Showing 21001 words to 24000 words out of 186400 words
Chapter 8 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt
yanda yake mata isgilanci, yatsunta biyu tanuna idanunta dashi tace "watch out for me Aliyu just watch out" tai gaba cikeda bala'i tadade rabonta datai fushi haka, yanda sukaci burin bikin nan dan so sukayi bayan bikinsu ta kalallame Alhaji tasamu yabama Khamis daya daga cikin kamfanoninshi amma yanzu Aliyu ya watsar musu da plan, fitowar yayar tata da Khamis da idanunshi sukai jajir fuskarnan yasha bullen mage yasa ta tsaya turus tana kallonsu tace "Yaya kiyakuri dan Allah" hannu yayar nata ta daga mata tana kallon yanda Aliyu ke buga kwallo abinshi a tsakar gidan ko kallonsu bayayi cikin fushi da kunar rai Khamis dake kallon Aliyun shima yace "wlh, wlh Mummy saina kas...." da sauri Yayar Mama tasa hanunta ta taushe bakin Khamis din tace "wuce mutafi" janshi sukayi dukansu maman su Rauda tabude musu mota suka shiga tana daga musu hannu tace "Yaya kiyakuri zan shawo kan Alhaji yanzu ranshi abace ne, itakuma aidai nasan ba'a shashin baban nata zata kwana badai ko, to zata fito zata samenine wlh na lahira saiya fita jin dadi" dan murmushi yayan tayi tace "karki damu Kareema zamuyi waya, muje driver" tama driver daya tukosu magana yaja motar, bin motarsu Mama taida kallo harya bace daga gidan, fitowa sauran matan Alhaji sukayi tsaki Amaryan Alhaji tayi datazo zata wuce tana habaici tace "ci akace yarana kedashi kaman gara, Alhamdulillah bandai haifi munafuka ba cikinsu mai siding da enemy, mtsssss" taja tsaki tawuce flat dinta tana turoma Mama dankwalin kanta gaba, bata gama dawowa daga iskancin da amaryan Dady tamata ba dayar matan Dady itama tazo zata wuce saida tazo daidai gabanta tace "Allah Bani kudi insai gida inje aikin hajji, ayiriririiii" taja guda, kafin ta kalleta tadan tabe baki tace "saifa hakuri fa, matsalan haifan munafuka kenan wlh natausaya miki Kareema, oh ni yatsu Allah dai yasa kar hawan jini yakamaki fasa auren nan dakika gama yadama duniya ai jarfa ne" wani irin harara Mama ta watsa mata danji take kaman ta zubamata duka tace "kyaga hawan jini baniba kinji Maimuna" baki matar tabude saikuma tasa hannu tarufe bakin tana kallonta kafin ahankali ta zare hanun daga bakinta tana wani irin munafikin murmushi tace "wai da zafi haka hajiya uwargida? Maida wukar, amma wlh kinban tausayi, sai kinayi kina tofama Rauda ayatul kursiyu inba hakaba ta shirya tozartaki ta kwance miki zani a kasuwa musha kallo" "Maimuna! Ya isheki, Ya isheki, wlh kikace zaki shigo harkana wuya zaki sha, ni dakalin majina ce wlh duk wanda yahauni saiya fado na rantse miki, kawai kifita daga harkata fakat" wani bazan kallo Maimuna tamata tace "baridai nabarki karki mutu a hannuna nasan kina cikin tsananin bakin ciki, mtssss" itama taja mata tsaki tawuce flat dinta kwafa Mama tayi tahaura dan stairs din gaban flat dinta shiga dakinsu, wani irin fadawa tayi kan kujera tana bubbuga gaban goshinta, fitowa Hajar tayi daga kitchen dinsu dauke da bowl din Indomie data gama dafawa da 2 boiled eggs, ajiye bowl din Indomie tayi kan kujera tazo inda maman su takeda sauri ganin yanda take bubbuga goshinta tace "Mama menene? Maiya sameki menene Mama?" cikin wani irin low voice na wacce ke cikin tsananin damuwa tace "give me water Hajar?" da sauri tajuya fridge taje tadauko mata bottle water tabude ta tsayaya a cup tamika mata, karba tayi ta shanye duka ta mika mata cup din tace "karamin" kara mata ruwan tayi tasake shanyewa ta ijiye cup din ta buga uban tagumi, tsugunnawa Hajar tai kaman zatai kuka ta dafata tana kallon fuskarta tace "Mama menene? Meya faru? Maiya sameki, keda Dady ne kosu Anty Amarya?" girgiza matakai Mama tayi ahankali kafin ta fuzar da iska tasa hannu ta sharce dan guntun hawaye dayake neman zubo mata daga ido tayi, da sauri Hajar ta rungume ta tace "Mama menene kike kuka? Meya faru bakida lafiya ne?" girgiza matakai Mama tayi ahankali tace "a'a lafiya ta kalau Hajara, Rauda ce Hajar" "Rauda Mama? Mekuma tayi ni banmaga shigowanta ba nadaiga fitan ta dazu lokacin ina kitchen ina dafama su Ihsan Indomie kafin sutafi islamiyya, meta miki Mama?" cijan lebe Mama tayi tana wani irin karkada kafa cikeda takaicin abinda Rauda tayi tace "koma me Khamis yama Rauda dasuka fita dazu basai takirani ni mahaifiyarta tafada minba? Amma saita kama tana kiran Aliyu tunda kanin uwartane wai Khamis wants to rape her, shikuma yagayama babanku harda karawa da baza'a bama Khamis auren nataba, yanzu ubanku yace aure fa ata fafur, Hajar bansan mesa yarinyar nan ta dauko jinin ubanku ba ko kadan bata biyoni ba wanan wata irin munafukar makiran yarinya na haifa hakane? Ke kinsan uban burin danaci kan bikin nan amma ta hargitsamin komi wlh duk kishiyoyina sai habaici sukemin abin yadawomin abin kunya, Yaya zanyi eh Hajar Yaya zanyi da Rauda wai iyye?" tai maganan tana sake share hawayen dake zubowa dan sun kasa tsayawa, rungume ta Hajar tayi sosai tana bubbuga bayanta, kaman zatai kuka tace "Mama kiyakuri dan Allah kinji, ai zata dawo daki batada wurin kwana daya wuce nan, so karki damu idan kika mata shegen duka saita tsorata musata taje tafadama Dady da kanta cewa zata aureshi tana son shi, don't worry Mama" Hajar tai maganan tana rungumeta cikeda tausayin mahaifiyar nata.
Karan da wayarshi keyi a aljihu 3quater shi yasa ya tsayar da ball din dayake bugawa yaciro wayar yana kallon screen din, sunan Abdul daya gani yasa yadanyi murmushi yay picking wayar yakara akunne batare dayace komiba daga tachan bangaren muryan wani guy ne yace "just get ready for me zanci ubanka ne idan nazo gani a hanya, so Leo you have the guts kadawo Nigeria kakasa kirana kafadamin ga Mummy anan tace itama bazatai magana dakaiba kuma wai nafadama ka kyauta" dan murmushi yayi Yazauna kan wani bench dake wurin cikin cool voice dinshi yace "give Momma da phone I wanna speak to her" wani mugun dariya saurayin yayi yace "ai kanada number ta yasin bani bada wayata dan rainin wayau, nidai ganinan zuwa" kara yasaki batare daya katse wayarba "auchhh Mumy shine harda dukana" murmushi yasake yi ahankali yace "hello Momma" muryan wata yar dattijuwa data amshe wayanne tace "Beta (Son) how are you?" "am fine Momma, Momma wai kina fushi dani?" dan dariya tayi na manyan mata dinan tace "don't mind him Beta, u know I can never get angry with you, tell me how are you doing?" adan shagwabe yace "fine Momma, I miss your pancakes am craving for it" zatai magana Abdul ya fizge wayar da gudu yace "kai ya isheka yima Mummy na shagwaba dan iska" dan murmushi yayi yace "come soon jor" murmushi shima Abdul yayi yace "alright am coming now get ready biki zamuje gobe" dan yatsine fuska yayi yace "gobe? Sunday fa" car key yadan duka zai dauka yace "yes dat my Chadian friend damukai school tare a CA ne zaiyi aure, zai auri wata yar buzuwan maiduguri anan Abuja take so gobe ne first event wushe wushe so baida friends a Nigeria banda mu, so get ready u must go da daddare ake wushe wushe din but mu tun rana zamu your clothes and mine sef yanzu tsaya na karbo mana, saina zo bye" yatsine fuska yayi yace "yeah bye" yatashi ahankali yana tafiya yasaki ball din akasa yay part dinshi yunwa yakeji sosai amma bai iya komiba yatsine fuska yayi ya shiga kitchen din yana kallon koina, shidai ya tsani abincin kuku da Dady yace idan yanajin yunwa yadinga kiranshi yana zuwa yanamai girki but baison girkinshi ko kadan shifa dayaci abincin da baima bakinshi dadiba gwarama ya zauna baiciba, fridge dinshi yabude yadauko kwalin farmfresh yogurt yabude ya ijiye kan saman fridge din yadauko daya daga cikin manya manyan babban fararen glass cups din dake jere a cabinet dinshi yazo ya tuttula yogurt din cikan cup din ya cika fam sanan ya rufe ya ijiye yoghurt din kan fridge din yadau wanda yazuba a cup yafita daga kitchen din yana kurba yakara so tsakiyan falonshi, remote yadauka ya chanza channel din dake aiki zuwa na sport ng inda ake buga ball sanan yazauna yana shan chill yogurt din yana kallon ball din, Aneesa ce tafado mai arai hakan yasa yasakeyin murmushi tareda dan lumshe ido ya janye cup din yogurt din daga bakinshi yana dan juya cup din ahankali yace "Boldest" dan murmushi yayi yamaida cup din bakinshi ya cigaba dashan yogurt din kaman wani dan karamin yaro, ahankali yakesha a sangarce kaman baison yasha.
[04/03, 16:35] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
1️⃣1️⃣ & 1️⃣2️⃣
_How to subscribe_
_*zaki tura 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watdsapp number na 07012181461. For those da basu da account you can also send MTN card ta watsapp number na saina saki a group din danake posting*_
_Free page_
Shigowa dakin Dady yayi sanye da jallabiya fuskarshi lema leman ruwa alamun kaman alwala yayi hada ido sukayi da Dady yana zaune kan kujera, bedroom dinshi Dady yawuce baiwani jima acikiba yafito dawani white iron jallabiya mai kyau namaka yafito daga dakin nashi yace "tashi kasa mutafi masallaci" turo baki yayi yana karasa shan yoghurt dinshi yace "ni banyi alwala ba" ajiye jallabiyan Dady yayi kan saman kujera yazo inda yake ya karbe cup din hanunshi yace "you and yogurt, give me the cup" ya karbe cup din ya ijiye akan center table yace "to tashi kashiga nan visitors toilet kadauro alwala Son, kaga anma fara kiran salla" gyadamai kai yayi yamike tsaye ahankali yana tafiya kaman baison yi ya shiga bayin Dady yabi bayanshi da kallo kafin yadau cup din yogurt din daya ijiye yawuce kitchen yaje ya ijiye a cikin sink, fitowa yayi daidai shima yafito daga bayin daure da alwala Jallabiyan Dady yadauka yamikamai karba yayi yasaka suka fita daga dakin sukai masallaci Dady nabashi labarin yanda yayi dasu Mama da Khamis dazu har mari saida yama Khamis lafiyayyu guda uku da yaso ya kulleshi ma da kyar yahakura bayan sunbabbashi hakuri, murmushi kawai yayi yanajin Dady harsuka shiga masallaci. Saida sukai isha'i sanan suka dawo gida zaiyi part dinshi Dady yace "let's go to side dina muyi dinner" girgixa kai yayi yanadan lumshe ido ahankali yace "am sleepy and am not hungry Dad, I love you gud night" tsayawa Dady yayi yana kallonshi kafin yadan numfasa yace "shikenan gud night kiddo I love you more" turo bakinshi yayi yace "Daddd kiddo kuma" hancinshi Dady yaja yace "kafito da mata namaka aure kaga idan nakara kiranka da Kiddo" dan dariya yayi yace "nay nay na" tallabe keyanshi Dady yayi yace "zakaci gidanku da nay nay na ne, motar waye a pake a gaban side dinka?" Dady yay maganan yana kallon gaban shashinshi dansai yanzu ya lura da motar, juyawa yayi ya kalli shashin dan murmushi yayi yace "is Abdul Dady, bye gud night bari naje" yafada da sauri yana tafiya, murmushi Dady yayi yace "su aboki anzo har ana sauri ko an manta dasu Dady" juyowa yayi da sauri jin maganan da Dady yayi da sauri yaje ya rungume Dady yay lamo a jikinshi ahankali yace "you know you are the best Dady in the whole world" shafa bayanshi Dady yayi yana washe baki yace "and you are the best son in the whole world Aliyu am a proud father to this yaro maijin magana just a lil stubborn and annoying atimes" dariya dukansu suka fashe dashi a tsakar gidan atare kafin sundanyi shiru yana jikinshi har lokacin, murya chan yace "Dad" anatse Dad dake rike dashi yace "na'am Gadanga na" ahankali yace "you are my Dady and My Mummy, kamaye gurbin Ummi, baka taba bari naji kewanta ba, you feel that hole in my heart, you are my everything Dad, and happy Fathers day" rungume shi tight Dady yayi his heart is so swollen kalman Mum daya fada yasa yatuna da marigayiya matarshi the best wife daharyau yakasa samun kamanta shiru sukadanyi for a while kafin yasaki Aliyu yana share hawayen dasuka cikamai ido da sauri dan karya gani sanan yay murmushi yace "wuce katafi Abdul na jiranka, zan aiko muku da abinci" gyadamai kai yayi ahankali yace "bye Dady" "bye son" juyawa yayi yay part dinshi Dady ya tsaya yana kallonshi saida yaga shiganshi yawuce yay part dinshi shima.
Ahankali yabude door din part dinshi babu kowa a falon sai manyan jakunkunan kwali da aka rubuta Men by Robanni wears ajiki hakan yasa yagane kayan bikin dazasu sakan gobene Abdul ya karbo musu din, hanyar bedroom dinshi yayi, bude kofa yayi ya shiga babu kowa adakin sai car keys da waya dake kan gado karan ruwan dayaji yasa yagane yana bathroom, dan ajiyan zuciya ya sauke ya zare jallabiyan jikinshi yay hanging a hanger yasaka a wardrobe sanan yazo yafada kan gado.
Bude kofan bathroom da akayi yasa yadago kanshi wani guy ne kusan kansu daya da Aliyun saidai Aliyu yadan fishi dan kaurin jiki dakuma haske dan Aliyu farin sosai Abdul ma farine but baikai Aliyu haske ba, fitowa Abdul yayi daure da towel a waist harara yana rike da karami a hannu dayake goge gashin kanshi dashi yazubama Aliyun dayay lamo akan gado yana kallonshi yace "dan iska kafin laifi kawani kwanta forming innocent right, kama ta shine malam" yay gaban mirror yana tsane jikin da towel kafin yaje gaban wardrobe din Aliyu yabude yadauko daya daga cikin pyjamas dinshi milk color yasaka sanan ya shiga bayi yaje yay hanging towel din back sanan yafito yay kan gadon ganin zai fado kanshi yasa Aliyu yatashi da sauri yanadan dariyan shakiyanci yace "leave me alone jor, karka karyani, shine kazo koka kirani" wayarshi dake kan gadon yadauka yace "I know kana mosque saisa I didn't call, wait before anything am hungry" hararan shi Aliyu yayi yatashi daga kan gadon yace "chop chop, Dady zai aiko mana da abinci, let's go, muje falo" tashi Abdul yayi yabi bayanshi suka fita falon daidai lokacin akai knocking kofa, Abdul ne ya amsa shikuma Aliyu yafada kan kujera. "yes come in" bude kofa akayi bodyguard su biyu na Aliyu suka shigo dakin daya dauke da manyan warmers guda biyu sai dayan kuma dauke da tray da slice fruits a bowls kekai, dining Aliyu ya nuna musu suka kai abincin wajen sanan suka juya suka fita, hanyar dining din Abdul yayi yazauna yana bubbude warmers din yana kallon abincin dake ciki kafin yadau plate da spoon ya debi ofada rice da smoke fish stew ya ijiye a gabanshi, wani bowl yasake dauka yadau spoon yacika bowl din da fried pepper chicken sanan yadaga kai ya kalli Aliyu dahar ya kwanta akan kujera yana daddana remote yana lumlumshe ido yace "let's eat Leo" yatsine fuska yayi yace "me aka dafa? Me acikin warmers din?" hararan shi Abdul yayi yafara cin abincin shi batare daya kulashi ba dan yaga iskanci Aliyu keji shikuma right now he's starving bari yabama cikinshi hakkinshi tukunna yanda Abdul kecin abincin was tempting his taste bud ahankali yatashi daga kan kujeran ya mike tsaye, dariya Abdul yafashe dashi ganin yatashi, karasowa dining din yayi yaja daya daga cikin kujerun dining din na kusada Abdul din dakemai dariya ya zauna fizge spoon din hanun Abdul din yayi yaja plate din rice din ya shiga ci, dariya Abdul ya shiga yi yace "nadaiji shege waya gayama anama abinci yanga" yay maganan yana daukan wani spoon suka shiga ci tare, he hardly eat much but because yanaci tareda wani sosai yaci abincin har Abdul na karamusu sukaci, baiwani ci pepper chicken din sosai ba yazuba juice ya kwankwada shikuma Abdul yaci tass, saida suka gama yace "this fruit kasasu a fridge Leo ni banda inda zasu shiga acikina while I clear the dining" gyadamai kai yayi yatashi ya dai bowls din yakai fridge shikuma Abdul ya kwashi plate yakai kitchen.
Gamawa sukayi sukai falo Abdul yadau jakunkunan kayan su yace "kaga kayanmu gobe zamu fita dawuri fa, mune abokan ango" tabe baki yayi yadan shafa kai yace "am sleepy sosai bangane mekake cewa, let's go to bed" waya Abdul yadauka yana gyara kwanciya kan kujera yace "kai kaje ni waya zanyi da" ya kashemai ido, tsaki Aliyu yayi yay hanyar bedroom yace "dan iska aikin kenan soyayya" daga murya Abdul yayi yace "bari kafara naka bazaka bari muhuta ba, kardai kazo kana mana kuka idan tace bata sonka" daga murya yayi daga bedroom yace "never" shima daga murya Abdul yayi daga falo yace "is a bet" tsaki Aliyu yaja yana cire rigan jikinshi yace "rubbish, why will I ever cry over soyayya? Allah kyauta" yatabe baki ya shiga bathroom yana tafiya da kyar so yake yay wanka yazo yay bacci.
Asuba tagari!!!!
_Suleja_
Shigowa dakin tayi tana gyara tsintsiyan laushin dake hanunta tana satan kallon Ammi, harara Ammi ta watsa mata tace "wai lafiya kike kallona haka?" dakin Ammi ta shiga da sauri ta ijiye tsintsiyan tafara gyara gadon saida tagama tsaf sanan ta sharo dakin tafito da sharan ta shiga dakinta ta sharoshi shima sanan tafara sharan falon Ammi sai hararanta take dan tai mata laifi tunda tai sabon wayan nan da Baffa yakawo mata take uban danne danne awayan data rasa nameme, tarasa uban me take dannawa awayan dababu komi aciki, dasafen nan ma daga ta dumama abincin kari saida taji kauri koda tafito taje kitchen abincin ya kone ga Aneesa agefe agaban murhun kan kujera tana daddanna waya bamata saniba tsabagen nisan datayi shine ta zuba mata dunddu ta karbe wayan har yanzu bata bataba saisa taketa satan kallonta tanaso ta roketa tabata amma bataga fuskar hakanba, karasa share falon tayi ta fitar da sharan tsakar gida sanan tawuce kitchen ta debo rushi