Showing 132001 words to 135000 words out of 186400 words

Chapter 45 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt

20 Jan 2025

18820

Dr Hafiz tagani tsaye ya zuba hannayenshi a aljihun wandonshi yana wani irin kallonta idanunshi sunyi jajir jijiyan kanshi sun fito sosai yana kallonta, wani irin dan tsoro taji dan tunda take ganinshi batama taba ganin fushin shiba, talk more of ganinshi yana kallonta haka kaman zai rufeta da duka to meya faru? Metamai?" ahankali tabude baki zatai magana yanuna mata hannunshi azuciye alamun tamai shiru, sanan yanuna kanshi yace "kin tsaya kina zubar da hawayen ki kan wani banza da baima damu dako kina raye ko bake rayeba, mutumin da mahaifinshi yasa a kulleki agidan yari mafi muni d worse of all prison yards na Abuja, kina hawaye akan wanda yaraba mahaifiyarki yarta guda daya tilo aduniya takasance cikin bakinciki, gamai sonki, someone that has always being by your side tun ranan da aka sakoki trying to keep you happy, trying to keep you company, mutumin da abandoned his work na ceto rayukan mutane and come here just to keep you company and make you happy you think am doing all of that for fun Aneesah?" yafaka mata tsawa, saikuma yay dan murmushi irin wanda za'a kira da murmushin nan mai ciwo yace "okay you asked for it and here we go" yay dan shiru kafin yace "ina sonki Aneesan! Ina sonki so banawasa ba, I love everything about you, your strength da aggressiveness sune abu na farko daya fara pulling heart dina zuwa gareki, I fell deeply for you, I love you so much but you broke my heart yau danazo naji kina kuka kan saurayin da kika wulakanta aduniya sabida shi, kikaso kizama wata irin hallita da inda yan uwanki weren't patient enough ba'a taru an taimaka miki ba da yanzu kin zama wata abun daban, shine kikema kuka haka, u hurt me girl thank you" yajuya cikeda zuciya yafita daga dakin yawuce waje ya shiga motarshi zuciyan shi na tafarfasa.








In kika karanta baki biyaba Allah ya isa.
Tafi minti goma sha uku a tsaye tana tunanin kalaman da Hafiz yafadi mata, ita Hafiz keso? Dama abinda yasa kullum yake zuwa gidansu kenan? Tadade tana tunane tunane kafin tafice kitchen, ahankali ta shiga kitchen din ta tsugunna kusa da Inna dake gindin murhu tana tukin tuwo tace "kawo in tuka tuwon Inna" dan waigowa Inna tayi ta kalleta ganin yanda muryanta yay sanyi tace "nariga nagama kya kwashe, naga Likita yafita cikeda bacin rai meya hadaku? Kindai san samari na wuyako kwanan nan, kin sami yaro mai hankali ga aikin hannu mai abinyi, gashi yanason yan uwanki ya daukemu kaman iyayenshi kinamai wulakanci karki baridai ya subuce miki kinajina ko" tunda Inna ke maganan take kallonta towai waya fadamusu soyayya suke daman, dan juyowa Inna tayi ta kalleta jin tai shiru tana ciro muciyan daga tukunya tace "kinmin shiru bakiji minace bane?" girgixa kai Aneesah tayi ahankali tace "ba soyayya mukeba Inna, kawai yayana ne" dawata irin dariya inna ta kwashe tace "hohoho su Aneesah an girma nikikema karya, mutumin daya shigo dakin Baffan ki yace yanason Baffa yamai izinin yafara neman nakine saisama kike ganinshi yana shigowa gidan nan kai tsaye danmu mukamai izini mun yarda da tarbiyanshi shine kikemini karyan kunya sannu kinji zulliya" Inna tafashe da dariya tamike tsaye tasa hannu ta dungure kan Aneesan datai shiru tace "tashi nidai ki kwashe min tuwon bari naje na kwaso daddawan da Mubarak yadakamini a turmi nazo na hada miya" fita Inna tayi tabar Aneesah cikeda mamaki da yakasa boyuwa daga fuskanshi.


Kika fitarmin da littafi ban yafemiki ba.
Washe gari misalin karfe shabiyu Baffa da Kawu Nasani da tuntuni suna gida basu fita ko inaba sukai baki wasu manyan mutane ne maza sunci kayan alfarma, falon Baffa aka shiga dasu sanan taji anata zancen dudda batajin me suke cewa but tanajin hayaniyan su sama sama, saida ana kiran sallan azahar ne suka fiffito tareda su Baffa aka tafi, itadai tana daki jinta take wani iri kawai takasa mance maganganun Hafiz.






Kika karanta min littafi batare dakin biyaba ban yafemiki ba, littafin nan nakudi ne pay 300 access fee.
Sallame sallan isha'i da akayi yasa Baffa yamike da sauri yafito wajen masallaci tun araka'an shi na farko ake kiranshi yarasa wake kiranshi haka, ciro wayan yayi daga aljihu ganin Alhaji Ibrahim Muhammad ne yasa wani irin mamaki ya kamashi harsaida yace "Alhaji!" wayar ya tsaya yake kallo ganin kiran na neman katsewa yasa yace bari yadauka yaji kuma dawacce yazo kara wayan yayi a kunne. "Assalamu Alaykum" Dady yamai sallama anatse, Baffa baikawo komiba ya amsa kaman wani abu baitaba hadasu ba. "waallaikumu sallam Alhaji yau agarin, ya aiki? Ya yara yakuma Iyali da fatan kowa lafiya?" shiru Dady yayi yana wani irin jin nauyin Baffa sabida rashin mutuncin daya musu tayaya ma zai fara ga yamai abinda yake tafe dashi? Baitaba abinda yakejin danasani dakuma kunyan kanshi ba kaman wanan kuskuren dayayi akan Aneesa, he is so ashamed of himself, jin shiru Baffa yace "naji shiru Ince dai lafiya ko?" ajiyan zuciya ya sauke dahar Baffa saida yaji sanan yace "Alhaji nasan hausawa nacewa rama mugunta ga mugu ibada ne, amma nasan muminai masu zukata mai kyau bakwa amfani da wanan karin maganan al'adan mu na hausawa, Alhaji ni mai laifi ne ninasan da hakan, amma ban isa na chanza abinda Allah ya tsara cewa zai faru ba, Alhaji ayau nazoma da gingima gingiman zancen guda Biyu dan Rukayya taki kallona kokuma saurarena, Alhaji kiyafemin laifin dana aikata akan Aneesa, na tafka shirme da shirin mata yasa nai hakan, ka yafemin, ka yafemin dan girman Allah, wlh nai nadama, nai nadama matuka ban kyauta ma amanan Aneesah daka damkamini a hannu ba na kuma karbeta a matsayin mahaifi ba, Alhaji kiyahakuri dan girman ubangiji" da sauri Baffa yace "haba Alhaji kadena rokona bakamin komiba tuntuni na yafema, Allah kuma ya yafemana gabaki daya, amma komi yawuce babu wanda ya isa ya ketare jarabawan Allah, so komi yawuce wlh" ajiyan zuciya Dady ya sauke yace "sai magana ta tabiyu, Alhaji Aliyu baida lafiya sosai wlh yau kwanan shi hudu a asibiti kenan yana fama da mugun ciwon kirji, Alhaji Dr yace zuciyanshi yadan kumbura wlh" Dady yakarasa maganan kaman zai saki kuka dayasa Baffa yaji yamugun tausayamai yace "ubangiji Allah yabashi lpy, karkadamu kaitamai addu'a, ammadai wanan batu baimin dadi ba, ciwon yaro babu dadi ko kadan" cikin wani irin yanayi Dady yace "Alhaji alfarma nazo nema wajenka, Aliyu na matukar kaunar Aneesah batun yauba, nasan nai kuskure shima bada sanin shi nai hakanba da bazai barni ba lokacin baya cikin hayyacinshi, Alhaji ku taimaka mini badanni ba bakuma dan halina ba sai dan Allah kubama d'ana auran yarku, karna rasa Aliyu dan girman Allah, Alhaji nina muku laifi please karkuyi punishing d'ana for the mistake of his Dady dan kaunar ubangiji ku dubeni da fuskan tausayi badanni ba dan girman Allah" yanda muryan Dady yasauya kaman wanda ke shirin kuka yasa Baffa yagane lallai lallai kam Dady na cikin masifaffen tashi hankali amma kuma a yanzu ahaka babu abinda zai iya mishi. Dan ajiyan zuciya yasauke yace "Alhaji mu manya ne, ba'asan manya da magana biyu ba ko kwana kwana kokuma yin karya ba, karkuma kazaci abinda zan fadamaka kodan ban hakura bane kokuma wani abun uhm uhm wlh ko daya, ciwo yawuce komi, Alhaji bazanma karyaba a yanzu haka kudin auren Aneesa ma akanwo shi, yau dinan akai komi nasaka mata rana wata daya da sati daya sabida mijin likita ne zaije PhD a Cuba 🇨🇺 anaso dazaran anyi aure saisu tafi Cuban tare, kayakuri amma a gaskiya babu abinda zan iyamaka da kaman kazo dawuri ne, ina maka fatan alkhairi sanan Allah yatashi kafadan Aliyu yasa kaffara ne, Allah kuma yabashi lafiya yabashi wata matar tagari, nabarka lafiya agaida mai jiki saida safe" Baffa ya katse kiran.
[19/04, 08:00] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






6️⃣5️⃣










Janye wayan Dady yayi daga kunenshi ya kalli Abdul dake tsaye gefenshi da baturen Dr Aliyun dayake tsaye shima duk suna jiran suji me Dady zaice amma yakasa magana sai Aliyun dake kwance kan gado an makalamai wasu irin abubuwa akan kirjinshi na asibiti yana numfashi sama da Kasa yake kallo, lumshe ido Daddy yayi alhakin Aneesah ke kamashi saisa abubuwan nan ke faruwa dashi, Rauda tarasu, Aliyu gashinan shima rai a hannun Allah, matayenshi dukya rabu dasu dan sune silan matsalolin shi, Rukayya tama tsani ganinshi, ga yaran shi duka agida Nannies daya dauko musu ke kula dasu, shi kanshi daurewa kawai yakeyi amma ko kadan baida kwanciyan hankali, dafa kadarshi da akayi yasa yadago kai Dr Aliyu ne, murmushi yamai yace "calm down Sir, I promise I will do everything in my power naga danka ya warke I promise you, just be strong for your Son" gyadamai kai Dady yayi yama kasa magana Dr yajuya yatafi, ahankali Abdul ya matso kusada Dady yace "Dady rana aka samata wai?" gyadamai kai Dady yayi ahankali Abdul zai saka wani maganan Dady yamike tsaye kaman wanda baida lpy yace "Abdul kazauna dashi ina zuwa" yafita Abdul ya bishi da kallon tausayi, a mota yasami bodyguard dinshi suka jashi sai gida, wuraren karfe goma da rabi suka shigo gidan, parking sukayi baima jira sun budemai ba yafito, flat din Ammi yawuce kofar yasa hannu zai bude yajita a kulle da sauri yay flat dinshi ba'a jimaba yadawo dauke da makulli yabude kofar, ahankali ya shiga babu kowa sai wanan mayen kamshin dakin nan nata dake tashi yay upstairs, ahankali ya tura kofar bedroom din Ammi da sauri Ammi dake kan dadduma tana addu'o'i ta dago kai ganin Dady ne idanunshi sunyi jajir yasa tadauke kai, ahankali ya shigo dakin tareda maida kofar yarufe yakaraso wajen dadduman yana kallonta, shafe addu'a Ammi tayi tamike tsaye tareda zare hijabin jikinta ko damuwa da yanda Dady ke kallonta batayiba gaban gadonta taje ta zauna tana kokarin cire dan kunnin kunnenta danso take tai bacci, ahankali Dady yazo wajen, zama yayi akasa tareda daura kanshi kan cinyarta yasaki wani irin kuka, to yama rasa mezaiyi abun duniya sunmai yawa, cikin kuka sosai yace "haba Rukayya, baki yafiya bazaki yafemini ba, nina miki laifi, ninama Aneesah laifi, please ki raba wanan zancen sa ranan Aneesah, don't punish my son over the mistake of his Dady, am sorry, bansan tayaya zan baki hakuri, kiyakuri badanniba badan halina ba kiyakuri dan Allah, ki tausayama Aliyu Rukayya, wlh natuba, nai nadaman abinda nayi" dago kanshi yayi da sauri suka hada ido da Ammi dake kallonshi kyam, ahankali yakama hannunta yana goge hawayen dake zubomai yace "naji ki rama dukan danama Aneesan, ki rama dan Allah kinji" ko alamun daga hannu batayiba hakan yasa yasaki wani irin kuka yana kallon yanda Ammi ke kallonshi yace "Rukayya wlh ina sonki kema kinsan hakan, kiyakuri for the sake of wanan cikin namu dakike dauke dashi kiyafe mini kibama Aliyu Aneesah" wani irin murmushi Ammi tayi tace "Alhaji kenan katuna sanda nake kuka haka ina rokonka ka sauraren? Ina ciwo ina fama da laulayi ina rokonka ka sauraren kamaji tausayina? Karabani da y'ata na kimanin sati hudu da kwana tara bansa abin sona araina ba kaji tausayina? Saidai kullum ka kama uwarta kana haiketa ba dare ba rana ba safiya ka maidani abinci amma y'ata nachan ka kulle ta agidan yari kaji tausayina?" lumshe ido Dady yayi wasu irin hawaye na zubomai masu bala'in dumi, tabe baki Ammi tayi tace "wlh d'a baifi d'a ba kaji yanda akeji, ciwo kuma Allah ne yadaura ma Aliyu shine kuma zai yayemai inyaga dama amma ko Aliyu na kakarin mutuwa ne bazan taba bashi y'ata ba kaje kajika dan gwal dinka kasha duniya daman fadi gareta dan hakin daka raina shike tsolemaka ido, danka baimin komiba yatace dai bazan bayarka kai amfani da kudaden ka da power ka kaje akero maka wata Aneesa ka kaima dan gwal dinka, sanan katashi please ka fitarmin daga daki cikin nan baison sautin kukan babba please saida safe" sosai yake kallon Ammi jikinshi yay sanyi yasan anacewa idan mutum mai hakuri yay fushi yanada wuyan sha'ani baitaba sanin abin yakai hakaba sai akan Ammi, tadau zafi bana wasaba, ko kallon rahama batamai kuma yasan shiyaja dan shima baimata kallon rahama ba. Yanaji yana gani tai kwanciyan ta tareda Jan bargo haka yadinga kallonta har bacci yay awon gaba dashi awurin.








_Kaduna_
Wuraren 9 bayan Baffa shida Na Sani suka fito daga masallaci ne sukai gida, afalon Baffa suka zauna sanan ya kalli Inna data shigo kawo musu abinci yake kiramini yarki Maman Hamma, murmushi Inna tayi tace to. Fita tayi ko minti uku ba'ayiba tadawo tareda Aneesah dake sanye da dogon hijabinta, tabarma Baffa ya nuna mata yace "zauna anan" zama Aneesah tayi ahankali tace "sannunku da zuwa Baffa" "yauwa Aneesa sannu" yay maganan yana karban ruwan da Inna ke bashi akofi sanan yace "kema zauna ayi maganar dake" zama inna tayi shikuma Baffa ya kafa ruwan abaki yasha iya shanshi sanan ya ijiye yace "masha Allah" kwalaye kwalayen dasuke jere afalon Baffan ne kusan guda ashirin da uku yay pointing yace "kinga wayan nan kwalayen Aneesah" gyadamai kai Aneesah tayi yace "kayan auranki ne, su goro ne, sweet dadai sauran su na saka ranan aurenki" wani irin faduwa gabanta yayi dahar saida Baffa ya gani yay murmushi yace "karki damu Aneesah, bazan miki karyaba wlh kinyi mugun sa'an miji, dan munje munyi usulin bincike abinki da haifaffen dan kaduna babu abinda bamu juyoba, Dr Zaid yaron kirkine shekarun shi talatin da shida aduniya, 36. Yataba aure sunyi zaman lafiya shida matarshi awurin haihuwa bayan ta haifomai yarshi mace Allah yamata rasuwa, sunan yarinyar Fareeda yanzu shekaran ta biyar, tun bayan matarshi ta rasu bai sakeyin wani aureba mahaifiyar shi ita ke tayashi rike yarinya, dudda an dameshi an dameshi yayi aure yaki dan acewanshi baiisamu wacce ta kwantamai araiba sai akanki, tun tuni yazo yanemi izini awurina akan yanaso ya nemiki idan babu kowa akasa na nunamai babu kufara fahimtar juna kafin jiya da daddare mahaifinshi ya kirani yace in sha Allah zasuzo yau mugana, shine gashinan babu maganan da mahaifiyar ki batasani ba, dudda tabarmana komi mune mahaifanki dama mukeda iko mu zabamiki miji sanan mu aurar dake bamu tauye mata hakki na matsayinta da uwa ba, dan har da baban yaron nahadata sun gaisa itama tai na'am dasu tace kome nayi gaskiyane, Ke mace ce Aneesah, rufin asirin kowace y'a mace shine gidan mijinta, baki komi agida, baki lalle, baki kitso, baki zuwa shago sanan baki boko, jamb dinki kuma sai shekara ta zagayo saisa naga tunda ga yaronan mai hankali, mai abin yi, kuma mai kaunar ki mizan jira gwara mu aurar dake dani da Nasani, da Innan ku, da mahaifiyar ki muka yanke wanan sharawaran nasan kuma aduk inda marigayi mahaifinki yake nasan yana farinciki da wanan lamarin na zani aurar dake, na rike amanar shi da kyau, yanzu ansa rana wata daya da sati biyu, muna fatan Allah ya kaimu lapiya sanan Allah ya sanya albarka a wanan auren" su Inna suka amsa da Ameen, Na Sani dake gefenshi ya kalla yace "kawo wanan kudin?" wasu yan dubu daidai Nasani yazaro daga aljihu sababbi yamikama Inna karba tayi yace "gawayan nan kudin, dubu dari uku ne, dubu dari iyayen yaro suka kawo kudin gaisuwan iyaye, sanan dubu dari mahaifiyar Aneesa tamin transfer dinsu dazu da yamma, Inaso kihada kudin nan ku mata kune kukasan kan kafintocin ku, kidau dubu dari da hamsin kisami kafinta daya iya gado da kujeru masu kyau kidau Aneesah kuje tare gobe in Allah yakaimu tazabi kalan kujerun datake so saiki bada deposit tunda kaman gobe ne zakiga wata daya tayi babu lokacin, daya dubu dari da hamsin din kuje kasuwa kusayo kayan kitchen da sauran kayayyaki da amarya ke bukata kindaisan yanda zakiyi dasu duk kiyi, in sha Allah kuma nida Na Sani zamu saida shanayen ta inhar an siya saimu karasa biyan kudin capita sai ayi wasu abubuwan da sauran kudin kinji" da sauri Inna tace "shikenan Baban Hamma Allah ya taimaka" kallon Aneesah da kanta ke kasa har lokacin Baffa yayi yay murmushi yace "dawani abunne Aneesah inkinada magana kiyi kinji banso na tauye miki hakki, kinada magana?" ahankali ta girgiza kai tace "a'a Baffa nagode" cikeda jin dadi Baffa yace "yauwa yar albarka, Allah yamiki albarka kinji, tashi kije ki kwanta gobe kinada zirga zirga keda Innan ku" tashi tayi ahankali tafita zuwa dakinsu fadawa kan gado tayi kuka kawai taji tafara yanzu so ake a aurar da ita, harda Ammi acikin maganan, shida tuntuni bai fadamata yana sonta bane sai yaune zai wani kame ya aureta wlh saiya sani Allah yakawo shi gobe. Sosai take kuka tama rasa meke bakanta mata rai, sosai Aliyu ke fado mata arai amma saita danne tunanin shi sabida maganganun da Ammi tamata, banda hakan ma haushin kowa na gidansu Aliyun take, shikuma Hafiz zai sani.
Inkika karanta baki biyaba banyafe mikiba.






Wasa wasa lokaci ke tafiya yau kimanin sati uku kenan batama saka Hafiz din a ido ba tun ranan dasukayi fada, ashe tafiya yayi yaje Sudan wani medical workshop na four weeks, kullum cikin gyaranta ake Inna tabata wanan tabata wanchan, yau amata farfesun ganda, gobe na cicibi, gata na azzakarin doki, haka dai take ci da kyar danba yanda zatayi idanunta sunyi zuru zuru duktabi tarame tarasa ita kanta meke damunta.






Satin Aliyu uku da kwana biyar a asibiti sanan yadanji dama dama dan yaga gane mutane yawani irin yin haske bau aka sallamoshi, bata wani magana sosai Dady da Abdul saisuyita mai maganan duniyan nan da kyar zai basu amsan guda daya, sai karfin hali baida karfi ko kadan amma kome zasumai sai yace su barshi shizai iya dakansu dan fushi yake dasu sosai ahaka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login