Showing 30001 words to 33000 words out of 186400 words

Chapter 11 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt

20 Jan 2025

18795

har sukakai anguwan su, a kofar gidansu ta hango Ammin su tsaye sanye da dogon hijabin ta hanunta rikeda waya, da hannu tamai pointing Ammi tace "ga Ammi na nan" rage gudu yayi tareda rage karfin wutan gaban motan sabida karya haska Ammin sosai tun kafin yay parking tawani irin bude motar da gudu tai wajen Ammi data tsare motar da kallo. "Ammi, Ammi, Ammi" kafin Ammi tace ma wani abu taje da gudun gaske tai tsalle ta rungume Ammin kaman wacce tai shekara bataga Ammin nataba, rungumeta tight Ammi tayi tanama Allah godiya. "Alhamdulillah" kafin ta dagota daga jikinta takama habarta da hannu daya tasa dayan hanunta tana share mata fuska tace "Alhamdulillah Allah nagode maka, you are ok ko Aneesa na?" hannun Ammi ta rike tareda gyada matakai tana murmushi hakan yasa Ammi tasake sata ajikinta ta rungumeta, shiru yayi ya tsaya a mota yana kallonsu, looking at affection din Ammi towards Aneesa yasa yaji he just wish Mummy shi was alife to hug him like this, he miss his mum so so sooo much, lumshe ido yayi ahankali zuciyanshi namai wani irin zafi.










Ahankali yajinginar da kanshi da kujera kirjinshi namai wani irin zafi, knocking glass din motar da akayi yasa yabude ido ahankali, Ammi yagani tsaye rungume da Aneesa a gefenta, ahankali ya bude kofar shibai masan mezaiyi ba yadai sami kanshi da kasa daga fuskarshi ya kalleta zaiyi magana Ammi tarigashi. "nagode, nagode bawan Allah, yanda ka taimaki Aneesa Allah ya taimaka maka adukkan al'amuranka, Allah ya haskaka rayuwan ka, kakawo mini ita har gida safe and sound, thank you so much, may Allah reward you abundantly" kasa ma magana yayi sai gyadamata kai da yayi ahankali, ganin haka yasa Ammi tadan bugi kafadar Aneesa da kanta ke kasa tace "bakimai godiya ba Aneesa" ahankali tajuyar da kanta ta kallai har lokacin kanshi akasa dauke idanunta tayi daga kanshi ta maida kan yatsunta data shiga wasa dasu ahankali tace "nagode sosai, Allah yasaka da alkhairi" murmushi Ammi tayi tace "mun gode malam saida safe, wuce mutafi Aneesa" jan hanun Aneesan tayi tasa key tabude kofar gidansu dahar ta kulle ta shiga, dan waigawa Aneesa tayi tasake kallon motar dudda bata iya ganinshi daga wurin amma saida gabanta yafadi da sauri ta shige ta maida kofar tarufe, sukai cikin gida, falo suka shiga ta ijiye souvenir da akabata akasa ta zauna kusada Ammi tana bude jakanta tace "Ammi barina saka chaji tunda akwai wuta, yautun safe bansama wayata chaji ba" ciro wayar tayi daga jaka tana kokarin kunna wayar kwan lantarkin falon yawani irin yin kara ya tarwatse da gudu tarike Ammi sabida tsoron dataji, salati Ammi tayi. "innalillahi tome kuma yasami kwan lantarkin ko karfin wutan yay yawane?" tai maganan tana kunna wutar toculan wayanta ta haska wajen wutan taga yanda yafashe, tsaki Aneesa tayi tace "Ammi dama wanan na dan dari uku baida kyau energy bulb yafi wanan yan darin dakike siyowa kyau, anmafa ce baya jan wutafa, bari naje nasiyo" tai maganan tana zage handbag dinta ta kwaso duka kudin da aka bata ta mikama Ammi tareda zare dubu daya ta mike tsaye tareda daukan hijabinta, Ammi dakebin kudin da kallo tace "wayabaki kudi dayawa haka Aneesa?" dan dariya tayi tace "amaryan tabani wai kudin lallena bari nadawo nabaki labarin abinda ya faru yau" dubu biyu Ammi tazaro cikin kudin tamika mata tace "gashi ki shiga gidan Maman su Muhammadu kice nace gashi injini" karba tayi tace "to" tawuce tafita daga dakin tana haskawa da wayanta dan tsakar gidansu dama babu fitila, bude kofar gidansu tayi tafita tana haska kudin hanunta da waya tacire dubu biyun tarike su separate sanan ta shiga gidan dat is next to them inda Ammi ta aiketa ta mika kudin tafito tana kalle kalle, idanunta ne suka sauka akan motan daya kawota ganin har yanzu motan na wurin baitafi ba, faduwa da gabanta yayi yasa tasauke kai da sauri ta dena kallon motar, tsallakawa tayi dayan side din tai wajen wani shago dayake chan gaba kadan, ta shiga tasayo kwan lantarkin mai kyau nadan dari biyar sanan tajuyo tanadan satan kallon motan tana tafiya towards there house, sosai mamaki yakamata ganin har lokacin motan na wurin tai hanyar kofar gidansu tana kallon motar, hannu tasa zata bude kofar gidansu saikuma ta janye hannun tasake juyowa ta kalli motan to kodai baida lafiya ne? Mutumin da tun dazu yakawo ta aiya kamata ace yatafi by now, in fact yamayi nisa ahanya, kasa hakura tayi ji kaman wani abu na fizganta tafara tafiya so take kawai taduba shi taga ko lafiya, ahankali take tafiya tana kallon motar kafin takarasa gaban motan taga yabude kofan motar hakan yasa ta tsaya chak takasa karasawa tadan kwantar da kanta tana lekawa, ahankali yasa kafarshi yafito daga motar yamaida kofar motar yarufe tareda jingina da motar ya rungume hannayenshi a kirji yana kallonta, faduwa gabanta yayi sosai sabida yanda idanunsu suka hadu da sauri tajuya zata koma ya kira sunanta for the first time. "Aneesah!" tsayawa tayi chak jin yanda yakira sunanta har ranta taji kiran sunan saida duka organs din jikinta suka amsa, murya chan kasa ta yanda ita kadai ne zata ijiyajin meyace calmly yace "come" sosai takejin maganan shi nazuwanma zuciyanta kaman command, kasa jurewa tayi tajuyo ahankali taa kallai, gyada mata kai yayi tareda dan lumshe ido sanan yabude su yadaura akanta, daga kafa tayi ahankali tataho wajen kanta akasa ta tsaya agefen shi kafafun ta nadan rawa sabida wani sanyi dasuke mata da batasan nameba, juyowa yayi yay facing dinta yana kallon yanda take wasa da kwalin kwan fitilan hanunta, murya chan kasa yace "ina kikaje?" batare data kalleshi ba kanta akasa tace "kwan lantarki naje nasayo" shiru yadan yi kafin ahankali yace "maisa baki aiki brother kiba yaje kika fito da dadaddare?" kanta akasa tace "uhm banda brother" "ke kadaine?" yatambaye ta immediately bayan tai maganan, gyadamai kai tayi batare datai magana ba, ahankali yace "what about your Dad?" dago kai tayi ta kalleshi hada ido sukayi da sauri ta maida kanta kasa, ahankali cikin wani irin siriruwar murya tace "yarasu" sosai kalman yarasun yadaki zuciyan shi hakan yasa yay shiru yana kallonta sai chan yace "sorry! Allah ya jikanshi" gyadamai kai tayi kaman zatai kuka dan sosai tuna mata da Baba, ahankali tace "Ameen" sukadanyi shiru batare dawani daga cikinsu yakara cewa wani abuba, dan dago kanta tayi ta kallai ganin ita yake kallo har lokacin yasa tace "in tafi?" girgixa mata kai yayi yace "No" tsayawa tayi duk tanajin wani iri yanda ta tsaya dashi danko kadan bata saba tsayawa da samari ba ita bamata dawani saurayin kirki dan batabasu lokaci. "me kikaje yi agidan bikin nan?" hanunta ta shiga wasa dashi kanta akasa tace "lalle naje yi musu" "lalle? You mean henna? Are you a henna designer?" gyadamai kai tayi tace "eh, na iya" dan murmushi yayi yarinyar nan bala'in burgeshi take bana wasaba, shidai in his life this is the first girl daya taba gani dayaji ta burgeshi, dago kai tayi ahankali kaman wacce take tsoron ta kalleshi tadan kalleshi tace "ya kanwar ka?" dan shiru yayi kafin yadan juyar da idanunshi cikin jin dadi yace "oh Rauda? Dama kin ganeni?" gyadamai kai tayi da sauri tace "eh tundazu ai naganeka, kunyi kama ai da ita saida kafita uhmm...uhmm" muryan ta ya sarke sotake tace yafita kyau amma takasa fadi hakanan taji tanajin kunyan tace mai haka, murmushi yayi sosai ganin takasa fadin abinda takeso tace mai, murya chan kasa cikeda zolaya yace "ashe kin iya kuka haka I tot mara tsoro bata kuka eh Fearless lady?" rufe fuskarta tayi da hijabi da sauri tareda yin murmushi akunyace tai gaba zata wuce dan maganan ta ya mugun bata kunya da sauri yace "wait" tsayawa tayi chak batare data juyowa ba sai murmushi take ya mugun bata kunya, cikeda murmushi tace "wat? kaga Ammi na zata zo tanemeni yanzu nan" tafiya daidai yake hanunshi zube cikin aljihu harya tako ya tsaya abayanta chak, yanda tajishi abayanta yasa taji numfashinta na neman daukewa da sauri tajuyo sukai facing juna yanda taga yana kallonta yasa taji takasa magana sai numfashi take fitarwa da sauri da sauri heart dinta is beating way too fast kuma batasan mesaba sai kyafkyafta ido take, one step yakara ya matso gab da ita ahankali yace "can we be friends Aneesah?"










Ba karamin faduwa gabanta yayiba jin kalaman dasuka fito daga bakinshi, rawa lips dinta yafara tanadan zaro idanu zatai magana yamika hanunshi ya karbi wayanta dake kan hanunta ya bude ganin ba key, danne danne ya shiga yi kafin ahankali yamika mata wayan yace "take" hanunta tamiko ta karbi wayan da sauri tajuya tai cikin gida tarufo kofa, hakanan yaji ko kadan baiji dadi data tafiba kaman yabita, komawa cikin mota yayi yabude ya shiga, kifa kanshi yayi akan starring mota ya fuzar da iska he seriously don't know what's wrong with him, tun daga fitowan Aneesa daga gidan bikin tareda Nihal idanunshi suka sauka akanta lokacin yana tareda Abdul a cikin mota, Abdul yacemai sutafi yace yaje shizai shigo anjima, haka ya dinga kallonta ta mota har lokacin databi motan su Lado da gudu da lokacin data shige lungun mota da lokacin data fara kuka tana waya, shidai baisan mesa ba he just love natsuwar yarinyar, yanda take tafiya a natse, da yanda take magana a natse, da yanda muryanta ke fita so gently and innocently bala'in burgeshi yake, boldness din yarinyar use to melt his heart, bai taba ganin yarinya dat match his taste like her ba, hakanan yaji he just wanna be her friend, a girl like her is worth associating himself with, wayarshi dayay kara yasa ya kalli wayan ganin Dad ne yasa ya ijiye wayan yasan fada Dady zai fara baifito da bodyguard dinshiba, tada motar yayi yaja yana lumlunshe ido he's so tired dan driving dinan dayayi, and he's so sleepy Allah dai yakaishi gida lpy kawai.






















Dakinsu ta shiga da sauri Ammi tace "meya daddar dake haka?" rasa abinda zatace ma Ammi tayi hakan yasa ta shiga kame kame kafin tace "uhmm Maman Muhammad ne ta shiga wanka saida najirata tafito fa Ammi" tai maganan tana hawa kan kujera dayake tanada tsawo tana hawa takai ta makala kwan lantarkin aiko wuta yakawo sanan ta sauko, dakinta tayi tacire kaya tadauro zani tafito, tsakar gida tawuce tadau bucket tajuye ruwan zafin da Ammi tadaura ta shiga bayi tayo wanka tareda dauro alwala fitowa tayi tawuce ta shige dakinta wani dogon rigan atampa tasaka sanan tadau hijabi tafito Ammi dake binta da kallo tace "bakiyi salla ba?" gyadamata kai tayi tana hawa kan dadduma tace "banyiba" magrib da isha tayi bayan ta idar tai shafa'i da wuturi, sanan ta cire hijabin tana sauke ajiyan zuciya ta kwanta akasa tana mikama Ammi kafafunta a shagwabe tace "wash Ammi kafana ciwo" murmushi Ammi tayi ta karbi kafafun ta daura kan cinyanta tace "raguwa kawai" matse kafafun nata ta shiga yi hakan yasa ta lumshe idanu wani mugun bacci na neman dibanta, kafeta da idanu Ammi tayi tana kara godema Allah daya bata yarinya mai natsuwa ga hankali, Aneesa is just a gift to her life duk rashin jinta inhar tace tak to ta natsu, she just pray Allah yabata miji nagari dazai kula da ita yabata all that she deserves, karasa matse kafafun tayi sanan tadan bubbugata ganin tai bacci. "Aneesa, Aneesa, tashi kije ki kwanta" bude idanu tayi dake cikeda bacci ta kalli Ammi, Ammi tace "tashi kije ki kwanta sannu yau mata sun aikatu" murmushi tayi ta mike tsaye tana tafiya ahankali tawuce, wayarta tadauka dake kan kujera ta wuce dakinta kwanciya tayi kan gado bayan tai bismillah sanan tai addu'an bacci wani bacci mai dadi yau awon gaba da ita.


_"why, why Aneesa? I trusted you, mena miki da zaki kasheni eh? I trusted you Aneesa, you are my friend, we are friends remember? I love you Aneesa, why, why, why, why, dama kin tsaneni, dama so kike ki kasheni, why Aneesa?!" yadaka mata wani irin tsawa da duka karfinshi daya rage kumfa na fita daga bakinshi, idanunshi sunyi jajir yana kakarin mutuwa hawaye na bulbulowa ta gefen idanun._ afirgice ta farka daga baccin daya kwsheta tana wani irin zufa komi na mafarkin datayi na dawo mata fresh, mutumin dazu tagani kumfa na fitowa daga bakinshi yana kakarin mutuwa yana mata all this maganganun itakuma tana gefenshi idanunta sunyi jajir sai kuka take ga ankwa a hanunta, batasan mesaba fashewa tayi da kuka sosai tana girgizakai, karan wayarta daya cika dakin yasa ta mugun firgita, da sauri tasa hannu ta goge hawayen daya bata mata fuska tamika hannu tadau wayarta dake gefen filon ta kalli screen din. "Aliyu" taga yana kira, faduwa gabanta yasake tazaro ido ta kalli time a jikin wayan 12:25Am.
[06/03, 09:20] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






1️⃣6️⃣


_How to subscribe_


_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting. You can also send MTN card ta watsapp number na 07012181461 for those dabasu da account_


_*littafin nan na kudi ne, duk wacce takaranta batare data biyaba ban yafeba, pay anan ko pay alahira, your choice 🤷🏿‍♀️ gumina ne, hakkina ne inada iko akai*_


Gudun kar Ammi taji karan ringing wayar daya cika dakin da kara tafito tace me takeyi da waya ware haka, wayake kiranta this night yasa tai picking wayar da mugun sauri hana kokarin hadiye kuka datakeyi takai wayar kunnenta batare datai magana ba, ajiyan zuciya Aliyu daya kasa bacci tun dazu dudda mugun baccin da yakeji yakasa sai tunanin ta yakeyi yasauke ajiyan zuciya ganin tadauka, murya chan kasa mai kunshe da sakonni da dama wanda shi kanshi baisani ba yace "Aneesah are you sleeping?" girgiza mai kai tayi kafin ahankali muryanta narawa sosai tace "a...a'a" tashi yayi zaune daga kan gadon jin yanda muryanta ke rawa kaman wacce ke kuka, murya chan kasa yace "Hey, are you crying?" girgiza mai kai tayi tace "a'a" jin yanda muryanta kefita yasa yaji wani irin damuwa ya dira aranshi, cikeda damuwa yace "are you sick?" "no" ajiyan zuciya yasauke jin lafiyanta kalau yace "is Ammi sick?" girgixa mai kai tayi tace "n...noo" cikeda damuwa sosai yace "why are you crying then a irin wanan lokacin eh Friend?" magana takeso tayi saikuma tafashe da kuka sosai sabida yanda ta tuna mugun mafarkin datayi, tashi hankali shi yayi da sauri yace "kidena min kuka yana dagamin hankali, talk to me" kaman bada ita yakeba ta cigaba da rera kuka ahankali, katse wayar yayi da sauri danjin kukanta yake har jijiyoyin zuciyan shi, ya lumshe ido tareda jinginar da kanshi jikin gado ya fuzar da iska, he's so damn worried sabida kukan dayaji tanayi zuciyarshi batada natsuwa, shi baimasan lokacin da zuciyarshi tafarajin damuwan wata aranshi ba sai akan Aneesa, tsaki yaja ya kalli wayan dayaketa jujjuyawa a hanunshi, sake dailing number ta yayi kaman zai katse saikuma ta dauka, murya chan kasa dake cikeda damuwa sosai yace "wats wrong with you Aneesa? Why are you crying?" murya chan kasa tace "babu komi" girgiza kai yayi yace "a'a, akwai abinda ke damunki tell me we are friends remember" yanda yake mata maganan ataushashe kaman mai lallshin ta shikuma ba lallshin yakeba yasa taji zuciyata ta natsu sosai. "tell me friend what is wrong with you? Why were you crying? Kinyi laifi ne Ammi tamiki fada?" hawayen fuskarta ta share tass kafin ahankali ta girgiza mai kai kaman yana gabanta tace "mafarki nayi" dan murmushi yayi for the first time tunda suka fara wayan yace "wat!! Mafarki kikayi kikema kuka haka?" dan murmushi yasake yi maidan sauti dayasa ta lumshe ido tabude su yace "you are one hella wired girl friend" yadanyi dariya kadan kaman ba Aliyu ba dat u hardly see him laugh, tsayar da dariyan yayi cikeda tsokana yace "tell me mafarkin mekika yi friend nima natayaki kukan to" juya idanunta tayi tareda dan turo baki a shagwabe tace "ai namiji baya kuka, kuma mafarkin tsoro ne sosai shiyasani kuka" cikin wani irin murya na shagwaba kaman yanda tayimai shima yace "frienddd come onnn is just a dream, just a dream" shiru tayi tasa hannu tadafe kirjinta heart dinta is beating way too fast sabida yanda takejin muryan shi, jin shima yay shiru kaman yana sauraron bugun zuciyan natane yasa tace "scary dream, very scary" gyara kwanciya yayi tareda jan bargo yana lallube kanshi dan sanyi yakeji gashi yakara karfin AC sosai, ahankali yace "scary how? Mafarkin is about wat?" da sauri tace "about you" hannu tadaura akan bakinta surprisingly dan bama tasan lokacin data fadi hakaba, gyara kwanciya yace "about me?" yay murmushi sosai yace "my friend had a scary dream about me, tell me about the dream, dodo nazama nazo nacinye ki kome am eager to know" girgiza kai tayi tana turo baki tace "ance babu kyau fadin bad dream" "but ai am your friend right Aneesah?" yatambayeta ahankali, faduwa gabanta yayi sabida yanda yay maganan, batasan lokacin data gyadamai kaiba tace "eh" murmushi yayi yace "alright, tell me, am all ears" shiru tayi na kusan 2min kafin tace "ni bansan meya faruba amma nai mafarkin na kasheka, but baka mutubafa amma nakasheka kumani bansan how ba, kumfa dai nata fitowa daga bakinka kana cemin mesa na tsaneka, maisa na tsaneka nakeson kasheka nikuma sai kuka nakeyi shine nafarka inata kuka" dariya yafashe dashi sosai harda dan dafe ciki, kaman zatai kuka tace "da gaske nake fa stop laughing" jin yanda tai magana kaman zatai kuka yasa yahadiye dariyan yace "okay, lemme ask you some questions" gyara zama yayi yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login