Showing 156001 words to 159000 words out of 186400 words
Chapter 53 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt
karfe shadaya zuwa shabiyu, Aneesah yarku na hannuna" wani irin hamdala Baffa yayi yace "Aneesah, Aneesah na wurinki Mai Martaba" "Aneesah na wajena saikun iso" kallon Ammi Baffa yayi dake kallonshi kaman zata hadiye shi jin yakira sunan Aneesah yace "anga Aneesah ankaita gidan sarki a Zaria, sarki da kanshi yakirani yanzu yace duk muzu fada harda yaron da iyayen wanda yakamata ta aura" fashewa da kuka Ammi tayi, Baffa yay murmushi yace "oya kushirya bari nafita nakirawo Na Sani sanan nakira Mahaifin Hafiz nafadamai me akeciki suzo muwuce Zaria"
Karfe goma duka family aka hadu kowa zaka gani murmushi yake jin anga Aneesah tana gidan sarkin Zazzau, barinma Hafiz dayaci wani mahaukacin kwalliya yasa wata farar Magic shadda dake kyallin bala'i ya shiga gaban mota akadau hanyar Zaria, Ammi jitake kaman tarufe ido taganta a gidan sarkin Zazzau din.
Shadaya da minti shabiyu tamusu a kofar fada tsaresu fadawa sukayi batare da an barsu sin shiga cikiba, saida suka fadi kosu suwaye dayake sarki yariga ya sanar dasu zaiyi baki daga kaduna yasa suka koma ciki suka sanar da sarki sanan yace a shigo dasu, shigo dasu akayi sukai parking motoci su a inda ake parking mota sanan suka fito Ammi sai kallon ko ina take kaman zataga Aneesah, sanan wayansu fadawa biyu suka musu jagora zuwa fada.
Fadan suka shiga dake da girma sosai babu kowa ciki sai Sarki dake tareda Sarkin gida, da kuma wawan sarki, nuna musu wurin zama sukayi suka zazzauna sanan Sarkin gida yasa aka gabatar musu da abin sha bayan anyi gaishe gaishe wanda yawanci shike amsasu dan Mai Martaba baiyi magana ba, saida masu shan ruwa suka sha suka gama aka natsu akai shiru sanan Mai Martaba ya gyaran murya alamun zaiyi magana, kara natsuwan akayi ana sauraron abinda yake shirin fada, anatse yace "muna muku barka da zuwa wanan fadan sarki mai albarka bayan haka akwai wanda muke jira kafin nafara gabatar muku da abinda yasa nakira ku, yariga ya sauka a airport na kaduna yanzu haka wayanda na aika sun daukoshi suna hanyan su na iso wa nan wanda ina kyautata zaton nan da yan mintuna sha biyar zamuga isowanshi, dan haka akara hakuri" babu wanda yace wani abu sai gyadakai da akayi akai shiru harda Mai Martaban da akema fifita kaman ba AC da sunfi kala shida bane ketashi daga dakin ba takowani sako.
Bude kofar fadan akayi wasu fadawa biyu suka shigo yasa kowa yadago kai yana kallon waye zai shigo, ahankali cover shoe kafar Dady yafara lekowa na hermes kafin ya shigo dakin yana sanye da babban riga nawani yadin da ake kira da presidency, yana zuba wani hadadden kamshi, fuskarshi dauke da murmushi dan cikin farin ciki yake sosai jin Aliyu na tare da mai Martaba, tsayawa yayi yacire kobashoe kafarshi sanan ya shigo yana kallon su Ammi da Baffa da mugun mamaki ganinsu azazzaune kaman yanda suma suke kallonshi da mugun mamaki barinma Ammi dake kallonshi kaman yau tafara ganinshi, karasawa yayi har gaban sarki ya duka cikeda girmamawa yana kwasan gaisuwa, murmushi Mai Martaba yayi yace "tashi tashi sami waje ka zauna tun dazu ake jiranka" tashi Dady yayi yakoma gefe guda yazauna kan daya daga cikin kujerun fadan yana facing Ammi dayaga idanunta sun kumbura sosai sunyi ja kana ganinta kasan tasha kuka yana mamaki meya sameta me kuma ke faruwa haka.
Murmushi Mai Martaba yayi ya gyara zama ya sauke ajiyan zuciya, cikeda natsuwa yace "nasan kuna mamakin haduwar ku dukanku anan ko, bakomi yasa nahada ku anan ba sai alkhairi, amatsayina na sarki, sarki mai amana da adalci dole ne nai ensuring peace and harmony ga Alumman dake karkashina, sanan na tunatar daku abinda Allah yace, sanan ya nuna muku hanya madaidaiciya, kutuna cewa kowani daya a cikin ku ranan gobe kiyama Allah zai tambayeni akanku badan komi ba saidan ni sarki ne kuna karkashina ne, Al Umman musulmi mu kasance masujin tsoron Allah dakuma karban kaddara ayanda tazo mana, nasan zakuce mesa naketa maimaita kalman kaddara? Abinda gabaki daya yasa natara ku anan badan komi bane sabida wani kaddararren Al amari ne daya faru, amma zan fara dakaine Muhammadu Ibrahim" ya fuskanci Dady dake kallonshi shima anatse.
Anatse Mai Martaba yace "kabani kunya Muhammad Ibrahim, na dauke kai mahaifi ne kai mai adalci, wanda yasan yakamata, Muhammadu a yanzu koda eh da gaske Aneesah ce tazuba ma Aliyu guba a abincin saiya kaita gidan yari kasa akulleta, duka duka guda nawa yarinyar nan take? Metasani aduniya? Bakasan hatsarin dake tattare da gidan yari zai iyasa tazama wani abun da zai zama annoba ga rayukan musulmai gabaki dayaba? Muhammadu akwai hanyoyi da dama na hukunta yaro koda kam kisa yayi, sometimes gidan yari bashine best option ba hasalima shine worse option, banda haka bakai bincike ba, baka zurfafa bincike ba karaba yarinya da mahaifiyar ta, baka kyautaba ko kadan kai kuskure babba" Dady zaiyi magana Mai Martaba yadaga mai hannu alamun yamai shiru sanan yajuyo ya kalli Ammi dayaga tana share idanunta da bayan hannu yakira sunanta. "Rukayyatu" ahankali Ammi tadago kanta ta kalli Mai Martaba, kirjinshi ya nuna mata yace "zuciya kwara dayace kacal Rukayya, koda tai baki kaman gawayi karki bita kema kiyi bakin, yayin dakika bita kukai bakin tare hakan zai dushashe duka hasken dake tattare da ke saidai duhu Rukayya" Mai Martaba yadanyi shiru kafin anatse yacigaba. "a lokacin da zuciya ta kuntata, tai nauyi ta baci sanan tai baki, farin ruwa zaki samo kar kar ki wanke ta dashi saita dawo tai haske ta haskaka, Annabi yafadi a hadisi ingantacce cewa Al amarin mumini akwai abin mamaki, duka alamuranshi gabaki daya alkhairi ne, idan abin farin ciki yasame shi, shakara saiya godema Allah, hakan kuma shine mafi alkhairi agareshi, sa'annan idan abin bakinciki ya sameshi sabara saiyay hakuri kuma hakan shine mafi alkhairi agareshi, nasan kin kuntatu Rukayya anma yarki shairin neman kashe rai sanan aka kaita gidan yari nasan ba'a kyauta ba, amma amatsayin ki na musulma kamata yay kiyi hakuri ki mayar da komi ba komi ba tunda har Allah yadubi zuciyarki ya tausayamiki ya bayyanar da gaskiya ai ya isar miki, inda bahaka ba zai iya yaki bayyanar da gaskiya yabar Aneesah ta karaci rayuwanta agidan yari batare daya bayyanar da gaskiya ba, ranan gobe kiyama saiya bayyanar da gaskiyan agaban jama'an duniya, Allah mai yanda yasone fa sanan mai yanda yaga damane, Allah yariga ya fitar miki da yarki yakuma wanke ta tass soso da sabulu bayan haka yamuku sakayya ta hanyar saka wayanda sukai abun su suka koma gidan yarin yarki tafito bai isaba Rukayya saikin rama da kanki? Saikin nunama Muhammadu kema yarki yace mai daraja? Saikin kuntata ma Muhammadu kaman yanda yakuntata miki sa'annan ta hanyar dazaki kuntatamai ya kuntatu shine ki hana danshi yarki dayake so sabida kinsan duk abinda yasami danshi yasame shine ko?" Mai Martaba yay maganganan yana bubbuga kafa aka yace "to bari kuji wanan maganan da kowa nake afalon nan, da ace Al Umman musulmai zasu kasance nasu rama mugunta da Alkhairi da duk wani ayyukan sabon Allah irinsu gaba, fada, tauye hakkin wasu da sauran su yaragu a doron kasa an zauna lafiya, misali ki dauka bayan Muhammad ya kullemiki ya an wulakantata an mata duka azaban dakika sani na duniyan nan a gidan yari bayan yarki tafito sukazo neman aurenta kikace kin basu da yaya shi Muhammadun zaiji?" Mai Martaba ya wurga mata tambayan, ahankali Ammi ta share hawayen daya zubo mata takasa magana shima Dady kanshi akasa yakasa dago kai, ahankali Mai Martaba yace "dazaiji dana sani, zaiyi nadama, sanan zai baki wani girma da karamci na daban azuciyan shi domin kinada siffofi na mace mumina, saliha kuma mai yafiya, daganan kuma babu abinda zai dinga hadaku sai alkhairi, bari nabaki misali nabiyu dan fashi ne yatareki yamiki mugun duka ya kwace miki kudi da sauran su cikin iko irin na ubangiji yakawo wata hanyan da yan sanda suka kamashi za'a saka case akotu amma kikace ke kin yafemai duniya wa lahira asake shi kina ganin wanan dan fashin bazaiji wani iri ba? To saidai in mutum ne da Allah yariga ya rubuta tun a lauhul mahfuz cewa shi wane baida rabo alahira ahaka zaiyi rayuwanshi yakare shine bazaiji wani iri kota chanza ba amma inhar yanada rabo aduniya saikiga ya shiryu sabida wanan aikin alkhairin naki. Hausawa nacewa rama mugunta ga mugu ibada ne inji wa? Awani hadisi sukaga hakan? Awani ayyan Al qur'ani sukaga hakan? Al Umman musulmi rama mugunta ga mugu ba ibada bane wanan ba koyarwan addinin mu bane! Rama mugunta da alkhairi shine ibada! Shine ibada! Shine ibada! Idan mutum ya cutar dake yanzu haka anjima tazo yace bani ruwa wane inkina dashi dauka ki bashi kinsami lada, Rukayya kindau zafi sosai wanda ba haka yakamata musulma tayiba kome Muhammad yayi miki karki ce zaki rama harki so ki raba soyayyan dake tsakanin danki da Aneesah" shiru yayi yana kallonsu daya bayan daya sanan yajuya ya fuskanci Hafiz da iyayenshi wanda tun shigowan shi yagane shine ango sabida gayun dayaci, ahankali yace "Hafizu" dagokai ahankali Hafiz yayi ya kalli Mai Martaba yace "dazun nan nagama kawo muku hadisi akan idan abin alhairi yasami mumini godiya yakema Allah idan kuma akasin hakan yasamai saiyay hakuri, kasani cewa komi mukaddari ne daga Allah sanan matar mutum kabarinshi, idan Allah bai baka abuba karka zafafa akwai tanadin daya makane, kadau kaddaran da hannu bibbiyu" shiru Mai Martaba yayi sanan ya kalli Sarkin gida dake zaune kusadshi yace "shigo dasu" cikeda girmamawa yace "Allah yaja zamanin sarki mai adalci" sanan yamike tsaye yafita daga fadan da sauri duk akai shiru kowa najira yaga wa akaje shigowa dasu. Wajen mintuna biyar sarkin gida ya dauka sanan yadawo yabude kofa ya shigo kowa na jiran yaga waye zai shigo abayanshi fuskar Aliyu ne yafara bayyana yana sanye dawani sky blue sabuwar shadda da aka mata aikin sarauta yana rikeda hannun Aneesa dake sanye dawani dogon hijabi har kasa mai hula fuskarta babu kwalliya amma tai wani irin kyau da haske na amarci, hada ido datayi da mutane biyu tak afalon Ammi da Hafiz dasuka kasa dena kallonta yasa ta tsaya chak takasa tafiya tana kokarin fizge hannunta dagana Aliyu da baima da alamun sakinta baikuma waigo ya kalleta saima tsayawa da shima yayi ganin taki zuwa, Mai Martaba ne yadubesu sanan yakira sunanta. "Fateema kuzo nan" yanuna musu gabanshi, ahankali tadago kafa suka taho kanta akasa takasa daga kai ta kalli su Ammi harsuka karasa gaban Mai Martaba zama Aliyu yayi inda mai Martaba yanuna musu yana rike da ita sanan itama ta zauna ahankali kusada shi. Akai shiru dakin kowa da abinda ke wakana a zuciyanshi. Andau kusan minti goma sanan Mai Martaba yay breaking silence din yace "Na daurama Aliyu da Fateema aure jiya a yanzu Aliyu Mijine ga Aneesa sanan Aneesah matar sunna ce ga Aliyu wanda dumbannin jama'a suka shaida akan sadaki naira dubu dari!" wani irin mahaukacin shiru dakin yayi da da ake shiru at least kanajin saukan numfashin jama'an dakin amma yanzu kaman an zare musu rai.
Ahankali Mai Martaba yace "ajiya misalin karfe biyu na rana ana wanan zabga ruwan saman Aliyu ya shigo garin kaduna cikin tsananin ciwo, da kyar da tambayan sunan Baffan Fateema yagano gidan, yay shiga irin ta mata ta hanyar saka dogon hijabi har kasa da nikabi da madubin idanu yaje yasato Aneesah" dagokai Dady yayi ya kalli Aliyun wani murmushi ne ya subuce mai yadaki zuciyarshi yace "that's my son!!" Mai Martaba yace "bai kawota ko ina ba sai wanan masarautan, bayan series of bincike da kuma lura danayi nagano cewa yaran nan are made for each other dan suna bala'in son junansu iyayensu sune suka shigo TSAKANKANIN SOYAYYAn su hakan yasa na aurar dasu! Dan nasan bazaku taba daura aure ba in akasan Amarya ta bata ba".
_like I said, the doors of VIP is always open for marasa son jira_
[29/04, 21:02] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
7️⃣7️⃣ & 7️⃣8️⃣
_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, marasa bank can also send MTN card 300_
_littafin nan na kudi ne karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan or pay achan_
_please note, read only at night_
Wani irin murmushi Dady yayi yana kallon Aliyun da kanshi ke kasa a ranshi yace "shege Aliyu, that's My Son".
Allah kadai yasan me Hafiz keji, hannuwanshi rawa suka shiga yi sosai yakeson Aneesah bana wasaba, tunda matarshi tarasu she's the only yarinyar daya taba gani yaji yanasonta har cikin zuciyan shi, zafi da zuciyan shi kemai yawuce misali, ahankali baban shi daya lura da yanayin shi ya mika hannunshi yakama mai kafada gamgam irin alamun be strong dinan, ajiyan zuciya ya fuzar yana karanto addu'a dazasu sama zuciyar shi natsuwa.
Ammi taji saukan zancen nan kaman aradu ne, she couldn't believe wat her ear just heard, Aliyu da Aneesah tane sukai aure haka Aneesah zata mata, haka zata mata.....
Gyaran muryan damai Martaba yayi yadawo da kowa daga dogon tunanin dasukaje, Hafiz ya fuskanta ahankali yace "Hafizu" dagokai Hafiz yayi ya kalli sarki da jajayen idanun nan nashi, cikin wata irin siga na lallaba mutum Sarki yace "kayahakuri Hafizu sanan kuma karka zafafa Al amarin, kadauka cewa haka Allah ya kaddara zai faru hakan kuma yafaru, idan Allah ya kaddara wance matarka ne ko ana ha maza ha mata saika aueeta, kaga yanda Allah ya kaddara Aneesah matar Aliyu ce koda ace Aliyu baizo yasace taba zakaga wani abu saiya faru dazaisa baza a daura auren nan dakaiba, iyayen Hafiz ina mai baku hakuri akan wanan lamarin daya faru kuyakuri, kuyakuri" murmushi Baban Hafiz yace "babu wata matsala daga bangaren mu Mai Martaba, maganar ka gaskiyace matar mutum kabarin sa, wlh mun hakura munkuma dauka ayanda Allah ya tsara, Aneesah ba matar Hafiz bace, sanan muna mata fatan alheri, Allah ubangiji ya basu zaman lpy, ahhh dan Allah mai Martaba kakace nacika azarbabi, tunda dai dama danka sanar damu wanan lamari ne ka kiramu dan Allah ina neman izinin ka akan zamu iya tafiya" ahankali Mai Martaba ya gyadamai kai yace "zaku iya tafiya Baban Hafiz, ubangiji Allah ya kiyaye hanya yakaiku gida lpy, mun gode da wanan karamcin" murmushi yayi yana dago Hafiz dayake zaune wurin kaman an dasashi, mahaifiyar shima ta mike tana murmushi wanda kallo daya zaka mata kagane she's hurt ta kalli su Ammi tace "sai anjiman ku" sosai Aneesa kewani irin kuka mara sauti she is feeling bad sosai for Hafiz dudda dama bawani soyayyan arziki sukayi ba but kobabu wanan he has been there for her kullum saiyazo yayta mata hira yana karanta mata novels hartazo tana walwala, sabida contribution din Hafiz ne tadawo normal haka Yaya yakeji yanzu?.
Mikewa tsaye Hafiz yayi da taimakon Mahaifin shi shi kanshi mai Martaba saida yaji wani iri dan yaga so kwatankwacin irin son dayagani a idanun Aliyu shima haka Hafiz ke sonta, ahankali yake daga kafa wasu fadawa biyu suka budemusu kofa juyowa mahaifin shi yayi cikeda murmushi yace "to mun barku lafiya, Allah yadawo daku kuma gida lpy" wani iri Aneesah taji kaman zata haukace batasan lokacin data dago idanunta dasukai jajir ba tsabagen kuka, hada ido tayi da Hafiz da Mahifinshi ke rike da shi zai fitar dashi waje, tunda take da Hafiz bata taba ganinshi a irin yanayin nan ba idanunshi sunyi jaa sun cika da kwalla sai kallonta da Aliyu yake ahankali Babanshi yajawo shi da baya baya yafita daga dakin yana kallon Aneesah har lokacin mahaifiyar shi tabisu tafita sanan fadawa suka rufo kofa wani irin fizge hannunta Aneesah tayi tamike da sauri tana kuka kowa nadakin yabita da kallo bude kofar fadan tayi daidai Hafiz na shirin shiga mota a parking space din dasukai parking motarsu dake facing fada, tsayawa yayi chak yakasa shiga ciki maman shi zata kirashi taga abinda yake kallo saitai shiru, dawani irin gudu Aneesah ta taho har gaban motan, tsayawa tayi gab dashi kaman zata shige jikinshi tafashe dawani irin kuka tama kasa bude baki tamai magana sai kuka, lumshe ido yayi yay shiru sai chan yabude idosu yana kallon yanda jikinta ke bari tanamai kuka kaman zata sume, murya chan kasa da bata fita sosai yace "bakimin komi ba Fateema I know how much Aliyu means to you, shine suna na farko dakika fara kiramin a healing process dinki, who am I nace zan shiga TSAKANKANIN SOYAYYAN gaskiya eh? Tayaya ma nazo harna shiga ATSAKANIN SOYAYYAn ku?" yadanyi shiru yana kallon yanda take kuka sosai tana kallonshi murmushi ya sakin mata ahankali yace "stop crying okay, ga mijinki chan yafito yana kallonki go and meet him, ina miki fatan alhairi arayuwan aurenki, Bissalam" yana maganan ya shige cikin mota tareda rufo kofa yana goge hawayen dasuka zubomai da sauri, Maman shi tace "mutafi Alhaji" kunna motar Mahifinshi yayi yaja sukabar wajen Aneesah ta duka akasa tana kuka sosai, she's feeling way to bad, super bad ma, ahankali Aliyu da idanunshi sukai ja yatako har zuwa inda take tsugunnawa yayi ahankali gabanta tareda daura hannunshi akan bayanta, murya chan kasa kaman zaiyi kukan shima yace "is okay, stop crying, let's go back inside wife" cikin wani irin masifa danji tayi mugun haushin Aliyun takeji ta ture hannunshi tareda mikewa ta kalleshi da jajayen idanun nan nata dake fitar da hawaye tace "don't call me wife am not your wife Ya Aliyu, kazo kaja kowa fushi yake dani, mesa baka barni anyi aurena da wanda yan uwana kesoba haaa, Ammi na fushi take dani, wanda yakamata na aura haushina yakeji