Showing 126001 words to 129000 words out of 186400 words
Chapter 43 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt
kazabura kamike tsaye, menene?" dago jajayen idanunshi Aliyu yayi dan mugun haushin Abdul yakeji, dashi da Momma da Dad dukansu su ukun, hanun Abdul din ya kabar daga kafadarshi yace "don't f*cking touch me Abdul, nafada maka stay away from me" yay maganan yana tsallake mug din daya fasan yay hanyar bedroom dinshi da sauri Abdul yabishi riganshi yarike tabaya yace "What's up with you Leo sabida Rauda tarasu ne kake wanan masifan? Sai dauremin fuska kake, kaki kulani tunda mukazo eh? Menene? Menamaka? I feel there's more to this your anger, talk to me Leo mena maka wai?" fizge bayan riganshi Aliyu yayi azuciye yay handar daki da sauri Abdul ya shiga gabanshi yatare kofan da bayanshi cikin fushi yace "wlh ba zaka shiga dakin nan ba saikamin magana" cikin wani irin zuciya Aliyu yayo kanshi ya chakumo mai riga idanunshi sunyi jajir, cikin tsananin fushi Abdul yace "dakanni mana tunda fada kakeso ayi, beat me kaji, nace kafadamin mena maka, why why why are you angry Aliyu?" cikin fushi Aliyu yace "please kamin shiru, I tot u are my blood Abdul, nadauka in my absence u can stand for me ako'ina aduniyan nan, u are the first person to know how deeply my love for Aneesah is, nasota tun kafin Dady ma yasan mahaifiyarta harya aurota yakawo ta gidan nan, how could you? You couldn't defend Aneesa na in my absence, kabari Dady yakaita Prison, do you have any idea what she went through a prison dinan? Kaga condition din prison din da aka kaita kuwa? Can't you defend my woman bayan kasan yanda matayen Dady suka tsaneni they can do absolutely anything possible to me eh? After everything dakamin kazo kanamin magana u think am that weak Aliyu you use to know? All of you consider me as a weak person kunkai wacce nakeso gidan yari, kun azabtar da ita sanan kana daukan zan nuna everything is okay? No, no, no way Man, bari kaji am not that old Aliyu that u know, and duk wanda yake da sa hannu aka kaimin Aneesa prison I will never be in peace with that person, I can't forgive you Abdul, I can't" yana maganan yajuya zai fita da sauri Abdul yabishi yarike shi gam sanan ya zagayo ta gabanshi ya idanunshi sunyi ja kaman zaiyi kuka, murya chan kasa yace "am sorry Aliyu, I am so sorry Cousin, kayakuri Leo, ni karan kaina kunyan kaina nakeji but what can I do? Eh, sai bayan Dady ya kaita prison naji a asibiti dayazo yake fadimana, dana fara karyatawa Aneesa bazata iya hakaba ya nunamana footage din I was shocked, I was flabbergasted, situation dinka at that moment na rashin lafiya yasa bansami daman bincike koyin wani abuba akan video I only watched it once nacigaba da lura dakai dan Dady is always going out ya kawo wayanan doctors din da zasu dubaka sanan yana zuwa embassy, karkai fushi dani dan uwana kai kadai gareni, I know how you feel, I know how strong your love for Aneesa is, true love never dies, we will go through this together, duk abinda kaga yafaru da soyayyar ku haka Allah ya tsara dama chan zai faru, babu smooth Love Leo, kowani soyayya nada nashi up and downs din, this is not time to be blaming anyone, this is time dazamu natsu mujira ayi sadakan bakwai sai mu sami Mum mubata hakuri, let's calm her down dan anzalunci yarta, an cutar da ita, and in sha Allah Aneesah ce matarka komin runtsi, komin wuya kaji kanina, we are in this together cousin" ahankali Aliyu ya dago kai ya kallai dudda kalaman shi sun ratsamai zuciya ya sosamai inda kemai kaikayi yace "thanks, but am fighting my battle alone" yana fadin haka yafice tareda bude kofan yafita tsakar gidansu, mutanene sosai da jama'an Dady zazzaune kan maka makan taburman da aka shimfida duk anzomai gaisuwa, waje Aliyu yafita ya tsaya yana kallon hanya, abun duniya sunmai yawa ga rasuwan Rauda sanan ga matsalan rayuwan shi da Aneesa, he feels like crying but bazai kara kukaba, he is strong, he is strong, he will handle this, hannunshi yadaura akan zuciyan shi ahankali yace "Anebaby" shiru yadanyi kafin ahankali yace "stay put, stay safe, am coming for u duk inda kike aduniyan nan, I l...ove ....you" yadanyi shiru ganin muryan shi narawa kafin ahankali yace "always". ganin kanshi yasoma masifar ciwo yasa yabude idanunshi ahankali kafin yawuce masallacin anguwan su yadauro alwala ya shiga cikin mosque din.
****
_Kaduna_
Hannunta tadaura akan zuciyanta dake wani irin bugamata tana ganin fuskan Aliyu, da last moments dinsu, her heart seriously yarns for Aliyu but abu daya tasani shine bazata taba auran shiba aduniyan nan, bazata taba aurenshi ba, ta tsani gidansu Aliyu sanan ta tsani Abba daya mata shegen duka yabada ita ga police, but she just wish she can see Aliyu one last time tanason taga halin dayake ciki yaji sauki?? Wani irin kuka take sosai mai tsuma rai, cikin kukan tace "Ammi, banson naje gidan nan, na tsani gidan, ni Ammi na kawai nakeson nagani, Ammi na, nadade banga mamana ba, na tsani kaina, I hate myself, banson kaina, ni nasan bansama mutum guba a abinci ba amma nagani a camera da idanuna cewan nida kaina nasa guba a abincin, aka kaini gidan yari bayan yan sandan sun kaini police station sunmin dukan bala'i dawata irin bulala, no body knows what I went through, aka kaini gidan yari, manya manyan matane nagani awurin, bansan me gidan yari ba but danaje naga suna neman kasheni yasa nima na farayi kaman su, na nemo wukake, da makamai duk wanda yazo kusadani illatashi nakeyi dan ko banyiba su haka zasuyi, duk jikina shaidojin bulala ne kala kala da makamai, I've grown thick skin, nakoya ta hardest way cewan dole saina koyi yanda zan kare kaina nima, na tsare kaina inba hakaba kasheni zasuyi, nagaji, nagaji da komi, kowa bayasona, wajen Ammi na zanje, kowa korana yake, ance ni mayya ce, ance banda imani sunsan irin wahalan danasha ne? Sunsan medame akamin?" tafashe dawani irin kuka dayasa Zaid yaji kaman ya tsugunna ya tayata yi, daga maganganunta yagane kaman ankaita gidan yari akan case din saka guba a abinci ne, to sunan namijin data fara kirafa Aliyu? Ko shine akace tabama guban?"
Ahankali ya tsugunna yazaro handky daga aljihun shi yamika mata yana girgiza mata kai murya chan kasa yace "kidena kuka, clean your tears" dago jajayen idanunta dake fitar da ruwa sosai kaman famfo tayi ta kallai, gyadamata kai yayi yace "please ki karba" ahankali tamika hannunta yasa mata, goge hawayen tayi ahankali da sun kasa dena zubowa, cikin kwantar da murya yanda koma mezai fadi zai shegita sosai yace "the feeling of mutum ya tsani kanshi sanan yanaganin kowa dake tareda shi ya tsaneshi shine abu na farko dake wurga mutum to depression, Aneesah!" ahankali tadago jajayen idanunta dake cikeda da hawaye ta kallai, kwayan idanun har kyalli suke yace "inada Sister her name is Fauzy she's just like you, the first time dana ganki hakanan naji wani iri, bazan iya barinki a condition din dana ganki ba, dudda abubuwan dakika min bantaba jin tsananki for once ba dan ganinki nake kaman kanwata, am a Dr dake da 2degree, surgeon sanan my second degree na karanci psychology, am a psychologist, I know alot about physical and mental state of person, nasan both normal and abnormal behaviour of mutane, when I first saw you Aneesah" dan shiru yayi ya lumshe ido yace "I saw a little young lady that was depressed, abinda nagani a fuskanki was anger, resilience, and a strong young lady that is forming she's strong yet her heart is as fragile as egg york, she misses her love ones but fushin datakeji yanagab da overpowering nata dan tana saukar da fushin ne akan kowa da wanda ya dace da wanda bai dace ba and that could lead you to abinda zaki iya nadama nan gaba, I want to help you but dole saida amincewar ki, can you take me as yayanki?" yay maganan yana kallon fuskarta da hawaye yagama wankewa, yanda take kallonshi idanunta sunyi jajir harsun soma kumbura ganin batada niyyan mai magana yasa yace "pls Fateema, allow me to become your brother, I want to guide you, namiki fada in kinyi kuskure and take care of you, help you overcome this tough phase of life, banda wata manufa, dan haka karki yi tunanin komi am just someone danasan Allah yahada mune danna taimakeki kin yarda?" yanda yay maganan yasa ta gyadamai kai kawai ahankali tana kallon fuskanshi sai taga lips dinshi kaman na Ya Aliyu saidai na Aliyu sunfi nashi pinkish sosai, Aliyu kuma yafi wanan haske sosai dudda shima yanada haske, wani irin murmushi yasakin mata ganin ta amince yace "yauwa yar kanwata, tashi kije ki wanko fuskanki to" da sauri Baffa da tunda ya ijiye su Ibrahim adaki yafito danyasami Dr yaji yanda Aneesa ke kuka abakin kofa ya tsaya ta bala'in bashi tausayi jin maganganun ta, ganin yanda Dr yabi da ita yasa hakanan Baffa yaji inama zaice yanason ta dan yamugun iya tafiyar da mutane kaman abinda ya karanta kenan. Dakinshi yakoma yay shiru yana jiran zuwan su Na Sani.....
Tashi tayi ahankali yana kallon fuskanta tafice, wanko fuskar nata tayi ta shigo dakin ta zauna abakin gado tana wasa da yatsunta, tasowa yayi yana gyara statoscope din dayake rikedashi yazo gabanta yace "meke miki ciwo yanzu?" batare data kallai ba tace "babu komi" hannunta yakama ahankali yay placing statoscope din yana sauraran heart beat dinta, sosai Aneesa ke kallon yanda yarike hannunta wani iri taji kaman shima ya lura da haka ne ya saki hannun yazauna a gabanta yana kallon fuskanta batare dayace mata komiba, dagokai tayi ta kallai kaman dama abinda yake jira kenan ahankali yace "kinjima yan uwanki rauni sosai, promise me zakije kibasu hakuri kinji yar kanwata" , gyadamai kai tayi da sauri yace "zakije da gaske?" gyadamai kai tayi alamun eh, murmushi yayi yace "ashedai kinajin magana kanwar nan tawa" murmushi tasakin mai for the first time tunda suka hadu jiya da mugun sauri ya janye kanshi sabida wani irin lotsawa da dimples dinta sukayi saida yaji kaman numfashin shi zai dauke yakuma rasa maisa hakan, mikewa tsaye yayi ahankali ya kalleta yace "gobe nazo nadubaki kanwata?" da sauri ta gyadamai kai, dan hararanta yayi cikeda wasa yace "waike baki iya magana bane, common talk to me, nazo nadubaki give?" murmushi tayi kafin ta juyar da kanta akunyace tace "kazo yayana" "shikenan I will come tunda kanwata nason ganina, bye" dagamai hannu tayi itama harzai fita sanan yasake juyowa da hannu ya nunata yace "No more fighting okay, promise me bazaki kara fada da kowa ba you will control your anger and d temper kome aka miki innazo kifadamin promise me" ahankali tace "I promise" murmushi yamata yace "and don't worry nasan duk inda Ammin ki take tunanin ki takeyi dan yarinyar ta akwai shiga rai, zata kiraki am sure" murmushi tamai sosai fiyeda nada sabida yanda yabata assurance cewa Ammi zata kirata, hakan yasa yajuya da sauri yafita hango fitowarshi yasa! Baffa yafito daga dakinshi, hannu Baffa yabashi bai karba ba saidai dukar dakai dayayi kasa yace "zan tafi Abba" cikeda da so Baffa yace "nagode sosai likita Allah yay albarka kaji likita, mun gode, wai ya sunan ne inata kiranka da likita" Baffa yay maganan yana dariya irinta manyan nan, ahankali Dr yace "sunana Hafiz Abdulwahab Zaid, saisa Dr Zaid yabini but Zaid din sunan kakanane" gyadakai Baffa yayi cikeda gamsuwa yace "masha Allah ba shakka, sunan mai dadin gaske, Allah yayi albarka Hafiz, Allah ne kawai ya aiko mana dakai, nagode sosai Allah yay albarka" sosai yakeso yama Baffa maganan Aneesa amma yana mugun jin nauyi hakan yasa yajuya yatafi Baffa yarakashi har kofar gida, bude motan yayi ya ijiye akwatin kayan maganinshi sanan ya zauna yatada motar yana tunane tunane Aneesa ta shiga ranshi ta zauna daram yarasa mesa tunko jiya dan bacci rabi da rabi yayi yana tunanin ta saisa yazo da wuri danda yay niyyan sai da daddare zaizo amma yakasa daurewa ya shiryo yataho yana zuwa kuma hayaniya da ihu dayaji yasa yafada gidan nan yaga aika aikan da Aneesa takeyi, Allah ya gyara yarinyar nan she seriously need therapy and insha Allah kadan kadan ahaka zaita bata har saita gyaru.
Gaban wani tangamemen gida a GRA yay horn budemai kofanBudemai kofan akayi yaja motar ya shiga ciki gidane babban gaske irin na yan gayun nan, parking motar yayi yasauko yana tafiya ahankali har zuwa flat dinsu bude kofa yayi, wata yar matace dakana ganinta zaka gane mahaifiyar shice a zaune sabida mugun kaman dasuka yi tana binshi da kallo wata mata haka na gyara mata kumban hannu, maida kofar yayi yarufe yace "Mum sanunku" hararanshi tayi ta kalli matan datake gyara mata kumban tace "please excuse me Charity" da sauri matar tabar falon, ganin haka yasa yafasa zuwa saman ya zauna kusada ita zaiyi magana ta kama lips dinta tace "kamin shiru I didn't ask you to talk" shiru yayi yana kallonta, cikeda masifa tace "zan sabamaka fa Hafiz, Allah inhar kana wasa da cikinka bazamu shiryaba, now just silenty stand up ka wuce dinning ka zauna nazo nabaka abinci, breakfast bakayiba kafita, jiya da daddare dudda uban hanyan dakashawo ga tuki all the way from Abuja lipton kawai kasha ka kwanta eh wani irin abune ina fama da little Fareeda taci abinci kaima ina fama dakai are you a baby" dan dariya yayi cikeda tsokana yace "to what I am before? Am your baby Mummy amman big baby ki" dariya Mummy tayi ta tallabemai keya tace "common tashi" tashi yayi ahankali yabita tana tafe tana mitan rashin cin abincin shi yana murmushi yace "Mum where is Princess?" kujera Mum tajamai yazauna akai tace "sunje saloon itada Rumana yin kitso" dan gyadakai yayi batare dayace komiba ba, lafiyayyen abinci ta zubamai jellof rice dayaji kaza sanan ta zauna kusada dashi ya turamai gabanshi kallon abincin kawai yake dan yasan bazai iya gamawa dashiba ko kadan amma yana tsoron magana Mum ta haushi da bala'i, spoon yajawo ya shiga ci ahankali kaman wani dan jariri.
*********************
_Bayan Sadakan Bakwai_
Yau kimanin kwana tara da rasuwan Rauda. Tun ranan da Rauda tarasu rabon da Ammi tasa Daddy a ido amma ko ajikinta dan ta tsani ganinshi daman, Alhamdulillah tsawan Kwanaki taran nan bata waniyi wahalan laulayi ba banda aman safe da kullum saitayi daganan kuma ko ciwon kai bataji, cikinta yafito sosai kaman cikin dayakai wata biyar, kullum saita kira Baffa yahadata da Aneesa su gaisa dudda daidai daso daya baitaba gayamata cewa ga wani abu dangane da Aneesan ba, kullum gayamata yake lafiyan ta kalau karta damu tacigaba da rayuwan gidan mijinta tana aikin lada domin aljanna ta na karkashin kafanshi ne, sunan zasu cigaba da kulamata da Aneesan.
Yau tunda ta tashi take da niyyan zata wanke kayan ta da sukayi datti dudda tanada yar aiki bazata taba bama yar aiki kayan ta ta wanke mataba, iyakan aikin yar aikin shine share tundaga dining har falo sai sharan gaban flat dinsu dakuma share kitchen da wanke wanke dudda uban laulayin datake daidai daso daya bata taba bari yar aikin taje sama ta gyara mata bedroom dinta ba da kanta takeyi hakama girki saidai randa batada karfin yi saita cema yar aikin tadafa mezataci da yamma saita tafi gidansu.
Hada duka kayan dazata wanke tayi a basket yawacinsu hijabai ne saikuma dogayen riguna datafi sakawa kwanan nan dansu sukafi mata dadin sawa, hijabi ta daura akan riga da zanin dake jikinta na atampa tabude kofar dakinta tafito ta sauko downstairs tana shakan kamshin hadadden turaren wutan da dakinta keyi wanda yar aiki ta kunna a burner ko ina yadau kamshi, kofar flat dinsu tabude tafito rikeda basket din tana zura slippers dinta ahankali.
Tunda tabude kofa Dady dake cikin mota da tundazu yadawo yakasa fita sai tunane tunane yake ya kafeta da ido yana kallonta, yarame sosai kana ganinshi kasan yanacikin damuwa bana wasaba, ga rasuwan Rauda, ga Aliyu na fushi dashi sosai, gakuma Rukayya da wani irin nauyinta da kunyan ta yakeji dako lokacin dayazo neman aurenta baijin yaji kunyanta da nauyinta hakaba, yagama wulakantar da yarta akan abinda ba ita ta aikata ba, baimasan tayaya zai fara bata hakuri da neman gafarar taba, shikadai yasan abubuwan dake damunshi arai, tunda tafito yake binta da kallo ya kafe cikinda dayadan fito ta hijabi da ido yanajin wani irin sonta da kewanta na ratsa kowani bangare dajijiya na jikinshi, ahankali yaga take tafiya da kafafunta dasuka sha Jan lallin gargajiya na salatef gwanin van sha'awa harta shiga laundry dinsu.
Matan Dady biyu tagani a laundry suna dan fira suna jiran kayan dasuka saka a washing machine din yagama wanke musu yasa taji kaman tajuya sabida ganinsu datayi saikuma tafasa ganin akwai washing machine har guda biyu dat are free, dan 4 manya manyan washing machines ne a gidan, ahankali takarasa ciki saida takai daidai wurinsu sanan tace "sannunku" wani irin banzan tsaki amaryan Dady taja ta kalli Amina matar Dady tabiyu tace "Amina ana magana fa" dan dariya Amina tayi tajuyo takalli Ammi daga sama zuwa kasa ta tabe baki sanan tajuya ta kalli Amarya tace "kinsandai ninafi karfinta wlh tayi kadan tasa akaini gidan yari kokuma tahadamin wani makircin saidai ke Amarya" wani irin dogon tsaki Amarya taja tace "wutsiyar rakumi tai nesa da kasa itama tasan nafi karfinta takowanni fanni, bana maulan abama y'ata aiki a bakery, bana tura yarana gantalin duniya ana zuwa ana lalle ana nemo kudi, gidan hutu na tashi ko anjiman nan nakira babana nacemai inason kaza zai aikomin dashi, tafitar da Kareema da makircin ta kullum sai uban saka hijabi kaman mumina ni tai bala'in kadan, tagama makircinta bata isa ta fitar dani daga gidan Alhaji ba tai kadan ne ina gayamiki, kuma kigayama yar agolanki ko an sakota daga gidan yari ta tafi gidan ubanta bazata zo tanacin kudin ubanda banata ba taje taci na