Showing 57001 words to 60000 words out of 186400 words

Chapter 20 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt

20 Jan 2025

18832

idanun Aliyun ta kalla ganin da gaske yake kuma tasan zai iya dukanta dan Ya Aliyu mugu ne kaman ya Abdul yasa ta kalli gateman din tace "sorry" hararanta yayi yace "bacemin daga gani" da gudu tajuya ta shiga falon su, kudi yaciro daga aljihu dabaisan yawansu ba yamikama gateman din da sauri ya karba yace "innalillahi wanan kudi haka Alhaji, me za'ayi dasu?" murmushi yayi yace "gudunmawata, agaishe da Amarya" wani irin ihu gateman yayi hakan yasa Aliyu yajuya yay ciki yanadan murmushi, mamaki yake haryau gateman dinan bai chanza haliba, daga murya gateman yayi yace "Allah baka mata kyakkyawa wacce zata dinga saka farin ciki kaman yanda kasani yau nagode Yallabai" ganin Aliyu yama shige ciki a binshi yasa yajuya yana murna.
Da sallama Aliyu ya shiga falon dayasha kayan alatu, wata kyakyawar matace zaune kan dogon kujera tadanyi kama da Dady kaman kanwar shi kokuma cousin dinshi, hanunta rikeda bowl din slice friuts ga Ihsan a gefenta idanunta sunyi jajir tana kumbure kumbure, hararan Ihsan din yayi yana tahowa yace "tashi daga wurin nan" tashi tayi daga kusada matar tai stairs shikuma Aliyu yazauna kusada Momma tareda karban bowl din fruits din hannunta yace "Momma na" tallabe mai keya tayi da hannu hakan yasa yadanyi kara. "aucch Momma zafi fa" hararan shi tayi tace "kamin laifi tunda kadawo bakazo ka gaidani ba sanan daga zuwanka zaka dinga cin zalun autana" yatsine fuska yayi yana kai fruits baki yace "Momma Ihsan batada kunya zan kakkaryata in batai hankali ba wlh" haba Momma tarike tace "ahhh lallai ba shakka to mafashi, kaji ko mafashi nace, daga kai har Abdul din duk wanda yatabamin auta saina rama mata wlh, yayyun banza yayyun hofi masu cin zalun kanin su kawai" dariya yayi sosai yatashi daga kan kujeran yana hawa stairs rikeda bowl din fruits dinshi batare daya tanka ba, Momma data binshi da kallo tace "gaurayen banza aje ayi aure anki sai mugunta, katada wanan mugafalin dabaida aiki sai bacci" dariya yayi yawuce wani daki na karshe a corridor, bude kofar dakin yay ya shiga hango Abdul dayayi yayi daidai akan gado yana bacci ba riga ajikinshi yasa yay kwafa yafito daga dakin ya kwalama Ihsan kira. "Ihsan" da sauri tafito daga dakinta tace "na'am, gani Ya Aliyu" "ehen get me a cold water, very cold one, wanda yafara kankara daga fridge" gyadamai kai tayi tasauka kasa ko 1min ba'ayiba tadawo rikeda ruwan sanyin a gora dayadan soma kankara tabashi tana kallon fuskar shi, bowl din fruit din yamika mata yace "take it to the kitchen" yawuce ya shiga dakin tareda rufo kofa, ahankali yake tafiya har gaban gadon yabude goran ya ijiye marfin ya kwantarda goran ruwan ya tsayayo abayan Abdul dake sharara bacci, ihu Abdul yayi tareda zabura yatashi zaune sabida masifaffen sanyin dayaji, fashewa da dariya Aliyu yayi yana komawa baya ya ijiye ruwan kan center table yana dariya sosai harda rike ciki, saukowa daga kan gadon Abdul yayi yadau ruwan yace "yasin saina rama" da sauri Aliyu yabude kofa yafita biyoshi Abdul yayi, Aliyu ya sauka da gudu ya zauna kusada Momma yace "Momma kinga Abdul ko zai watsamin ruwan sanyi" daidai Abdul ya iso shima ganinshi kusada Momma yasa yakasa karasawa wajen ya tsaya anan gaban stairs Momma dake kallonshi tace "kazo mana ishashe, sai shegen son bacci kaman zakara, ai koda baizo yatasheka ba dani dazo kaga ainihin tashi, nafadamaka bazaka kara bacci mai kyau agidana ba, kai aure kaje gidanka inkaga dama kai baccin kwana uku babu maidamunka kaida matarka ne, amma muddin anan gidanne to ko kagama baccin lafiya da lumana" yanda ya daure fuska yana kallon tijaran da Momma kemai agaban Aliyu yasa Aliyu ya fashe da dariya, keyanshi Momma ta tallabe tace "kaima harda kai ai" gwalo Abdul yamishi yace "Allah kara" turo baki Aliyu yayi kaman zai mata kuka, dan murmushi Momma tace "ga abincin ku chan a dining inkunga dama kuci, gaurayen banza" tashi Aliyu yayi sukayi sama abinsu ko takan abincin basubi ba.




_duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafeba_
_Duk mai son book dinan should chat me up 07012181461_
[16/03, 13:02] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






2️⃣9️⃣










Zama sukayi akan gado Abdul zai fara masifa da sauri Aliyu yace "please jekai wanka inaso karakani hospital ne" da sauri Abdul yadaura hanunshi kan goshin shi yace "bakada lafiya ne Leo? Mekema ciwo?" girgiza mai kai yayi yace "am fine" "tome zakaje kayi a hospital?" kaman baiso yay magana yace "I wanna go see someone" kallonshi Abdul yayi irin anya Aliyu ne yay maganan nan kuwa dan yasan baida abokanai shi yanama shiga mutane ne dahar yasan wani dazaije dubawa a asibiti, ahankali kaman mai koyan magana yace "s...o..meo..ne? Someone Leo, waye someone kuma?" dan shiru Aliyu yayi yana kallonshi yarasa taya zai fadamai, dariya Abdul yafashe dashi yakoma kan center table yazauna yana daura kafa daya kan daya yana facing dinshi yace "shegen gora, koka fadamin gaskiya kokuma ko nan da chan like chan fa kofar dakina dinan da sunan rakaka wani wuri bazani ba, so tell me d truth" dan yatsine fuska Aliyu yayi yace "please now, kaga nagaji ni nai driving har nan hannuna duk sun sage karakani mana," da sauri Abdul yace "naji to tell me, who is someone, mace ne ko namiji?" hararan shi Aliyu yayi kafin yadauke kai murya chan kasan makoshi yace "mace" huuuuuu! Wani irin ihu Abdul yyi da ko Aliyu saida ya firgita yakoma cikin gado da sauri yace "are you okay me haka" hawowa gadon Abdul yayi da sauri ya dafa cinyar Aliyun yace "who is she? Yaushe kuka hadu Leo?" shiru Aliyu yayi kaman wanda ke tunani saikuma yadan numfasa yace "I just like her, she's just a unique being, her uniqueness yasa zuciyata zabota" kallonshi Abdul yakeyi yanda yake magana a yangance yana fitar da kalaman daidai dan murmushi yayi yace "itace batada lafiya saisa duk ka rame haka?" lumshe ido yayi kafin ahankali yabude idanunshi harsun dan chanza launi sunyi ja murya chan kasa cikeda damuwa yace "please tashi ka shirya" yanda duk yay wani iri yasa Abdul yaji tausayin shi dan yaga son yarinyar a idanunshi hakan yasa yasauka kan gadon ahankali yawuce ya shiga bathroom baiwani jimaba ya watso ruwa yafito ayanda yabarshi yazo ya tarar dashi yawuce wajen wardrobe dinshi shiryawa shima yayi cikin manyan kaya kaman na Aliyun yay kyau ya feffesa turare yajuyo yace "let's go" tashi yayi ahankali hannu Abdul yamika mai yace "car key karkazo ka kashe ni ahanya hakanan banyi aure na more ba" dan murmushi yayi saikuma ya yatsine fuska yazaro key yabashi karba yayi suka wuce suka fita, kallo Momma tabisu dashi kafin ma su karasa saukowa daga stairs tace "sai ina haka yan samari?" Abdul zaiyi magana Aliyu yarigashi yace "yanzun nan zamu dawo Momma" tabe baki Momma tayi tace "kwaji dashi kayan tusa, intai tsami maji, adawo lpy" wucewa sukayi suka fita suka shiga Abdul ke driving har asibiti, saukowa sukayi sukai ciki suka shiga reception, nurse din jiyace tana ganin Aliyu tagane shi da sauri tafito daga bayan kanta tasha gabansu tace "Sir barka da zuwa, kunsha bambam ne da patient din koba ita kazo nema ba?" gyada mata kai yayi ahankali, da sauri tace "ai bamasu dade da tafiya ba, an sallame su, wlh ansalame su suntafi gida, saida ma nataya namanta daukan jaka namusu rakiya har mota" shiru Aliyu yayi duk yaji ba dadi, ganin yama kasa magana yasa Abdul yace "thank you bari mubisu" ya kalli Aliyu yace "let's go" binshi abaya Aliyu yayi suka fita ganin duk yanda Aliyun yayi yasa yace "kasan gidan sune?" gyadamai kai yayi. "inane?" ahankali yace "Suleja, Sulejan mu?" gyadamai kai yayi daidai sun karaso mota suka shiga Abdul yay reverse suka fita daga gidan.












Tunda suka isa gida Ammi ta shiga kitchen tafara hada musu abinci itakuma Aneesa dasu Baffa suna falon su suna mata fira danji da ita suke bana wasaba Baffa ma da kanshi yafita yasiyo mata gyada dafaffa gwangwani biyu aiko sai ci take aranta sai murna take ashe haka akeji da mutum idan yay rashin lafiya ko wash tace sai an tambaye ta meke damunta.
Shigowa Ammi tayi da manyan kulolin tuwo ta kalli su Baffa tace "akawo miya Alhaji kuci yanzu" girgiza mata kai yayi yana tashi saga gefen Aneesa yana kakkabe riga yace "bari mudan shiga gari nida Na Sani, bayan isha maci kokai zakaci yanzu?" girgixa mai kai Na Sani yayi yace kinji ko, yajuyo ya kalli Aneesa yace "mezan siyo miki inzan dawo?" washe baki tayi tace "Baffa kashu nakeso" hararanta Ammi tayi tace "aikin kenan kwadayayya" rufe fuska tayi da hannu tana murmushi Baffa yadaga ma Ammi hannu yace "kinga, kinga ki barmin diya tahuta yaushe duka duka tafarfado dan haka dole taci tasha abinda takeso, zan taho miki dashi, anjima ai wayanki kinada kati ko" gyadama Baffa kai tayi tace "to kimin flashing danna tuna" da sauri tace "to saikun dawo Baffa" wucewa sukayi suka fita ta kalli Ammi tareda kyalkyalcewa da dariya kwafa Ammi tayi tace "zan cinmiki ne" tawuce tafita daga murya tayi tace "Ammi nazo nataya ki?" daga kitchen Ammi tace "sha zamanki, nama gama kaye kayen kitchen zanyi" Ammi tadau tsintsiya tana gyara kitchen din dan ansoma kiran magrib, turo kofar gidansu da akayi yasa ta ijiye tsintsiya ta leko tsakar gidan wani dan yaro ne yakara so tsakar gidan, fitowa Ammi tayi daga kitchen din tana kallon yaron tace "kai lafiya baka iya sallama bane" murmushi yaron yayi yana jan hanci yana share majinan kan hancin shi yadaga murya yace "Assalamu Alayyykummm wai ance Aneesa tazo awaje" da sauri Ammi tace "injiwa ye?" "nima bantaniba" yay maganan yana goggoge majina da hannu tsumman dake jikin window kitchen dinsu Ammi taja tadan barki kadan tazo gaban yaron tace "zo ashare majinan" sharemai majinan hancin tayi dana hannun shi sanan ta wanke mai hannun da ruwan dake cikin bucket din gaban rijiya tace "wai ance waye?" da gudu yaron yajuya yafita, yaye labulen bakin kofar su Ammi tayi tadaure fuska tace "waye yazo neman ki?" zuru zuru tayi tace "nima bansaniba Ammi" baki Ammi tabude zatai maganan saiga yaron ya shigo da gudu yace "wai yace Yusuf security ne" dan zaro ido Aneesa tayi tace "laaa Yusuf, Ammi mai budema mutane kofan shagon mune, security, hala Madam ta aikoshi" dan jimm Ammi tayi kaman mai tunani kafin tace "dauko hijabi kije kecemai rashin lafiya kikayi saisa basu ganki ba" gyadamata kai tayi takoma falon tadauko baby pink hijabinta har kasa dayay mata kyau fuskanta yay dan fayau aciki ta zura kafanta a slippers batare data tsaya saka safa ba tawuce tafita ahankali tabude kofa tafita, a kofar gidansu taga Yusuf Security zaune kan dan machine dinshi dama uniform dinshi bai chanza ba zuwa kayan gida, ganin Aneesa tafito yasa yasauko daga kan machine yana murmushi yana kallonta daidai lokacin Abdul yayi parking next to kofar gidansu Aneesan daga shi har Aliyu sun zubama on Aneesan data fito daga gidansu tana tafiya ahankali ido, karasowa gabanta Yusuf yayi cikeda damuwa yace "lafiya baki zuwa aiki Aneesa? Maiya same ki fuskan ki duk yay wani iri haka kin kumkumbura idanunki sun fada ciki" ahankali tace "rashin lafiya nayi yau aka sallamoni daga asibiti, ya akayi kasan gidanmu" cikeda damuwa kaman zai hadiyeta danso yace "innalillahi Aneesa rashin lafiya, no wonder tunda nadena ganinki nadena jin dadin rayuwana wlh ko aikin bayamin dadi sam sam, na damu iya damuwa shine nace bari kaga ko bango duniya kike inhar a Sulejan nanne saina nemo gidanku naji ko lafiya" dan murmushin yake tamai koba komi yay kokari tunda har yay tattaki yazo yaji ko lafiya, dan murmushi tasake yi tace "nagode" yanda tai murmushin tana dan juyakai yasa yaji zuciyar shi ya narke ahankali yace "wayyo Allah na, murmushin ki na haukata min zuciya da kwanya" gimtse fuska tayi tana kallonshi ganin haka yasa yasaki dariya yana daga hannu yace "maida wukan to, haba Aneesa sarkin masifa, ke baki bari ta tafasa balle to kone ba'a dan zolayan ki"




Ahankali Abdul dake kallon su Aneesan batare daya kalli Aliyu ba yace "is she the one Leo?" jin shiru Aliyu bai amsashi ba yasa ya juyo ahankali ya kallai su ya gani yana kallo idanunshi sunyi ja sosai kirjinshi na bugawa da sauri sauri danko shi yana ganin yanda kirjin ke sama da kasa tagaban rigan, da sauri yace "Leo, Leo are you okay?" wani irin bude kofa Aliyu yayi yafita daidai lokacin Yusuf ya zura hannu a aljihun wandon shi yaciro dari biyar ya mikama Aneesa yana murmushi yace "ga wanan asai su lemu asha Aneesa" da sauri ta girgixa kai tajuya zata shiga gida tace "kabarshi nagode, saida safe" hannu yasa yakama hijabinta yace "a'a wlh saikin karb......" wani wawan mari aka dauke shi dashi dayasa Aneesa dake kokarin bude kofa juyowa da sauri dan bama tasan yarike mata hijabi abinka damai dogon hijabi, hada ido tayi da Aliyu da idanunshi sukai jajir yana wani irin kallonta, Yusuf dafe kuncin shi yayi dan marin ya mugun shigan shi yana kallon fuskan Aliyun, dauke kai Aliyu yayi daga kallonta ya fizge hijabinta daga hannun Yusuf din yanamai wani irin kallon tsana jiyakr kaman ya chakamai wuka, janye hannu Yusuf yayi daga inda Aliyu yamai marin ya kalli Aneesa yace "waye wanan Aneesa?" cikin fushi Yusuf ya kalli Aliyun yace "kasan koni waye dakamare ni, kasan me tsakanina da Aneesa, kasan tun yaushe nasanta nake rainon sonta axuciya kasan koni waye? A whole chief security officer ka mara" cikin mugun zuciya Aliyu yanunamai machine dinshi yace "take your bike and get out of here right now and never come back" "baza'a bar nan dinba, kuma wlh zan nunama kai kuskuren mari na" hannu yadaga zai kodama Aliyu mari da sauri Aneesa ta shiga gaban Aliyun kirjinta na daukan uku uku hakan yasa Yusuf ya tsaya tsak batare dayay marin ba, dan juyowa Aneesan tayi suka hada ido da Aliyun dake kallonta da sauri ta dauke kai ta maida kanta kan Yusuf tama rasa mezata ce gabanta sai faduwa yake itadai kawai bataso Yusuf ya daki Aliyun dan tasan baida karfi, bakinta har rawa yake tace "uhmmm karka marai, yakuri katafi please" cikin fushi Yusuf yace "natafi Aneesa kikace?" gyadamai kai tayi da sauri kaman mai koyan magana tace "uhnnn.....eh, k...katafi" cikin fushi Yusuf ya kalli Aliyun tareda mai pointing idanunshi da yatsu biyu yace "watch out, zakasan katabo haifaffen dan Suleja" yahau kan machine dinshi ya burga azuciye yabar wajen bin machine din tayi da kallo harsaida tadaina hango machine din sanan tajuyo ta kalli Aliyun cikin fushi tace "why did you slap him meruwan ka dashi eh?" cikin tsananin zuciya Aliyu yace "why are you talking to him? Nace kiyi magana dawani ne eh?" ganin yanda yake magana kaman zai daketa yasa ta saukar da kanta kasa batare da tace mai komiba shikuma abinda ya tsana kenan, tsawa yadaka mata kishi kaman zai hadiye zuciya yamutu yama manta da bata da lafiya yace "am talking! Mesa kikamai magana? How dare you talk to him haryana rike miki hijabi" faduwa gabanta yayi cikeda tsananin tsoro da sauri tajuya ta kalli kofar gidansu tsoron kar Ammi taji hayaniya tafito take gashi magrib yayi sai kallonsu masu wucewa ake, bakinta na rawa sosai cikin bacin rai tace "wai me ruwanka dani eh? Kadenamin ihu, karka sakemin ihu" tana gama maganan tai fuuu tabi ta gefenshi zata shige gida hanunta ya rike chak da sauri tadago kai ta kallai, fizgota yayi back azuciye.




_*how to subscribe*_
_zaki turo 300 ta account 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment ta watsap number na sainai adding dinki a group din danake posting_
_you can also send MTN card 300 for those dabasu da account_
_duk wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa_
[16/03, 15:30] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






3️⃣0️⃣










Kaman ya jawo tsinke haka tadawo luuu numfashinta na fita sama sama kaman zata suma, cike da masifa sosai kaman zai daketa Aliyu yace "how dare you walk out while am still talking to you" kasa magana tayi sai hanunta datake kokarin fizgewa, kara matse hannun yay da kyau dayasa ta runste ido da karfi sabida zafi, cikin muryan fushi Aliyu yace "get this straight I love you Aneesa, I Love You and I don't share what I Love, koma waye kike tareda su kirabu dasu this should be the last time dazan kara ganin kina magana dawani inba hakaba u will see my other side, and you're not gonna like that, last warning!!!" sakin hanunta yayi azuciye yawuce wajen mota, dago kai tayi tana kallon motan daya bude ya shiga tana shafa inda yarike dake mata mugun zafi idanunta sun cicciko da hawaye zuciyarta na tafarfasa, da sauri tasa hannu ta share hawayen wani irin masifa yataso mata, wajen motan daya shiga tayi kaman zata tashi sama ta window inda yake da glass din yake arufe ta tsaya, glass din tinted ne bata iya ganinshi dukan glass din tayi da duka karfin ta da hannu hawaye na cika idanunta cikeda masifa tace "ba'a sonka din, ba'a sonka din do your worse, ance ba'a sonka din" yanda take bubbuga glass din motar zaka zaci fasawa take shirin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login