Showing 87001 words to 90000 words out of 186400 words
Chapter 30 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt
dariya, juyowa tayi ta kallai yanda yake dariya sai taji ya bala'in burgeta hakanan saitaji duk damuwam datake ji dazu ya kau sabida yana dariya, turo baki tayi cikeda masifa ta kalli yanda yarike mata hannu tace "nika saken ba kyau namiji nataba macen daba muharraman shiba, nika saken" tsayawa yayi yana kallon bakinta yanda takemai tsiwa kaman ba itace tagama lallashin shi dazu ba barkono kawai, murmushi yayi kafin ahankali a shagwabe yace "to ni karkije ko ina stay with me inba hakaba I will not be able to very well, kinji Anebaby" dauke kai tayi tareda gyadamai kawai ganin yanda yake mata wani shagwaba ahankali ta zauna kan kujeran shikuma yacigaba dacin abincin as usual ahankali kaman wani karamin yaro yana kallonta, tun tana kallonshi yanaci harta fara gyangyadi dantagaji kafin ahankali wani bacci mai dadi yay awon gaba da ita danta gaji sosai.
Ture abincin yayi yadaura both his elbows akan table din yabuga uban tagumi yana kallonta, yanason Aneesa, yanaso ta yanaso ta sama da tunanin shi, she's just the definition of matar dayake so, dazaran ya shirya da Dady zai mishi maganan ta dan bazai taba bari innocent brave and fearless yarinya haka mai addini ta subuce mai ba, ahankali yaji tafara jan munshari ware ido yayi surprisingly this is the first time yake jin mace na minshari matso da kujeran dayake kai yayi kusada ita, lumshe ido yayi yanajin saukan munsharinta kan fuskanshi what is love without loving your woman's flaws? Ahankali yace "i love you girl" murmushi yayi kafin yamika hannunshi yadaura kan lips dinta dasuke abude firgigit ta farka tabude idanunta dake cikeda bacci tace "me haka kake tonona eh?" murmushi yayi yanuna mata stairs yace "muje naraka ki ki kwanta you are sleeping babyna" tashi tayi ahankali tana sosa ido tai gaba yana biyeda ita abaya har sama, dakinta tabude ahankali ta shiga, shigowa yayi shima yana kallon dakin yanda gadon kenan agyare, hijabinta tasa hannu zata zare tadago idanunta ta kallai yanda ya tsaya daga jikin kofa yana kallonta ahankali cikin muryan bacci tace "to kawuce kafita" gyadamata kai yayi yace "Alright gud night" juyawa yayi yasa hannu zai bude kofan saikuma ya juyo ya kalleta itama kallonshi take murmushi yamata murya chan kasa yace "I love you Fateema, Swt dreams" murmushi tayi tabude bathroom dinta ta shige akunyace hakan yasa yabude kofa yafita yasauka kasa yay hanyar fita, sauka idanunshi sukayi akan wayanta dakuma littafan ta datake assignment dasu,v karasawa wajen yayi tsugunnawa yayi ahankali yadebi littafan ya tattare tareda wayanta yay stairs hawa yay yayi sama, ahankali yabude kofar dakinta ya shiga daidai lokacin tabude bayi tafito tana sanye dawani spaghetti hand cotton half night gown baby pink, ihu tayi tabude kofan bayin takoma ciki da gudu shikuma ya tsaya yana binta da kallo murmushi yayi sosai yakara so ciki ya ijiye mata abubuwan nata kan gado sanan yawuce yafita tareda rufo mata kofa.
[21/03, 17:46] Aishat Muhammad: Tadade abayi dudda taji budewan kofan shi amma taki fitowa sai daga baya sanan tabude kofan ahankali tadan leko ganin babushi yasa tasauke ajiyan zuciya tafito gabaki daya tai wajen kofan su da gudu ta kulle sanan tadawo ta kwanta kan gado tanaji wayanta na ringing taki dauka dan tasan shine kuma mugun kunya takeji tai magana dashi ahaka bacci yay awon gaba da ita.
Kaman amafarki taji muryan Ammi na kiranta. "Aneesa, Aneesa wai bazaki tashi daga baccin nan ba" firgigit ta farka ganin yanda gari yay haske sosai har rana tafito ysa tazabura tamike tsaye, buga kofan dataji anayi yasa yakalli kofan tai wajen kofan da sauri tabude Ammi ce ta shigo tana sanye dawani black hadadden bakin riga taci gayu tabi Aneesa dake murza idanu da kallo tace "dan iskanci sai yanzu kike tashi iyye?" kaman zatai kuka ta janye hannunta daga ido tace "Ammi nagaji jiyane saisa bantashi da wuriba" "common wuce kije ki dauro alwala kizo kiyi salla kifito kisamen a kitchen" gyadama Ammi kai tayi tajuya tai bayi Ammi kuma tawuce kasa.
Salla tayi tazura doguwan riga na atampa tafito a kitchen tasami Ammi tana girki, ahankali ta shigo tace "Ammi ina kwana" hararanta Ammi tayi tace "wuce kidau tsintsiya ki sharo ko ina har baranda, ki tattara takalmomin nan dasuka hargitse gefe daya" gyadama Ammi kai tayi tadau tsintsiya tafita tafara gyara falon tsaf har dining sanan ta shiga shara har zuwa bakin kofa takai sharan sanan ta kwashe ta kunna turaren burner dinsu dtazuba turare dakin yadauki kamshi sanan tadau tsintsiyan tabude kofa ahankali dan gyara varandan su kaman yanda Ammi ta gaya mata, idanunta ne suka sauka akan wata babban mota irin ta company mai suna Fitness Equip ana sassauke wasu manyan machines dabata san na meye ba agaban flat din Aliyu, hango mazan datayi yasa takoma daki hijabi tadauko tasaka sanan tadawo wajen idanunta ne suka sauka akan na Aliyu data ganshi tsaye kusada wani mutumi yana sanye dawani Beach 3quter dawani logo brown shirt ajikinshi magana yake amma yana hango ta yay shiru ya tsaya yana kallonta har saida mutumin da kemai magana ya juyo dan yaga meyagani me yake kallo dayasa yay shiru baya magana, dauke kai da sauri Aneesan tayi taduka tafara shara, kwala mata Aneesa taji anyi da sauri ta dago daga sharan datake, Abba ne tagani yana sanye da farar jallabiya da hula as usual shiga shi ta asuba ya tattaro yaran gidan gabaki daya harda Hajar dahar lokacin fuskanta yake a suntume, da hannu yamata alamu yace "zonan Aneesa" ajiye tsintsiyan tayi ahankali tafito ta karaso wajen tana kallon fuskan Dady ahankali tace "ina kwana Dady" murmushi Dady yamata yace "kin tashi lpy, kumuje ku gaida yayanku" Dady yay gaba duk suka dunguma suka bishi abaya hannunta Rauda takama tace "Aneesa how are you" batasamu ta amsa ba sabida kaiwa inda Aliyun yake tsaye da mutumin dasukayi Abba yajuya ya kalli Hajar ya mugun daure fuska yace "zoki gaida Yayanki" dayake duk iskancin ta tana tsoron Dady yasa tataho ahankali kanta akasa Aliyu ya zubamata ido yana kallonta, ahankali tace "ina kwana Ya Aliyu" ba yabo ba fallasa yace "fine, how was your night?" ahankali tace "Alhamdulillah, uhmm Ya Aliyu am sorry about yesterday" murmushi Dady yayi jin taji warning din dayamata, gyadamata kai Aliyu yayi yace "never mind" ahankali tace "thank you" dan murmushi ne ya subuce ma Aneesa sosai abin yamata dadi, da hannu Dady yace "oya Aneesa you and Rauda kuzo ku gaida yayanku" Rauda dai da gudu tafada jikin Ya Aliyu yau wace rana tazo taganshi freely, makalkaleshi tayi tace "Ya Aliyu gud morning" "ke cewa nayi ki karyashi" Dady yafada yana hararanta, ahankali Aliyu ya kalli Aneesan hada ido sukayi sanan ya kalli Rauda yace "ya ciwon cikin?" kaman zatai kuka tace "yadena" gyadamata kai yayi ya kalli Aneesan ahankali ta saukar da kanta kasa tace "ina kwana Ya Aliyu" batare daya kalleta ba dan yasan idanun Dady na kanshi yace "how was your night?" batare data kalleshi ba tace "Alhamdulillah" dan juyowa yayi ya kalleta yanda hijabinta yadan zame baya ana ganin gaban gashinta ga gashin goshinta ya kwanta sosai, kasa daurewa yayi ahankali ya tsugunna yadau Amal dake ta kallonshi yana mata wasa sanan yadan kalli Aneesan hada ido sukayi da hannu yamata alamu yace "ja hijab dinki gaba" da sauri Dady ya kalleta yace "yayanki yace kija hijab dinki gaba suman ki awaje Aneesa" jan hijabin tayi gaba shikuma Aliyu ya tsugunna yana wasa da yan kanenshi yaran sai washe mai baki suke Dady na murmushi ganin yanda yake murna Hajar kam kaman ta chakamai wuka takeji, kallonsu Dady yayi yace "to kuwuce aje a shirya school" ahankali Aliyu ya shashafa kan yaran yace "bye girls" yaja kunen Rauda yace "bye" washemai baki tayi tace "bye Ya Aliyu na" tajuya tabi bayan Aneesa sukai gaba, kallonshi Dady yayi yace "Gadanga na, sport zaka farane wanan kayan gym din daka sayo fa" daure fuska yayi yace "I don't wanna talk to you Dad" murmushi Dady yayi cikin kwaikwayan yanda yamai magana yace "haba Gadanga na har yanzu ba'a dena fushin da Dady ba, Dady fa yace a yakuri iyye, adan kalleni mana ko sau daya nai kewan yarona fa" murmushi ke cinshi amma ya danne yay kini kini darai shi adole fushi yake da Dady, murmushi Dady yayi cikeda son dan nashi yace _"Baba Aliyu mangyada baya bacci, ranan haihuwan shi ba wahala ko daya, yafado turus kaman namijin tarwada, tashi ingank...."_ fashewa da dariya Aliyun yayi tun kafin Dady yakarsa wakan his Dady is just the best, ahankali yay hugging Dady murya chan kasa yace "I love you old man" murmushi Dady yayi yadan tallabe keyanshi yace "I love you too yarona, my one and only Son, rigimammen yaro kawai" murmushi Aliyun yayi yadago sai a lokacin ma yatuna aikin da akemai kallon Dady yayi yace "stop calling me rigimamme in front of people Dad" dariya
Dady yayi yajuya yana kallonsu yace "aikin me sukema haka?" dan yatsine fuska yayi yace "I want to create a gym ne, wanna start working out" haba Dady yakama cikeda mugun mamaki yace "working out, Aliyuuuu! Kaina zakai work out" murmushi yayi yace "yes, meet my instructor ma" yanunama Dady mutumin da suke magana dashi dazu, gaisawa Dady yay da mutumin Dady yakasa dena mamaki wai Aliyu ne zai fara exercise harda su gym instructor gareshi lallai, ikon Allah zaiga yanda hakan zaiyu yaron dabai jure wahala.
_duk wanda yakaranta bai biyaba, Allah ya isa, chat me up in kinason book Dinnan 07012181461_
[28/03, 11:16] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
4️⃣1️⃣
Kallon Aliyun Dady yayi yana kokarin yagano wani abu dan shidai yasan inba wahayi akama Aliyu kowani abuba babu abinda zaisa yaron nan yatashi rana tsaka shi exercise zai fara, gyadamai kai yayi kawai dan he's not convinced yace "to shikenan kayi sauri kagama sai kazo kai breakfast abangaren Mummy ka, kobaka ma gamaba kazo kayi breakfast dan nafiso mudinga breakfast atare" gyadamai kai Aliyun yayi yana lashe lips da sauri Aneesa data tsaya tana kallonsu sabida yanda suka bala'in burgeta ta duka tafara sharan, Dady nason Aliyu so ko dabata taba ganin irinshi ba, shima Aliyun nason Dadyn shi, kuma wani irin soyayya sukeyi irin na yan gayu, irin soyayyan uba da d'a na kasashen waje dasuke gani a TV, ganin Dady yataho yasa ta tsayar da sharan, murmushi yamata ya shafa kanta yace "sannu da aiki yar albarka, my brave girl mara kuwuya" dan dariya tayi Dady ya iya wasa da yara, kofa Dady yabude ya shiga ciki itakuma ta cigaba da sharan tanadan satan kallon Aliyu, inda dane da tuni ta gama sharan dan barandan dabaida wani girma, dayake da abinda take kallo shiyasa bata gama ba.
Motar data kawo kayan ne tai reverse tafice daga dakin, fitowa Aliyu yayi daga flat dinshi sanye dawasu kayan exercise na kampanin ceegar, purple rigane armless hoodie sai wani gajeren wando daya tsayamai a guiwa, yasaka sport shoes na Nike yafito yanadan kakkabe hannu yana kallon inda Aneesan take datai kaman bashi take kallo ba tana sharanta abinta nanko idanunta nakanshi, kallonshi instructor yayi yace "are we ready Leo?" gyadamai kai yayi with full confidence shi adole soyake ya burge Aneesa yau, wani adjustable dumbbell instructor nashi yadauka kaman yadau tsinke abinka da wanda aikinshi kenan yace "are you ready Leo, squat, spread your legs and give me your hands" squatting Aliyu yayi ya bubbude kafa kaman yanda instructor yayi agabanshi yamikamai hannu, ahankali instructor yasakama Aliyu dumbbell din ta hanyar dauramai a hannu yace "let's go, lift it up in the count of 3, one, two, three" wani irin ihu Aliyu yayi Instructor na zare hannunshi daga kan dumbell with yasakan mai nauyin duka, ko lifting dumbbell din up baiyiba yahau sakin ihu "auuchhh Daddddd, ahhhh hannuna, auuchhh" da sauri Aneesa tadago kai rike karfen barandan su tayi kaman zatai kuka tana kallon Aliyun dataga yay wani iri da hannu kaman hannunshi na shirin ballewa yana kiran Dady, the thing looks funny amma tausayi yabata dan tasan ita tasashi da yanzu yana zaman zaman shi, dariya instructor yayi yana gyara position din dumbbell din a hannunshi yace "oh common u can do it, is just 80kg dumbell fa, saika saba da wanan zan kaga 100kg dumbell, lets go, let go lift it up" kaman Aliyu zai sakin mai kuka ya girgiza kai a shagwabe yace "ni bazan yiba kacire mini kona kirama Abba na wlh" kyalkyacewa da dariya Aneesa tayi at this point the whole Aliyu thing looks funny wlh, bata taba ganin lazy namiji irin Aliyu ba ita yama akai takeson wanan mutum haka Allah na tuba ai koni zan iya dagawa sama, akwai shi a shagon madam ta backyard tafa taba dagawa fa kuma bawani nauyi koda yake dadai nauyi but ba sosai ba, kyalkyacewa da dariya tayi hartana buga kanta da brander abin yay kara da sauri Aliyu yajuyo ganin Aneesa ce ke dariya sosai tana kallonshi yasa ya kauda kai, kafin yakara waigowa da sauri hada ido sukayi ta daure fuska kaman ba ita ke dariya ba tamai alamu da hannu idan bakayi ba forget bazan aureka ba dinan, wani irin namijin ihu Aliyu yayi yay lifting karfen sama gabaki daya yana huci da baki kaman macen dake nakuda, yanda taga hannunshi na rawa kaman yana shirin sakinshi kasa jijiyoyin wuyan shi dana kanshi duk sun bullo tsabagen nauyin abinda yadaga kana ganinshi kasan yanacin wuya, tausayi taji yabata sosai daukan tsintsiyan tayi tabude dakinsu ahankali ta shiga dan bazata iya jure taganshi yana aikin wahala ba kuma ita tasashi.
Daddy ne kadai zaune afalo yana kallon news ganinta yasa yace "ki shirya, anjima idan Yayanki yagama tarkacen training dinchan zansa yakaiki saikiyi registration din jamb ko, mamanki tacemin baki riga kinyi ba" murmushi tayi tace "to Abba" tawuce kitchen ta ijiye tsintsiyan sanan ta wanke hannu tazo tana taya Ammi aiki sinasir Ammi keyi da safen nan daga taji Dady yace yanajin cin sinasir shine tafara yi bamata fadamai shizatayi ba, sai around 10 suka gama tsaf Aneesa ta dinga fito da warmers din tana jerasu a dinning, waya Dady yadauka yakira Aliyu. "leave that training kazo kai breakfast" katse wayan Dady yayi saida Aneesa tagama ajiye komi a dinning harda cucumber zobo juice din da Ammi tayi sanan tawuce sama danta watsa ruwa, dakinta ta shiga bayi direct tawuce wanka tayi sanan tafito wata hadadiyar pink atampan da Dady ya saimata ta dauko tasaka an mata dinkin Riga da skirt daya kamata ya bala'in mata kyau, mai kawai ta shafa ko hoda bata tsaya shafawaba sabida kwala mata kira dataji Ammi tayi tace "ganinan zuwa Ammi" wani karamin hijabinta na zaman gida tadauko baki daya tsayamata acinya tasaka, sanan tafito ta maida kofan tarufe, tundaga saman takejin kamshin turaren Aliyu alamun ya shigo kenan ahankali take tafiya kanta akasa harta fito falon baki Ammi tabude zatamata masifa dan tuntuni ita suke jira basu faracin abincin ba gashi Dady zai fita Dady yadaga mata hannu yace "kinga bance kima y'ata fadaba bakiga wanka tayiba, zauna abinki muci abinci" Dady yay maganan yana nuna mata kujeran dake gefen na Aliyu, ahankali taja kujeran ta zauna, Ammi tadau plate mai kyau ta zubama Dady sinasir da miyan, tadau wani bowl tazubamai farfesun kayan ciki sanan ta kalli Aliyu tace "mezakaci son?" ahankali yace "coffee Mum" dan hararanshi Ammi tayi tace "nasan zakasha coffee namaka shi daman, but zakaci abincin dazai kama maka ciki" mug ta dauka ta tsiyayamai coffee sanan tamika mai zuma tace "gashi kasa daidai" da sauri Aneesa ta fizge zuman kafin ya amsa tace "Ammi cikawa zaiyi wlh ya iyacin zaki" wani irin kallo Ammi tabita dashi surprisingly, Aliyun ma dago kai yayi ya kalleta for the first time tunda ta shigo dakin, Ammi zatai magana Dady yace "ya akayi kikasan Aliyu dason zaki daughter? Aiko hakane, samishi kadan kinji" dan murmushi Aneesa tayi akunyace sabida kallon da Ammi keta binta dashi tasan sai tace nata Yaya2 akayi tasan Aliyu nason zaki, adan kunyace tadago kanta hada ido sukayi da Aliyun dake kallonta dauke kai tayi tamika mai zuman tace "gashi kasa" da sauri Dady yace "samai daughter na kinji" ahankali tasaci kallon Ammi ganin takoma gefen Dady tai zamanta abinta kaman ma bata ganinta yasa tajawo coffee Aliyu dake binta da kallo ta zubamai zuman daidai sanan ta juyamai ta turamai gabanshi tadan saci kallonshi tareda sakinmai harara, murmushi yayi yadau mug din yakai baki, Ammi tace "samai sinasir kema kisaka" zubama Aliyun tayi dayawa ta ajiyemai agabanshi sanan itama tazuba nata tadawo ta zauna, ahankali takecin abinci duk wani motsi dazatayi akan idanun Aliyu hakan yasama takasa cin abincin da kyau gashi yay shegen dadi girkin.
Saida Dady yagama sanan ya kalli Aliyu yace "Son take Aneesa to inda zatai jamb registration okay, nizan fita saina dawo" dan dukowa yayi ko damuwa baiyi ba ya sumbaci goshin Mami rufe fuska da hijabi Aneesa tayi akunyace Aliyu yay murmushi aranshi yace "I will do more to you yarinya".
Shafa kan Aliyu Dady yayi sanan ya shafa kan Aneesa yace "saina dawo yarana" ahankali Aliyu yace "bye Dad" "saika dawo Abba" Aneesah tafada ahankali tanacin abinci fita Dady yayi yarufo musu kofan duk suka gama cin abincin Aliyu ne yafara ture abincin kadan yarage dan girkin yamai dadi sosai Ammi ne tace "badai harka cinye ba" murmushi yayi yace "nakoshi Mum, bari naje nai wanka" ya kalli Aneesa yace "get ready" da sauri Ammi tace "wlh kaman kasani dan wanan wasanta yay yawa Aliyu" daure fuska Aneesa tayi tareda turo baki Aliyu yay murmushi yawuce yafita, saida Ammi taga yarufo kofa sanan ta kalli Aneesan tace "ya akayi kikasan yanason zuma harda fizgewa?"