Showing 72001 words to 75000 words out of 186400 words

Chapter 25 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt

20 Jan 2025

18802

shima Dady yayi duk inta cemai Abbana dadi yakeji sosai gatada yawan godiya kaman maman ta, wucewa yayi yafita yay part dinshi, tundaga falo yaga falon yay tsaf tsaf abinda matayen shi basayi Kenn saidai mai aikinshi yamai, murmushi yayi yanabin ko ina da kallo yay bedroom akan dadduma yaga Ammi sanye da hijabi tana karanta wani littafin zikiri nashi, ganin Dady yasa ta rufe ahankali ta ijiye ta mike tsaye tana kallonshi yanda ya jingina da kofa yay folding hannu a kirji yana kallonta,
[14/03, 08:14] Aishat Muhammad: Karasowa tayi har gabanshi hanunshi daya rungume takamo takai bayanta kafin ahankali ta shige jikinshi ta rungume shi murya chan kasa tace "ina kwana yallabai na" lumshe ido Dady yayi yana shafa tattausan bayanta murya chan kasa yace "best greeting ever, morning Yallabiyar Yallaban ta" dan dariya dukansu sukayi atare dan yanda Dady yay maganan was damn funny, yana rungume da ita yay wajen wardrobe dinshi yabude wani fitinannen shadda mai ruwan sky blue yaciro nashi da nata dinkaku nata doguwan riga an mata stone work daga sama zuwa kasa murya chan kasa yace "ataimaka a shirya ma yallabai cikin kayan nan" murmushi Ammi tayi batare data ce mai komiba ta cire hijabin ta shiga shiryawa kaman yanda shima Dady ya shiga shiryawa cikin kayan yana kallonta, rigan kaman an aunata juyowa Ammi tayi ganin ita yake kallo yasa ta nuna kanta tace "aunani kayi batare da nasani ba ne Alhaji na" dan dariya Dady yayi yace "dole nasan ya abinda nakeso yake tahonan kiga" yaja hannun Ammi zaunar da ita yayi agaban kujeran madubi ta zauna sanan yakoma wajen wardrobe din wani dan akwatin sarka yadauko yadawo yaboye a bayanshi yace "rufe idanun" kulle ido Ammi tayi ahankali yabude akwatin wani sakan zinare ne mai bala'in kyau yaciro ya sanya mata ahankali Ammi zata bude ido yace "a'a ba yanzu ba" da kunne da awarwaro yasaka mata yana kallonta ta madubi yanda tai kyau ahankali yace "bude idanun" ahankali Ammi tabude idanunta tana kallon kanta amadubi yanda sakan zinaren yamata kyau wani irin dan ihu Ammi tayi ta rufe bakinta tana zaro ido ganin gold sarka ajikinta kafin ta tashi da sauri tafada jikin Dady da gudu tana tsalle kaman wata yarinya tace "is so beautiful, so gorgeous, oh I love it, thank you mijina, abin alfahari na" yanda ta kanannade Dady yasa yaji yana neman zaucewa cikin dishashewan murya yace "zaki hanani kai yara makaranta ko Rukayya kike min wanan abu haka wash Allah" dariya sosai Ammi tayi ta daga shi tareda tashi dashi zaune tace "tubanake" dariya Dady yayi yadau mayafi ya yafamata da kanshi kayan data cire ya linke yasaka a wardrobe dinshi yakama hannunta yace "muje" fitowa sukayi daga dakin sunyi kyau bana wasaba har store compound din ya kaita yana nuna mata komi kafin ya dauko new lunch box na yanmata da kuma goran bottle na yan gayun yaran nan karba Ammi tayi daga hannu shi ta tayashi rikewa sanan suka fito sukai shashinta, daidai lokacin Aneesa ta sauko tana sanye da dogon rigan atampa milk da gold sai wani milk color hijabinta mai hula har kasa ganin Ammi yasa tai wajen Ammi da gudunta Dady na dariya yazauna kan kujera, kallonta Ammi tayi tace "ina zaki kika shirya haka" murmushi tayi tace "Abbana ne yace na shirya zai kaimu hadda" ahankali Ammi ta kalli Dady intace bataji dadi ba tai karya yanda Dady ke nuna ma Aneesa so yasa ta cikin yaran nashi da gaske shine yafi komi yimata dadi a lamarin, batare da Dady ya kalleta ba yana kallon TV yace "bazaki je kibama yarinya na abinci ba sai kinsata latti tawas harta wuce da minti goma" murmushi kawai Ammi tayi cikeda son Dady ta kalli Aneesa tace "muje kitchen din, mekika dafa haka yaketa kamshi?" binsu da kallo Dady yayi harsuka shiga kitchen yanajin yanda suke hira Aneesa na dariya Ammi ma nadan dariya, hada mata abincin Ammi tayi sanan ta hada tea tajuye agoran Ammi sai kallon Aneesan take the joy she's seeing a fuskar Aneesan kadai yasa taji she can withstand koma wace irin kaddara ce inhar daga gidan nan just so wanan happiness dinan bazai gushe daga fuskan Aneesa ba, goran tamika mata Aneesa ta karba duk tarike suka fito Dady ya mike tace "yauwa muje" hannu Aneesa tadagama Ammi tace "bye bye Ammi na" hannu Ammi ta daga mata tace "ayi karatu da kyau, Allah bada sa'a, Abu Aneesa adawo lafiya" wani irin kallo Dady yamata kafin yafaki idanun Aneesa ya kashe mata ido tareda wurga mata kiss, girgiza kai Ammi tayi tana murmushi aranta tace "na auri dan duniya dan boko" parking space sukayi inda Aneesa taga kusan duka yaran datagani jiya yan manya manyan suna wurin duk sanye da maroon hijab mai baje da alamu shine hijabin makarantan, babban sune wacce bata mata fuskan taba ta jiya dake ta Harare Harare a falon Dady tagani tsaye tana danna waya tana taunan cingum, "ban wayan nan Hajara" Dady yay maganan babu alamun wasa kaman zatai kuka tace "Dady fa kirana akayi ka yakuri" "will you give me that phone ba'a hanaku zuwa makaranta da waya ba" and kiyarda cingum din bakin nan naki kafin na kifa miki mari" yarda cingum din tayi tamikama Dady wayan kaman zatai kuka ta tsani islamiyya da wanan had dan mutum yagama University amma Daddy yace saita dinga zuwa haba bude musu babban motar family car Dady yayi mai kiran sienna amma tafi sienna ma girma yace "ina Rauda maisa bata fitoba" ahankali Hajar datai kini kini da rai tace "cikinta ke ciwo" baice komiba dan yasan Rauda nason zuwa makaranta shiga motan sukayi ko wanne dauke da lunch box dinshi yaran sai gaida Aneesa suke Dady yarufe motan ya shiga gaba yaja motar soja yabude Gate suka fita.




Haddan nada dan nisa da gidansu babban makaranta ne wanda yaran manyan mutanen abujan nan keyi, ga security agaban gate din dake tsare su dan yaran senators da sauran sune kafin azo ayi kidnapping a premises din wajen parking Dady yayi parking yafito yabude musu suka fiffito kowa yay hanyar ajinshi itakuma Aneesa Dady yace ta tsaya, saida duk suka tafi Dady ya kulle motar ya kalli Aneesan yanda yaga tai zuru tana kallon makarantan dan tamafi wani makarantan boko kyau yace "muje karkiji tsoro ba'a duka saidai in baka bada hadda ba, so you have to be serious kinji ko kidage inkika haddace Al qur'ani duk abinda kikeso inhar inadashi saina miki aduniyan nan" murmushi tayi cikeda jin Dady tace "to Abbana zan dage" daidai nan suka karasa principal office din ganin Dady yasa daga malamai ustazai guda biyu da principal din wanda yake tsoho gashi fari balarabe dan balarabe ne mai karantan duk suka tashi suna gaggaisawa. "Alhaji kaine da kanka" cikeda fara'a dan yasaba dasu yace "eh y'ata nakawo" "bismillah ku" zama Dady yayi yanunama Aneesa kujeran kusada shi zama itama tayi Dady yace "akaramakallahu ga y'ata nan, daga islamiyya har hadda nakeso asata" gyadakai malami yayi yana kallon Aneesa kafin ya kalli Dady yace "shikenan ba matsala, zamu gwada ta sai musan ajin daza'a sata" faduwa gabanta ya shiga yi, ya dauko form da sauran abubuwa yace "acike wanan agida gobe kokuma Ince sati mai zuwa sai abata takawo" "to, to shikenan" Al qur'ani yadauko yabude chan suratun Ma'ida shafi nabiyu yace "bismillah, karanta mini nan naji" karba Aneesa tayi ahankali hannunta har rawa yake, kafadanta Dady yakama yana murmushi yasan she's nervous which is normal ahankali yace "relax karkiji tsoro gani anan, karanta musu muji" gyadama Dady kai tayi tanajin natsuwa, ahankali tai gyaran murya tafara karantawa bata sauke ba amma t iya hada baki hakan yasa zata iya karanta ko ina a Qur'ani, shiru Dady yayi yana sauraran muryanta dake da wani irin dadi saida tagama karanta shafin sanan malamin yace "barakallahu fiki, masha Allah ina ganin zamu sata aji hudu dan tanada matsala da tajweed, mataki na biyar kokuma nace aji na biyar su sun kware a tajweed" gyadamai kai Dady yayi cikin gamsuwa yace "to to shikenan ba matsala" daya daga cikin malamin ya kalla yace "akaita aji" gyadamai kai yayi Dady yace "tashi kibishi ajinki za'a kaiki" gyadama Dady kai tayi tabi malamin suka fita shikuma Dady yabiya kudin komi both hadda da islamiyya almost 150,000 sanan yabiya kudin littatafan ta both na hadda da islamiyya dazasu bata kusan dubu talatin sanan yamusu sallama yawuce yatafi dama sabida Aneesa ne yasa yau yakawo su da kanshi direban dake kaisu makaranta yaje yadauko su daban me a gidan.




_duk wacce takaranta batare data biyaba, Allah ya isa_


A parking lot yay parking yafito part din Aliyu yayi baya falo hakan yasa yay hanyar bedroom dinshi yana kwlamai kira. "Son, Gadanga gusar yaki" hannu yasa zai bude bedroom din Aliyu yariga shi ta hanyar budewa yafito yana sanye da white singlet sai white wandon shadda ajikinshi yana kamshi sosai da alamu yagama wanka ne, dan yatsine fuska yayi yace "kadawo Dad" gyadamai kai yayi yace "dauko rigan muje to" dan turo baki yayi batare dayace komiba yakoma ciki shifa yagaji da wanan daukan shin da Dady yake duk in yayi sabon aure yace sai yaje ya gaida matar, rigan yasako yafito ko saka boturi baiyiba tsabagen rigima da yakeji, fess Dady yasan rigima yakeji saisa yaki biyemishi yace duk wacce tafitar min da littafi waje Ban yafemata ba wlh "mugani ka manta baka saka boturin rigan ba" yay maganan yana makala boturin yace "kayan sun maka kyau Gadanga, telan yay kokarin wlh, yana cikin kayan da Abdul yakaima dinkin ko" gyadama Dady kai kawai yayi yace "eh" suka fita daga dakin sukai hanyar part din Ammi bude kofa Dady yayi da sallama ya shiga Aliyu biyeda shi, ahankali yasa kafanshi ya shiga dakin wani hadadden kamshi ya daki hancin shi wani irin sanyi ne yaji ya ratsa shi ahankali ya maida kofan dakin yarufe yana kallon koina aranshi yace no bad dan ko ina a gyare zama yayi akan kujera Dady ya zauna kusada shi tareda kwalama Ammi kira. "Rukayya" daga sama Ammi ta sauko ahankali tana gyara lullubin mayafin ta tana kallon yaron datagani kusada Dady data kyautata zaton shine Aliyu kaman su daya da Dady saidai yafi Dady kyau sosai da haske, babba ne yanada dan jiki kadan yana sanye da faran shadda idanunshi kan TV yana kallon abinda akeyi a news, karasa saukowa Ammi tayi tace "barka da dawowa" yanda muryan Ammi yadaki kunnuwan Aliyu kaman yataba jin muryan yasa ya juyo da sauri hada ido sukayi da Ammi gani yayi kaman yataba ganinta awani wuri amma yamanta, cikamai ido sosai Ammi tayi murmushi ya kakalo tareda saukar da kanshi kasa ahankali yace "ina kwana Mum" cikeda so kodn yanda mahaifinshi keson yarta Ammi tace "Aliyu, Masha Allah yau gani ga d'ana Aliyu, sannu kaji Son, katashi lpy?" gyadama Ammi kai yayi yace "Alhamdulillah Mum" yay dan shiru yarasa me a kecewa murya chan kasa yace "welcome Mum, Allah sanya alheri" murmushi sosai Ammi tayi ganin yanda yaron keda natsuwa tace "tashi muje nahada maka breakfast kaji" tai hanyar dining tareda jan kujera daya baya ta kalli Aliyun dahar lokacin yakasa tashi tace "taho Aliyu" tashi Aliyu yayi ahankali cikeda kunya Dady sai washe baki yake kaman zaiyi ihu sabida murna, kujeran da Ammi ta nunamai yazo yazauna sanan tace "yauwa, akwai shayi, chips da liver source, sanan akwai pancake, me zanyi serving naka ko nadafa maka wani abu?" zaiyi magana Dady yakara so yaja kujeran dake kusada Ammi yace "tunda anga yara an manta da uba ai saimuzo ko ba'a gayyace muba" dan murmushi Ammi tayi ta shafa gemun fuskar Dady tace "tuba nake Yallabai na, bari naji da danmu saina dawo kanka kaji ranka shi dade" shi kanshi Aliyu baisan lokacin dayadan saki murmushi ba sabida yanda Ammi tai maganan so lovely, ahankali yace she's nice. Kallonta Dady yayi cikeda so yace "shikenan nahakura afara bama danmu to, yanason pancake sosai" gyadamai kai Ammi tayi tace "tom shikenan" plate ta jawo ta dibanmai pancake dat were looking so inviting tadau honey tace "kanaso da Honey ne Aliyu!?" gyadama Ammi kai yayi hakan yasa ta zubamai honey akai, sanan tadau cup tazubamai ruwan shayin dake kamshin kayan kamshi tasa spoon ta ijiye mai agaban shi ta matsar da madara da milo girgiza mata kai yayi yace "just sugar Mum" "OK okay, bakasha da madara" gyadamata kai yayi murmushi tayi tadau sugar tamika mai tace "very soon I will know my son likes and dislike ko" murmushi yasake yi hakanan yaji yanason matan she's so nice to him dudda baisan kodan taga Dady awurin bane but he felt gud yadade yana craving for this kind of affection and care amma bai samuba, karban sugar yayi ahankali yace "thank you Mum" murmushi daga Dady har Ammi sukayi atare, Ammi taja kujeran kusada Dady ta zauna tana kallon abincin tace "oya kafara ci to ko kunya na kakeji" girgiza ma Ammi kai yayi, Ammi ta kalli Dady dake binta da kallo kaman zai cinyeta yanaji kaman yabata duka duniya sabida abin nan datama Aliyu tace "Me zan baka yallabai na?" ahankali Dady yace "kome Yallabiyata tabani zanci" murmushi Ammi tayi tace "angama" chips tazuba musu a plate daya ta hada musu tea. Ahankali Aliyu yadau pancake din baida wani interest kan abincin sosai yakai bakinshi ahankali ya gutsura wani irin dadi yaji da baitaba ji ba the pancake is the fluffiest pancake daya tabaci in his life, Oh my God, like Oh-my God, shafa kunenshi yayi ya cigaba daci yadade rabon shi da pancake shidai arayuwan shi yansosn pancake dudda Dady na yawan cewa wai da pancake Mumy shi ta yayeshi saisa tundaga lokacin yakeso dan da aka yayeshi har cikin dare yana farkawa yayta kuka yana cewa pankyyyy, Mummy Pankyy saisa wani zubin idan Dady zai rsokane shi sai yace mai pankyyyy boy kawai shi kadai yake tunanin shi yanacin pancake din saida yaji yayi dam sanan yature, Dad da Ammi da tuntuni suke kallonshi yace "akaro ne Son" girgiza kai yayi yana shafa cikinshi yace "am okay" murmushi Ammi tayi tace "ashe haka kake son pancake, zan dinga sa Fatyma namaka in sha Allah" tashi yayi tareda daukan bottle water yakoma falo kwanciya zaiyi Ammi tace "banda kwanciya Son, ka zauna in abincin ya kwanta saika kwanta ko" gyadama Ammi kai yayi ya zauna yana chanza channel, ahankali Dady yakama hannun Ammi yarike gam kallonshi Ammi tayi lumshe ido yayi kafin yabude murya chan kasa yace "thank you for being a mother to my son, nagode Rukayya Allah yamiki albarka" girgixa mai kai Ammi tayi tace "karka kara godemin I can do anything for you Alhajina, yaro mara magana haka ba um ba umum" murmushi Dady yasake yi yay kissing hannunta yajuya ya kalli Aliyu yanda ya zauna hankali kwance yana kallon kwallo a binshi yace "bai taba shiga dakin matana yasake hakaba dan dolema nake sashi ya shiga, ko shashina he hardly come sabida su, jibi yanda yasake anan sabida yanda kikamai, Allah yamiki albarka nagode" murmushi sosai Ammi tayi ta tashi tana tattare flat din dasukaci abinci dashi Dady ya shiga tayata suka kwasa sukai kitchen atare suka wanke sanan suka fito suka dawo falo suna hira inka gansu zaka dauka Ammi ita tahaifi Aliyu kawai fatane dan Ammi bakace shine zaisa kagane ba itace maman Shiba, shima Aliyun yasake da Ammi sosai ahaka Momma da Abdul da Ihsan sukazo aka cika part din Ammi, Ammi ta shiga kitchen tana girki Momma taitai Ta tsaya Ammi Ammi ta hana Ihsan Momma ta tura itama da kyar Ammi ta yarda ta tayata, wuraren 1 Dady dasu Aliyun suka tafi masallaci Ammi kuma da Ihsan dahar tasaba da Ammi suka shiga jera abincin a dining Ihsan tace "Mum yaushe Aneesa zatadawo? Momma tace ta hadamu kawance" dan dariya Ammi tayi ta kalli agogo ganin daya yasa tace "baban ku yace karfe biyu suke dawowa daga haddan so nan da awa daya" murmushi Ihsan tayi zata kara magana Momma tace "ke dalla kin dami mutane da surutu" da sauri Ammi tace "kyalesu yaran yanzu ai haka suke, Aneesa tafi aku surutu" duk dariya suka shiga yi Ammi tace "ai bari inashan fama, Aneesa da surutu hmmm ba'a magana saidai in bata saba dakaiba" bude kofan da akayi yasa suka dago kai Dady ne da Abdul sai Aliyu, Dady ya zauna kusada Momma ya kalli Ammi yace "
[24/03, 10:22] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






3️⃣5️⃣






Dady yace "Ummu Aliyu akwai enough food yar abokina na hanya, wacce zata zo muga yazata kasance ai nafada miki ko" fashewa da dariya Abdul yayi ganin yanda Aliyu yay kini kini da fuska, kallon fuskar Aliyun Ammi tayi tadanyi murmushi tace "shikenan Alhaji, kutaso kuzo kuci" tashi dukansu sukayi sukai dining banda Aliyu da ranshi yake abace, Momma tace "Beta are you not eating?" daure fuska yayi yace "am not" Momma zata kara magana ahankali Ammi tace "kuna damun min d'a fa" dan dariya daga Momma har Dady sukayi Momma tace "Aliyu kayan haushi, munkusa ganinku arana indai wanan rubabben yaron ne" girgiza kai Ammi tayi tadau tray ta daura plate of fried rice da chicken akai sai coconut juice a jug da glass cup tafito daga dining duk Dady dayay kaman yanacin abinci yana kallonta, dan karamin stool taja takawo gaban Aliyun da kunya yakamashi ganin itada kanta tazo, stool din taja ta daura tray akai sanan ta zauna gefenshi abincin ta dauka ta mikamai tace "don't mind them ga abincin ka kaci bazasu ganmu arana bako" ahankali as usual yanda yakema Dady, a shagwabe yace "banda apatite nacin abincin Mum" dan shiru Ammi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login