Showing 60001 words to 63000 words out of 186400 words
Chapter 21 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt
yi, ganin hannayenta namata zafi tsabagen bugawa yasa ta tsaya tasake sa hannu ta share hawayen daya zubomata ta juya tana kallon kasan wajen tana neme neme, hango bawon ayaba datayi ata gaban motan yasa takoma gaban motan da sauri ta tsugunna ta dauko bawon ayaban ta jefama gaban motan da duka karfin ta kaman shitake jefamawa tace "baza'a rabu dasu dinba, nafi son dukan su, mezanyi dakai masifaffe dakai, sai feeling kaman ka isa dakowa sai kace wani dan sarki, dan kazo da wanan akwalan motan mai kama da bons, kuma daga yau ka kara dawowa gaban gidanmu saina faffasama tayoyin wanan bakar motan, mummunan mota kawai" ta tsugunna ta kwashi kasa a hanunta ta watsa ma glass din Abdul ya ware ido tareda kama baki yace "toooooo" da yatsa ta nuna motan tace "karka kara zuwa anguwan nan, kuma kaima last warning, Allah kasake zuwa saina dauko tabarya na rotsa glass din gaban nan" tawuce tai gidansu a zuciye Aliyu nabinta da kallo barinma cute feet dinta da babu safa ajiki dan saiyau yaga feet nata da kyau yatun masu kyau dake dauke da white fitted nails farare fat.
Wani irin fashewa da dariya Abdul yayi har yana buga kanshi kan abin tuki. "wayyo Allah na cikina, Mommahhh cikina zai fashe" yarike ciki dahar murdamai yake tsabagen dariya da kyar yay shiru ya kalli Aliyu dayaga ya lumshe ido kaman mai bacci nanko duk yagama ganin abinda Aneesa tamusu yace "ashe yar bala'i ka dauko mana Aliyu, wai wai wai nida Anty barkono, chab" yakara kecewa dawani mahaukacin dariya, bude ido ahankali Aliyu yayi dasukai jajir yazuba mai su, hannu Abdul yadaga cike da dariya yace "sorry, sorry nadena" yay shiru yana shafa baki yana kallon glass din motar dayay jajir dan jar kasane a anguwan yace "wai, I mean look at our glass kaman wayanda suka fito daga rami, Allah yasa motarka tama haka da tawace da yasin saika wanke ta, Leo a ina kasamo barkonon nan?" yakara kwashewa da dariya, hannu Aliyu yasa zai bude motan yafita yabarmai dan he's just adding salt to his wound da sauri Abdul yarike shi yana danne dariyan dake cinshi yace "yakuri, yakuri inato zaka? Ihakuri haba Only Friend, but honestly I love her I mean the girl, damn! Masifanta ya mugun burgeni Leo, am just wondering yanda kaida ita zakuyi rayuwa under the same roof kai zuciya ita zuciya inkuka sami mis understanding sunan gidanka gidan kas....kasa Le..." yasake kecewa da dariya, ji Aliyu yake kaman ya shakeshi yahuta kawai ahankali hawaye ya gangaro daga idanunshi yana kallonshi da sauri Abdul ya tsayar da dariyan kaman ba shine ke dariya ba cikeda damuwa yace "Hey Leo mehaka kuma daga wasa, please stop" handkerchief din cikin aljihun shi yaciro da sauri yamikama Aliyun yana shiga taita yin shi, ahankali ya karba ya share hawayen tareda fuzar da iska mai zafi, bude motan Abdul yayi tareda daukan towel din share glass din motar, dariya yakeso yayi ganin yanda Aneesa taci uban motar da kasa saikuma ya gimtse dariyan dan fess Aliyu zai iya tasa shi agaba yay tamai kuka, share glass din yayi tass amma dudda haka motar nan dole sai taje car wash yakoma ciki ya zauna tareda tada motan yafara tafiya ahankali, agaban wani masallaci yay parkin suka fito sukai salla sanan suka koma mota yatada motar yana kallon hanya batare daya kalli fuskar Aliyun ba yace "if you want to win a woman's heart Leo dole ka sauke mata kai, allow her ta tattakaka yanda takeso tawuce tadawo if possible ma ta zubar da shara akanka, ance duk sarautan sarki a wajen matar shi bawa yake dawowa, I believe you know this girl (Aneesa) morethan I do, I just saw her yau harna gane who she is, kaiko nasan this is not d first time daka fara ganinta u understand who she is and yet kana mata zuciya da zafi agabanta, no no no that's very wrong, I understand how you feel seeing wacce kakeso tareda wani but you have to calm down and act maturely, yarinyar nan barkono ce and ta hanya daya ake winning zuciyan mata irinta" yay maganan tareda dan satan kallon Aliyun ganin yanda ya natsu yana kallonshi yasa yay dan murmushi yace "zan baka misali guda daya, ka dauka anyi serving nnaka abinci dake da yaji sosai abincin yaji barkono, harshen ka da bakinka da labban ka duk suka haukace sabida yaji by the time dazaka dauko sweet kabude daga leda ka jefa abakin kafara tsotsa just give yajin a minute or so zakaga dadin sweet din ya rinjayi yajin tun kanajin yajin har saiyazo yabace all you could feel is sweetness of your sweet, so just be like a Sweet towards this girl and trust me you will win her over, be sweet, be gentle, don't hit it hard take it slow one step at a time, forget baaba zata shigo hannu ne tsaf fine boy like you, Dady's Boy fa for that matter" dan murmushi yayi hakan ba karamin dadi yama Abdul ba daman yay hakane dan yasashi murmushi saikuma yayi fuzar da iska yyi yace "let's go home wlh yunwa nakeji".
Ganin babu Ammi a tsakar gida yasa tasauke ajiyan zuciya alwala ta dauro da sauri tawuce ta shiga dakinsu daidai Ammi ta sallame salla tace "hayaniyan menake taji awaje?" rasa me zatace tayi da kyar bakinta yasamo magana tasoma hadawa tace "wasu yara ke fada shine Yusuf yaraba su, yama tafi dama basu ganni bane shine yanemi gidanmu yazo yaji lafiya" charbi Ammi ta dauka tace "ayya, angode to, zokiyi salla kici abinci kisha maganin dare" hawa man dadduman tayi ta kabbarta salla Ammi kuma ta tashi tana kawomata abincin dazataci da magungunan ta tana idarwa tazauna tanaci bayan tagama tasha maganin da kyar shima dan Ammi tamata da gaske ne, suna falo har aka kira isha'i sukayi sanan suka cigaba da hira.
Sallaman Baffa sukaji saikuma ya kwalama Aneesa kira. "Fateema" tashi Aneesa tayi da sauri tafita yana ma wurin zaure tace "sannu da zuwa Baffa" yar ledan hanunshi yamika mata yace "ga tsaraban kinan, jeki cema maman ki Alhaji yazo ta gyara yanzun nan zan shigo dashi" wani irin tsalle tayi tana murmushi tace "tom " dasauri tajuya takoma daki dawani irin gudu taje tafada kan jikin Ammi dake kan dadduma tace "Ammi Baffa yace kici gayu Abba yazo zai shigo dashi" hararanta Ammi tayi tace "to bismillan su mana wani gayu zanyi ni? Namasan shairin kine" ashagabe tana turo baki tace "ni Allah saikin yi, kinji Ammi na please" tai maganan tana daga Ammin tanajan hannunta tashi Ammi tayi tace "nidai nabani da dake Aneesa" dariya tayi sosai taja Ammin sukai dakinta ta zaunar da Ammi kan gado jikinta harwani rawa yake tabude sip din Ammi wani leshi taciro da sauri Ammi tace "lafiyan ki kuwa Aneesa? Da daddaren nan zansa leshinnan dake da nauyi?" kallon leshin Aneesa tayi tana murmushi tace "au hakane wlh Ammi murna nake banmasan me nakeyi ba" tabe baki Ammi tayi tace "kyaji dashi, mikomin wanchan doguwan rigan atampan" tamata pointing wani atampa mai kyau daukowa Aneesa tayi takawo mata sanan tace "yauwa bari naciro hijabin dazai shiga dashi" komawa sip din tayi Ammi kuma yacigaba da shiryawa, wani mustard hijabi taciro mai hula daya dace da doguwan rigan tajuyo har Ammi tagama sa kayan da sauri tawuce gaban madubi hoda ta dauko da kawalli da man baki, kallonta Ammi tayi ganin ta kwaso kayan kwalliya zatai magana Aneesa kaman zatai kuka tace "ni Allah saina miki" shiru Ammi tayi babu yanda ta iya, karasowa tayi ta shiga mata light makeup ta shafa mata man baki sosai Ammi tai kyau har tazo tanajin wani iri dan tamanta rabonta datai kwalliya haka, sallaman dasukaji nasu Baffa yasa Aneesa tace "kisa hijabin bari naje na gaida su" fita tayi da sauri daidai Baffa ya shigo da Dady dayaci manyan kaya na milk shadda sai kamshi yake bazawa, babban dadduman su dasuke shimfida ma baki Aneesa ta dauko ta shimfida tana murmushi tace "Abba sannu dazuwa" cikeda fara'a yace "lallai y'ata ta warke masha Allah, naji dadi, ya jikin?" "Alhamdulillah naji sauki Abba ka zauna" tanunamai dadduman zama yayi tareda yin bismillah, Baffa yace "jeki kira Maman ki saiki dauko tsaraban ki kizo musha a tsakar gida" gyadamai kai tayi tajuya da sauri tai dakin Ammi, Ammi na zaune kan gado tasaka hijabin tai kyau sosai kaman wata sabuwan amarya wani irin tsalle tadaka tafada kan jikin Ammi tana dariya, salati Ammi tace "innalillahi, Oh Allah, haladai kinyi alkawari ne saikin karyani kafin gobe da safe ko Aneesa" kyalkyacewa tayi da dariya tace "Ammi na wlh dadi nakeji, Baffa yace kije, nidai natafi, Ammi na kimai firan nan naki mai dadi" dukan da Ammi ta daga hannu zata maka mata yasa ta tashi da sauri tafita daga dakin tana murmushi ledan tsaraban ta tadauka Baffa dake kallonta yace "yauwa muje" murmushi Dady yayi yace "laaaa ni baza abani ba" da sauri tazo gaban shi tabude mai ledan tace "a'a Abba gashi kasha" tafada akunyace, dariya yayi yace "nagode Allah amfana" cikeda fara'a Baffa yace "yakara auki daharna fara kukan zuci zaka shanye mana kashu dinmu" dariya dukansu sukayi Aneesa tabi Baffa suka fita tsakar gida a binsu suka zauna kan tabarma suna hira suna sha.
Saida Ammi taji fitansu sanan ta tashi ahankali sosai takejin kunyan yanda Aneesa tamata gayu kaman wata yar yarinya, ahankali tayaye labule tafito falon kanta akasa idanun Dady kyam akanta ko kyaftawa ba yayi, karasowa cikin falon tayi zata zauna akan kujera Dady ya nuna mata gefenshi da hannu kan dadduman yace "zoki zauna anan Rukayya" dan dago kai tayi suka hada ido da Dady gyadamata kai yayi hakan yasa ahankali takaraso wurin dadduman ta zauna inda yake nuna mata kusada shi amma adan kwai gab tsakanin su.
Ajiyan zuciya Dady yasauke yana kallonta murya chan kasa yace "kinyi kyau sosai Rukayya" kasa dagokai Ammi tayi dan maganan yabata kunya murya chan kasa tace "barka da zuwa, ina yini, ya aiki" murmushi yayi sosai yace "baza akalleni ba Rukayya, idanuwana na kwadayin ganin fararen idanun nan naki masu sanyaya ma Muhammad Ibrahim zuciya" wani irin masifan kunya kalaman shi suka bama Ammi ahankali tadaure tadago kwayoyin idanunta dasuka sha kwalli ta daura akan Dady, wani irin lumshe ido yayi kafin yabude su ahankali ya kalleta murya chan kasa yace "godiya nake yallabiyata" sallama Aneesa tayi ta tsaya abakin kofa tana jiran abata izinin shigowa, ahankali Ammi tace "shigo" shigowa tayi dauke da best tray dinsu mai kyau da maltina mai sanyi ke kai sai kulan tuwo da miyan kuka dayaji wake da kifi da dan bowl dake dauke da ruwan wanke hannu sai goran ruwan Eva maidan sanyi Baffa yasiyo maltinan da ruwa, karasowa tayi ta ijiye tray tace "Abba ga abincin ka nan, Ammi na tadafa ai zaka cinye ko" da sauri yana kallon fuskan Aneesan yana mata murmushi yana masifar son yarinyar yace "kwarai kuwa, tunda Ammi ki tadafa ai dole na cinye harda side kwano" murmushi sosai Aneesa tayi tadan saci kallon Ammi data watsa mata harara tamike tafita daga dakin takoma wurin su Baffa.
Kallon Ammi Baffa yayi cikeda so ahankali yace "nagode da karamci, musamman kikamin girki dole na cinye abincin hasken idaniyata" murmushi Ammi tayi tasa hannu zata jawo tray dan serving nashi yace "zanci anjima kadan, yanzu lokacin kine bana cin abinci ba" murmushi Ammi tayi tama rasa mezatace itadai wanan mutum na kashe mata zuciya da kalamai.
Gyara zama Dady yayi yana facing Ammi dake wasa da yatsun ta yanda Aneesa keyi, ahankali yace "ina kaunar ki sosai Rukayya sabida ina ganin kaina aduk lokacin dana ganki, ayau nazo wurinki dauke da batu biyu danake so namiki masu mahimmanci" shiru Ammi tayi ta baci dukkan natsuwan ta sabida yanda taga yanatsu shima alamun maganan dazai mata mai ma'ana ne, dan ajiyar zuciya yayi yace "Rukayya banso mugina rayuwan mu kan karya kokuma yaudara, Inaso mugina rayuwan aure na amana da tsantsan kauna da jinkai, maganan farko dazan miki shine kome zaki gani agidana badaga wurina ba wurin matana kiyakuri bazan miki karyaba matana sai ahankali, sai ahankali kome zasu miki baruwanki dasu ba zaman su kikeba zamana kike, banso kiyi koyi da dabi'oisu, sonake nakara aure konadinga samin kwanciyan hankali daga wurinki" yay dan shiru kafin ahankali yace "sai magana tabiyu, marayan d'ana Aliyu shekaran shi ashirin da tara yanzu, mahaifiyar shi tarasu tun kafin yadan tasa, inaso kihada shi dashi da Aneesa kirike minsu amana Rukayya, matayena basa sonshi ko kadan abinci inba ina gidan nanba nace akaimai ba'a kaima, baida hayaniya ko kadan zaki ganshi, baida fada, baima cika magana ba, Komi nashi inaso yadawo wurinki, nabaki shi Rukayya kece mahaifiyar shi zuciyata ta yarda sanan ta aminta dake, kirike minshi amana kinji Rukayya hope ban hadaki da aiki babba ba?" dan murmushi Ammi tayi tace "ko kadan, d'a nakowa ne, baka hadani da aiki ba, nakuma gode da matsayin daka bani namaka alkawari zan kula dashi amana, bqzaka taba samuna da zalunci ko ha'intar shiba, na karba, na karbi Aliyu da hannu bibbiyu, Allah ya shige mana gaba" "Ameen" Dady yace yana wani irin jin son Ammi aranshi. Shiru duk sukayi suna kallon juna Ammi ce tafara breaking kallon ta nunamai tray tace "abincin ka zai huci kaci dan Allah" murmushi Dady yayi yace "ina zan iyacin abinci batare danasan ranan da zan mallaki Rukayya amatasayin matata ba uwar yarana guda biyu Aliyu da Aneesa" wani irin cute smile Ammi tayi batare data kalleshi ba, cikin wani irin murya Dady yace "idanuna na maradin wanan sassanyar kallon naki mai sanyayamin rai gimbiya" dagokai Ammi tayi ta kallai, ahankali yace "yaushe zaki bari na mallakeki kidawo mallakina?" ahankali Ammi tace "duk randa kakeso Yallabai" washe baki Dady yayi yace "yau Wednesday ko" gyadamai kai Ammi tayi, murmushi yayi yace "ran jumma'a nakeso adaura auren bayan antaso daga masallaci inyaso zan iya kara miki ko kwana biyu ne ko sati daya kigama shiryawan ku na mata saiki tare ko Gimbiya" dan murmushi Ammi tayi tace "hakan ma yayi, Allah yasamana albarka aciki" dan lumshe ido Dady yayi yabude yace "ina kaunar ki sosai Rukayya," yy maganan ahankali yana kallon Ammi kaman yana jiran tacemai wani abu murmushi sosai Ammi tayi tamika hannunta tadauko kulan abincin ta ijiye kusada shi tana kokarin budewa ahankali tace "ina kaunar ka nima Yallabai tun ranan dana fara ganinka" numfashin Dady yakusa daukewa da sauri yace "wayyo Allah na ban ruwa Rukayya zuciyata ta dadada dayawa, dole in kora da ruwa" murmushi sosai Ammi tayi tana girgiza kai tadauko ruwan tabude ta mikamai tana kallonshi kafa ruwan yayi abaki ya asha yana kallonta kafin ahankali ya mika mata goran, karba tayi tace "kaci abinci to" faraci yayi ba karamin dadi abincin yamai ba tass yaci ye tuwon hakan yama Ammi dadi ba kadan ba, ya wanke hannu yana share baki sanan ya kalli agogo goma saura tashi yayi yace "bari intafi, amma fara bani izinin tafiya tukunna" murmushi Ammi tayi tace "nabaka" "tom saida safe" gyadamai kai tayi tace "Allah ya kaika lafiya, nagode" har bakin kofa taraka shi yatafi su Baffa suka rakashi waje Aneesa ta shigo tareda rungume Ammi tana murna, yarane suka shiga shigo da jakunkunan na kayan kwalama daga baya kuma saiga su Baffa abinci tanasu suka ci suma suna mata maganan ran jumma'a za'a daura auren wai inji Alhaji. Karan shigowan sako dataji yasa tabude.
_na manta ban gayamiki ina tsananin kaunar ki kafin natafi ba, ina miki Son so, ki kulamin da kanki gimbiyata, Allah yamiki albarka, saida safe_
_Alhaji Muhammad Ibrahim_
Murmushi Ammi tayi ta ijiye wayan bata taba sanin zata karason waniba, bama tasan Yaya akai Dady ya sace mata zuciya ba kodan sabida yanda yakeson Aneesa ne? Kokuma sabida yanda Aneesa keson shine? Kokuma da iya maganan shi da halin taimakon shine? All she knows is tanason each and every single shade of him.
_duk wacce takaranta bata biyaba itada Allah, duk maison book dinan ta tuntubeni ta 07012181461 watsapp_
_masu fitarwa dama ku watstsatsu ne, saika kuka watsawa, ban yafemukuba kuma, rubabbu kawai_
[20/03, 12:10] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
3️⃣1️⃣
Gida suka karasa bayan sun tsaya sunyi sallan isha'i, thank God Momma bata falo dakinsu ya wuce direct dan ko kadan bazai iya tsayawa mata magana ba, ko takalmi bai cireba yafada kan gado yaja bargo yarufe tundaga kanshi har zuwa kafafunshi, inda ace zai biyema zuciyan shi kuka kawai zaitayi batare dayasan mezaiyi ya sanyayamai raiba, he's so soo maddd, so angry, ya tsani yaga Aneesa dawani tanamai magana jiyake kaman zai fadi yamutu, baima san tayaya zaiyi describing yanda zuciyan shi kemai zafiba idan ya ganta dawani, jiyake kaman ana daddatse mai zuciya da babban wuka, wani irin wahalallen bacci ne yay awon gaba dashi yana cikin tunani. Abdul ne yabude kofar dakin ya shigo zaimai magana yaga har yay bacci ya dunkule agado looking so innocent ko kayan jikinshi ma bai cireba yana sauke ajiyan zuciya daddaya, ahankali yazauna abakin gadon yana kallonshi yana tunani yaushe har soyayyan barkono yakama shi haka? Rashin amsan tambayan shi yasa shima duk yunwan da yakeji yaji takoma ciki ya kwanta gefen Aliyun shima batare daya cire kayaba nan wani shegen bacci yay awon gaba dashi.
Momma dake kitchen dasuka shigo ne tafito Ihsan dake biyeda ita tafito itama, Ihsan ta kalla tace "jeki kiramin su suzo suci abinci" sama Ihsan tayi bata wani jimaba ta sauko tana dariya tace "Momma duk sunyi bacci ko takalma basu cireba" girgiza kai Momma tayi