Showing 123001 words to 126000 words out of 186400 words

Chapter 42 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt

20 Jan 2025

18831

basu zaci zata iya amfani da wukan ba sukayo kansu da gudu.










Wani irin ihu da Mubarak yayi yakoma baya yasa da sauri Baffa dake zaune kan yar kujeran dakinshi yana sauraron labarin BBC hausa na safiya yana kallon Inna na zubamai man shanu kan dumamen shi itama tana sauraron labaran da yakeji ya rage karan da sauri yana gyara zama jin kaman yaji ihu, hayaniya dasuka ji na yaransu yasa atare suka Mike tsaye da sauri, Inna ce tafara yaye labulen ganin yanda hannun Mubarak auta ke fitar da jini sosai yasa tasaki salati tafito da sauri tai wurin Baffa biyeda ita shima yana saurin, karasawa wajen tayi takama hannun Mubarak dake kuka sosai yana kallon jinin dake zuba daga hannunshi tace "innalillahi, menene haka? Meya yankeka Hamma na eh dan Autan inna shi?" cikin fushi Khaleelu na kallon Aneesan dahar lokacin na rikeda wuka tana kallonsu yace "Aneesah ce ta yankeshi shine dan inamata fada wai inna karacemata kala saita parkamin ciki nima" da sauri inna ta zare dankwalin kanta tareda warware wa ta nannade hannun Mubarak tana kallon fuskan Baffa dayay shiru yana kallon Aneesan kaman wani wawa, yanda take hararansu ta damke wukan gam a hannu kaman jira take wani yazo ta fideshi, ahankali Baffa yadaga kafa tareda karasawa inda take hannunta dake rike da wukan takama yarike cikin rashin wasa yace "bani wukan?" kallon fuskanshi tayi ganin yanda yay kini kini da rai yasa ahankali ta sakin mai wukan ya karba, sanan yace "kinyi sallan danace kije kiyi?" girgixa mai kai tayi alamun a'a tana cije pink cute lips dinta, hanyar dakinta yanuna mata da hannu yace "wuce kije kiyi salla kafin na mugun saba miki" sakin lips dinta datake taunewa tayi ta bataraii cikin fushi tai hanyar dakinta ta yaye labule ta shige, ahankali Baffa yajuyo hannun Mubarak din ya karba ganin Inna tariga ta kulle wajen yasa yace "sannu ya isa haka kubar maganan maganan, kuwuce kuje kusha kokon ku, zan sayo maka pain killer kasha Mubarak" wucewa duk sukayi dan suna mugun jin maganan mahaifinsu basuma Baffa gardama koma yayene ko akan miye, yarage wurin daga Inna dake kallonshi saishi, dago kai yayi ya kalleta zaiyi magana tajuya fuuuu tawuce, ajiyan zuciya ya sauke cikin tsananin damuwa sanan ya tsugunna dayan wukan daya gani acikin kwanukan wanke wanken ya dauka yay dakinshi ijiye wukaken yayi a wuri daya ya killace su gudun karta kara dauka sanan ya zauna gaban tuwonshi yana kallon tuwon dake turiri danya dumamu sosai ya fuzar da iska cikeda damuwa, wanan lamarin yafi tunaninshi ta bayanshi shine dama haka yara kedawowa in aka kaisu gidan yari??? Inko har hakane koma wani laifi yaro zaiyi gwara a hukunta shi agida dan zuwanshi gidan yari tabarbara komi yake saima dai yamaida yaro abinda yafi da worse and worse and worse.kika karanta batare dakin biyaba, Allah ya isa, ban yafemikiba.


Ahankali yasa hannunshi yashiga laluba aljihun gefen riganshi kaman mai neman abu, waya yaciro yakira number Na Sani bayan ya dauka yace "anjima kazo Na Sani, ina neman ka" da sauri yace "to Yaya, dama inada niyyan zuwa zanma kawo Jamila taga Aneesan itama" ajiyan zuciya Baffa ya sauke yace "shikenan saikun tahon" marfin samiran dumamen shi yadauka yarufe, sanan yay shiru yakai kusan minti goma ahaka yana tunani sanan yamike tsaye yafita daga dakin.










Dakin Inna ya shiga tana zaune ita da yaran sunashan koko da kuli kuli, Mubarak kuma yanasha da biscuit data bashi idanunshi sunyi jajir sai sannu takemai, Inna ya kalla ganin babu Aneesa adakin yace "maisa baku kira Aneesa ba tazo kuyi karin kumalon tare?" cikin fushi kaman jira Inna take tace "sokake naje kokuma natura yarana ta farka min cikin su, inta illatamin yara hakuri fa kawai za'a bani bayan ancuceni, inhar yarinyar nan yanka mutane take wlh mai gida bazan iya zama da ita ba uwarta nachan gidan miji tanashan dadi ni ina nan ina fama da wahalan ta dakuma jinyan yara, iyakan gaskiyata nafadi maka dan naga ba Aneesan dana sani bane, Allah kadai yasan iyakan yawan abubuwan data koyo a gidan yari wanan Aneesan yar daba c........" hannu Baffa yadaga mata yana mata wani irin mugun kallo batare dayace mata komiba, yaransu sunriga sun tasa so ko kadan bayason suna fada da Inna agabansu banda hakama Inna mace ce mai kirki, matace ta gari, ga hakuri, yasan Aneesa ce tabata mata rai dan yana kallon yanda Aneesa tamata dazu dayace taje tai alwala, gashi kuma ta yanke Mubarak amma to Yaya zaiyi? Hanunka na rubewa ka yanke kayar ne? Aneesa yarshi ce, koyaya ta dawo dole ya so ta sanan ya kula da ita, shine waliyunta shine komi nata, dole yarike ta a hakan yana kuma mata addu'a Allah ya gyara mai ita, sanan Allah yafito mata da miji nagari. Ahankali ya zauna kan kujeran falon sanan ya kalli Ibrahim yace "jeka kiramini Aneesa Ibrahim" tashi Ibrahim yayi yafita, yaye labulen dakin Aneesan yayi da sauri tadago kanta ta kallai tana kan dadduma, tashi tayi da sauri tana dunkule hannu kaman wacce zatai dambe tace "lafiya kokazo ramamai ne?" daga sama zuwa kasa ya kalleta wani masifan haushin ta yakeji sabida yanda takeyi, tabe baki yayi yace "kinzaci kowa irinki ne mahaukaci eh? Nidai Baffa yace nazo nakiraki" yana fadin haka yajuya abinshi dawani irin mugun gudu Aneesa tafito daga dakin nata, tsugunnawa tayi tadau dutse gaban bakin kofanta ta daddage ta jefama Ibrahim din sai bayanshi tace "uban waye mahaukaci eh? Uwarka ce mahaukaciya baniba" wani irin juyowa Ibrahim yayi dutsen data jefamai ya bala'in shiganshi daurewa sosai yayi dan baiso yay ihu ko kuka ta rainashi kaman yanda Mubarak yamata dazu, dawani irin zuciya yayo kanta tana tsaye babu alamun guduwa tace "kataba ni kaga" baiyi wata wata ba ya wanka mata lafiyayyen mari mai kyau bai sauke hannunshi ba kaman ba ita ya maraba ta daddage ta kama hannunshi da duka hannayenta takai bakinta sai bakinta ta datse hakoranta akan fatarshi ta dannamai wani azababben cizo, dayan hannunshi yasa yana tura mata kai baya yana huci sabida tsaban azaban dayakeji amma ko gezau, jin tayago fatarshi da hakoranta tadago fatar sama kaman wata vampire yasa yay wani irin tsandara masifaffen ihu. "Abbbaaaaa!" jin ihun Ibrahim yasa daga Baffa, Inna da yaran suka zabura suka mike har ana rike rigen fita.
[15/04, 07:53] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






6️⃣0️⃣






_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461, marasa banki can also send katin MTN to WhatsApp number na_




_duk wacce takarantamin littafi batare data biyaba wlh ban yafemata ba_


_duk wacce ta fitar min da book waje itama ban yafemata ba_










Ihu Inna tayi. "innalillahi wa innailaihi raji'un jama'a zata kashemini dana" tai wajen da gudu tana kallon yanda Aneesa taki sakin hannun jini na diddiga kasa ta zubama Aneesan duka abaya tana ihu tace "ki sake shi" da sauri Baffa yadaka mata mugun tsawa. "ke Aneesah, ki sakai" ko kallon Baffan batayiba, ihu Inna tayi tace "wlh wlh bazan tsaya ki kashemin d'a agabana ba bari kiga kina karyan kin zama yar daba ce" inna tai hanyar garken awakan su da gudunta tana ihu. "Fateema, Fateema, Fateema bazaki sakaiba so kike na dakeki eh Fateema" Baffa yafada ko kadan bayason yataba ta bala'in tausayi take bashi, ga Khaleelu da Mubarak sun kumbura fam kaman su chaka mata wuka sukeji amma babu hali sabida Abba dake wurin. Da gudu Inna tadawo rikeda sandar kora shanaye tadaga zata rapka ma Aneesan dataki sakin hannun Ibrahim dake mugun kuka yana ihu Baffa yarike sandar cikin fushi yace "karki kuskura ki rafkama yarinyar nan sandar nan nagaya miki Maman Hamma" fashewa da kuka Inna tayi tana kallon Ibrahim daya fara kiran sunanta yana zufa yana kuka harda majina. "Inna, Inna kice tasakeni" rufe ido Inna tayi tace "ka saken mini sandata baban Hamma, kashe shi zatay......." kasa karasa maganan tayi ganin bayan wani namiji dake sanye da white long sleeve t-shirt, yasa hannunshi dake sanye da wrist watch na rolex ya damki kumatun Aneesa da karfi, pressing kumatunta da karfi ta yanda yakai har kashin hakorinta Aneesa jitayi kaman zata mutu sabida mugun matsemata kumatun dayayi irin yanda akema yara subude baki dan dole a zuba musu magani bashiri tasaki hannun Ibrahim dawani irin sauri ya fizgi Aneesan yay baya da ita Inna da Baffa sukaja Ibrahim dake seriously bleeding fin na Mubarak ba Aneesah ta dagamishi fata wlh sosai tsabagen cizo dan dole sai anyi stitching.
Wani irin kallon Aneesan dahar lokacin yaki sakin kumatun ta yake yana kallon yanda jini ya bata pink lips dinta yana mata wani irin kallo tana kiciniyar kwace kanta amma takasa. "are you Mad? Ke vampire ce? What's all this? Wacce irin mace ce ke?" Dr Zaid yafada cikin fushi, da sauri Inna tasakin ma Baffa Ibrahim din dayake kokarin daure cizon sabida jinin dayake yi tayo kan Aneesan tace "zokibar gidan nan zokibar gidan nan wlh bazan zauna dakeba" ta kalli Dr Zaid dayaki sakinta har lokacin tana share hawaye tace "kaga bawan Allah yanzun nan ko minti gomafa ba'ayi ba ta yanki autana da wuka gashichan a daure wajen da tsumma dan jinin ya tsaya, shine fa baban su yatura Ibrahim yakira ta tazo ayi karin safe saidai mukaji ihun Ibrahim kaga yanda ta dayemai fata kuwa, Ke mayya ce, wlh saikin bar gidan nan bazan taba zama da annoba ba, ban tsaneki ba Aneesa amma bazan iya zama da abinda ke cutar dani dakuma y'ay'ana ba, munji kinfi maza karfi kinyi kokari, atafa mata amma zoki barmin gidana tafi chan wajen uwarki tanachan tanashan dadinta gidan sanata". Ahankali Zaid yake kallon Aneesan yanda ya matse bakin nata yaci ace tai kuka amma ko alamun hawaye babu saidai idanunta dasukai jajir, ahankali ya saketa, yowa tayi kaman zata dakeshi ya rungume hannayenshi a kirji yana mata wani irin kallo kasa dukan nashi tayi cikin fushi tace "wlh ka kara kamamin baki sainai fata fata dakai shiga shara ba shanu dakai aka....." dauketa da akayi da mari yasa takasa magana tadago kanta Baffa ke tsaye akanta yana huci ya nunata da yatsa yace "kul Fateema, kinma nagida bance miki komiba bazan taba bari kima na wajeba, rashin kunyar da fitsaran naki harda wanka ya taimaka miki ya kawoki gida, sanan yamiki treatment batare daya karbi ko anini ba iyye kina hauka ne?" cikin fushi tana hararan Zaid da har lokacin yana rungume da hannu tace "to me ruwan shi da ni Baffa, wlh inya kara tabani saina faffarka shi baisaini bane" bakaramin haushi Baffa yaji tabashi ba hakan yasa yasake dauketa da mari yace "nike miki magana kina bani amsa Aneesah iyye" lumshe ido da sauri Zaid yayi hakanan yaji yaji saukan marin har kanshi, fuuu Aneesah tajuya batare data sosa wurin marin ba dan karta kofsa kanta agaban su Zaid da Khaleelu sumata dariya Baffa ya fizgota cikin fushi da fada da bata taba sanin Baffa dashiba yace "ni nake miki magana kina juyawa nagama dakene eh?" saukar da kanta kasa tayi ta shiga wasa da kumbunanta batare datace komiba, cikin fada sosai Baffa yace "duk randa kika kara taba wani a gidan nan dan cikinsu banga wanda bai girmeki ba wlh saina barki dasu sun kakkaryaki tunda angayamiki karfin namiji dana mace daya ne, fitinanniyar yarinya kawai wuce kibani waje shashasha" yanda zuciyarta ke tafarfasa ko yasa taji kuka ya tsaya mata a wuya amma ta dage ta danneshi sunyi kadan suga hawayenta, tsawa Baffa yadaka mata yace "bakiji nace ki batce mini daga gani bane" fuuu tajuya tashige dakinta, Baffa ya fuzar da iska tareda hade hannu ya kalli Dr Zaid zaiyi magana da sauri Zaid yakama hannun Baffa ya girgiza kai akunyace yace "a'a Abba, a'a dan Allah karka fadamin abinda kake shirin fadamini, muje naduba yaron datajima raunin" yay maganan yana sakin hannun Baffan sukai inda Ibrahim ke zaune yana zuba sosai idanunshi sunyi jajir ga danshi danshin hawaye yaji azaba, ga Inna da yan uwan shi gefenshi duk ransu abace sai sannu su kemai, cikeda tausayi yace "sannu kaji, muga hannun" karban hannun yayi ya warware tsumman da inna tadauremai saiga jini dan taba sama saman fatan Zaid yayi yaga fatan tariga tadaga, dago kai yayi Baffa yace "halan sai anyi dinki" gyadamai kai Zaid yayi ya kalli Khaleelu da shi kadaine lafiyayyen kasancewan hannunshi yabaci da jini baiso yabata jikinshi yasa yace "zo" da sauri Khaleelu yazo, Zaid yace "sa hannu a aljihu kaciro key motata kaje waje ka bude zakaga kit na asibiti akan dayan kujeran, ka dauko ahankali akwai abubuwan fashewa aciki ka kawomin" da sauri Inna tace "yi maza yayansu" ciro key Khaleelu yayi yay waje da gudu baiwani jimaba yadawo dauke da baban kit din, Zaid yabude ya dauko spirit yazuba akan ciwon ihu sosai Ibrahim yayi shi kanshi Baffa saida yatausaya mai, saida yay dressing ciron dan cire any kind bacteria to avoid infection sanan yay stitching Ibrahim saida yay kuka sabida zafi sai sannu su kemai, saida yagama tass sanan ya duba na Mubarak shi yankan wukane batasame shi sosai ba wanke mai hannun kawai yayi yay dressing, Inna tace "nagode nagode likita Allah yabiyaka, yanzu nawa zamu bayar wanan aikin" akunyace Zaid yace "haba Umma danna duba kannai nane saikun biya, haba mana" murmushi Baffa yayi ahankali kaman bashine yagama fushin da itaba yace "har kunyan ka nakeji sabida nasan abinda tamaka, dan Allah zaka iya dubo marajin maganan nan zazzabin yasauka wlh sosai jiya bayan kamata karin ruwan jiya" akunyace dan yana wani irin masifan jin kunyan Baffa yace "to Baffa" da sauri Baffa yace "ka shiga ciki" statoscope yadauka yay hanyar dakin Baffa kuma yadaga Ibrahim yace "kumuje ciki" sukai daki.




Chan kasa Zaid yay sallama tareda yayi labulen yana kallonta akan gado yaganta zaune ta kumbura fam jira kawai take tafashe, dago jajayen idanunshi tayi ta kallai batare datai magana ba dan intai magana zata iya tai kuka kuma bataso tayi dan murmushi Zaid yayi cikeda tsokana yace "meto na share hawayen da gudu dankin ganni" cikeda fushi Aneesa tace "Allah kyauta inmuku kuka, a ina kaga ina kuka eh? A ina? Kawuce kafitan mini daga daki wlh konai kasa kasa dakai Allah kuwan" baki yakama kaman yaro yay kaman zaiyi kuka cikin tsantsan salon tsokana yace "wayyo Allah Mummy am scared, tsoro nake, tsoron Fateema Aneesa almasifatu jarababbiya oh my God, hahahaha" ya kyalkyace da dariya yana kallon fuskanta yana pointing dinta da yatsa sokawai yake ya tunzurata tataso, tsayar da dariyan yayi ya kalleta tareda jan gajeren tsaki yana pointing dakin da yatsa kaman yana pointing kashi yace "stupid girl, kazama, babu abinda kika iya sai yanka mutane yar daba kawai, look at inda budurwa kamanki ke zama, look at your dirty room, daki sai wari duk kin cikashi da warin jikinki kazamiya kawai, ko akafa aka dauramin mace irinki akace na aura bazan taba aura ba wild gir....." bai karasa maganan ba Aneesa tazo gabanshi kaman an jehota tana kallon fuskanshi tace "ka kara fadin one single word against me saina kasheka Allah dama ance kisa nike, ta kanka zan fara na kwarai, ka kara cewa wani abu akaina kagani" sosai yakejin saukan numfashinta akan fuskarta, yana kallon right into her eye ball yace "u are a fool, kin dauka fada yankan mutane shine solution to your sorrows, venting your anger akan wanda all they wish for you is love and happiness shows how full u are, kazamiya wawiya mafadanciyan yarinya mai cizon mutane kaman karya" hannu Aneesah tadaga azuciye zata wanka mai mari ya zubamata wani irin kallon dayasa taji takasa saukar da hannun nata kan fuskarshi dudda yanda kirjinta kemata zafi da daci, cikin kakkausar murya yace "maran, maran and free your soul, release and vent this anger akan wani and be yourself" hannunshi ahankali yadaura kan hannunta data kasa saukewa kasa tana kallon fuskanshi ya matse ahankali while looking at her yace "I don't know you tun jiya dana hadu dake nake tunanin ki, kin bani tausayi matuka, you are too young for wanan mugun prison din, my question is why are you this violent? What is the matter with you, allow me to help you okay, make me your friend, menene, menene menene? Tell me meke damunki, are you missing your mum?" da sauri Aneesah ta kawad dakai sabida hawayen dayake zuwan mara data kasa hana kanta tana kokarin komawa kan gadon, hannunta yarike gam batare daya saketa ba, bakinta narawa sosai fuskarta facing the other side tace "ka......s....sakeni, s....ken mini hannu" murya chan kasan makoshi yace "saikin fadamin abinda ke zuciyan ki" cikin ihu dawani irin kuka dake zuwa tundaga zuciyanta dayazo mata cikin wani irin murya kuka tace "A...a....l.....i...y.....u!" tafashe dawani irin kuka sosai tana kokarin durkushewa kasa, sakin hannunta yay ahankali ta durkushe kasa gabaki daya........






Faduwa mug din coffee dake hannunshi yayi yamike tsaye da sauri tareda dafa kirjinshi, lips dinshi nawani irin rawa yace "A.....anee.....s...sah" da sauri ya shiga juyawa yana kallon ko ina a dakin dan tabbas yaji muryan Aneesah takira sunanshi cikin kuka.
[15/04, 07:57] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






6️⃣1️⃣ & 6️⃣2️⃣






Da sauri Abdul dake kusada Aliyun a kan kujeran yatashi ganin yanda Aliyu ya zabura, kafadarshi yataba yace "menene Leo? Jibi yanda kafasa mug,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login