Showing 48001 words to 51000 words out of 186400 words

Chapter 17 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt

20 Jan 2025

18813

"lafiya lau Abba" murmushi Dady yasake yi yace "gud girl, babu abinda ke ciwo ko? Ko asakeyin allura ne?" da sauri ta girgiza kai tai kaman zatai kuka, dariya Dady yayi hakan yasa Ammi ma tadan murmusa koba komi maison naka abun kaji dadi ne, dariya Dady yayi ya kalli Dr daketa murmushi yace "tokanaji ko likita Ya'ta batason allura karka kuskura kamata" ya kalli Aneesa yace "idan Dr yamiki alluran zan dawo anjima kinfadamin kinji" da sauri ta gyadamai kai tana murmushi sai taji inama shi baban tane tanason Baba sosai tana bala'in son Baba, dan juyawa Dady yayi ya kalli Ammi da kanta ke kasa yace "cigaba da bama y'ata abinci ai baki koshi ba ko?" gyadamai kai tayi tana murmushi, Dady ya juyo ya kalli Ammi datamai kyau sosai dan tasaka wani maroon hijabi yace "kinji ko" dan dago kai Ammi tayi ta kallai hada ido sukayi da sauri tasauke nata tana kokarin debo rice din a spoon tace "angode Alhaji, Allah yasaka da alkairi, Allah yabiya bukatu yasa damu duka a gidan Aljanna" atare daga Dr har Dady sukace Ameen, Dady yasake kallon Aneesa daketa kallonshi tana murmushi yace "zan tafi anjima zan dawo nasake dubaki kinji, ki dinga jin maganan mahaifiyar ki kinji sanan kowani nagani aka baki kisha ki warke sabida kar mahaifiyar ki taitai shiga damuwa kinji" dago kai Ammi tayi ta kalleshi yanda yay maganan yatabata har zuciya, gyadamai kai Aneesa tayi ahankali tace "saika dawo, Allah yabada sa'a Abba" murmushi Dady yayi yanaji kaman yamaida yarinyar yarshi yace "Ameen nagode da Addu'an, muje Dr" Dr ya kalle Ammi yace "idan tagama ci ki danna alarm din gefen gadon nan zanzo" to Ammi ta amsa Dr yabi bayan Dady da sauri har wajen mota yarakashi Dady yamai kyauta mai tsoka sai godiya yake sanan ya shiga motan bodyguard yarufe yakoma gaba yatada motar suka bar asibitin, Dady sai tunani yake dan yaje shashin Aliyu bayanan ina yaje this early morning? Sai kirashi yake baya shiga.


_duk shegiyar data fitar min da littafi waje Allah ya isa, duk kuma wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa, ban kuma yafeba_
[12/03, 09:12] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_








2️⃣4️⃣


_how to subscribe_
_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461, sainai adding dinki a group din danake posting. Marasa banki zaku iya turo katin MTN ta WhatsApp number na*_


_duk wacce takaranta bata biyaba Ban yafeba_










Wuraren karfe biyar na asuba Dr dawata nurse rikeda paper suka shigo dakin, Ammi dake rikeda hannun Aneesa dahar lokacin ke bacci bata tashi ba hancin ta har lokacin da oxygen dan she's really finding it difficult to breath shike bata support, ganin Dr sun shigo yasa Ammi tasaki hanunta ta mayar ahankali ta ijiye ta mike tsaye tana kallon Dr tace "Dr har yanzu bata tashi ba, meke damunta dan Allah kufada min?" karasowa gaban gadon Dr yayi yana mikama nurse din papers din hanunshi yana cire stethoscopes daga wuyanshi yace "don't worry Ma, your daughter will be fine, tana bukatan baccin nan dakikaga tanayi" yay maganan yana sauraran heart beat dinta saida yagama dubata tsaf sanan yadau wani allura dasuka taho dashi yama drip din da aka makala mata alluran sanan ya karbi paper hanun nurse din yana rubuce rubuce, saida yagama sanan yajuyo ya kalli Ammi tareda yimata murmushi yace "karki wani damu maleria ne ke damunta mai karfin gaske dan maleria ta yakai 4+, thank God kun kawota asibiti on time dazamu iya rasata but karkiji tsoro yanzu zamu barta on admission muna bata care nan da 2days muga yanda zata kasance, karki damu yarki zata sami lafiya saidai akwai abubuwa da dama daza'a kiyaye dazaran tasamu lafiya" ajiyan zuciya Ammi ta sauke bata iya cewa komiba sai kallon fuskan Aneesan datake yi, Dr yace "muje na nuna miki masallaci kije kiyi salla saiki dawo" gyadamai kai tayi tawuce tabisu suka fita yakaita masallacin asibitin dake kusada Gate, bangaren mata tawuce tai salla.










Shida saura yatashi daga bacci da kyar shima sabida Dady daya ta dashi ne ta hanyar kiran wayan shi, sauka daga kan gado yayi ya shiga bathroom baiwani jimaba yadauro alwala yafito ya shimfida dadduma dan anriga an idar da salla.
Idar da sallan yayi ya jingina da gado yana azkar yarasa mesa every single breath dazaiyi taking sai Aneesa tafado mai arai, dan fuxar da iska yayi yamika hannu yadau wayarshi dake kan bed yadauko yay dan jim yana kallon wayan kafin ahankali ya kunna yay dialing number Aneesan.....














Wuraren shidda tana zaune a masallacin asibitin tana lazimi wayar Aneesa dake tareda ita ya shiga ringing, da sauri ta danna gefe tai muting ringing wayan tana kallon number dake kira danba suna ajiki, bata daga kiran ba harya katse, aka sake kira akaro na biyu da sauri tai muting ringing din tana kallon number still number dazu ne shima bata dagaba harya katse, sake kira akayi akaro na uku yasa Ammi ta tashi tafita daga masallacin da saurinta tana kallon number tokodai yan lalle ne? Dan sune suka iyama Aneesa kiran safen nan dansu tambaya ko tana nan bazataje aikiba zasuzo, danna wa tai tai picking takai kunne cikin muryan ta irin na wacce tadan manyanta tace "Assalamu Alaykum" shiru Aliyu daya rasa sukuni so kawai yake yaji muryanta yayi jin ba muryanta bane, muryan babba ce, ciro wayan daga kunne Ammi tayi ta kalli wayan ganin har lokacin ba'a katse wayar ba yasa tasake maidawa kunne tace "Assalamu Alaykum, hello, hello banaji, waye? mahaifiyar Aneesa ne, batada lpy yanzu haka muna asibiti a asibiti muka kwana idan yan lalli ne karkuzo gida dan bama nan"




Wani irin faduwa gaban Aliyu yayi da inda yanada history heart problem saiya iya collapsing....


Jin still shiru ba'ace komiba yasa Ammi taciro wayan daga kunnenta tace "ba'aji network nada matsala wlh" tasake maidawa kunnenta tace "bama nan karkuzo lalle muna asibiti" tacire wayan daga kunnenta ta katse wayan.








Rawa jikin Aliyu yafara da sauri yasake dialing number dan gani yayi kaman kunenshi ba daidai yajiba Boldest dinshi dayagani ji looking strong ne za'ace batada lpy, picking Ammi tayi tace "hello, hello" shiru yayi ya kasa magana dan bala'in nauyin Ammi yakeji, katse wayan yayi da sauri ya shiga Google map dan nemo inda wayar take so yake yay tracking din wayan kaman yanda yay jiya dan wayanshi nada karfin tracking any number, jiyama haka yay har yaje cafe daya ganta. _"Spectrum private hospital, Abuja"_ yanunamai, tashi yayi daga kan dadduman ya zura bedroom slippers dinshi ko tsayawa chanza pyjamas din jikinshi baiyiba yadau car key yafito yay wajen motar shi yabude da sauri ya shiga yatada, horn yayi aka budemai Gate yaja motar da shegen gudu yafita daga gidan.










Rike wayar Ammi tayi tana mamaki waye yake kira haka da batajin maiyake cewa dan tabe baki tayi tasaka takalmin ta tawuce cikin asibiti, ganin kofar dakin dasuke abude yasa takarasa da sauri ta shiga, ido da ido sukayi da Aneesa dake kwance kan gadon idanunta sunyi ja sun kankance looking pale kana ganinta kasan ciwo ya lallasata, Dr da nurse akanta suna, dubata har yanzu oxygen din nanan dan yanzu matsalan numfashin is her major problem temperature ta yasauko sosai, da sauri Ammi takarasa shigowa dakin tazo bakin gadon tana leka Aneesan tace "Aneesa, Aneesah na, kin tashi" dan lumshe ido tayi tabude cikeda rashin kuzari tana kallon Ammi tana numfashi da kyar, juyowa Dr yayi yana murmushi yace "kigode ma Allah kin haifi strong girl, your daughter is a very strong girl, ta tashi, yanzu nan zaki tambayeta metake son ci kije kidafo mata ki kawo mata, she needs good healthy food dan batada karfi ko kadan and kikawo mata wasu kaya dan kayan nan yakamata ta chanza su ki kawo brush dan amata brush" gyadamai kai Ammi tayi da sauri tana murmushi tana kallon Aneesan wani irin dadi takeji ganin ta tashi tace "to Dr, zan iya mata magana ko?" dariya Dr yayi ganin yanda Ammi ke maganan yace "sure, but kiyi sauri she needs to eat food kafin nan da karfe goman safe" gyadamai kai Ammi tayi taja kujera tazauna tarike hannun Aneesan gam dake kallonta, hannu Ammi tasa ta shafa tulin sumanta dan ancire mata hula takira sunanta ahankali. "Fateema na" atare Dr da nurse suka kalli juna sukai murmushi d bond between a mother and her daughter is just an exceptional bond, Allahu akbar! Juyawa sukayi suka fita tareda rufo musu kofa, matse hanunta Ammi tayi kaman zata hadiyeta tace "meke miki ciwo yanzu eh?" lumshe ido tayi tabude, dan murmushi Ammi tayi tace "sannu kinji my brave child, my strong girl mai karfin baban ta, Aneesan maman ta, mezaciki nadafa miki, namiki koko da kosai?" shiru tayi tana kallon Ammin hakan yasa Ammi tace "namiki alale? Waina ko masa? Burabusko? Kus kus?" duk shiru tayi tana kallon Ammi, dan Jim Ammi tayi tana tunani kafin tai murmushi tace "namiki shinkafa da kaza da Fanta mai sanyi?" ahankali ta gyadama Ammi kai tana lumshe ido, dariya sosai Ammi tayi tace "oh Aneesa na dason cin dadi, wanan bakin ya iya kwadayi, bari to naje namiki, full kaza zan saya na soya miki kinji bazan dadeba zan dawo" ajiyan zuciya tasauke tana kallon Ammi tanadan lumlumshe ido bacci nason sake kwashe ta, tashi Ammi tayi taja bargon asibitin dake kan gadon ta lulluba mata ganin tsigan jikinta na tashi alamun sanyi takeji, dagokai tayi ta kalleta ganin har takoma bacci yasa tadau jakanta ta da wayan Aneesan da nata tazuba ciki tabude kofa tafito daidai lokacin Dr yafito daga dakin dat is opposite nasu yace "zaki tafi madam?" gyadamai kai Ammi tayi, yace "don't worry your daughter is under our watch but kidawo kafin goman safe she need the food" ahankali Ammi tace "nagode likita" "saikin dawo" tawuce ta fita tana tunani yanda zatayi duka duka dubu ishirin da bakwai ne a hanunta ragowan kudin da aka biya Aneesa na lallen, yanzu ciki zata shiga kasuwa tasoyoma Aneesa kayan shayi da kuma cefanen abinda zata dafa mata, sauran kuma tasan anjiman nan tana dawowa zaa' bata takarda dazataje tasayo mata magungunan yanzu idan za'a sallame su tayaya zata biya kudin komi? Saisa ita General asibiti taso su kaita yafi sauki amma mutumin nan yakawo ta nan dole takira yan uwan baban Aneesa ta sanar dasu suna asibiti, ita kadai ke tunanin nan tana tafiya har saura kiris machine yabugeta da sauri ta koma baya kafin taga wani mota dake shouting Suleja Suleja, ta tsayar dashi da sauri ta shiga.












Da gudu ya shigo asibitin, Parking yayi a parking lot din asibitin yabude motar nashi yadirko kasa yamaida yarufe yana danna lock, yana kallon ko ina na asibitin, ahankali yafara tafiya yana dosan reception bude kofa yayi ya shiga nurses biyune awurin daya a tsaye daya a zaune gaban kanta, suna ganinshi suka zubamai ido ya bala'in musu kyau dan wani dark blue pyjamas ne ajikinshi da white bathroom slippers daya haska farin kafarshi ya karamai kyau bana wasaba, bai damu da kallonshi dasuke yiba yakaraso gabansu kafin ma yay magana atare sukace "good morning sir" dayar dake zaune kan kujera tace "how can I help you sir" dan yatsine fuska yayi sabida yanda suke wani washemai baki hannu yadaura kan goshin shi cikeda damuwa yace "anyone by name Aneesa was place on admission jiya?" babbar littafin dake gabanta ta kalla tace "one minute sir bari naduba ma dan banine a night ba yallabai" ta shiga duba jiya ganin babu sunan Aneesa kodaya yasa tadago kai tace "babu Aneesa da aka kwantar jiya, infact one admission ma mukeda shi jiya da daddare and a A&E ne ma" sake shafa goshin shi yayi trying to calm kanshi down tunda dai yaga location din asibitin nan yasan suna nan, dan ajiyan zuciya mai karfi ya sauke cikeda damuwa yace "mace ko namiji ne wanne a
A & E?" "mace ne sir" wani irin ajiyan zuciya ya sauke ya sauke hanunshi daga goshin shi yace "show me the room please inga ko itane" har rige rige suke sukace lemme take u, tsayawa yayi kallonsu saikuma yajuya da sauri kirjinshi na bugawa, ta tsayen tace "dalla keki zauna bari nakaishi nazo" ta fito tai gaba da sauri tanadan kwarkwasa tace "let's go sit" tai gaba yana biye da ita har A&E amma single room court, har gaban dakin Aneesa taje tabude kofan ta shiga ciki ta waigo ta kallai tace "shigo kagani ko itace kake nema sir, she's even sleeping" daga kafarshi dayaji yamai wani irin sanyi sosai yayi kaman wanda baisaba tafiya ba ya shiga dakin yajuya yana kallon kan gadon.








Numfashin shi tsayawa yay chak ganin Aneesa kwance kan gadon asibiti, jinin dake running through his vein freezing yayi for some seconds, ya tsaya chak yana kallonta ko motsi yakasa yi kaman an dasashi awurin, yakasa gasgasata Aneesa yake gani daya rabu da ita jiya akan gadon asibiti, an lullubeta da bargo tundaga kafa har wuya sai fuskanta kadai dakenan ba'a rufeba, hancinta sanye da oxygen da yana iya ganin yanda breath dinta ke sauka da fita ta abun, idanunta a lumshe gashin idanunta sun kwanta lubbbb, kanta babu dan kwali, goshinta kwance da tulin baki kirin gashi kanta ma abude dan babu dan kwali.
Juyowa Nurse din tayi ta kalleshi murmushi kwance kan fuskarta tace "Sir itace wacce kake neman? Dan itace wacce aka kawo jiya da daddare tana convulsing seriously da kuma nose bleed, itace kake neman?" gyadamata kai yayi yakasa dauke idanunshi daga kanta sai wani irin kallonta yake, dan murmushi nurse din tayi tace "saika fito to" tawuce tafita daga dakin tareda rufe
kofar.




Wani irin kallon Aneesan yake kaman this is the first time yafara ganinta in his life, ahankali yadaga kafanshi dayaji kaman bazai dauke shi ba yana tafiya ahankali har zuwa gaban gadon yadan kwanto da kanshi yana kallonta yama rasa mekemai dadi, he knows he really likes Aneesa dan she poses some qualities daya tafi da zuciyan shi, her heart is as pure as gold, she's bold, fearless, her smile is alluring, her facial look is pulchritudinous, kwayoyin idanunta dazzle ko acikin duhu, gata very calm, hijabin dakoda yaushe yake ganinta ciki na masifan burgeshi what a statuesque lady she is, baitaba ganin mace that's so enthralling kaman Aneesa ba, he never knew cewan she means so much to him hakaba sai yanzu daya ganta laying on a sick bed looking helpless, hanunshi narawa sosai yadaga yakai yadaura kan hanunta dake kwance gefenta, wani irin motsi tayi kaman her body feels his touch batare data bude idanunta ba, hanunta dake da tushi sosai yakama yarike ya matse gam kafin ahankali yay bending kanshi over yakai fuskarshi saitin fuskarta yana kallon fuskanta kasa daurewa yayi sabida yanda wani abu ke fizgan shi jiyake kaman ya dauketa yazare ciwon yasama kanshi ita yaganta looking healthy and doing her normal activities, ahankali ya lumshe idanuwanshi tareda saukar da lips dinshi kan tiny goshinta dake dauke da black hair dake kwance lub lub, goshin so warm sabida zazzabin dabe gama sakinta ba ya sakin mata wani irin light emotional love peck dat comes from his heart dan baimasan lokacin dayayi ba yadaiji karan peck, motsi tayi tareda bude idanunta dasuka kankance sukai ja tana budesu kip kip kaman wacce ake shirin mari tana tsoron bude idanunta duka ta budesu tana gani dishi dishi ta shiga dan motsi sabida duhun datagani asamanta dawani kamshin turaren daya ratsa hancinta, dan dago kanshi yayi ahankali sabida motsin dayaji ya kalleta hada ido sukayi yana kallonta in a very cool way cikeda tausayin ta, kujeran dake bayanshi yaja yazauna yana rikeda hannunta ya matso kusada gadon sosai yana kallon fuskarta still, cikin wani irin murya chan kasa da dagashi sai ita zasu iyajin meyake cewa yakira sunanta. Duk wacce takaran ta min littafi daidai da layi daya batare data biyaba ban yafeba zaki biyani randa baki dashi, maison littafin yamin magana ta watsa 07012181461 "Aneesah" lumshe ido Aneesa tayi da sauri tanajin yanda yarike hanunta gam kaman his whole life is in her hands amma ko kadan batada karfin fizgewa dan batada karfi kodaya she's so weak, hannunta daya rike yakara matsawa yama rasa mezai mata yaji dadi yakai hannun saitin bakinshi ahankali yay pecking hannun hakan yasa tasake bude idanunta dasuka kankance ta kallai, da ido shima yake mata wani kallo kafin murya chan kasa cikeda raunin zuciya yace "I love you Aneesah" dudda tana cikin ciwo amma saida maganan da yanda ya furta maganan yasa kirjinta yabuga da sauri ta rufe ido takai almost minti daya tasake bude idanun ahankali ta kallai, gyadamata kai yayi murya chan kasa yace "yeah, I love you Aneesah, with all my heart" yadanyi shiru yana kallonta kasa jure kallon dayake mata tayi ahankali tajuyar da kanta ta kalli dayan bangaren dakin kirjinta na dukan uku uku ga kanta dataji yasoma sara mata, Jan kujeran dayake kai yayi baya yatashi tsaye ya rankwafo kanta hannunta dayake rikedashi yakai ya daidai saitin zuciyan shi yay placing gently, kafin yasa dayan hanunshi yajuyo da fuskarta suka hada ido, murya chan kasa yace "my heart beats for you, be strong for your love Aneesa, be strong for me, be fine for me, ki warke dan na nunamiki irin son danake miki" dan shiru yayi yana kallon yanda hawaye yafara gangarowa ta gefen idanunta zasu gangara kunnenta hannunta yasaki yasa yatsunshi ya share hawayen dasuka zubomata yana girgiza mata kai.










Kaman ma yakara karfin hawayen ne suka cigaba da bulbulowa, kai yadaga ya kalli reading din abinda ke bata oxygen kafin ahankali yasa hannu ya janye roban oxygen dake jikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login