Showing 36001 words to 39000 words out of 186400 words
Chapter 13 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt
yayine? Inaaa!! Bazata yuwa duk fadan da zasuyi shida Aliyun saidai suyi amma yagama fita daga gida batare da bodyguards dinshi ba, filo yajawo yadaga kanshi yadaura kan filon, yatashi yabude clean bathroom dinshi ya shiga yadebo warm water awani small bowl da karamin towel yazo ya tsugunna anan bakin gadon yakamo hanun yasa towel din yana gogewa, yatsine fuska Aliyu yayi cikin bacci alamun yanajin zafi ba karamin tausayi yabama Dady ba hakan yasa ya shiga huramai iska akan hannun ahankali yasake relaxing cikin baccin yacigaba da baccin tareda sauke ajiyan zuciya, tashi Dady yayi yakoma bathroom din ya ijiye komi yafito yadau wani pain relief balm daya ijiye a dakin nashi yazo yakamo hanun ya shafamai sanan yaja bargo yarufamai yarage karfin AC yajuya yafita daga dakin yana tunanin Maiya sameshi kafin yawuce yaje falon shi yadauko briefcase dinshi yafito bodyguards dinshi suka budemai mota ya shiga yamayi latti wlh yau zai shiga Chambers dama dayanda zaiyi dabaije ba Aliyu is his number in this life, haka yadinga tunani har yakai House of Representative, Federal Republic of Nigeria.
_*duk wacce takaranta book dinan batare data biyaba ban yafeba wlh, pay your access fee is just 300, wtsapp 07012181461*_
Takai kusan 2min atsaye chak awurin takasa matsawa sai rawa da jikinta keyi, kafin ahankali ta janye hijabinta tana kallon wajen, mai keken dayazo wucewa ta tare da sauri dan kunya takeji bana wasaba yanda kowa ke kallonta a wurin, shigewa tayi tace "express road zani" tada keken yayi yaja sukai gaba har express road yasauketa tafito dari biyu ta dauko tamikamai tajuya da gudu Yusuf zai tsaya yimata magana tabude kofa ta shiga abinta, Fatima sai kallonta take kaman yau tafara ganinta, backyard tawuce straight ta bude staff toilet ta shiga da gudu tarufe kofan tabude tap ruwa na zuba tafashe da kuka sosai tana taushe bakinta she's so angry, Aliyu ya mugun bata mata rai, ita wata irin mutum ne da ta tsani dizgi a bainar jama'a tun tana yar yarinya, ko dukanta Ammi zatayi inhar tamata agaban mutane saitai kusan kwana biyu bata fitaba taita kuka agida dan tanada kunya, kuma inhar Ammi tadaketa agaban jama'a kozata kasheta bazatai kuka ba saita daure sai jama'a sun tafi saitafara kuka, batason amata fada agaban mutane she's just naturally like that abin gets to her ne emotionally, shine Aliyun nan da bamata sanshi ba yakama yana mata tsawa kaman wata yarshi harzai mareta, sosai tafashe da kuka, cikin kuka sosai tabude jakanta taciro wayarta hanunta har rawa yake ta shiga contact dinshi ta danna ma number shi delete ta ijiye wayan takara kifa kanta awurin tana kuka sosai, jin ana shirin bude kofa yasa da sauri ta deba ruwan ta shiga wanke fuskarta, Fatima ce tashigo bayin tana hararanta tazo gefenta gaban wash hand basin din tana dan rera waka. "angwada nawa yace bayayi, da akaje gidan namiji saiya kadomu yace bazai bayarba shine muka gudo bayi muna kuka ahayye nanaye" Aneesa najin ta amma ba tace mata komiba, gama wanke wanke hannun tsokana Fatiman tayi tazo zata wuce tana waken ta ta bangaje Aneesa zata wuce, cikin tsananin fushi Aneesa ta fizgota batai wata wataba ta daga hannu ta daura mata clean mari, ihu Fatima tayi zata rama Aneesa tasa kafa ta kwashe ta sai kasa, tabita kasa ta kara daura mata wani marin tace "nasha gayamiki kifita daga harkana kinki, mene miki kika bangaje ni, ba fada kikeso ba zan koya miki hankali yau" takara zuba mata wani mari ta hade hannayen Fatiman ta murde su da karfi, ihu Fatima tayi, gwabe bakinta Aneesa tayi ta tashi daga kan cikinta tace "ki kara tonana" taja hijabinta da wayanta da jakan tafita daga bayin cikeda fushi, Fatima kasa tashi daga kasan tayi ta daga murya tace "wlh sainaga bayanki aduniyan nan Aneesa, sainaci mamanki dan ubanki, wayyo Allah na reshen bayana" dafa bango tayi tamike tsaye da kyar da sauri ta kakkabe jikinta dan batason Yusuf yagane Aneesa ta kayar da ita akasa ta wanwanke hanunta daya baci da kasa tawuce tafita daga bayin ta shiga store kitchen tabiyo Aneesa ta tsaya abakin kofa tarike kugu tace "ni kika mara Aneesa? Wlh sainaga bayanki aduniyan nan zaki ga" cikin masifa sosai dan ranta abace itama Aneesa yake tawani buga bowl din dake hanunta akan table ta kalli Fatima tace "ga fili gamai doki ubanki kafasa, kin zaci ke kadai kika iya hauka ko, sainaci ubanki" tafinciki bowl din tai kofan da gudu inda Fatiman take tsaye da gudu Fatima tafice ganin Aneesa ta haukace mata tana haki Ashe Aneesa ta iya fada haka, tsayawa Aneesa tayi abakin kofa tarufe kofan da karfi tana masifa. "dakin tsaya kiga inban kakkarya kasusuwan jikin ki da kwanon nan ba, da wlh saina kwaba cake dinan da namomin jikin ki" taja tsaki ta tsugunna jikin kofan Aliyu nafado mata arai sosai sama da dama, takai kusan 1min a tsugunne kafin tamike tashare hawayen daya zubo mata ta mike tawuce ta debo flour, kana ganin yanda take aikin kasan ranta abace yake.
Wuraren five na yamma yatashi daga baccin da tsananin ciwon kai, ahankali yabude ido ya yaye bargon da Dady yarufe shi dashi hanunshi dayaji yamai tsami ya kalla yaga an shafamai mai, dan murmushi yayi dan yasan aikin Dady ne ahankali yatashi ya zauna yana kallon wayarshi dake kusada side lamp ijiye, kafe wayar yayi da ido yanaji kaman yadauka yakira Aneesa, kawad da kanshi yayi da sauri daga kallon wayan yamike tsaye ahankali yana yatsine fuska yana tafiya ahankali, bathroom ya shiga yadauro alwala yafito, dadduma ya shimfida yay salla yadade kan dadduma yay shiru yana kallon wayar ahankali yamike tsaye ya linke dadduman yawuce yafita, abinci ya ganni kan dining ko kadan baijin cin komi, kitchen dinshi yawuce yabude fridge sliced fruits dinshi dasukai sanyi sosai ya kalla su yakeso yaci but baida karfin ci baida apatite, cup yadauka yadauko yogurt ya zuba farm fresh strawberry flavour yacika cup yamaida sauran fridge yafito yazauna kan dogon kujera yana kallon tashan kwallon dake aiki yakai cup din baki yana kurban yogurt din sanyin yogurt din na sanyaya mai wuya hakan yasa yasake relaxing tareda lumshe ido, fuskar Aneesa yagani tanamai murmushi.
[08/03, 07:28] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
1️⃣7️⃣
_how to subscribe_
_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting. Zaki iya turo katin MTN na dari uku ta watsap number na for those of you dabasu da account*_
_littafinan na kudine duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafe mata ba, nabarta da Allah_
Tawani rike kugu cikeda masifa tace "ban fadamiki kifita harkan Yusuf dinaba ba, Aneesa banson shishigi kije kinemi saurayin ki mana saikinmin snatching" hararanta Aneesa tayi kafin taja tsaki tabi ta gefenta tawuce ta shiga cikin shago abinta so take tai sauri tai baking snacks sabida dazaran madam tazo tabarta tayi, bakery ta shiga tadau rigan aikin ta ta daura kan rigan jikinta tadau mini hijab din tasaka sanan tafara aiki, shigowa bakery Fatima tayi ta tsaya a bayan Aneesa tace "nike miki magana zaki wuce kiyi gaba abinki?" ajiye whisk din dake hanunta Aneesa tayi ta kalli Fatiman tace "Fati wlh idan baki fita daga harkana ba zan miki mugun jina jina, saurayin ki Yusuf babu abinda zanyi dashi ko shine namijin karshen duniya kifita daga harkana nagaya miki" itama ihu Fatima tayi tana mata tafi aka tace "eh, eh, kema kifita daga harkana ihu mayyar saurayi, saurayi snatcher" Aneesa zatai magana taji wayanta na kara da sauri tai wajen jakan ta tabar Fatima na surutan ta, ciro wayar tayi daga jaka ganin Aliyu ne yasa bata dauka ba ta maida ta ijiye tareda jan dan karamin tsaki tawuce ta koma ta shiga buga egg dinta da whisk bata kara cema Fatima komiba harta gaji da bala'in tafita daga wurin, cakes tafara hadawa tasaka a oven sanan ta shiga yin dough nasu chicken pie. Wuraren sha daya ta gama bakin almost 100psc tai recording ta dauko tafito takawo ma Fatima agaban kanta takoma tafito da sauran sanan tawuce backyard ta wanko hanunta da kafarta sanan tafio tanaji wayanta na ringing tasan Aliyu ne yasa batama bi takan wayan ba tawuce tafita tai sama tawuce office din Madam, knocking tayi aka bata izinin shiga bude kofan tayi ahankali ta shiga Madam ta dago daga rubutun datake ta tsareta da ido tace "Anesh na you" gyadamata kai Aneesa tayi tace "good morning ma" ajiye biron Madam tayi tana dauko wani paper tana dubawa tace "morning, why are you here? Menene yakare a store dama naga sugar yay kasa da corn flour, menene babu?" dan sosa gefen fuskarta tayi dan dagajin yanda Madam ke magana tadauka wani abune babu tazo fada, mayar da kanta kasa tayi tana wasa da yatsunta ahankali tace "Ma, ummm dama, dama sonake naje nai registration din jamb nariga nagama baking shine nazo daukan permission dinki naje yanzun nan nadawo saina cigaba da komi" nan da nan dan annurin dake kan fuskar madam ya bace tace "dole saikinje yaune?" dan rage murya tayi tace "Baban mu yace naje yau" wani kallo Madam tamata tace "baban ku?" gyadamata kai tayi tace "eh kanin baban mu" dan tsaki Madam tayi tace "ince dan nasan babban ku yamutu, kinyi baking abinda zai isa" da sauri ta gyadakai tace "eh bazan wani dadeba tunda rana batayiba lokacin ne ake cika wurin yanzun nan zan dawo" tsaki madam takaraja dan ko kadan bata so ta tafi tace "okay nabaki 2hrs,yanzu is eleven by 1 ko highest 1: 30 kodawo kobaki gamaba dan I can't stand loosing customers due to your negligence again yau" gyada mata kai tayi da sauri ta tsaya tana jiran tabata izinin fita, buga taburin madam tayi tace "bazaki wuceba bakisan time dinki kikeci ba" da sauri tajuya tafita daga office din tawuce kasa ta shiga rigan aikin da hijab din tacire tadau dogon hijabinta tasaka sanan tadau wayarta dake kan saman jaka tana dubawa 20miss calls datagani yasa tace "20" bude wayan tayi da sauri ta shiga gabaki daya 20 miss calls din duka na Aliyu ne, maida wayan tayi cikin jaka tace "to menene yaketa kirana haka" dan murmushi tayi taunawa da yace she's his friend tawuce tafita daga dakin tace zan kiraka anjima inmun koma gida, Fatima nata kallonta kaman zata hadiyeta wajen kofa tayi da sauri Yusuf yabude mata yana kallon fuskarta yace "ina zaki Aneesa?" batare data kalleshi ba tace "inda ka aikeni" tayi wucewarta, binta da kallo yayi yarike baki dama Aneesa bata da kunya? Yatambayi kanshi kwafa yayi dan duk Fatima ce taja Aneesa dake bala'in girmamashi ta raina shi haka.
Keke napep ta tare tace "Suleja ICT center zaka kaini malam" "hamsin, hau muje" hawa tayi dan batason tsayawa ciniki da masu abin hawa har gaban ICT center taje taga students dayawa duk yan registration din jamb, kudin tabiyashi ta wuce ta shiga ciki wayarta dake cikin jaka sai ringing yake.
Ciki ta shiga ko ina dalibai da kyar tasamu taje gaban kanta daya daga cikin ma'aikatan ta gaida tace "malam dan Allah nazo registration ne yaya zanyi?" zufan daya cika goshin shi ya goge dan wajen is so crowdy dudda akwai manya manyan fankoki amma kaman bakomi wani takarda ya nunamata yace "keji ki rubuta sunan ki, za'ayi ta kiranku according to numbers ne" gyadamai kai tayi tace "nagode" tawuce da sauri wajen paper dataga wasu dalibai na rubuta sunansu tsayawa tayi abayansu suka gama sawa sanan taciro byro daga jakanta ta matsa tareda daukan paper number 178 anan zata sa suna, kambu mutane har nawa agabanta itada awa biyu madam tabata sunanta tarubuta kaman wacce ke tsoron paper duk tunani ya kasheta. "Fateema Rufa'i Mai Kwato!" da sauri ta daga kanta jin ankira full name dinta ware ido tayi ganin wani malamin su daya koyar da ita tun daga SS1 a makaranta har zuwa SS3, shine malamin further mathematics dinsu, Malam Auwal Mazimaziz haka yan makaranta suka radamai ko maganan shi ake idan kace Malam Auwal baza'a taba ganewa ba saidai kace Mazimaziz kokuma kace dy/dx daga wani bene taga yake saukowa rikeda wasu takardu da yawa a hanunshi yana kallonta dogon namiji ne handsome black dashi yana sanye dawata faran yadi kanshi da hula yana kallonta murmushi tayi sosai tana kallonshi harya karaso mutumin data tambaya dazu yaje wurinshi yabashi takardun sanan yakaraso ta inda take akunyace tace "good morning Malam" murmushi yayi shima yace "good morning Fateema" murmushi tayi tace "Malam dama kananan" dan hararanta yayi yace "look at you tunda kukai waec da Neco muka sallameku kin kara waiwayan school kizo kidubamu ne? Inda kinzo aida kin gani ai mara zumunci kawai" a kunyace tarufe fuskar ta da Hijabi ita tai mamaki ma dayake mata fara'a haka Mazimaziz ai shine the most wicked Teacher a makarantan su, ko sajent saiya sallama mishi a iya duka, gashi ko test dinshi kafadi saiyay duka sunci dukanshi a makaranta kaman ba gobe. "jamb kikazo siya?" tambayar dayayi ya katse mata dan tunanin dataje da sauri ta gyada kai tace "eh nazo ai registration amma mutane nice number one hundred and seventy something" dan murmushi yayi yana zama akan kujeran gaban kantan yace "banda abinki ai da sassafe ake zuwa dan dalibai nada mugun yawa anan" dan zaro ido tayi kaman zatai kuka tace "bansani ba ne wlh" dan shiru yayi yana kallon fuskarta yanda tai kaman zatai kuka tana kallon wajen yanda aka cika ko ina. "Fateema" da sauri ta juyo ta kallai mikewa tsaye yayi yace "lemme see you off, kizo gobe da sassafe as early as seven zansa wani yay miki, ko yanzu ma aiki yamai yawane danasa yay miki but kizo gobe as early as seven fa kina jina" gyadamai kai tayi tana binshi abaya suna kukustawa dan fita daga wurin tace "okay sir" fitowa sukayi tana biyeda shi wani irin mummunan faduwa gabanta yayi Aliyu tagani tsaye yana sanye da jeans black dawani sky blue shirt yadan bude boturin kirjinshi idanunshi sanye da bakin glass ya rungume hannunshi a kirji dayake rikeda wayarshi Samsung galaxy fold, yana facing cafe din, yan matan premises din Cafe sai kallonshi suke dan yay bala'in yin kyau kaman bature, da sauri ta dauke kai daga kallonshi kirjinta na dukan uku uku ya akayi yasan tana nan? Ya akayi yabiyota? da sauri zuciyata yace a'a bake yabiyoba hala yakawo wanan kanwar tashine itama tai registration din jamb bake yabiyoba, dan ajiyan zuciya ta sauke. "Fateema kinajina kuwa?" Malam Auwal yamata tambayan da sauri ta dago kai ta kalleshi tace "sorry sa banji mekace ba" dan murmushi yayi yace "hayaniyan dalibai ne yay yawa but gobe idan kinzo ina jiran amsan kinji" da sauri tace "amsan mene malam?" dan shiru yayi yana mata wani kallon daza'a iya kirada naso yace "Fateema, tunda kikabar school I've been looking day and night for a way dazan hadu dake, from the first time dana taba shigowa ajinku a SS1 dan daukan ku further Maths Allah ya jarabceni da sonki Fateema, na yaba da natsuwanki ainun, kinada baiwa daba kowane zai iya sanin hakan ba, burin kowani kamilin namiji shine yasamu mace irinki a matsayin mata ya killaceta a gida a binshi babu mai ganin mai ita, tundaga SS1 nake rainon sonki har zuwa yau saisa kikaga nafi tsananta miki a aji kan kowa, in duka ne kece tafarko kuma alhamdulillah ina alfahari dan kin kasance daya daga cikin dalibai na dasuka fi kowa iya further maths a makarantan nan" tunda yafara ambato kalaman son nan ta saukar da kanta kasa dan wani kunya ma taji yabata aranta tace kagamin mugu yagama cin uban nawa a makaranta ne yanzu kuma yake sona. "Fateema" da sauri tadago kanta ta kallai tareda dan kakalo mai murmushi yace "bakice komiba" rasa mezata ce tayi sotake ta kalli inda Aliyu yake kuma har wani shakkun kallan wajen take zatai magana yadanyi dariya yace "don't worry nagane nagane, bani wayanki kiga nasa number na" rasa yanda zatayi tayi hakan yasa tazamo jakanta daga kafada ahankali ta zage zip din jakar tana kokarin ciro wayar kokadan batason ta bashi number kuma tarasa yanda zatayi, wayar taciro tadago kai ta kallai yanda yasakin mata murmushi yasa tadanyi mai murmushin yake tamikamai wayan ahankali.
Tunda yake baitaba undergoing wat he's going through a tsayen nanba ganin yanda Aneesa takema wani kato murmushi yasa yaji zuciyar shi tamai wani irin masifar daci, internally jikinshi ke rawa ganin tadauko waya ta mikamai yasa taji wani zuciyan dabaita bajin irinshi ba yataso azuciye ya shigo cikin premises din cafe ya dumfaro su.
_*duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafeba, in kinason book dinan ki tuntubeni ta WhatsApp number na kaman haka 07012181461*_
[10/03, 07:28] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
2️⃣0️⃣ & 2️⃣1️⃣
_How to subscribe_
_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din danake posting. Zaki iya turo katin MTN na 300 for those dabasu da bank*_
_Today is the DAY!!! I must give you my sincere, warm and outstanding shout out to my VIP group, you people are not just Very Important people you guys are my