Showing 6001 words to 9000 words out of 186400 words

Chapter 3 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt

20 Jan 2025

18794

farare turawa ga shisha pot agaban su da manya manyan bottle din wine da glass cups, suna ganin shi sukai ihu. "you are late Leo" haka suke kiranshi da Leo tun farkon shigan shi school idan za'a kira sunan shi Aliyu saidai suce Aleo shine friends dinan nashi kawai suka cire A din farko suka radamai Leo, zama yayi kusada black guy din Wanda shikadai ne yay kama da dan Nigeria cikinsu sauran duk da turawa ne. "ahhh wash, my legs" black din dake kusada shine yace "where are your guards Dady's boy?" daga yanayin yanda yay maganan zaka gane tsokanar shi yake nema hakan yasa sauran suka fashe da dariya sosai, hararan su yayi yace "I came alone" "whowhowhow! Kai nawa, lemme just call this a white lie right guys?" ya tambayi sauran mazan atare sukace "yeah, is a white lie" sukahau dariya ganin iskanci sukemai yasa ya kalli bar attendant din wurin yace "non alcoholic wine pls" da sauri mutumin yajuya dan zuwa daukomai, juyowa yayi ya kallesu ganin duksun tsareshi da ido suna shan shishan su yace "wats up guys?" wani daga cikinsu ne cikin harshen turenci dan duk da turenci suke magana yace "magana muke akan irin matan damukeso mu aura in the future, I personally Leo want to marry sangartacciyar yarinya, yarinyar yar gayu mai kyau wacce tasan gata, yar gidan masu kudi, kai wacce irin mace kakeso ka aura Leo?" daidai lokacin bar attendant din yakawo mai wine din dayay requesting karban wine din yayi daya zubamai a glass cup, Bash dan Nigeria dake kusada shi ya kalli wanda yama Aliyu tambayar yace "me kake tambayar Leo irin matar dazai aura, kaima kasan Leo ready made yar gata zai aura, am sure yarinyar president zai aura?".














Tabe baki yayi jin maganan da Bash yayi yakai wine dinshi baki yana kara shigewa cikin kujera da kyau, ganin baida niyyan magana sun saba dama da iskancin shi yasa daya daga cikin turawan mai suna Frodd yace "ni inaso na auri matan data girmeni sosai at least tabani 10 good yrs" atare dukansu sukai kallai harda Aliyu dake sipping red wine dinshi, daga musu gira yayi yace "yes, idan ka auri wacce ta girmeka tafi riritaka, tafi kula dakai, tana kuladakai kaman dan kwai cus it took her a very long time kafin tasameka so u will be well taken care of, you are just like an asset awurin ta" dariya dukansu sukayi banda Aliyu da yadanyi murmushi kana ganinsu kasan suna enjoying hiran dasukeyi abunsu ganin yana murmushi yasa sukace "come onnnnnn Leo tell us yours" dan bude ido yayi ya kallesu saikuma yay murmushi ya daga glass cup din hanunshi yana kallon wine din yay shiru kaman yana tunani dan fuzar da iska yay kadan ya gyara zaman dayay akan kujeran mai kama da kwanciya ya daura glasscup din akan kirjinshi yace "I don't think I will ever get married but if I will matar danake so na aura" yay shiru yasa hanunshi yacire glasscup din daga kan kirjinshi yadaga sama tareda bude idanunshi ya kalli glasscup din dayake dan girgizawa ahankali yace "inaso na auri mace dat is not from a wealthy home, rich girls are too stupid and proud I hate them" ya yatsine fuska kadan cikin sassanyar muryanshi yace "I want a hardworking smart girl mara son jiki a kazar kazar girl" yasake yin shiru yana girgiza cup din yace "a good cook, obidient and gently being, a girl that She sees me for me, I want Inner Beauty in a lady not facial, if her heart is beautiful am okay" yay dan shiru kafin ahankali yace "I want a girl that am naturally attracted to, attraction is the basis of love and marriage, and if the spark isn’t there, it’s something that’s really hard to fake" yay shiru yace "a girl that is not too expose mai kunya, yarinya mai hankali da taimako" yadanyi shiru kafin ya yatsine fuska ahankali yace "I just want a girl that will beat my imagination, I want a girl that will beat all this qualities I listed and be more and more and more" dan murmushi yayi ya ijiye glasscup din yace "anyway nasan they're no such girls on this earth, so I ain't gonna stress myself with marriage, nowadays girls are too lousy guys" yasake yatsine fuska agajiye duk dariya sukahau yi Bash yadan buga kafadarshi yace "u are just talking ne, irinku har kuka kukema soyayya, aure maybe ma duk saika rigamu aure muna nan dakai" kabar da hanun Bash din yayi yay hamma yana duba rolex din hanunshi ganin kusan 1:30 nadare yace "night guys am sleepy, I will be travelling tomorrow" atare duk sukace "where to?" tashi yayi ahankali yace "home" Yajuya ahankali yana daga musu hannu yay waje, bacci yakeji bana wasaba da kyar yakai parking lot aka budemai mota ya shiga ya kwantar da kanshi jikin kujera ya lumshe ido sai bacci.










Murmushi bodyguard dinshi yayi kawai bayan yarufe kofan motar baiga laifin babanshi ba dayake hadashi da security komi Aliyu yakeyi a shagwabe a sangarce kaman ba namiji ba, kaiwa gida sukayi yay parking suka fito ya zagayo yabude kofan yadan bubbuga kujeran yace "we are home sir, wake up lemme take you to bed" bude ido yayi ahankali ya kallesu ahankali yatashi yaziro kafafunshi kasa bodyguard din zai rikeshi ya harareshi cikin bacci yace "don't touch me" yay gaba suna biye dashi har upstairs yabude dakinshi ya shige yafada kan gado batare daya cire takalmi ba, ciremai takalmin bodyguard din sukayi sanan sukaja bargo suka rufemai jiki ya rage karfin AC, dayan kuma ya kashe wutan dakin suka juya suka fita already tun dazu da rana suka hadamai kayan dazaiyi tafiya dasu gobe.
[02/03, 16:58] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






4️⃣




_how to subscribe_


_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turomin evidence of payment to WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*_


_*Zaki iya turo katin MTN 300 ta WhatsApp number na sainai adding naki a group din danake posting*_






_Free page_




Bangaren Aliyun Dady yabude da wani card, ya shiga Aliyu dake tafiya ahankali biyeda shi, hadadden dakine nagani na fada, an gyara komi tsaf sai shining furnitures din keyi dan Dady yasa an gyara komi, zama yake shirin yi Dady yace "a'a Son aje ayi wanka eh dan saurayin baban shi" gyadama Dady kai yayi kaman zaiyi kuka yay hanyar bedroom dinshi daidai lokacin Rauda tashigo falon rike da katon basket data lodo all abinda zatai amfani dashi tamai girki, ganinta yasa Dady ya washebaki yace "yauwa yar albarka, shiga kitchen ki hadamai" "to Dady" tace tana leken Aliyun dake shirin shiga daki, hada ido sukayi tasaki wani murna tawuce kitchen. Sea food pasta takeso tadafamai dazaiji shrimps sosai, ruwa tasaka a wuta ta rufe pot, sanan tasa wani pot a wuta tana hada tomato sauce, ruwan na tafasa ta zuba spaghetti danya tafasa tacire, in less than 30min tahadamai hadadden spag dayaji shrimps sai kamshi yakeyi.








Wani hadadden plate ta dauko ta zubamai tasaka a tray, tabude fridge dinshi taga akwai drinks masu sanyi dat means Dady duk Yasaka an saka, tadauko drink tadaura akan tray da glasscup goran ever water tafito, yana kwance afalo sanye da pyjamas farare yay filo da cinyar Dad suna hira kasa kasa dako ita bata iyajin abinda suke cewa sai murmushi yakema Dad, karasowa tayi dauke da tray taja table ta dauramai abincin akai ta zauna agefenshi tace "ci abinci yayan mu" tai maganan tana rikemai hannu, kanta ya shafa ahankali tareda yatsine fuska yace "is too hot I can't eat it bari yahuce, ya school Angel?" murmushi tayi sosai tace "fine Yayan mu, ina 100level computer science education, ni course din wuya yakemin Yayan mu sosai" zaiyi magana Dady yamike tsaye yana gyara babban riganshi yace "bari naje na watsa ruwa na kwanta tunda kun manta dani" dariya dukansu sukayi kafin ahankali yace "good night Dad" murmushi yayi yace "yauwa Yarana, saida safenku, dazaran tafara damunka da surutu ka kadota dan kasha gajiya ga Rauda aku kuturu ce" dariya tafashe dashi taboye fuskarta abayan Aliyu tace "Yayan mu ai banda surutu ko" dan murmushi yayi yace "don't mind Dad ya iya shairi" hararan su Dady yayi yawuce yafita daga dakin, abincin ya kalla yace "go and bring another fork let's eat together" , ware ido tayi saikuma tanunamai cikin ta tace "kar cikina yafashe ni nakoshi, ci karage saina rufe nakai kitchen" daukan fork din yayi yafara ci ahankali, kafeshi da ido tayi ganin yamata bala'in kyau, rabonta dashi kusan 1yr kenan yanzu, ya kara kyau ya kara kiba, yakara cika da zati, gadan gemun daya tara dan kadan dake shining tsabagen gyaran dayakeji, sosai tai nisa akallonshi bama tasan harya gamaba saida ya dungure mata kai sanan ta farga tareda kyalkyace dariya takalli abincin tace "harkagama harya isheka dan wanan zakaci?" ruwa yadauka yakai baki yace "yeah, am ok, dauka kikai kitchen kidawo" dauka tayi tai hanyar kitchen shikuma yacigaba dashan ruwan goran dake hanunshi, dawowa tayi tasake zama kusada shi kaman zata cinyeshi tun tana karama take mugun son Ya Aliyu, shima haka yakeji da ita duk cikin kannenshi itace ta isa tazo bangarenshi ta shiga ko ina tafito, tun tana karama inhar yana nan yana daukanta sufita yasiyo mata abubuwa dayawa sudawo, ita kemai girki ta gyaramai bangaren shi, da ita kadai yake shiri duk fadin gidansu, tashi yayi daga kan kujeran da sauri ta tashi itama, hanunta yakama sukai hanyar bedroom dinshi abakin gado ya zauna ya nuna mata daya daga cikin akwatunan da bodyguard suka shigomai dashi yace "take it to your room" wani irin murmushi tamai ta tashi da sauri tai wurin akwatin, zama tayi a kasa ta kwantar da akwatin tabude, turarukan matane guda hudu adan mini fine bag, sai wani kit da sauri ta dauka ta bude agogo verosky ne da bracelet dinshi, ihu tayi dan tadade tanason abun batada shi, sauran kayan kuma riguna ne masu kyau na mata ciki da singlets, cikin tsananin farin ciki ta dago kai dan tamai godiya taga haryay bacci yana saukar da numfashi ahankali.
















Murmushi tayi ta kwashi kayan ta mayar cikin akwatin ta hadasu tsaf tarufe ta tashi takaraso gaban gadon daya ke kwance ta tsugunna ta kafamai ido tana tunani, sosai takeson Ya Aliyu sama da duka yan uwanta, su 21 ne yaran Dady, Ya Aliyu shine first born agidan, itama ta girma batasan maman shiba but Anty Hajar tasanta dan tana around 6yrs ta rasu, hawan jini yakasheta, Mama ta taba fadamusu Aliyu yakusan haukacewa da Ummin shi tarasu dan ya shaku da maman shi sosai, bayan Ya Aliyu sai Maman su ta haifi Anty Hajar, sai ta haifi har maza biyu amma duk suka rasu bayan sunzo duniya, sai ita, sai kaninta dukansu mata guda 6, amaryan Dady yaranta mata guda uku, sai ta tsakiyar itama yaranta mata guda Takwas, bawasu manya bane dayake gasan haihuwa ake agidan, daga ita sai Anty Hajar ne kawai manya duk sauran yaran yarane basu wani tasaba. Deep down tausayi sosai Ya Aliyu kebata bana wasaba gidan nan kowa ya tsaneshi harda Maman su itacema oga, she's sure ayanda Mama ta tsaneshi inda zata sami hanyar kasheshi zata iyayi, ita tarasa meyay musu meya tsaya musu? Maiya kare musu wanan mugun tsana haka daga ina? Gashi baima dawani magana, bayama kulasu sabida yanda ko kaunar ganinshi basayi duk sun rabashi da kaninshi, itama da karfi da yaji tanunama Mama itafa saita kula Yayan su koda ba mahaifiya daya ta haifesu ba ubansu daya ai, kuma jini guda ke yawo ajikinsu, Ya Aliyu is just somehow that she can not even define, he's very cool saiyaga daman kulaka zai kulaka, sanan yanada fushi yanada bakar zuciya but he's always keeping calm baimaso yana fushi, gashi baida kwari komi ahankali yakeyi sanan shi mata basama gabanshi, shi kawai gashi nanne soo somehow, sa'oinninshi maza by now suna cikin kogin soyayya koma sunyi aure sun ijiye iyali shiko batamaga alamun sha'awan aure tattare dashiba ko halinsu Mama ne dayagani yasa yadauka duk haka mata keda bakin hali ya tsani aure oho but she just wish, hope and pray Ya Aliyu will meet the love of his life soon and experience that feeling of knowing someone out there is dying for you, is crazy for you, and can do anything for, love feeling is just the best ne, tarasa mesa duka matan Dady dukansu ukun bazasu soshi and hold him like a Son ba why, yanzu kenan duk yaron da mahaifiyar shi zata mutu tabarshi haka zaiyi rayuwa kowa na kyaranshi? This isn't right at all.






Tashi tayi ahankali jikinta duk yay sanyi taja jakanta tareda kashemai wutan dakin tafita ta rufemai kofan falo tawuce part dinsu, ahankali tabude kofar su gudun kar Mama taji ta maida kofar tarufe sanan tadaga akwatin dan karyay kara tai dakinsu, bamata kunna wutaba ta lallaba ta ijiye akwatin gefen gadonta ahankali kaman munafuka, fincikota dataji anyi saida tadan saki gajeren fitsari kunna wutan dakin akayi taga Yayarta Hajara ne tsaye jikin kofa sai maman su data mugun daure fuska tana rike da ita, sosai jikinta yafara rawa hakan yasa tace "M...Mama menayi?" hannu Mama tasa ta dauke ta da lafiyayyen mari ihu tabude baki zatayi Maman su tace "wlh, wlh kikamin ihu ubanki yaji ya shigo dakin nan saina miki abinda bantaba mikiba tunda na haifoki duniya" gyada mata kai tayi tsabagen rudewa tasa hannu takama bakinta tana kuka sosai mara kara, cikin mugun fushi Maman su tace "wato dan ubanki tunda Aliyu yabar garin nan nahuta yanzu yadawo kin fara, Rauda ni, ni, ni nan uwarki karimatu in tsugunna in haifoki kifito tanan Rauda" ta daura hannu gaban zanin jikinta tace "nasha azaban nakuda na kwana biyar, bayana kam har tofin yaasin akamini tsabagen yanda kika shirya karyashi kafin ki fito, sanan dakika tashi fitowan kika fito ta kafa nasha bakar azaba nice yau Rauda kike nunamin wani kasurgumin katon banzan namiji, mai kama da basamuden chan yafi ni ni mahaifiyarki, iyye Rauda? Nasaki ki daukomin zanin gado, Rauda ni zaki watsarma da wankakken zanin gadona fari kal akasa sabida kinga Aliyu, dan ubanki ciki daya kuka fito da Aliyun?" shiru Rauda tayi bata bata amsaba sai uban hawaye dake fitowa daga idanunta, cikin tsananin fushi Mama takara kamo gaban rigan ta bakinta na kumfa tace "kibani amsa, ciki daya kuka fito da Aliyu?" girgiza mata kai tayi cikin kuka tace "Yayan mune Mama" wani mahaukacin mari Mama takara sharara mata tace "dan ubanki menasha taraku nake fadamuku? Aliyu ba dan uwanku bane, babu ruwan ku dashi yanda baida uwa hakama baidaku, kuba yan uwanshi bane, haka zai karake rayuwanshi baisan dadi da soyayyan dan uwaba, ku dauka ko jini vaku hada dashi ba, yaron da ubanku ya fifitashi kan kowa na gidan nan uban me za'ayi dashi eh?" cikin kuka sosai Rauda tace "amma Mama shi aka fara haifa a gidan nan, kafin dukanmu, kuma Dady na nuna yafi sonshi ne sabida duk kunki bama marayan yaron soyayyar mahaifiya dukkun tsaneshi, maiya muku? Bai taba zaginki ba, bai taba miki rashin kunya ba, inya gaisheki baki amsawa bama kya kallonshi saisama yadena, duk kun rabashi da kowa, Anty Hajar ma bata gaidashi duk kun hana kaninshi gaidashi saidai idan sunga Dady ne zasu gaidashi, haba Mama kiji tsoron Allah, _d'a na kowane_ maiya muku eh? Idan yanzu kika mutu akamana haka yaya zaki dingaji akabari" shaketa Mama tayi ahaukace jitake kaman ta kashe ta tace "nikike kirama mutuwa Rauda akan Aliyu? Ba dangin iya bare na Kaka, saidai ke kimutu baniba kinji shegiya wacce ta debo jinin dangin ubanta mai bakin zuciya" ganin idanunta na juyawa yasa Anty Hajara da itama take mugun jin haushin kanwar nata sabida taurin kanta tazo ta cire hanun Mama daga wuyanta tace "ya isa haka Mama" cikin fushi da mugun masifa jikin Mama har barbar yake tace "Hajar ki barni na kasheta, baidai tafison wani kato akan uwarta ba, goben nan zakiji kishiyoyina sun faramin habaici na haifi munafuka, zataci ubanta ne saisa gwara ai aurenta da Khamis ta tattara tabar gidan nan ta tafi gidan mijinta nahuta inba hakaba bakin cikinta zai kasheni ne, dama Khamis din yacemin gobe zaizo yadauke ki kufita kibishi kufita dan kin gama zaman gidan nan balle kije kinama wani kato girki kega kuku yakarata chan daci a restaurant shidai da gidan ubanshi ba amma wlh bazaici abincin gidan ubanshi ba zan gyara miki zamane Rauda" ahankali Hajara trying to calm Maman su down tace "ya isa Mama kiyakuri, Bazata sakeba" dan shiru Maman tayi tana kallon yanda Raudan taduka tana kuka sosai mara kara kafin tai kwafa ta kalli hadadden akwatin data shigo dashi tace "kuma shegen akwatin nan kona shege zanyi" tasa hannu zata dauki akwatin da gudu tarike akwatin cikin kuka tace "Mama dan Allah ki barmin abuna" hannu Mama tasa zata fizge akwatin tarike gamgam tana kuka, cikin kunan rai Hajara tace "wai bazaki saki akwatin ba Rauda kanin ubanki ne yabaki akwatin, kisaki akace" cikin kuka sosai ta girgiza musu kai taki saki dan son abubuwan ciki takeyi sosai, Mama jitayi kaman ta kashe Rauda tahuta zata jibgeta Hajara tai sauri ta tare tasa hannu ta daki hanun Raudan tace "sake shegen akwatin" ta hankadeta tareda fizge akwatin tamikama Mama dan ayanda taga mama tasan zata iya jima Rauda ciwo ayanda ta zuciyan nan. Karban akwatin tayi ta kalli Raudan dake kuka kaman zata mutu tai kwafa tajuya tafita daga dakin tsaki Hajara tayi ta balla mata harara tahau kan gadonsu cikeda takaicin Raudan tai baccinta, sosai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login