo ya bayyana mata zahirin abinda ake kira da Namiji.

A yanda ta lura el'mustapha ya shiga cikin wani hali na damuwa, ko da suka shiga mota yana gaba da driver bai sake magana ba, ita kuma tana tare da uwani a baya, ko kadan batayi tunanin kallon inda uwani take xaune ba saboda wani haushinta da take ji a xuciyarta.

Suna isowa gida jiddah ta fara fita daga motar bata tsaya sauraren su ba tayi ciki abinta, Uwani kuwa jakarta ta dauka jikinta ya fara sanyi daga yanayin el'mustapha tun a Lagos bai qara mata magana ba ko yunqurin hada ido da ita, to meke nan?

El'mustapha inda yaransa ya nufa suna gaisawa cikin mutunci da nuna yanda sukayi kewar uban gidan nasu.

Yana shiga falon twins suka xo da gudu suka rungumeshi,

Daddy is back, daddy daddy....

Ya rungume su yana dariya cikin farin ciki, saboda halin da yake ciki Sam ya manta baiyi masu tsaraba ba abinda bai taba yi ba yayi tafiya bai kawowa yaran komai ba.

Daddy me ka siyo mana? Abinda yaji Aryan na fadi kenan, ya dubi yaron yana fadin,

Daddy ya manta bai siyo komai ba aryan, arham ya tunxuro baki.

Amma daddy kai kace a waya gobe xaka siyo.

Kubari na huta sai inje in siyo maku anjima.

Suka soma tsalle, har dakin sa suka bisa suna surutu yana biye masu.

Ki hadawa el'mustapha abincin sa kafin ya fito, jiddah ta fada tana kallon banan.

To anti nama kammala maki dan'waken da kika ce ko na xuba maki ne.

'Yauwa xubamin naci ko anan kitchen ne ta fada tana qoqarin xama.

Dariya banan tayi tana kallonta, anty a kitchen xaki ci.

Yi sauri ki hada masa banan kafin ya fito, kixo kije kasuwa kinsan me xaki siyomin.

Banan ta girgixa kanta tana qoqarin hada kayan abinci,

Ko da yake idan na gayamaki yanxu dariya xakimin bari har ki gama tukunna.

Murmushi kawai banan tayi ta miqa mata plate na dan waken, kallonsa kawai jiddah tayi sai da yawun ta na tsinke yaji kaya sosai.

Ta dauki abincin el'mustapha ta fita, tana jerawa a dinning ya fito twins na biye da shi har lokacin.

Har qasa banan ta gaidashi kanta a qasa, ya amsa yana qoqarin xama a dining, suma duk suka xauna.

Jiddah fa shine abinda ya fito bakinsa yana kallonta, ta juyo tana fadin tana kitchen..... Idanun su suka sarqe a karo na biyu, jikinta ya dauki rawa ta juya da sauri tabar gurin.

Jiddah fushi take dashi kenan abincin Ma yau baxata yi serving din sa ba, da kansa ya xubawa twins kowane da plate din sa kafin ya xuba nashi.

Uwani ta fito daga daki tana taunar cingam, tayi mamakin ganin el'mustapha yana cin abinci shi kadai, a tunanin ta xai neme tane suci tare tunda yasan tana jin yunwa ko breakfast bai bata a acan ba.

Kitchen din ta nufa tana tafe tana girgixa jikinta saboda el'mustapha ya gani, bata sani ba Sam bata gaban sa abinci kawai yake ci amma hankalinsa da nutsuwarsa duk sun tafi gurin tunanin jiddansa.

Tana shiga kitchen din ta kalli abinda jiddah keci ta yatsina fuska, kafin ta dubi banan.

Ke me kuka dafa mana ne wai, banan ta dube ta,

'Anty uwani baa ce nayi girki dake ba, yaya kawai akace nayi wa girki.

Uwani ta dubi jiddah sheqeqe kafin ta dubi banan.

'au nida gidan mijina sai ayi girki a hanamin, ok sai ance kiyi girki dani xakiyi kenan, to ni me ake so naci ko ni xan shigo kitchen din na dora.

Banan tace akwai abinci na gida gaba daya acikin gida nasan baxasu rasa cire maki naki ba.

Uwani ta dura mata ashar, el'mustapha ya dago yana kallon hanyar kitchen din cikin son jin hayaniyar me akeyi.

Ke har kin isa ki gayamin abincin da xanci, nima ai personally ce a gidannan😂, ina da iko kamar wacce ta ajiyeki, duk abinda xatayi nima xanyi.

Jiddah ta dubeta bayan ta ajiye plate din dake hannuta,

Uwani idan kin fahimci maganar banan tana gayamaki ne baa bata ikon ta dafa abinci da kowa a gidan nan bane sai ni da el'mustapha kadai,

Uwani ta dube ta, ok kece kika daure mata qafa take iskanci Kala Kala a gidannan, haba no wonder yarinyar nan ta rainani yanxu da kike mgnr baa bata ikon ta dafa abinci dani ba hala ni ba matar gidan bace ko kuma ke me kika fini a gidan, nima fa yanxu mace ce kamar kowa fa adaina min kallon yarinya nasan komai yanxu.

Ai nasan ke macece ba sai kin fito kin fadawa duniya hakan ba, akwai masu aiki a gidan ki saka su dafa maki.

Ke banan ke xaki dafamin abinci, ina jiranki yanxu kada ki batamin lokaci, ta juya ta fice a fusacce.

Wlhy baxan mata girki ba sai dai kome xai faru ya faru cewar banan.

Ba kya tsoron ta maki duka ne banan, jiddah ta fada tana qoqarin wanke hannunta a sink.

Duka anti, ai na wuce shi a gurinta sai dai ke da kika ajiyeni, yanxu fa na girma candy xanyi na wuce tunanin ta, idan ta dake ni ramawa xanyi.

Jiddah ta dube ta tana fadin nima watarana haka xakice kin wuce na dake ki banan, sannan ko uwani bataci arxikin komai ba ai taci na el'mustapha ina ke ina dukan matar mai gida, dan haka kiyi haquri ki dora mata ai ba komai bane, duniya yanda ka dauke ta haka take daukar ka, bana so ki xama daya daga cikin mutanen da basajin maganar manyansu.

Shiru banan tayi amma xuciyarta xafi take, tana ji a ranta watarana sai dai tabar aiki a gidan dan wlhy sai tayiwa uwani dukan tsiya a gidan musamman idan ta cigaba da yiwa jiddah rashin mutunci a gabanta, ko kadan baxata jure ganin ana wulaqanta mata anti jiddah ba.

Jiddah ta fito daga kitchen din riqe da hijab din ta a hannu,

Kallon twins tayi tana fadin idan kun gama cin abincin kuxo kuyi shirin xuwa islamiya.

Momy ai daddy yace xamu je yayo mana tsaraba,

Xakuje da dare bayan kun dawo, be fast aryan dubi yanda kake cin abinci.

Kallonta kawai el'mustapha keyi har sanda ta fice wannan halin ko inkula da jiddah ke nunawa akansa ba qaramin tada hankalinsa yake ba, shi bai masan yanda xai fuskance da mgnr ba.

Ya tashi ya nufi dakin uwani, kallonta yayi fuskarsa tamau ba alamar wasa.

Xan gargade ki akaro na biyu game da jiddah, saboda jiddah kike a matsayin da kike yanxu ba dan haka ba ke kinsan baki isa na tsaya ina hada numfashi dake ba, idan kunnuwana suka qara jiyomin kina mata rashin mutunci irin na yau xan maki abinda xai sa ki tsane ni, gidannan da duk abinda ke cikinsa na jiddah ne ita keda ikon komai nawa, matasayinku ba daya bane matatace ta har abada ke kuma auren shekara daya ne kada ki manta, ina qara jajjada maki ki tsare kanki akan jiddah.

Kayi haquri honey insha Allah xan kiyaye,

Mtsewwwww ya fice, ta bisa da kallo lallai anci moriyar ganga dole xaa yarda kore, Kaji dadin abin kaxo kana wani noqewa, ai sau biyu kayi min nasani ban manta ba ko kotu mukaje xan iya bada shaida, bari girkina ya qara xagayowa wani xan qara sakama kuma, kuma gidannan baxan barshi ba sai dai jiddah ta barshi baxaku tabbata har abada ba,  wlhy baka isa ba daga kai har jiddah maganin ku xanyi a gidannan muje xuwa.

Gabaki daya yinin ranar bai sami fuska a gurin jiddah ba, shi kadai ke walagiginsa a gidan sai twins din sa,

Haka da dare ma bayan sun dawo shi da twins yana kallonta ta saka ya'yanta gaba suka barshi anan falon, kuma jiddah dai tana sane da girkintane tunda kwana biyu yayi acan tare da uwani.

Sam bata jin haushin uwani kamar yanda take jin na el'mustapha,

'Washe garin ranar da kanta ta shirya twins cikin shirin makaranta, bayan sun tafi ta soma kiciniyar hada masa kayan breakfast.

Ta gama komai tana jerawa a dinning ya fito cikin shirinsa na fita office,

Kallo daya tayi masa ta kawar da kanta gefe, ya qaraso gabanta idanunsa akan fuskarta.

Xan jure kowane irin hukunci daga gare ki amma banda wannan fushin jiddah, kiyi min abinda duk xaki min tun daga kan fada, duka koma menene indai xai sanya ki huce daga wannan fushin kidawo da walwalar ki.

Shiru tayi xuciyarta na qara hauhawa kamar yanda kunnuwanta keyi mata kururuwar muryar uwani a ranar,

Ta lumshe idanunta ta qara budewa sai ga hawaye sharrr nabin kuncinta, el'mustapha ji yayi kamar shima ya tayata kukan, bai qara magana ba ya juya yabar falon batare da ya waiwayi breakfast din ba yana qara jin tsanar uwani a xuciyarsa domin itace sillar komai.

Yinin ranar sukuku jiddah tayi, tunanin banan duk jikin ne na jiddah shiyasa komai da jiddah keyi a ranar duk ita tayi, akai akai take xuwa duba jiddah tana tsoron kada xaxxabi ya rufe ta kamar ranar.

Ta rarrashi xuciyarta dan meyasa xataga laifin el'mustapha tunda itace ta tilasta mashi auren ta kuma dole xai sauke nauyin dake kansa na ganin ya baiwa uwani haqqinta dan baxai xuba ido yana kallon uwani ba ita kanta din an cutar da ita, shikenan uwani ta gama sanin sirrin mijinta shiyasa har take yada mata habaici, meyasa uwani baxata kwantar da hankalinta ta gyara rayuwarta suyi xama na aminci ba kamar sanda suna gaban iyayensu.

Da xuciya daya ta taimakawa uwani saboda ciwon ta da kuma darajar iyayenta, maqasudin Ma jin uwani na qoqarin yi masu asiri ta rabata da el'mustapha ya qara sanya ta amince da auren ashe bata tsira ba.

Alamar bude gate din gidan taji wanda babu tantanma tasan el'mustapha ne ya dawo,

Ta tashi ta nufi toilet ta wanke fuskarta, har ta fito bataji alamar shigowar sa ba, window ta nufa ta daga labulen tana kallon motar.

El'mustapha na xaune cikin motar, kansa na sitiyarin motar ko me ke damunsa ta fada a bayyane yayin da gabanta ke tsananta bugawa, kada fushinta ya janyowa el'mustapha wata matsalar.

Ta fita daga dakin ta nufi harabar gidan, har ta isa gurin motar el'mustapha bai san ta iso ba, ta glass din motar ta tura hannu ta jijjigashi hade da fadin baban twins,

Ya dago firgigit yana kallonta, ganin haka yasa jiddah taja baya tana dariya hade da ware masa hannayenta dan ta kawar dashi daga halin da yake ciki.

Oyoyo Baby is back..... Nan da nan ya balle murfin motar ya fito, jikinsa na rawa ya rungumeta, ya matseta sosai a jikinsa hakan yasa tagane sosai yaji dadin hakan, taja hannunsa suka shiga cikin gidan.

Xaunar dashi tayi bakin gado ta dawo gabansa ta tsugunna tana kallonsa,

'menene wai duk naga kayi wani iri ka canxa, are you not happy with me, jiddanka fa?

Yatsun hannuwanta ya matse a hankali, kallonta yake murya a sanyaye, kiyi haquri ki yafemin jiddah, kin ganni tare da uwani alhali bakisan tare xamu je ba, wallahi wallahi na miki rantsuwa Allah ne shaidana ganin ta kawai nayi a Lagos banma san yanda akayi taje can ba.

Murmushi jiddah tayi hade da Jan dogon hancinsa,

Nasan wacece uwani nasan xata iya, kuma bayan haka uwani matarka ce You have the right kaje da ita duk inda kake so a duniyar nan ba wanda xai hana, ka daina rantse min, fushin da kaga ina yi dakai bacin rai ne amma kayi haquri.

Yanxu ya xanyi dake jiddah, me xanyi na tsira daga gurinki bana son bacin ranki ko kadan a tare dani.

Nikam a gurina ka tsira baban twins, bana xargin mugun nufi a xuciyata game da kai ko uwani, dan haka bayanin da kayimin na gamsu, na yarda da kai, na amince Ma 100%, abu daya da xan tunatar da kai adalci kada ka juyamin baya saboda uwani.

'Na amince dake kamar yanda kika amince dani jiddah, da yardar Allah baxan juya maki baya ba baxan baki kunya saboda adalci ba uwani bata da matsayin da xan gujeki saboda ita.

Shiru tayi bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login