Showing 120001 words to 123000 words out of 186400 words
Chapter 41 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt
sunsan hakan but bazasu taba iyayin abinda Kareema tayiba, basu tabamai tunanin kisa ba ko wani abu makamancin hakan, burin su kawai su kuntata mai, su ganshi cikin kunci koda yaushe, suga shida Alhaji na fada always shikenan kawai nasu, Maman su Rauda ta dauko da zafi.
Ganin yanda Dady yakasa motsi sai kiran sunayen Allah dayake yi yasa officer yamiko hannu yakarbi ipad din yamikama police din kusada shi tareda jan hannun Dady yadagoshi yamike tsaye, officer yay dan murmushi yace "for the first time ashekaru ashirin da shidda danake aikin dan sanda nan, ayau danka yanuna mini ban iya aikinaba, sanan bansan kan aikinaba kuma na yarda dashi dari bisa dari, video kawai muka kalla mukai arresting baiwar Allah nan batare damun tsananta bincike ba, bayan munsan babu abinda technology ba yayi, babu abinda ba'a amfani da technology mu nayau ayi, visuals can be deceptive, ana manipulating time and everything a video, bayan ga asalin criminal din nan tana tareda kai mukai arresting yarinya" yay pointing Maman su Rauda da ta shiga girgixa mai kai, tace "wlh shairi akemin Alhaji karka yarda dasu, shairi akemin, hala matar chan kudi tabaku tasa kuyi haka ko" tai pointing Ammi dake zaune abakin kofar ta har lokacin tana kuka sosai, tace "nasan wlh shairi akemin, Alhaji karka yarda shairi akemin wallah......" wani mahaukacin mari Dady ya kifamata yasa takasa magana, cikin daga murya Dady yace "kinsan kuskuren dakikasa na tafka kuwa Kareema?" yasake kaimata wani marin yace "kinsan alhakin dakika sa yahau wuyana, kinsan kuskuren dakika sa nayi kuwa? Kinsan yanda na zalunci marainiyar Allah yarinyar datake kallona amatsayin mahaifinta wacce da babu ita da mahaifiyarta bata yarda ta auren ba, ita tasa mahaifiyarta tasoni, do you even have any idea abinda kikasa nayi kuwan? Wanan wani irin kalan makirci ne iyye?" dukanta ya shiga yi sosai kaman yasami jaka, cikin fushi da ihu, da zuciya yace "nasake ki saki daya, na sake ki saki biyu, na sake ki saki uku, nai nadaman, nai dana sanin saninki arayuwata harya kaini ga aurenki, nai nadaman aurena dake, wlh ban yafe miki ba, banyafe mikiba duniya walahira Kareema" rikeshi Officer yayi ganin yanda yafasa mata baki yace "calm down Sir" ya warware ankwan dayake jikinshi ya nunama Maman Rauda yace "Madam! You are under arrest for attempt murder, shairi dakuma batama Aneesa suna sanan da sawa dakikayi akai arresting nata ta hanyar framing dinta, you have the right to remain silent inba hakaba kome kikace will be used against you in the court of law" fashewa da kuka Maman Rauda tayi tana kallon Dady dawasu irin idanu da baisanta dasuba tace "na tsani Aliyu da duka zuciyata, na tsaneshi da duka rayuwata , na tsaneshi da dukannin numfashin danake fitarwa da shaka a kullum, kuma kaikaja, kafifita yaron nan kan kowa kaman yaron gwal saisa naso na kashe shi dan inga yanda zaka rayu babu shi, idan zuwa zaka dingayi kabarinshi kana kwana dashi kokuma zaka bishi kabarin abinne ku tarene, kuma bari kaji ko yau, ko gobe, ko jibi, ko gata nasami daman kashe Aliyu saina kashe shi in kashe banza, harbi dai ko rataya ce makomata ko? To saime akaina aka fara mutuwa, ko banza nadai kashe abin sonka, danka namiji" dagokai Rauda tayi da tunda aka fara abun kanta nakasa tana kuka ta kalli Mahaifitar tata, kallonta Mama tayi daidai officer yafara janta tace "eh nafada, kalleni da kyau, kedama matsiyaciya ce kina kallona da shegun idanunki masu kama dana mayun daji, Hajar ce kadai kesona daman" ta kalli sauran matayen Dady tace "kunji dadi yanzu yan bakin ciki? Kumadai naga bason Aliyun kukeba dan haka ahada harda ku duka akaimu chaji opis din" daidai officer yakaita gaban motan su, polisawan suka shishiga aka tada mota, officer yabude bayan tashi motar zai sata aciki, wani irin fizge kanta Maman Rauda tayi da gudu tadau babban scissors din cutting flowers da gardener gidansu ke amfani dashi da tundazu take harinshi tai kan Aliyu, Rauda ce tafara lura da ita officer yabita da gudu yace "ke, Ke, Alhaji" ya kwalama Dady kira ya dago kai afirgice dan yay nisa atunani, daidai Aliyu shima yajuyo jin officer ya kwalama Dady kira dan Ammi dake kuka sosai yake kallo tundazu, daidai Mama ta jefo mai scissors din da hannu ganin officer ya fizgo ta ta hanyar janyo bayan riganta, Rauda tawani irin yin mugun tsalle ta rungume Aliyu with all her power, scissors din chak! Ya sauka akanta sai gefen bayanta ya bullo harta gaban cikinta ya yanki saman fatan cikin Aliyu slightly, abunka da sharp scissors na cutting plant sharp yay penetrating, wani irin ihu Dady yayi Ammi ma ta tashi azabure, sauran matayenshi ma haka, Hajar ma da kannin Raudan haka atare duk sukai ihu. "Raudaaaa!!!!"
[13/04, 09:06] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
5️⃣8️⃣
Wani irin zaro idanu Maman Rauda tayi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un Rauda!" takasa gasgata abinda idanuwanta ke gane mata.
Aliyu ko motsi kirki yakasa saima wani irin rike Raudan tsam dayayi ajikinshi yakara barinta yanajin yanda take wani irin nishi akunne shi, arude Dady ya shiga kiciniyar karbanta yace "Rauda, Rauda Gadanga bani ita kaga" fitowa sauran polisawan da sojojin sukayi aka tsaitsaya ana kallo ahankali Dady ya karbeta jini na fitowa ta gefen bakinta tana wani irin nishi, taushe baki da hannu Hajar tayi tana kuka sosai, arude Dady da hankalin shi ke gab da fita daga jikinshi yace "call the Dr Aliyu, call him" ya kalli Raudan datake wani irin nishi hawaye na fitowa daga idanunshi yace "stay with me kinji y'a, u will be fine okay, likita yanzun nan zaizo, yayanki zai kira Dr" yay maganan yana dagakai ya kalli Aliyun daya fitoda waya amman yama kasa tabawa tsabagen rudewa yakasa dena kallon Raudan yanda jini ke fita tawajen scissors din yanabin interlock din tsakar gidan, Dady zaiyi magana yaga Rauda tadaga hannunta ahankali tana rurrufe idanu ta mikama Aliyu wani irin zubewa Aliyu yayi kasa ya kama hannunta gam saiga hawaye sharr da sauri ta girgixa mai kai tana wani irin nishi da kyar tabude bakinta dake fitar jini sosai tace "no crying uh'uhn, be strong for me, be a very strong man Ya Aliyu, k.....kada...wo namiji, inaso kahada kan kowa na gidan nan let's our family be united, no more sluggishness ka...ji" da sauri Aliyu yadaga kai wasu hawayen nazubomai sosai, murmushi tadanyi cikin tsananin azaba ta lumshe ido ahankali tace "D....a..d" da sauri Dady daya daurata kan cinyarshi yace "na'am Rauda na" hannun Aliyu tasake rikewa da kyau tace "Ya Aliyu na son Aneesah ka auramai ita, Dady!" tasake kiranshi da sauri Dady da muryanshi ke rawa sosai yace "na'am Rauda" dan shiru tayi takasa magana saikuma tabude idanunta ta kalli Hajar dake tsaye tana kuka sosai tana kallonta, murmushi tamata ta kalli Aliyu dake rikeda hannun ta hawaye nabin idanunshi, murmushi tamai tace "in Aneesa ta haifi Baby girl zakasa sunana Ya Aliyu?" dawani irin sauri Aliyu ya gyadamata kai hawaye na gangarowa daga idanunshi ya matse hannunta yace "yes Rauda, I will name her princess Rauda, the best, the most sweetest and the most caring little sister in the world" murmushi tayi sosai da saida duka hakoranta dasuka hade suka bayyana, hannunta daya rike ta shiga kiciniyar kwacewa hakan yasa yasaki hannun yana kallonta ahankali takai hannun kan idanunshi ta lakato hawayen dayake yi tareda girgiza mai kai tace "daga yau no more shading tears, no more crying over any abu dake damunka, kome kakeso kome kedamunka ka tashi tsakar dare ka gayama Allah, show the world ba old Ya Aliyu bane, u are strong, u are a fighter, u are capable, I hate seeing you cry, karka kara kaji" hannunta dake kan fuskarshi ya damke wasu hawayen na shirin fitowa ya hannasu ya fuzar da iska heart dinshi nawani irin strengthen and getting tough, wani irin ajiyan zuciya ta sauke sanan tajuyo da kanta ahankali tazubama Maman ta da officer yarike gam ido, yanda take kallon Mama yasa jikin Mama ya shiga rawa saita saki wani irin mugun kuka tace "kiyafeni Rauda, dan girman Allah kiyafen, kiyakuri, nayi nadama, inda nasan kezan sama da banyi ba wlh" wani irin numfashi Rauda ta shigayi tarike hannun Ya Aliyu gam da sauri ya kalleta, numfashin ta shiga yi da sauri da sauri ta juyo ta kalli Aliyu tana wani irin nishi lips dinta na rawa da sauri Dady yace "call Dr Aliyu" arude Aliyu ya shiga neman number Dr, ahankali Ammi ta tsugunna Dady yabita da kallo, hannunta ta daura kan goshin Raudan dake wani irin nishi jinin na bulbulowa sosai tana kallonta tace "la'ilaha illallah, Muhammadu Rasulullah, la'ilaha illallah Muhammadu Rasulullah" duka wajen daukan kalman akayi ana bata ahankali bakinta yadauka tayi kafin ta lumshe idanunta rup, hannu Ammi tasa tacire dankwalin kanta dayake babbane ta warware tarufa matashi ta kalli daga Dady harsu Aliyu dake jiran tacemusu wani abu ta girgixa musu kai alamun takoma ga mahallicinta.
Wani irin uban ihu Maman su Rauda tayi. "wayyoooooo Allah na na shiga uku na lalace, Rauda, na shiga ukuuuuuuu, mena aikata ni Kareema? Na kashe y'ata? Wayyo Allah na, wayyo Allah na, wayo wayo" juyowa Dady yayi da jajayen idanunshi ya kalli officer yace "dan Allah kufitar min da matanan daga gidan nan" turata cikin mota akayi tanaji tana gani aka fita da ita.
Kafin kace me mutane sun cika gidan da anguwan ma makil, bayan sallan la'asar akai jana'izan ta aka kaita makwancin ta.
_Ya Allah ka jikin dukkan musulman dasuka rigamu gidan gaskiya, Ya Allah ka gafarta musu, Ya Allah kakai haske kabarinsu, Ya Allah kasa sunhuta, Ya Allah muda bamu riga munkoma gareka ba Ya Allah kasa mu mutu muna musulmai, Ya Allah kayafemana kurakuran damuka aikata, Ya Allah ka karemu zuwa hanya madaidaiciya. Ya Allah ka dubemu badan muba badan halinmu ba ka warkan da alumman ka daga wanan cuta ta corona virus, Ya Allah ka kawomana karshen ta, Ya Allah ka tsaremu ka tsare alumman musulmi gabaki daya, Ameen Ya Rabbil Alameen_
_*Good Morning GGM*_
[13/04, 09:13] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
5️⃣9️⃣
_How to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya. For those dabasu da account zaku iya tura katin MTN ta WhatsApp number na 07012181461_
_*see in bakida kudi karma kisake ki karanta littafin nan dan wlh banyafe miki ba zaki biyani hakkina alahira*_
_*keda kika biya access fee kikai joining group dina danki karanta littafi ba littafina kika siyaba so bakida anything kimin sharing book waje, saisa nai free pages, masu neman free pages kuje Wattpad dina "mamanshakur" and read, inhar kika fitarmin da littafi waje wlh keda Allah, Allah baya yafe hakkin wani sai in shi ya yafe miki*_
_kaduna_
Sanin batajin dadi yasa Baffa yahana Inna karta tadata da asuban ya shiga dayan dakin yatado yaranshi maza guda uku dasuke gida, Khaleelu, Ibrahim da Mubarak sukai alwala suka dunguma suka wuce masallaci.
Wuraren tawas nasafiya Baffa ya shigo gidan yabar yaranshi a makarantan asuba da akeyi a masallacin, inda matasa maza da mata suke haduwa amusu karatu sai karfe taran safe ake tashi. Da sallama ya shigo gidan yatsaya wajen akuyoyinshi da shanaye yana dubasu ya kwalama Inna kira. "Maman Hamma" daga kitchen Inna ta amsa. "na'am mai gida kadawo?" "kinbama awaki dusan kuwa?" tana juye tafashashen ruwan zafi a kullin koko data dama tace "eh najuye mai gida" shikadai Baffa ya shiga magana yana dudduba awakan yace "shine sukemin kuka kaman basu ci komiba da safen nan" tashi yayi ya kakkabe hannunshi tareda wankewa dawani ruwan dake cikin botiki sanan ya yarfe hannu yana tafiya cikin gida, Inna daya hango a kitchen tana kokarin hada musu kari yasa yay dakin da Aneesa take da sallama ya yaye labulen tareda tura kofar dakin hasken rana ya shigo dakin ya sauka akan fuskarta, dan motsi tayi sabida hasken daya hasko fuskanta da kyau, karasowa ciki Baffa yayi ganin karin ruwan yakare dayake nurse din jiya tanunamai yanda zai cire mata koda yakare kafin likitan yazo yasa yakarasa yakama hannunta tareda ciremata ya zauna ata baki bakin gadon yana kallon fuskanta yana tunani, gabaki dayan Aneesa da mahaifinta take kama banbancin su shine bata dauko hasken fatar shi ba saita dauko bakin fatar mahaifiyarta, bala'in tausayin yarinyar yakeji yarasa mesa ga mahaifiyarta tai aure, ga abinda mijin mahaifiyar yamata, in sha Allah kome zaiyi sai yayi mata dan yaga tafara walwala tadawo kaman da, zai mata duk wani abu dazai mantar da ita wahalhalun datasha gidan yarin nan dudda baida karfi amma duk inda zai samu saiya samo danya bata jin dadi. Ajiyan zuciya ya sauke yakai hannunshi ya daki filon da kanta kekai bude idanunta dake cikeda bacci tayi tai kini kini da rai kaman dama fada suke, murmushi Baffa yayi yaja hancinta da hannu yace "nine ke tashinki, tashi kiga gari yariga yawaye" yay magana yana dagata danta zauna, ahankali ta tashi ta zauna, hannunshi yakai yataba wuyanta yace "ya kikeji yanzu? Meke miki ciwo?" murya chan kasa tace "bakomi" shiru yayi ganin yanda take amsa shi dai dai kaman tana fada dashi, kaman ance dole saita amsashi, ahankali yace "tashi kije kidauro alwala kizo kiyi sallan safiya" tashi tayi tafita daga dakin tana tafiyarnan daidai kaman yar gidan sarauta tafita tsakar gidan daidai Inna tafito daga kitchen rikeda katon botikin kokon data dama, cike da fara'a ganin Aneesan tafito ga doguwan riganta data bata ya mugun yimata kyau gwanin ban sha'awa yasa tace "har kin tashi ne yar arziki, ya jikin?" ko kallon inda take Aneesa batayi ba tawuce abinta ta buga kofan bayin kaman dashi take fada kofar yabudu ta shiga ciki takara bugo kofan, kofan yarufe, karkada kai kawai Inna tayi tareda yin murmushi taji zafi amma batawani ji zafi ba tasan ba laifin ta bane, ta yaye labulen babban falonta ta shiga ta ijiye botikin a tsakiya tareda kwaso kofuna na robobi irin masu marfin nan ta zuzxubama kowa sanan tafito takoma kitchen din tana hadama Baffa dumamen tuwon jiya, ta hadamai asamiran shi tai dakinshi, fitowa shima Baffa yayi daga dakin Aneesan jin Inna na kwalamai kira......
Inkinsan bakida kudi karma ki karanta min littafi dan wlh banyafe miki ba, duk wacce ta karanta bata biyaba Allah ya isa.
Fitowa Aneesa tayi daga bayin bayan tadauro alwala daidai lokacin yaran Baffa sun shigo gidan, dawowan su daga islamiyan safe kenan suna dan hiransu, Khaleelu da Ibrahim sun girmeta, Khaleelu yanzu yanada 25yrs, saurayine kawai yanada karamin jiki ne dan jikin Innan su yadauko saisa baka gane ya girma, sai Ibrahim shikuma yanada 23 shi yamafi Khaleelu girma inka gansu zaka zaci shine babba dan har gemu gareshi gashi ustazu yanada kokarin sosai a fannin islamiya shi capinta ne, sai Mubarak wanda yake sa'an Aneesan yadan bata watanni da bazasu wuce uku ba zuwa hudu, washe mata baki dukansu sukayi ganinta tafito daga bayi, tun jiya da daddare suke so suje dakinta Inna tahanasu akan batada lpy, wani irin mugun tsaki Aneesa taja ganin yanda suke kallonta suna washe mata baki kaman tace sumata dariya. "mtswwwwww" tawuce tagabansu tai dakinta batare data kallesu ba, da sauri Mubarak dake sa'anta yace "kai badai ni kikama tsakin nanba yarinya? Wlh saidai su Ya Ibrahim kikamawa dan lallasaki zanyi mara kunya kin san halina ai yanda nake daddakaki in munzo Suleja" Aneesah harta shiga daki taji maganan Mubarak din karaf a kunenta da sauri ta daga labule tafito ta tsaya abakin kofa da kyau tana kallonsu daga wurin ta kalli Mubarak tareda nuna kanta da yatsa cikin kunan rai tace "dani kake wayan nan maganganun?" da sauri Mubarak shima cikin zafin kai irin na saurayin dake tasowan nan yace "a'a da wata nake tunda akwai wata bayan ke a tsakar gidan ne" kwafa Aneesa tayi tace "Allah yasoka dan inda dani kake da banga abinda zai hanani parke ma bakin nan dakai magana dashi ba, dogo ba hankali kawai" cikin fushi Mubarak yataso zaiyo kanta Khaleelu baban wansu yarike shi yace "me haka bakasan bakuwar mu bace? Aneesa cefa dakuke wasa tare lokacin da ake zuwa da ita datana yarinya, ka manta Aneesan da Abba ke kwasan mu muje Suleja ganinta, me haka? Common yar uwan ka ce, share, forget" cikin fushi Aneesa tace "barshi karma ya share baisanni bane, zan gwadama hankali yaro, dogo ba hankali kawai" cikin fushi Mubarak keson kwashe hannunshi daga hannun Ya Khaleelu yace "Ya kagani nitake cema dogo ba hankali ko, wlh takara cemin dogo ba hankali saina fasamata baki wlh kuwan" da sauri Aneesa tace "shege kafasa ance dogo ba hankali, kazo inhar kai dan halak ne" wani uban tsalle Mubarak ya daka ya fizge hannunshi yay cikin gidan ganin yana tahowa yasa Aneesa ta shiga waige waige, wukan data hango a makwarara inda aka kai kayan wanke wanke yasa tai wurin da gudunta ta tsugunna tadau wukan ta rike da kyau ta kalli Mubarak din dake zuwa kaman namijin zaki tace "kazo kaga wlh saina maka barakaka" da sauri Mubarak yakarasa gabanta batare daya damu da wukan data daukaba dan yasan duk wargi ne yasa hannu yadaga zai kifamata mari Aneesa ta daddage tayanki fatar hanunshi da wuka, atare daga Khaleelu har Ibrahim sukai ihu dan duk