Showing 63001 words to 66000 words out of 186400 words
Chapter 22 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt
tace "Aliyu da Abdul ai saidai Allah ya shirya domin kam duk kanwar ja ce" ta gyara zama tana kokarin daukan remote dake kan dayan kujeran tace "jekici abincin ki Ihsan".
Sai wuraren shadaya sanan Aneesa tabaro wurin Baffa dasuka wuce dakin zaure dasuke kwana itakuma tadawo daki, kulle kofa tayi dan tasan Ammi ta riga ta kwanta, dakin Ammi ta wuce straight Ammi na zaune kan gado tana linke kayan data cire, kallo daya tama Aneesan ta dauke kai, murmushi Aneesa tayi takarasa kan gadon ta zauna kusada Ammin, kayan ta karba takarasa linkewa ta tashi tai wajen sip din Ammi, sip din tabude tana kokarin maida kayan ciki tace "Ammi kinason Abban? Naga su Baffa sunce jibi ne bikin" tana maganan tana jera kayan a sip, jin Ammi ba tace komiba yasa ta juyo ta kalleta, hada ido sukayi da Ammi dake kallonta, washe baki tayi takaraso ta zauna kusada Ammi tareda daura hanunta kan cinyar Ammi tace "eh Ammi, bakice komiba" dan murmushi Ammi tayi tace "kina sonshi to Aneesa, ba dole na yarda ba" washe baki tasake yi tace "nagode Ammi na, Ammi kinga ko nizan miki lallen biki, in miki kwalliya dakomi ko Ammi" tabe baki Ammi tayi tace "nine zanyi wani lalle saikace bikin yar yarinya" kaman Aneesa zatai kuka tace "wlh nisaina miki, Ammi na mai shegen kyau kinji" tabe baki Ammi tayi tace "naji to, Allah kaimu da rai da lafiya" Ameen Aneesa tace haka tacika Ammi da surutu har Ammi tagaji tace mata tamata shiru kota maketa, gabaki daya tama manta da batun wani Aliyu daya bata mata rai dazu, bamata so ta tuna ko kadan, mamanta is getting married so she's super excited.
_masu iya magana sunce rana bata karya, saidai uwar diya taji........_
Yau dubannin jama'a wayanda suka halarci sallan jumma'a a babban central mosque in Suleja, wanda ya kunshi mutane da dama daga ciki harda abokanen Dady na wajen aiki da kasuwance, Aliyu, Abdul, dakuma Baban Abdul (mijin Momma), shi kanshi Dady dayaci wata fitinannan shadda wacce taci sunanta shadda, dakuma su Baffa da fuskokin su ke dauke da annuri, limami ya daura aure tsakanin Alhaji Muhammad Ibrahim da kuma Rukayya Hamisu, inda su Baffa da mutane da dama suka shaida sai murna ake ana hayaniya, sosai Aliyu ke murmushi he's trying his best yaboye damuwan shi dan baiso Dady yagane, today is a happy day for Dady baiso yaga any sign of something a tattare dashi ya shiga damuwa, yanada matsala daya addabi zuciyan shi ainun rabonshi da Aneesa tun ranan nan, yakira layin ta taki dagawa daga bayama kashe wayan tayi gabaki daya, gajiya ma Yayi da amsa gaisuwan mutane ganin kanshi yafara masifan ciwo ya kalli Abdul dake kusada shi shima yana sanye cikin shadda fara kaman tashi yace "am going home" da sauri Abdul yace "me haka? Kasan Dady zai nemeka ko" yatsine fuska yayi yace "stay kai, am having headache, inya tambayeni kacemai naje gida" yana yin maganan yay tafiya yana kallon Dady dake washe baki kaman anmai kyautan makka yana gaisawa da mutane, yawuce ya shiga mota yaja zuwa chan Abuja dan yasan koyaje gidan momma dake nan Suleja dakwai hayaniya kuma baison hayaniya ko kadan, yana danna mota cikin gidan Maman su Rauda na fitowa daga motar ta datai parking, wani natsiyacin kallo tama motarshi ko damuwa baiyi a yabude yafito yay side dinshi batare dayama inda take second look ba ballema yasan wats she's up to, kwafa Maman su Rauda tayi tace "inhar ban koyama Aliyu hankali ba aduniyan nan basunana Kareema ba wanan alkawari ne namaka, wlh kuwa" tai kwafa tawuce dakinta.
Bude part dinshi yayi ya shiga yaji ko ina na kamshin turaren wuta lumshe ido yayi yabude dan yana mugun son kamshi kuma yasan aikin Rauda ne hakan yamaida kofar yarufe yya hanyar bedroom dinshi, kaya yarage ya shiga wanka koyaji dadin jikinshi, baiwani jimaba yafito yana yatsine fuska sanye da bathrobe yafada kan gado tareda daukan wayanshi yana kallon number Aneesa yanaso yakira but yasan koya kira bazata dauka ba, ahankali bacci yay awon gaba dashi.
_Bangaren su Ammi, Suleja_
Yau jumma'a tun kafin a daura auren wuraren karfe takwas nasafe Momma da kawayenta suka kawo akwati guda goma inda saiti bakwai na Ammi ne dake cike da hadaddun kaya da an dinka wasu wasu kuma ba'a dinka ba saiti uku kuma na Aneesa ne da aka cikamata da kaya na yamma ta harda dogunayen riga Aneesa harda kuka, few kawayen Ammi na anguwan ne suka tarbesu itakuma Ammi taki fitowa har suka tafi anata guda daga baya aka daura hadadden abinci dan tun jiya Dady ya turo da motan kawo abinci Aneesa tama Ammi hadadden lalle bana wasaba ta shirya Ammi cikin wani lace mai kyau sky blue da fari ta rungume Ammi yafi sau dari sabida yanda Ammi tai kyau sanan takawo wani farin babban mayafi ta yafama Ammi, Ammi sai amsan gaisuwa take tana murmushi ka ganta itada Aneesa zaka zaci y'a da kanwa ne, Aneesa itama wani farin lace tasaka mai ratsin pink shima dadin ne yaaaimata takai aka dinka mata tai kyau telan dudda bai aunata ba amma chip chip yamata yafito da shape dinta sosai bana wasaba sai murna take ko ita ke aure albarka.
Wajajen karfe uku anguwan ya cika da maza da mawaka ana wake Dady, Baffa ne ya shigo ya leko ya kira Aneesa dake tsakar gida tana nan tai chan tama kasa zama waje daya da gudu tai wajen Baffa a zaure, baki Baffa yarike yace "wai wai wai, masha Allahu, ashe haka yar tawa keda kyau aida kyar naganeki wanan kyau haka" wani irin cute smile tayi cike da zumudi tace "Baffa an daura? Yanzu Abba yadawo mijin Ammi na?" tafada cikeda wani irin murna gyadamata kai Baffa yayi yace "kinsan mezakimin yanzu anjima zamuyi hira, yanzu jeki kawomin maman ki nan dakin mu ta zauna kifito, sabon baban ki keson yimata magana" da sauri Aneesa tace to Baffa tajuya da sauri takoma cikin gida Baffa yakoma waje ko minti daya ba'a yiba shida Dady suka shigo zauren tareda Baffa dakin su Baffa yabude ma Dady yace "shiga ka zauna na aika Aneesa takirata, cikin gidan mata sun cika abinka da gidan sha'ani" shiga ciki Dady yayi ya zauna yana murmushi yanadan girgiza kafa yawani irin kosa yaga Ammi ta shigo.
Har gaban kofar dakin Aneesa takawo Ammi dake wani irin jin kunya sosai sanan tawuce takoma cikin gida da gudu, bin bayanta da kallo Ammi tayi tana sauke ajiyan zuciya kafin ahankali tasa hannu tabude kofar dakin ta shiga ciki ahankali da sallama, mikewa tsaye Dady yayi yana yana gyara babban riganshi dayasha lafiyayyen aiki yana kallon Ammi, kasa jure kallon daya ke mata Ammi tayi hakan yasa ta saukar da nata kan kasa, ahankali tashigo tana taku daidai anatse har gabanshi kafin ta tsugunna ahankali zata gaidashi da sauri yawani irin riketa batare daya bari ta tsugunna ba yadago ta tashi tsaye tayi tana kallon fuskarshi kaman yanda shima yake kallonta wani irin kyakyawan runguma yabata tareda sata a kirjinshi da kyau yahada da malummalum da hannuwanshi yawani irin zagayeta yana sauke ajiyan zuciya ahankali tareda lumshe ido yana shakan dadaddan kamshin turaren dake tashi daga jikinta, lamo Ammi tayi tana sauraron yanda beat din zuciyar shi ke sauka a natse it feels gud to be back, bakaramin natsuwa taji ya shegeta ba da wanan runguman dayamata ba, sunkai kusan 5 minutes a rungume da juna kafin ahankali Dady ya dagota tareda tallabe fuskarta yana kallon simple makeup din da Aneesa tamata yace "karki kara cewa zaki tsugunna ki gaidani kinji Matata" gyadamai kai Ammi tayi tareda dan lumshe ido tabude su ahankali, ahankali ya sumbaci goshinta tareda rike mata hannu yay kan kujeran dayake ya zauna sanan ya zaunar da ita gefenshi yajawo kanta ya kwantar akan kirjinshi yanadan shafa mata baya, Murya chan kasa ta yanda daga ita sai shi zasu dinga jin abinda suke cewa yace "Alhamdulillah, ina tsananin farin ciki da wanan ranan Rukayya, I feel blessed dana same ki a matsayin mata sanan ina rokon Allah daya bani ikon kula da ke da yaranmu biyu yanda yakamata" gyadamai kai Ammi tayi kanta na kirjinshi tace "Ameen" murmushi Dady yayi yakama hannu ta da Aneesa tamata lalle yana shafawa lallen ya masifar mai kyau murya chan kasa yace "Rukayya anya zan iya hakura har kiyi satin dayan danace zan baki kiyi dan kikarasa shirye shirye kuwa?" yay dan jimm sai chan yace "ana daura auren nan dana ganki yanzun nan a matsayin mallakina, matata wacce nakeda iko da ita sainaji bazan iya daurewa ba kuma banso ko kadan na takura miki wlh" daya yanda yake maganan dudda kanta na kirjinshi bata ganin fuskarshi tasan yana cikin damuwa ne and one thing datama kanta alkawari shine kaman yanda har mahaifin Aneesa yakoma ga Allah yabonta da kyawawa dabi'unta yake haka zata kasance ga Dady, she will never give room dazaisa Dady yay complain akanta ba, zatabi mijinta zatai kyautatamai, zata karenshi sanan ta kare dukiyar shi, ta kula da komi nashi domin al jannar ta na karkashin tafin kafanshi ne, ahankali tadago da kanta daga jikinshi ta kalleshi tace "kayakuri kadagamin kafa kabani yau kadai sabida nasamu na hada komi nawa, inyaso gobe saikazo ka daukemu mutare, nima nakosa na kasance tareda mijina abin sona, sanan abin alfaharina, uba ga yarana biyu Aliyu da Aneesa, an dagamin kafan nahada komi yau Abu Aliyu?" Ammi tai maganan tana shafa gemushin har zuwa kumatun shi ahankali with love and compassion, Dady jiyayi kaman kanshi zai tarwatse arayuwan shi yanason mace data iya lafazi masu dadi da taushi sanan da sanyaya ran mai gida, matan shi babu abinda suka iya arayuwan su banda habaici da yada magana, wani zubin sukamai habaici saiyaje office yafara rubutu zai ma gane bakin zaren habaicin, just at yanda Ammi tanunamai he's in total control of her, what a submissive wife sanan akarshen maganan tace mahaifin yarana biyu tasake karyawa da Abu Aliyu, tsabagen yanda maganan tamai dadi baisan sanda yajawo ta yadaura ta kan jikinshi ba, ahankali ya sumbaci bakinta ko kadan Ammi bata hanashi ba yakai kusan minti daya yanayi anatse kaman zai cinyeta sanan yasaketa yakai bakinshi saitin kunenta yace "nagode Gimbiya ta, Allah yamiki albarka Rukayya, gobe karfe hudu bayan sallan la'asar zan aiko motoci akawomin abin sona Ummu Aliyu, Abu Aneesa na tsummayan Ummu Aliyu ina sonki Rukayya sosai, don't ever change wayan nan kyawawan dabi'un kinji abin sona" gyadamai kai tayi tace "naji abin sona Abu Aneesa, I love you wujiga wujiga, zan iya tafiya ko yallabai baigama daniba tukunna" washe baki Dady yayi yana dariya irin ta manyan nan feeling bossy yace "a'a Yallabai baigama da Yallabiya ba, yadai kusa, kafafuna sunmin tsami ne sosai nafi awa biyu a tsaye wajen daurin auren nan" tashi Ammi tayi daga jikinshi tace "wai wai bari muga kafan" zama tayi a gefenshi tareda dan dukawa takamo kafan Dady dake sanye da cover shoe ta daura kan cinyarta, ahankali ta zare cover shoe din Dady sai kallonta yake kaman zai hadiyeta safan tacire ta ijiye kan hannun kujera tasa hannu ta ahankali ta shiga matsamai feet din Dady ya lumshe ido sosai yakejin dadin yanda tamai, almost 20min tadauka tana mammatsamai kafan harsaida dan gyangyadi yasoma saceshi tun yana kallonta sanan tasaka mai safa ta mayar ma da takalman shi ta ijiye kafan ahankali gudun kar ta tasheshi sanan ta matsa kisada shi tashafa sajen shi bude ido yayi tareda kama hanunta ya sumbaci hannun yana murmushi yace "nabaki izinin zaki iya tafiya kar anemeki" wani irin rausayar da kai Mami tayi tace "godiya nake mai gida" har bakin kofa yarakata yabude mata kofa tafita tana mai murmushi tai cikin gida, guda kawayenta suka shiga yi suna mata kirari Aneesa sai dadi takeji kaman zata mutu haka aka wuni sai bayan magrib baki suka fara tafiya Aneesa ta gyara gidan tass Ammi taje tai wanka da ruwan turare dana yan magungunan data hadama kanta dan Dady yabata kudi dasu tasaisai abinda take bukata na gyarani jiki.
Washe gari koda gari yawaye daidai da tsinke Aneesa bata bari Ammi ta daga ba ita ta gyara ko ina tahada ubansun abinci a big pot dan tasan anjima kadan zasuyi baki, sanan ta hura wani wutan ta daura ruwan wanka kafin tawuce ta shigo daki tai wurin Ammi, kallonta Ammi tayi tace "sako hijabi kije wajen Maman Aisha ki kiramin ita, sonake ragowan abincin nan da baban ki yakawo ayi biki dashi duk tazo ta kwasa ko" gyadamata kai Aneesa tayi tace "zataji dadi sosai kuwan Ammi dama baban su yanzu baya aiki" hijabi tasa taje takira maman su Aisha tare suka dawo ita tawuce kitchen tadaiji yanda maman su Aisha keta godema Ammi harda kukan ta, girkin takarasa taje tai wanka tadawo daki dama tariga ta ijiye kayan dazata sa tai gayu sosai yauma lacey takara sawa pitch wayaga ansami lace daban daban kyau tayi.
Wuraren bayan la'asar din kaman yanda Dady yafada motoci suka cika anguwan kaman za'azo daukan budurwa, Momma ce tazo da kawayenta guda uku suka shigo dakin kebewa tayi da Ammi dataji tana so sosai dan kallo daya kacal tama Ammi tasan zatafi sauran matan Dady hankali ta shirya Ammi tasa mata alkyabba akan hadadden lapaya dake jikinta sanan aka hadu da kawayen Ammi yan anguwa aka kai Ammi mota, Momma ta turo bodyguard ciki Aneesa na nuna musu kayansu dazasu kai mota akwatin nan su dayan abubuwan dasuka tattara duk suka tafi dashi tadauko dogon hijabin ta har kasa pitch tasa da takalmin ta mai kyau look so decent and magical tafito ta kulle gidan tajefa key cikin jaka tazo da sauri motan da akasa Ammin ta aciki Momma dataji tanason Aneesa tace "zoki zauna wajen maman ki" da sauri tazo dan dama tafiso ta zauna wajen Ammi ba dayan motan ba, motan daga Ammi sai momma sai kuma ita, kawayen momma na motan farko su kadai, sai motan karshe kuma kawayen Ammi ne aka dau hanyar City Abuja. Aneesa sai kalle kalle take oh yanzu zasu koma new gidansu ne.
Agaban wani katafaren tangamemen gida da sojoji guda uku ke waje akai horn wani soja daban daga ciki yabude musu kofa suka shiga, tundaga Gate Aneesa ke kirga manya manyan flat din dake makeken compound din, bata taba ganin hadadden gida hakaba ko gidan dataje kwanaki tai lalle albarka, babu kowa atsakar gidan saidai kofa dataga ana bubbudewa kaman an hada baki ana lellekowa, a parking space akai parking da sauri direban yafito ya zagayo yabude musu itadai Aneesa sai kallon ikon Allah take, Momma ce tafara fitowa ta kalli Aneesa dake murmushi bakinta yaki rufuwa tace "fito daughter" ahankali Aneesa tafito da kafar damanta dake cikin safa ta ijiye akan interlock din dake kasan gidan wani irin faduwa gabanta yayi tareda wani irin sanyi dataji ya shiga tundaga kasan kafan nata har zuwa brain dinta, "menene daughter?" tambayan momma yasa tadawo daidai murmushi tayi tace "kashina ne yay kara kas kas Mommy" dan dariya Momma tayi tace "gajiya ne kin aikatu saisa anjima kafin ki kwanta saikiyi wanka da ruwan zafi zakiji dadi" gyadama Momma kai tayi tafito gabaki daya wani irin iska ne taji yakada ta harsaida hijabinta ya shiga rawa ga sanyi daya ziyarci kowani gaba na jikinta, fito da Ammi Momma tayi Ammi tafito daga motan wani irin guda Momma tasaki kaman dabiyu tai gudan kawayen Ammi suka fara wake kawayen Momma na amshi suna tafi akai hanyar flat din Ammi itadai Aneesa na gefen Ammin ta, Rauda dake falo dukta kosa yafito ta kalli maman su datai kini kini da rai itada hajar suna keke ta window tace "Mama please kibarni naje na ga sabuwar matan Dady" dakuwa Mama tamata tace "inkin isa kifita kigani, mai bakin hali, mara mutunci yarinyar dabata kishin uwarta" tabe baki tayi tawuce fuuu tai dakinta cikeda fushi dajin haushin Mamansu.
_Duk wacce takaranta batare data biyaba, Allah ya isa, keda Allah, mai son book tamin magana 07012181461_
Abakin kofan flat din Ammi Momma ta tsayar da kowa ta kalli daya daga cikin kawarta dake rike dawani buta irin butan da dinan na silver dake cikeda ruwa tace "kawo butan Hauwa tai alwala sai a shiga daki" Ammi suka ba butan ahankali Ammi ta tsugunna tafara alwala ana guda ana wake saida ta gama tass sanan aka sa tai bismillah aka bude kofa ta shiga da kafar dama kasa kulle baki Aneesa tayi dataga dakin da akace na Ammin sune, dakine mai benefa a tsakiya, innalillahi komi na dakin sabo fill ga kamshin furniture's nan ko ina, kawayen Ammi ma kasa shiru sukayi sai masha Allah ake, azuciyoyin su suna ashe saisa taki aure jira take saita zaba takuma dirje, wanan gidan arxiki haka dole tai zaman kusan shekara sha tara ba aure gashinan yanzu ai yabiya ta chasko Alajin Allah kice bana sai makka su Rukayya da yarta. Sama sukayi da Ammi yayinda ake shigo da kayansu ciki har dakin Ammi suka kaita dayaji kaya gawani lumtsetsen gado royal, Momma takama hannun Aneesa suka fita daga dakin Ammi su biyu kacal wani daki dake kallon na Ammi tabude dakin yaji kaya ga fenti baby pink ta kalli Aneesa dake kallon ko ina tace "ga dakin ki nan" wani irin ware manyan idanunta Aneesa tayi ta nuna kanta tace "yanzu wanan hadadden dakin ne nawa Mummy?" gyadamata kai Momma tayi tace "eh naki ne daughter" wani irin rungume Momma Aneesa tayi tana tsalle tama manta batasaba da matan da kyau ba tsabagen murna tace "thank you, nagode nagode nagode Mummy kinji" sai kuma tasaki kuka sosai Momma taji Aneesa ta burgeta dan itama kaman Dady take tanason appreciative person komin kankanin abu ka nuna kaman a maka kyautan makka ne abun namata dadi, hannu tasa ta share hawayen datake tace "mena kuka? So kike maman ki ta shiga damuwa?" da sauri ta girgixa mata kai tace "Mummy dadi nakeji am happy, Ammi na is happy, kina sonta kuma Abba nason ta, jibe gidan da kuka bamu saisa nake gode miki, thank