Showing 9001 words to 12000 words out of 186400 words

Chapter 4 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt

20 Jan 2025

18792

Rauda taci kuka harta godema Allah ahaka bacci yay awon gaba da ita awurin.
[02/03, 16:58] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






3️⃣




_How to subscribe_
_*zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turamin evidence of payment to WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*_


_*zaki iya turo katin MTN 300 ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group danake posting*_




_Free page_




Da asuba ya tashi da kyar shima sabida alarm din gefen gadonshi ne daya saita yatadashi, tashi yayi ya shiga bathroom, yadade aciki kafin yafito cikin wani blue bathrobe, zama yayi abakin gado ya shafa manshi mai kamshi a tsanake sanan yatashi wardrobe dinshi yaje yabude yaciro wani black belted cotton poplin cargo trouser da wata farin logo print t-shirt na Ambush yadauko yasaka, yabude bangaren rigunan sanyin shi yana tunanin wanda zai saka kafin yajawo wata logo embroidered wool fleece jacket itama ta Ambush, yasaka rigan tazauna ajikinshi tamai kyau sosai, yadau designers turarukan shi ya fesa sanan ya shimfida dadduma yay salla yana sallame wa yaji ana bugamai kofa, yatsine kofa yayi sanin mayun nanne, da kyar cikin isa da izza yace "come on in" bude kofa bodyguard din yayi rikeda wata yar karaman tray da small mug of hot coffee kekai, karasowa gabanshi yayi ya ijiye tray kan dadduman yace "have this sir, we are leaving in the next 10min" daure fuska yayi yace "where is d other guard? Lucas is his name right?" yay maganan yana mai alamu da yatsa ayangance, gyadamai kai bodyguard yayi yace "yes he's Lucas, I left him outside he's packing out luggage to the car" yatsine fuska yayi as usual yatashi daga kan dadduman yahau kan gadon yazauna yamai pointing coffee da yatsa alamun yabashi ysha, daukan coffee yayi da sauri ya mikamai karba yayi yakai bakinshi yay sipping dan ficili ya zare daga bakinshi batare daya kalli Guard dinba yace "where is my phone? Dad dina yakirani?" "your phone is here sir" yakarasa kusa da bedside lamp yadau wayarshi dat was lying there yadauka ya danna wayar dababu any security lock ajiki yace "No sir, babu miss call din kowa" dan kwafa yayi baisake cewa komiba yacigaba dashan dan coffee ayangance sanan ya gama yatashi ahankali yay gaba bodyguard din ya gyara ko ina sanan ya kashe wuta yabiyoshi waje harya shiga mota yawuce ya shiga gaba suka wuce Airport.










Sai fushi fushi yake sabida Dad baikiraba shikuma bazai kirashi ba saisama yabarma bodyguard din wayar dan yasan in yana hanunshi zai iya yakirashi, ya tsani British Airways dan sunada wani banzan dabi'an batarma da mutum luggage saisa tun jiyan yasa suyi booking air France, sai tunanin uban zaman dazaiyi cikin jirgin yake inhar basuyi stopover ba flight dinshi is 18hrs flight inkuma jirgin ya tsaya for fueling ko cleaning kokuma wani dai emergency, kokuma weather issue zasu iya 20hrs or more than sef saisa he came prepaid yasa kayan sanyi idan ya shigama he will request for a blanket or showel duk wanda suke danshi gaskiya shi bazai saka pyjamas din airline ba, kuma yanada matsalan jin sanyi sosai, checking in sukayi suka karbi ticket sukai departure lounge basu wani dadeba suka fara boarding karfe 7:15 jirgin su yadaga sai kallon lokacin yake yana kokarin hararo wat time is it yanzu a Nigeria, dan Nigeria is almost 9hrs ahead of California, dan murmushi yayi ganowa dayayi yanzu darene a Nigeria probably hala Dad yay bacci saisa bai kirashi ba.










8:40 na dare jirgin su yasauka a Abuja, fitowa sukayi kana ganinshi kasan yagaji sosai saukowa suka farayi bodyguard dinshi biyeda shi, wuraren Tara suka gama komi suka fito ta arrival sai kalle kalle yake ya tsaya chak dan baiga wani nashiba baiga wani direban gidansu ba baiga Daddy ba, wani irin haushi ne yakamashi yamikama bodyguard hannu alamun yabashi wayarshi, karban wayan yayi dayariga ya kunna mai ya shiga dialog Dan kiran Dad dinshi, fizge waya yaji anyi daga hanunshi da sauri yadago kai wani magidanci ne kamansu daya sak dan shima farine sol alamun tsufa daya bayyana tattare da magidancin ne zaisa kawai kagane ba yan biyu bane uba da d'a ne, dudda fushi yake da Dad amma baisan lokacin dayasaki wani murmushi ba yawani irin rungumeshi ba so tight yace "Daddd dy" murmushi sosai mutumin yayi yana bubbuga bayanshi yace "na'am Aliyu na, sarkin zuciya, Aliyu an mazajena" dariya daga shi har Aliyun sukayi sanan yasake shi ahankali yana kallonshi kaman yanda yake kallonshi yace "muje kahuta kagaji da yawa karka fadi" sukai wajen mota bodyguard na binsu abaya, motoci biyune bodyguard suka shiga dayan Daddy da Aliyu kuma suka shiga motar Daddy, kwanciya yayi ya daura kanshi kan cinyar Dad yana yatsine fuska, kallo baban nashi ya binshi dashi yana mamaki yaushe Aliyu zai chanza yadawo namiji, son jikinshi da rashin kuzari is too much, hanunshi ya chusa cikin kanshi yana mishi head massage yace "sannu kaji Son kagaji sosai ko?" gyadamai kai yayi idanunshi a lumshe yace "bakaine kawani ce mutum yadawo ba, I need hot bath jikina kaman an kakkaryani Dad" "tooofah, sannu yaron kirki, muna zuwa gida zakai wanka kaci abinci saikai wanka abinka" gyadamai kai yayi a shagwabe yana sauke ajiyan zuciya yanajin dadin yanda Dad kemai headmassage din.










Agaban wani babban gida sukai horn wani soja yabude musu Gate din, tashi yayi ahankali ya zauna yana kallon babban gidan nasu da babu kowa a ciki, shiga ciki sukayi sukai parking bude musu kofar motar akayi, ahankali suka fiffito daga motan yana kallon gidan, babban gidane dake dauke da manya manyan flat flat guda hudu, sai daga tachan dayan bangaren kuma wani babban flat guda daya ne, shidai babu yanda zaiyi da Dad ne amma harga Allah baison dawowa Nigeria ba, ya tsani gidan mahaifin shi sosai, he hates this house with all his heart, dafashi da akayi yasa yadaga kai ya kalli Dad din yadan turo baki kaman mai shirin yin kuka, murmushi Dad yamai tareda sumbatan goshinshi yace "all is well Aliyu am here for you kaji relax, muje" gyadamai kai yayi suka fara tafiya bodyguard kuma nawajen mota suna fito da kayayyakin su daga boot, wata yar budurwace doguwa dabazata wuce 20yrs ba sanye dawata doguwan rigan atampa tafito daga wani daki dasuke kira da laundry tariko wani white folded zanin gado a hanunta tajuyo, ganin Aliyu tareda Dady yasa ta tsaya chak tareda bude baki cikeda mamaki danko kadan Dady bai sanar dasu zai dawoba, tsayawa Aliyun yayi shima yana kallonta da idanunshi dake cikeda gajiya, murmushi Dady yayi yace "gata wajenka nan ai banfada mataba I want to surprise her taganka kawai kaman daga sama" murmushi sosai yayi yana kallonta batare dayace mata komiba ya daga mata gira daya alamun kallon fa baki sanni bane? Watsar da zanin gadon tayi akasa tsabagen rudewa tasa hanunta takai kan saman idanunta ta murza idanun irin ta kara tabbatarwa ba gizo idanunta kemata ba sanan tabude su, tagadai still dai yana tsaye inda yake kusada Daddy dake sanye da babban riga that means Yaya Aliyun tane, wani irin ihu tayi dayacika gidan. "Yaya Aliyuuuu, Yaya Aliyu oyoyo" ta tafi dawani irin mugun gudu hakan yasa yabude mata hannu da gudu taje tai wani irin tsalle tafada jikinshi ta rungumeshi sosai her heart couldn't contain her happiness sai kuka, hakan yasa Dady yace "kagamin shagwababbiyar yarinya, kin wani dane jikinshi zaki karyamin shi saikuma ki sakinmai kuka dukshi kadai, haukatashi kikeso kiyine daga dawowan shi, cikashi" kojin maganganun Daddyn suma batayi sai kuka take bayanta ya shafa ya bubbuga alamun tai shiru, jin karan bude buden kofofi wanan nabin wanan yasa yadago kai matayen Dadyne kowacce tadan leko dakai daga flat dinta ga yara manya da kananu duk sunaso sufito suga ihun mai akeyi a tsakar gida sun hanasu fita, fuskarnan bayabo ba fallasa duk sai kallonshi suke kaman yau suka fara ganinshi, babban cikin matan ne tadan tabe baki tace "ahhhh manyan baki su Aliyu ne agarin, mutanen turai saukan yaushe ko sanarmana ba'ayi ba, hala cinye dan gwal din zamuyi maigida" tasake tabe baki tana kallon Rauda da har lokacin ke rungume da Aliyun tace "sannu da zuwa Aliyu, kekuma ina zanin gadon danace kikawo min uwar shishigi?" kafin Rauda tai magana Dad yace "ahadama Aliyu lafiyayyen abinci Kareema" dan juya ido tayi tace "haba Alhaji saida abinci yakare kasan yawan yaran gidan nan gasuda shegen ci barin ma yaran Amaryan ka, aida kafadamana zaizo dasaimu saka dashi a girki, shi yaro kasan bacin abincin yan aiki yakeba dasai ace suhadamai koyar Indomie ce, kaga kumani wash Allah" tadan yatsine fuska tana dafa kafarta tace "kasan ina fama da wanan ciwon kafan bazan iya shiga wani kitchen ba Alhaji sanyin kashi dazaran dare yayi saidai kaji kasusuwana nakiran salla" shiru Dady yayi yana kallonta baiso yay hayaniya agaban Aliyu da dawowan shi kenan baiso yatadamai da hankali da sauri Rauda ta tashi daga jikin Aliyun tace "nizan ma girki kaji yayan mu, maizan dafama?" kafin ma yay magana Kareema tace "wai bazaki wuce kidau zanin gadon chan dakika watsar akasa kije ki shimfidamin agado ba" wani mugun kallo Daddy ya watsa mata yace "kije ki dauka dakanki, girki zatama dan uwanta" Daddy ya kalli Raudan datai zuru zuru dan tsoron masifar uwarta take Yace "wuce je store ki dauko all abunda zakiyi amfani dashi kizo side din Aliyun kiyi girkin awajen" gyadamai kai tayi tace "to Daddy" tama Ya Aliyun murmushi tajuya da sauri tawuce, Dady ya kalli sauran matan biyu dasuka tsaya suna kallonsu yace "duk baku iya gaisuwa bako" ko wacce da kallan nata reaction din dasukayi da kyar sukace "sannu da zuwa Aliyu" ko amsasu Aliyu baiyiba Yajuya yay part hanyar side dinshi, Amaryan Dady mai suna Amina tace "yaro baisan ya gaida manyan Shiba saidai asa manya su gaidashi sabida sonkai, mumadai Allah bamu y'ay'a mazan nan, kuma kar wata takara kiran yarana " dan juyowa Dady yayi ya kalleta jin yanda take jefanshi da kananun magana ta shige dakinta baice komiba amma wlh duk zasuci ubansu yasan maganin su, shida sune su zuba indai kan Aliyun dudda sun haifamai yara zai iya sakin yan bura'uba yakawo nany su kulamai da yaranshi, billahillazi duk wanda zai tabamai Aliyu marayan danshi nan mara uwa sai yay yakin biafra da mutum.
[03/03, 08:58] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






5️⃣ & 6️⃣




_how to pay your subscription fee_
_*zaki turo 300 ta account dina 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta WhatsApp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting*_


_*for those da prefer su tura kati, you can also send MTN card na 300 ta WhatsApp number na 07012181461 saina loda nasaki a group din danake posting ATSAKANKANIN SOYAYYA_










_Free page_






Sallame salla Ammi tayi
sake kwalamata kira akaro na uku tayi. "Aneesa wai bazaki tashiba, idan kika bari nazo dakin nan sai jikinki yay tsami, kindaisan abubuwan dake gabanki yau ko" da kyar ta iya bude ido jin Ammi na masifa tana kiranta jiya taci aiki a shago bana wasaba saisa tagaji haka, dama duk jumma'a haka take uban aiki a shago dan masu zuwa party nazuwa placing order dayawa kuma duksaitayi, da kyar ta sauko daga gado har bata gani da kyau tana dafa bango tafito daga dakin tafito Ammi tabita da kallo tai tsakar gida bayi ta shiga dan lokacin har gari yasoma wayewa fitowa tayi tadauro alwala takoma daki tadau hijabi ta sanya, akusada Ammi ta tsaya ta kabbarta salla, data idar tai karatun Al qur'ani sanna ta sallame ta gaida Ammi ahankali, amsawa Ammi tayi tace "tashi kije kidaura ruwa a wuta" gyadama Ammi kai tayi ta tashi ta zare hijabin jikinta tafito daga dakin tai kitchen wuta ta kunna ta daura pot din ruwan wanka dake cikeda ruwa tadau tsintsiya ta share tsakar gidan fess sanan ta shiga dakin dakin Ammi ta tattaro ta gyara sanan tawuce nata dakin ta gyaro shima tahada da falo ta gyara tafito da dattin ta kwashe, tadawo ta kunna turaren wuta sanan tafito tasauke ruwan daya soma shirin tausa daga wuta ta daura dumamen tuwo tahada ruwa ta shiga bayi, wanka tayi tana fitowa ta sauke tuwon dayayi tasa miya sanan tai dakinta, mai kawai tashafa tadau doguwan riganta na gida baki ta zura tafito lokacin wajen 8 nasafe ta zuba abincin ta dan tasan Ammi bata breakfast early tadawo ciki ta zauna kusada Ammi tafara cin tuwon dayay dadi miyan harda wake aciki, ahankali takeci harta cinye sanan ta kai kwanon kicin ta wanke hanun ta ta dauraye baki tadawo ta zauna kusa da Ammi, da hannu Ammi tanuna mata dakinta tace "daukomin purse dina" tashi tayi tai hanyar dakin Ammi tafito rikeda wata bakar purse ta zauna kusa da Ammi tamika mata karba tayi tabude purse din ta ciro kudaden dake ciki wanda suke na Aneesan na lallen datakeyi take tara mata dubu biyarne Ammi tamika mata tace "kije kisiyo kayan lallen, sanan kisiyo handglove banson yanda kike bata hanunki haka, kiyi sauri kidawo dan nasan anjima kadan yan lallen zasu fara zuwa yau asabar kina gida" karban kudin tayi tana kallon agogon bangon dakin ganin Takwas da rabine yanzu yasa tace "karfe tara kasuwan lallin ke budewa, Ammi ki faramin tsifan kafin lokacin" tai maganan tana zare hulan kanta tulin kitson kanta datai shuku na hannu yawani zubo har gadon baya, hulan data cire Ammi ta daura ta mayar mata tace "sokike kije kasuwa dakai daya da rabi, aga nan yay kato nan yay kadan, Tara zaki fita yanzu takwas darabi minti talatin yayma kitson nan kadan, yanzu jeki fara shiryawa ne, kafin kigama shirin lokaci yayi" kaman zatai kuka ta tashi tai hanyar dakinta, sip dinta tabude tadauko wani gogaggen atamparta riga da skirt dakeda dilli dillin ja, sai ta dauko jan hijabin ta dayakai mata har guiwa ta maida sip din tarufe tacire rigan jikinta ta shiga shiryawa, riga da skirt din yay mata kyau sosai gaban madubinta taje ta shafa hodanta tadau man baki tashafa a lips din sai abin yay kaman tasa pink lipstick, dawowa tayi tadau hijabin tasaka daya kwanta a fuskarta tadau karaman jakanta tafito, baki Ammi ta tabe tace "kasuwan aka cima kwalliya haka yan mata kodai nai siriki ne akasuwan" akunyace tace "laaaaa Ammi" dariya tadanyi ta dauke kai cikeda kunya tadau kudin dake gefen Ammi tace "nifa hoda kawai na shafa Ammi" tura kudin tayi cikin jaka tayi har lokacin taki kallon Ammi tace "natafi Ammi" "adawo lpy, ki adduan fita daga gidafa, kuma adaga kafa kar aje ana yauki akasuwa hmmm" Ammi tafada cikeda zolaya, murmushi sosai tayi tasa hijabi tace "to, Ammi idan yan lalle sunzo kice sujirani bazan dadeba" "shikenan, saikin dawo, kiyi addu'an fita daga gida" ficewa tayi daga dakin tai addu'a tafita daga gidan.














Around 8:40Am Hajar tabude dakin nasu ta shigo tana kallon Raudan dake kwance kan gadonta idanunta sunyi suntum suntum tace "kije Mama na kiranki adakinta, Khamis kuma yazo yana falo" ko alamun tashi batayi ba hakan yasa Hajar tamata ihu. "wai bazaki tashi kije kiran da mama ke mikiba mara kunya" tashi tayi ahankali tana turo baki tafita daga dakin, dakin Maman su ta shiga, Mama na zaune kan katafaren gadonta ta mimmike kafafun tana shan farfesun kaza, watsa mata harara tayi tace "sai yanzu kikaga daman zuwa rasakunyar beran tanka" ahankali tace "ina kwana Mama" hararanta Mama tasake yi tace "daban kwana ba zaki ganni anan ne?" matsar da farfesun tayi gefe ta sauko daga gadon, gaban wardrobe dinta tayi tabude taciro wani sabon dinkakken atampa na mustard da brown anyi dinkin riga da skirt sai mustard veil da mustard flat shoe mai kyau, mika mata Mama tayi cikin daure fuska tace "ai tun asuba kikai wanka, gasunan shirya anan yanzu nan Hajar zatazo tamiki kwalliya kitafi yana falo" karban kayan tayi ahankali ranta abace ta cire rigan ta ta shiga sakawa ahankali, rigan ta tsaya tana kallo yanda net ne daga ta kirjin ana hango boobs dinta, hannu tasa a wurin ta dago kai ta kalli Mama da itama ita take kallo cikeda masifa tace "miye to?" cikin dan shakakkiyar muryanta tace "ana hango kirjina Mama is net" harara Mama ta watsa mata tace "naga dai Khamis zaki aura har ubanki yasan da zancen, banda haka Khamis dandan Yayata ne na yarda da tarbiyan shi, yaro mai natsuwa da hankali ga kunya, me kike nufi mai zaimiki? Besides wanan dinkin mai net din wuyan ai shinaga yan mata ke yayi yanzu saisa na bada amiki irin shi dan haka karki kara cemin komi" daidai lokacin Hajar tabude kofar dakin ta shigo dauke da kayan kwalliya murmushi sosai Mama tayi tace "kaga yar albarka maijin maganan uwarta, bazaki taba ganin mara dadi ba arayuwanki Hajar saidai kiga daidai, yimata kwalliyan sutafi sai dare yau" murmushi Hajar tayi jin ddin maganan maman su, taja kujera ta zaunar da Raudan data dawo kaman gunki ta shiga mata makeup din, cikin 5min tagama mata sosai tai kyau, tadau gyalen ta yafa mata a kafada tace "tashi kuje" kallon gyalen tayi kaman zatai kuka tace "ahaka Anty, jibi kirjina fa" mugun kallo Mama ta watsa mata tace "barganin kinyi gayu bazai hana na lallasaki da safen nan ba, dan ubanki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login