Showing 15001 words to 18000 words out of 186400 words

Chapter 6 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt

20 Jan 2025

18797

mai kofar da gudu almajirin yafita yana tsalle yana kara kallon tulin kudin da tunda yake baitaba ganin kowani a gidansu yarike irinsu ba, tada motar yayi yana tafiya yana sake trying number data kirashi dashi baya shiga sanan yana kiran asalin number ta shima baya shiga, sosai yashiga cikin tsananin damuwa ahankali yake tuki a dogon layin da baya ma ganin jama'a ciki, harya shanye layin shi baiga kowaba hakan yasa yasake yo kwana yajuyo tundaga nesa yake hango gyalen Raudan daya gyara mata dazu dasafe da kanshi akasa kan wani dutse iska na karkadashi, tun kafin ya iso wajen da gyalen yake yay parking baima tsaya rufe motar da kyauba yataho dasauri tsugunnawa yayi yadau gyalen ahankali yana kara kallon gyalen this is definitely gyalen Rauda, sake bugawa kirjinshi yayi wats happening to my sister ya tambayi kanshi, rike gyalen gam yayi Yajuya yana kalle kallen gidajen kan hanyar yaciro waya yana kokarin kiran Dad.....








Jan Raudan yayi da batada karfi ko digi ajiki har yanzu jin kennenta take dummm kaman banata ba Aneesa da jikinta yafara rawa sosai ganin yanda yawani irin daure fuska tasaki wani irin wawan ihu. "Ammiiiiiii! Wayyo Allah n..." buge bakinta yayi azuciye yace "yau zakici uwarki, gwara wanan" yanuna Rauda dake sauke ajiyan zuciya kawai yace "su sunsan inda zasu ganni a duniyan nan , keko baki sanni ba, daga yau baki kara haduwa dani, shiga shara ba shanu banga uban abinda zai hanani yimiki fata fataba dama daga ganinki zakiyi man shanu" ya jasu duka biyun kaman raguna yay hanyar kofar dakin zai shigar dasu, Aneesa sai tutturjewa take, wani irin bugo Gate din da akayi da karfin bala'i yasa dukansu ukun suka waigo, ido da ido Khamis yay da Aliyu dake sanye cikin wani Milk wagambarin shadda da aka mishi dinkin fitted yaji aikin hannu, yasa takalmi irin na yan gidan sarauta dinan kanshi babu hula sai bakin gashin kanshi dake masifar kyalli kaman ya shafa man gashi, idanunshi sanye cikin dark shade abinda yaboye jan da idanunshi sukayi kenan tsabagen yanda ranshi yakai ga baci, yana tsaye wajen Gate amma saida kamshin turarenshi yakai har inda suke gaban kofa ko ina yadau kamshin shi, ganin Aliyun yasa wani irin karfi yazoma Rauda tawani irin fizge hannunta daga rikon da Khamis yamata ta tashi tsaye tazo da gudu tafada jikin Aliyu tasaki kuka sosai takasa magana, ganin haka yasa Aneesa ma da gabanta ke faduwa bana wasaba ta fizge hijabin ta da Khamis yarike ta taho da saurinta gefensu Aliyun ta tsaya kirjinta na bugawa kaman zai tsage, dan wayancewa Khamis yayi yakakalo murmushi yatako ahankali yana dumfaro su da sauri Rauda tasaki Aliyu takoma bayanshi ta labe tana kuka hakan yasa Khamis ya tsaya chak a tsakar gidan yakasa karasowa gabansu, hannu Aliyu yasa yazare dark shade din dake idanunshi ya zubama Khamis jajayen idanunshi dayasa yaji internal organs dinshi na girgiza cikin wani Husky harsh voice yace "how dare you raise those your filty hands on my sister, how dare you touch her" hausawa sunce tabarman kunya da hauka ake nannade ta, cikeda borin kunya shi adole shi shine yace "who is your sister? Raudan ce sister ka?" ya tambayi Aliyu cikeda kallon isgilanci yace "as far as am concern and base on wat I know ko mahaifiyar ta tacha cewa kai ba wan yaranta bane, you guys are not blood related, bama tasan da zamanka ba, kuma mahaifiyarta tabani izini na dauketa nakaita yawon ido karmu dawo sai dare gatanan u can ask her and hear for yourself, banda hakama who do you think you are to talk to me in such manner nafika matsayi da iko akan Rauda, am her Mum's elder sisters first son, and her husband to be, ko ubanka yasan da hakan so back off please, ke Rauda let's go" yay maganan yana tahowa yazohar gaban Aliyun yasa hannu zai jawo Raudan cikin wani irin fushi Aliyu ya kwasheshi da mahaukacin mari. "Tau!" da sauri Aliyu yarike hanunshi sabida zafin da hanunshi yadauka ya murza hanun kaman zaiyi kuka yace "aauchhhh" yana yarfe hannun, yanda yayi saida yasa Khamis fashewa da mugun dariya dudda marin ta shigeshi dan har gefen fuskar da Aliyun ya mara yay ja abunku da fari, da yatsa ya nuna Aliyun dake yarfe hannu yana yatsine fuska yace "wanan ne, wanan ajebotan kuka kira yay protecting naku daga ni? wanan malalacin namijin daya rako maza duniya wanan maza matan dayamafi mace yauki kaman kubewa ne kuka tunanin can beat me up?" hannu yakai yafara bude boturan gaban shaddan riganshi yace "zan nunama u have messed with the wrong guy ni haifaffen dan kwari ne ba girman turai ba, girman tasha, kar har purewater na saida a park" fashewa da kuka Rauda tayi dan tasan Ya Aliyu bai iya fadaba ko kadan ta jijjigashi tace "Ya Aliyu mugudu please" itama Aneesan jikinta rawa yafara ganin Khamis cikakken dan tasha ne kam yana magana kaman dan wiwi, riganshi ya zare ya yar akasa ya matso gaban Aliyu ahaukace yasa duka hannayenshi ya daki kirjin Aliyu da saida yay baya kaman zai fadi yace "kai ubanka yaci ubanka kaji, dan babar ka nataba kanwar taka uban me zaka iya? Eh nace ubanme zaka iya?" Khamis yay maganan kaman dan daba yana hura hanci, Aliyu ya kafeshi da ido he really do not know how tayaya ma zai fara fighting dinshi ba, indako yasani daya kusan kashe yaron nan, cikin kuri yay pointing Aliyun da yatsa yana murmushi ya kalli Aneesa da Raudan dasukai zuru zurun barinma Rauda dake kuka wiwi za'a dakinmata yayanta yace "do you all see what am saying, bakazo shigarma kanwarka dat I was trying to rape bane? Then beat me up now Aliyu, are you scared Mama boy? Beat me mana, kawa Allah ka dakan, baku ganiba matsoraci bane, kai" ya dungure ma Aliyun goshi da yatsa Aliyu yasakeyin baya, Khamis ya nunamai yatsar shi ta tsakiya yace "f**k you Aliyu, I said f**k you mezaka iya? Daken mana kaji tsoro ne eh? Eh malalaci?" yanda yakema Aliyun daya tsaya kikam yana kallonshi tijara yamugun sosa ran Aneesa saitaji kaman tai kuka dan daga ganin yanda Aliyu ya mareshi da farko ya shiga yarfe hannu zaka gane baida karfi kona sisi, kallon yanda Rauda ke kuka sosai abayanshi take alamun batada hope zai musu dukan tsiya sanan yama yayan nata dukan tsiya shima hakan yasa taji wani karfi yazo mata da bata taba jin irin that kind boldness ba in her life, cikin wani irin izza ta shiga gaban Aliyu tana taku dai dai tana clapping hands dinta cikin isa da takama tana clapping din tana kallon fuskan Khamis din dake kallonta kaman yanzu yafara ganinta, tsayar da tafin tayi tace "kasan mesa nake tafa maka?" tai wani murmushi ganin baice komiba kawai kallonta yake kaman wani wawa tace "wani zubin idan kare na haushi idan kai tafi saikaga yadan natsu" cikin fada yace "nikike cema kare?" cikin dakewa ta nunamai yatsa tace "quit, am still talking" samun kanshi yayi dayin gum ganin yar yarinya namai magana kaman uwarshi, tace "what differentiate human being da animals is ability to think and reason which bakada duka biyun you are just a dog malam which yayan mu bazai taba iya biyema yadawo kaman kaiba ko?" tadan juyo for the first time ta kalleshi idanunshi da nata suka sarke faduwa sosai gabanta yayi tadan kyafkyafta ido sau biyu pink lips dinta sukadanyi rawa ahankali tace "ko?" gyadamata kai Aliyu yayi batare dayasan yamayi ba, juyar da kanta tayi tace "kai mailafine bagaremu ba kadai har agun Allah, sanan kanada bakin zage zage kana turashi kanaso yabiye maka kuyi fada, wai intambayeka man do you know who is a Man?" wani matsiyacin kallo tamai ganin yanda yasaki baki yana kallonta tace "A Man baya tsayawa yay physical fight da kowa dan physical fight dangrades one's level, banda haka a Man is someone who has control over his heart ayayin dayake cikin tsananin fushi which is abinda yayi yanzu, kazaci kana ihu kana cika kana batsewa kana tunanin by d time dayake so yaci ubanka you can match his level ne eh?" tamai tambayan tana hura hanci daya kaman wata boss tana kallonshi, dan murmushi Aliyu yasaki for the first time ya rungume hannayenshi a kirji, ganin har lokacin Khamis din baice komiba ya tsaya yana mamakin tane yasa tace "and yanzun nan zan nunamaka idan yatashi yace zai ci uban naka u can never match his level of power, kwabaka zaiyi kaman yanda ake kwaba dibila tsaya kagani" tai maganan tana tsugunna wa a wurin duk suka bita da kallo kasan dake bakin Gate din ta kwasa da hannunta dayawa batare da duksun luraba dan hijabinta yarufe mata hannu sundaiga ta tsugunna mikewa tsaye tayi Khamis din nabinta da kallo hannunta tadaga un expectedly ta watsamai kasan a fuska aiko suka shiga idanunshi biyu, ihu yayi. "wayyo Allah na, wash Allah idanuna, sainaci durun uwarki yarinyar nan" yayo kanta yana sosa idanunshi dayakasa budesu tsabagen kasan data sakamai a ciki matsawa gefe tayi da gudu ta kalli Ya Aliyu dake binta da kallo tace "Yayan mu yimai shegen duka ramama kanwarka abinda yamata bazai iya ramawa ba idanunshi cike suke da kasa" ware manyan idanunshi Aliyu yayi yana kallon this wired girl, gyadamai kai tayi da sauri tace "ka zaneshi, daddaki azzalumin" jin daga ta inda take magana yasa Khamis yay wurin yana murza ido yace "dan uwarki ubanwa yace miki koni makahone zai iya tabani ne wanan ragon" dawowa tayi kusada Aliyun ta kallai tace "yimai lilis u can do it, zo zan nuna maka inda zaka dinga duka ajikinshi zokaga" tai gaban Khamis din dake bubbude kafa yana sosa idanu kaman mahaukaci tsabagen azaban kasan dake cikin idon, ta nunama Aliyu cikin shi daya fara dan tara teba dama babu riga ajikinshi tace "zoka naushi nan" turashi Rauda tayi tace "muci ubanshi Ya Aliyu ka rama mana" ahankali Aliyu yadaga kafa yana kallon Aneesa dake nunamai cikin Khamis kaman wawa yakaraso kusada inda take yana kallonta still, zare ido tayi tsabagen jin dadi zasuci ubanshi tarage murya kaman mai shirin gulma tace "yauwa naushi nan".














Tanunamai gefen cikin Khamis, farin hanunshi Aliyu ya kalla ya dunkule ahankali yana kallon Aneesan data cije lebe irin ya dunkule hanunnan da kyau dinan tana kallon hannun tana nunamai cikin Khamis din dake sosa ido, daddagewa Aliyu yayi yabugama Khamis uban nishi aciki atare daga Aliyun har Khamis din sukai ihu harsaida Aneesan takoma baya da gudu dan tsoro sabida ihun da Aliyu yayi yana yarfe hannu kaman zaiyi kuka ya kalleta yace "it's hurt, ahhhh, aucchhhh, alottt" sosai yake yarfe hannu hakan yasa ta matso ahankali tana leken Khamis din daya zube akasa dan naushin ya shigeshi gashi yakasa bude ido balle yarama, tsayawa kusada Aliyun tayi dake yarfe hannun nashi dayay jajir tasaka yatsa abaki tana cija danso take suci uban Khamis sosai, kalle kallen compound din ta shiga yi kafin idanunta su sauka kan rigan Khamis din dayacire ya yar da sauri tai wurin rigan tsugunnawa tayi ta dauka ta shiga wurga rigan tana kaman lilo dashi rigan ya shiga kanannadewa danso take tamaida rigan dorina, binta da kallo Aliyu yake yana murza hanunshi harsaida tagama tazo gabanshi da sauri ta mikamai dorinar rigan tace "gashi yayan mu, rama mana da wanan tunda baka iya fadaba, yimai shegen duka da wanan" tamikamai rigan, karban rigan yayi yana kallon fuskarta, nunamai Khamis din tayi tace "zaneshi karka ragamai, ko akotu irinsu bulala tamanin ake musu kaima yimai 80" da sauri ya kalleta yace "80?" kallonshi tayi akaro nabiyu idanunsu yakara sarkewa faduwa gabanta yayi hakan yasa ta kyafkyafta ido sau biyu ta gyadamai kai batare data iya magana ba ta kawad dakanta, ahankali Aliyu yakarasa inda Khamis din yake azube yana sosa ido ya daddage ya shaudamai ihu yayi. "Aliyu wlh idan idanuna suka bude saina kasheka dagakai har shegiyan na..." zubamai nabiyu Aliyu yayi da karfi hakan yasa Rauda ta rungume Aneesa cikeda murna suka shiga tsalle kaman sunsan juna Aneesa harda tafi wani masifar dadi takeji fiye da tunanin mutum, cigaba da dukanshi Aliyu yayi da rigan sunamai tafi itada Rauda harya yarda rigan ya zauna agefe yana haki yagaji, da sauri ta kalli Rauda tace "ina zuwa bari kuga" da sauri tabude gate tafita jakanta tabude ta ciro wani kwababben bakin lalle da mai saida lallenta yahada mata as sample dan kafin tasiya saitasa ya dama mata tadanyi Zane kadan a hannunta ta wanke dan taga iya bakinshi dan kwanaki tasai lalle ko kadan baya baki dudda hydrogen din datake zubamai, shigowa tayi da sauri rike da ledan lallin ta kalli Aliyu tace "Yayan mu daga shi ka zaunar dashi kaga" kasa mata musu Aliyu yayi Yajuya yadago Khamis din da karfi ya zaunar dashi, tace "yauwa rikemin hanunshi tabaya" tsayawa abayanshi Aliyu yayi yarike hanunshi gam, da kyar Khamis dabaya iya bude ido ke magana yace "wlh duk kun shiga uku koba yauba yau ranan kuc...." bai karasa maganan ba Rauda tazare flat shoe kafarta tai bugamai abaki aiko sai jini, dariya sosai Aneesa tayi dayasa dimples dinta lotsawa tana kallon Raudan tace "dama kinada karfin nan tuntuni kiketamai kuka matsoraciya" takarashe maganan tana dariya sosai kafeta da ido Aliyu yayi ko kyafta ido bayayi kaman ance ta kalli gabanta suka kara hada ido shiru tayi ta saukar da idanunta kasa tadan matsa gaban Khamis din sosai kirjinta na bugawa tana gyara bakin ledan lallen, ahankali ta shiga zanamai bullen mage tundaga gefen bakinshi har zuwa wajen sajenshi uku uku sanan taja wani dogon layi tundaga kan hancinshi har zuwa goshinshi shidai Khamis sanyi sanyi da waiwayi waiwayi yakeji akan fuskarshi amma yarasa me akemai, fashewa da dariya sosai Rauda tayi ganin abinda Aneesa tamai harda bubbuga kafa akasa kaman ba itace tagama kukaba da barkakken riganta, mikewa tsaye Aneesan tayi itama tana kallon fuskanshi ta harari Rauda cikeda murmushi tace "am happy you are now smiling nidai nagudu gida, you guys should run for your lives, kugudu kafin idanunshi subude" ta kwasa da gudu tabude Gate tafita da sauri Rauda tabita tana kwala mata kira tace "baiwar Allah, baiwar Allah baki fadamin sunanki ba to" juyowa Aneesa dake kwashe kayanta nakasa awajen Gate din tayi ta kalli Raudan tai murmushi tareda rataya jakanta akafada tace "sunana Nana Fateema" "can we be friends? Inason ki sosai you are so bold wat a fearless lady, a ina kike? Inane gidan ku? Anan Suleja kike?" Rauda tai maganan tana karasowa gabanta murmushi tasakeyi zatai magana idanunta suka sarke dana Aliyu dake tsaye jikin Gate yazuba mata idanu hanunshi zube a aljihun riganshi yana kallonta sosai gabanta yafadi, dan kyafkyafta ido tayi tana kallonshi kafin ta juya da sauri tama Rauda waving hannu tace "bye Friend" daidai lokacin keke napep na zuwa tareshi tayi ta shiga ciki sukai gaba dukansu tsayawa sukayi a inda suke sukabi keke napep din da kallo har yafita daga layin.
[04/03, 16:28] Aishat Muhammad: [11/02, 05:11] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






9️⃣




_How to subscribe_


_*Zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting*_




_*zaki iya turo katin MTN 300 in baki da banki ta watsap number na 07012181461, sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya*_














For a moment harta manta da matsalan datake ciki dasuke magana da Aneesa not until lokacin da keken data shiga ya bacema ganinta, juyowa tayi ahankali hada ido sukayi da Aliyun dayamata wani irin mugun kallo da baitaba mata irinshi ba kafin yafito daga cikin gidan yay wurin motarshi da sauri tabishi bude mota yayi ya shiga hakan yasa tabude dayan side din ta shiga tana kallonshi batada burin daya wuce yacemata wani abu amma saibaice ba, kunna mota yayi batare dayace mata komiba hannayenshi duk ciwo sukemai yaja motar, sosai taji jikinta yawani irin mugunyin sanyi hakan yasa ta saukar da kanta kasa gabanta sai faduwa yake, da azababben gudu yakejan motar Haryakai kai gidansu uppan baice mataba wani mahaukacin horn yadanna daya daga cikin sojojin gaban Gate yazo yabude musu Gate din yaja motar cikin gidan a tsakar gida yaga Dad sai zirga zirga yake yana sanye da jallabiya mai ruwan goro dayake yau weekend baifitaba yana gida, ganin motar Aliyu yasa tun kafin motar yay parkin yay wurin motar, daidai Aliyu yay Parking yabude motan yafito ranshi abace, tsareshi Dad yayi yadaura duka hannayenshi akan kafadarshi yana nazarin fuskanshi cikeda tashin hankali yace "Son kakirani kana cewa menene menene, banma gane mekake cewaba sai kuma ka katse wayan, were you attack? Nasaka bodyguard bin bayanka gashinan kuma kadawo, wat happen to you Gadanga na iyye? Ya akayi idanun ka sukaija hakk...?" kasa karasa maganan yayi sabida sauka da idanunshi sukayi kan hanun Aliyu, yanda yaga hanun Aliyun yay jajir kaman ya kone da ruwan zafi yasa da sauri yasaki kafadar Aliyun yakamo hanun yarike arude yana kallo yace "wat happen to your hand Son? Maiya sameka, talk to me Aliyu? Me haka hanunka yay jajir where you attack?" Dad yay maganan kaman zaiyi kuka dukya birkice, ganin yanda Dad din ya rude yasa yadan yatsine fuska tareda fizge hanunshi yace "am fine Dad don't worry am fine" yay maganan yana bin gefen Dad yay dayan side din motar, Dad yabishi dasauri yace "don't tell me you are fine Aliyu, mai ya sameka idanunka sukai ja haka hanunka yay ja shi...."cikin fushi yabude kofar motar, lekowa Dad daya biyo bayan Aliyun yana tambayanshi maiya sameshi yayi ganin Rauda zaune kan kujeran gaban motan rigan ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login