Showing 147001 words to 150000 words out of 186400 words

Chapter 50 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt

20 Jan 2025

18830

to me kenan ina Aneesah jama'a?" da sauri Baffa yace "kira number ta" da sauri Salamatu tace "wayanta da duka kudadenta na wurina, suna cikin purse dinta ajakan dana rike mata" wani irin baya luuu Ammi tayi zata fadi da sauri Inna tarike ta tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Ke maman Aneesah tashi in sha Allah babu abinda yasami Aneesah, hala wani wuri taje, toko tana tareda ango ne?" da sauri Na Sani yace "ga ango nan dake tare duk damu wajen daurin aure" kawayen Aneesan ne dasuka ji hayaniya suka fito Baffa yace in kika karanta baki biyaba Allah ya isa "kai ku dudduba ko ina kuga, dagota mu kaita gida ta kwanta" taso da Ammi Inna tayi tabude ido da kyar saikuma tafashe da kuka tace "ina Aneesah na sace mini ita akayi kome gabana nafaduwa sosai wlh" tana kuka Inna tawuce da ita cikin gida, Hafiz sai kallon Ammin yake jikinshi nabashi kaman dawani abu, ahankali Baffa da duk yay wani iri yakarasa wajen Baban Hafiz, Baban Hafiz yace "lafiya daiko? Azo afara daurin auren ga limam nan ya shirya" cikeda tashi hankali Baffa yace "Alhaji a dakatar da daurin auren wlh ba'aga Aneesah ba saisa kaga maman ta ma nakuka yanzun nan" chak Hafiz ya tsaya yana wani irin kallon Baffa a rude, Baban Hafiz ne yace "kaman ya ba'a ga Fateema ba" cikeda tashin hankali yace "to yanzun nan maman Fateema taji gabanta nata faduwa shine ta aika Mubarak yakira Aneesah yaje yadawo yace ai kawar Aneesah tace bata kirata ba tun dazu, shine fa kukaga sun fito nima nabisu gidan ganin yanda suka rude, kawar kecemana dazunan nan taga wata nata mai nikabi doguwa mai kiba tasaka glass tazo tace wai Ammi nakiranta tace tabiyota suzo yanzu shine fa she's no where to be found wlh, kuma duka gidan bikin nan daidai da mutum daya bamuda shi mai nikabi" wani abokin Hafiz be dake tsaye kusada Hafiz yace "dazu danake shigowa naga wata katuwar mata sanye da bakin nikabi da hijabi harda glass achan ta baki bakin anguwa tafito daga wata brand new car ko ledan seat din ba'a cireba ferrari" "innalillahi wa innailaihi raji'un, meke faruwa ne haka? Lahaula" Baffa yafada cikin tsantsan tashin hankali, da sauri wani cikin mazan abokan Hafiz yace "nima exactly naga wata haka data shiga wanan gidan" yanuna gidan fatin, yace "kuma naga fitowanta tareda wata data saka milk color hijabi mai hula tajawo hulan gaba banga fuskarta ba sukai wajen layi" cikin tashin hankali Na Sani yace "Aneesah ce, itakeda Milk color hijabi, towai wacece matar nan? Me zatama Aneesah, yanzu a ina zamu nemo Aneesah?" ahankali Hafiz yazare malum malum din jikinshi ya mikama best friend dinshi tareda zaro key mota da sauri Baban shi yace "ina zaka Hafiz?" da idanunshi dasukai ja sosai yace "police station zani" yana maganan yafice da sauri best friend dinshi yabi bayanshi Su Baffa da sauran mutanen daurin auren aka babbazu ana shiga lungi lungu na anguwanni around ana neman Aneesah.
Inkika karanta baki biyaba Allah ya isa.




Wasa wasa fa tun ana ganin abin kaman wasa abu yadawo gaske dan gashi ana kiran sallan isha'i babuma alamun Aneesah, Ammi tasha kuka tasha kuka daga bayama amai tafara kwarawa mugun zazzabi ya turniketa saida Baffa yakiramata nurse tazo aka mata alluran bacci dantaki dena kukan sanan aka samu tai bacci aka cigaba da neman Aneesah.


Wanan kenan!!!!
[23/04, 08:21] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






7️⃣2️⃣










Wasu irin hadaddun kaya sarki yasa aka shigo dashi adakin da aka kai Aneesah dan shiryata, baban Aliyu mutum ne da baijin zaitaba manta alkhairan shi agareshi ba sunsan juna da dadewa tun kafin yazama senate president, tun yana matsayin ambassador din Nigeria na US yasan baban Aliyu, dan awurin nema yahadu da mahaifiyar Aliyu sukai aure abinsu, aturai aka haifi Aliyu shi citizen of US ne, har yazo yabar aikin yakawo ta Nigeria kafin daga baya Aliyu na around 5 zuwa 6 years tarasu.




Wanka akasa Aneesah daduk tai zuru zuru tayi sanan tadauro alwala, sanan wata kuyanga datake makeup tazo tamata hadadden makeup, aka shiryata cikin english atampa da akayi riga da skirt vkaman dama chan anyi dinki an ijiyemata ne sabida yanda yakamata yamata dadas ya mugun fito da shape dinta barinma rigan dayadan kamata ta kirjin hakan yasa boobs dinta sukadan yi popping out ta wuyan rigan kana ganin tudunsu sosai, wani babban bakin mayafi akazo aka dauramata akai, sanan aka fesheta da turare, wata matane ta shigo jakadiya dawasu bayi na binta matar ta manyan ta sosai kana ganinta kasan uwargidan sarki ne, murmushi tama Aneesah datai zuru zuru tareda kama hannunta ta mikar da ita tsaye tace "tashi muje nakaiki inda mijinki yake" waje suka fito bayin nabinsu tafiya taga sunyi me tazara sanan suka kai wani sasa agidan, saiga wani flat kwal daya tak a sasan, kofar matar sarki tabude mata tace "shiga kije ki sami mijinki yana uwar daka a kwance, baida lafiya sosai zuciyarshi nada matsala tafi" ahankali Aneesah ta gyadamata kai tawuce ciki tana kallon dakin, falone babba sosai da komi na abin bukata nayan gayu ke ciki, sai wata yar corridor nan tayi, kofa taya tak data gani a corridor tasa hannu tabude ahankali, Aliyu tagani kwance kan makeken bed din dakin ana mai karin ruwa, ancire mai rigan jikinshi anbarshi dagashi sai dogon wandon shaddar shi da singlet yana bacci, ahankali tamaida kofan tarufe tajuyo tareda jingina da kofan tana kallonshi yanda yay wani iri looking pale sosai, yanda kirjinshi ke bugawa ta tsaya tabi da kallo jitayi kuka yazo mata ahankali takarasa cikin dakin har gaban gado zama tayi ahankali abakin gadon tana kallon fuskarshi this is the first time tunda tahadu da Aliyu a duniyan nan tasan tamai wanan kallon, cewa Aliyu nada kyau is understatement, farine sosai gashi da dogon hanci, ga cikan gira dake wani irin shining kaman ya shafa relaxer, yanada karamin baki dakenan pinkish ga smooth kwantaccen gemunshi dakenan bakin kirin akwance, sosai take kallon yanda jikinshi ya murmude kafin ahankali ta saukar da idanunta kan kirjinshi dataga yana wani irin bugu, hawaye taji yazubo mata, ahankali takama hannunshi dataji da zafi sosai kaman wuta tarike tana kallonshi hawaye yasake gangarowa daga idanunshi kafin ahankali tasaki kuka chan kasa, takai almost one hour tana kuka saida aka kira magrib tamike tsaye ahankali ta bude kofar datake gani wanda ya kyautata zaton cewa bayine, alwala ta dauro tafito batasan inane gabas ba hakan yasa tai facing wani wuri ta kabbarta salla tayi sanan ta zauna a dadduman tana addu'a gabanta faduwa yake barinma inta tuna Ammi ko yanda take shakkan Ammi bata shakkan Hafiz hakama, Hafiz ko kadan baidameta ba kodan batawani sonshi ne oho Ammi kawai take tunani, knocking dataji afalo yasa ahankali ta mike tsaye tana kara rufa da gyalenta da kyau sanan tafito kaman matsoraciya har zuwa wajen kofar ahankali tabude kofan wasu kuyangu uku tagani dauke da tray dake dauke da hadaddun kulas suka gaidata matsa musu tayi hakan yasa suka karasa dining suka jera komi sanan suka mata sallama suka rufo mata kofa.












Komawa bedroom din tayi ahankali take tafiya dan batada karfi ko kadan takarasa kan dadduma tazauna ahankali intace hankalinta a kwance yake tai karya kirjinta sai kawomata gida yake yana beating fast fast, tsoron datakeji sosai yake abayyane a fuskanta, kiran sallan isha'i da aka kira yasa ta mike tsaye ta kabbarta tai sallan tana idarwa tai shafa'i da wuturi ta zauna akan dadduman tareda juyowa ta jingina da bango tana kallon Aliyun dahar yanzu yana yanda yake akwance tana kiran sunayen Allah ko zuciyanta zai natsu, kwankwasa kofa da akayi yasa ta mike tsaye ahankali tareda linke dadduman tafito har falon zuwa wajen kofa bude kofan tayi ahankali mai Martaba tagani da matar shi ta dazu saikuma wani mutumi stethoscope din dake kan wuyanshi ne yasa tagane likita ne, akunyace ta dukar dakai tadan duka tagaida su tace "barkanku da zuwa" tai maganan tareda gyara musu hanya, matar mai Martaba ce tafara shigowa tareda dago fuskar Aneesah tana kallon fuskanta kaman mai nazari tace "zonan" kama hannunta tayi har gaban dining taja kujera ta zaunar da ita shikuma Mai Martaba da Dr sukai dakin Aliyu, kulolin abincin matar Mai Martaba ta shiga budewa kafin ta kalli Aneesan cikeda mamaki tace "bakici komiba" murya chan kasa Aneesah da kanta ke kasa tace "na koshi Mama" plate matar mai Martaba tadauka sanin bazata iya cin abincin ba yasa tadeban mata pepper soup sanan ta zuba mata coconut drink a cup takawo gabanta sanan tadawo kusada ita ta zauna, hannunta takama tarike kafin takai dayan hannunta kam kumatun ta tasha fa tareda sakin mata murmushi tace "Fateema nasan yanda kikeji yanzu haka, tunanin iyayen ki, faraba daidai sauran su, karki damu komi will be fine I promise you, kinsan mesa auren ki da Aliyu yafaru ahaka? Sabida haka daman Allah ya kaddara zai faru yariga ya rubuta ke matarshi ce so dole komi yafaru ahakannan dakika gani, gani gamai martaba duk muna tareda ku gobe Mai Martaba zasu kira iyayenku za'a hadu anan awarware kowani matsala ta sauki In sha Allah, karki damu kinji kisaki ranki, ga mijinki nan baida lafiya, ciwon zuciya gareshi sosai kimai addu'a sanan ki kula dashi kinji, ki kwantar da hankalin ki sanan ki sama zuciyarki natsuwa kinji" gyadama Matar mai Martaba kai tayi cikeda ban tausayi hawaye suka tsayayo sharrr da sauri ta share hawayen, ahankali Matar Mai Martaba tace "oya sha pepper soup dinan kisaka abu acikinki bakici komiba, nataho miki da kayan bacci sune awanan ledan dawasu kanana karki kwana dana jikin nan naki kinji" sake gyadamata kai tayi, murmushi tayi dan hakanan taji tanason yarinyar tace "tofaraci" spoon tadauka tafaraci ko kadan abincin babu taste abakinta amma babu yanda ta iya saida ta cinye duka sabida yanda tasata agaba.


Fitowa da mai Martaba yayi tareda Dr yasa matar ta mike tsaye, karasowa mai Martaba yayi har dining din tareda yazaro wata waya mai kyau yamikama Aneesah yace "ki rike wanan Fatima idan yafarka cikin dare kikaga dawata matsala tattare dashi numberta na ciki ki kirani ki sanar dani, kitashi kije ki kwanta sanan ki kwantar da hankalinki saida safe" karban wayan tayi cikeda girmamawa tace "saifa safe, nagode Allah ya saka da alkahiri" murmushi matar Mai Martaba tayi tace "saida safe" tabi bayan mijinta suka fita tareda rufo musu kofar.
Inkika karanta baki biyaba Allah ya isa.


Tagumi tabuga tana kallon kofar dasuka fita takai kusan minti ashirin ahaka sanan tamike tsaye kaman mara laka, tadau ledan kayan bacci tawuce corridor, bedroom dinsu tabude ahankali ta shiga Aliyu na bacci har lokacin kaman ma alluran bacci akamai dan heart dinshi yahuta, karin ruwan da akemai ancire anbarshi shi kadai yana sauke ajiyan zuciya ahankali, ganin yanda tsigan jikinshi keyi kaman yana tashi yasa tagane kaman sanyi yakeji, karasawa gaban gadon tayi taja bargo tarufamai tana kallon fuskanshi jitake kaman ta zauna taitamai kuka, kaman ma tadauke mai ciwon gabaki daya takeji, takai kusan minti biyar tana kallon fuskarshi ahaka atsaye sanan tadau ledan kayan tawuce bayin dakin sotake tai wanka tawanke wanan makeup din dan fuskarta gabaki daya nauyi takemata dan bata sababa, bayi ta shiga tacire kayan jikin nata sai wani irin shegen kamshi jikinta ke fitarwa tsabagen yanda ta mugun dahuwa da turaren yan chadi, tass ta linke kayan sanan tai wanka da ruwan zafi sosai da akwai sababbin sabulai abayin tadau kwara daya tabude na dove tayo wankanta sanan tafito, tsayawa tayi agaban makeken mirror dake jikin bango bayin tana goge jikinta tana kallon gashinta dayasha gyara ga kamshin dayake yi, saida ta tsanar da jikin nata tass sanan tabude ledan wani riga da bacci ne red color, rigan normal rigane tanada open neck da spaghetti hand, sai wando dayake nan gajere yafi iyakanshi cinya kaman bomshort yake, tsayawa tayi tana kallon kayan babu yanda zatayi bazata iya maida wanda tacireba dan kayan are not soft yasa ta saka kayan baccin danko babu komi tasan darene babu mai ganinta bandama haka Ya Aliyu bacci yake baccin da she's sure na alluran bacci ne, hadaddun turarurukkan datagani akasan ledan tadauko ta feffesa sanan maida kayan datacire ciki tadau ledan tareda dago kanta ta kalli madubin tayi wani irin mahaukacin kyau wandon ya mugun bayyanar da hips dinta dan tanada hips hijabin datake sawane ke boyeba, dan small nipples dinta ne sukai shooting out tagaban rigan baccin dayake soft cotton yard ne kayan bacci, kasa saka bra tayi dan bra da Hafiz yasako mata akwati sun mata kadan sosai bra yakamata saisa takasa mayarwa dan boobs dinta ciwo suke mata, gashin kanta ta kalla yanda yake aparke da ribbon yawani irin kwanta pontail din na lilo shi kadai gashin kasan keyanta dana goshinta sun kwanta lublub sabida kema leman ruwan dake tattare dasu, fatar jikinta nawani irin glowing sabida tsabagen gyaran dataji, ita kanta tama kanta kyau dan she looks kaman mata cele, she looks kaman irin yaran masu kudin nan ajebota dabasu san menene wahala ba in this life, ajiyan zuciya tasauke gabanta ya shiga faduwa sabida Ammi data kara fadomata ita haka Allah ya yita duk iskancin ta Allah ya zubamata wani irin tsoron Ammi ne barinma intasan tabbas tamata laifin.
Bude kofa ahankali tayi ta fito.






_remember akwai VIP idan bakison jira, chat me up in kinaso_
[25/04, 20:43] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






7️⃣3️⃣ & 7️⃣4️⃣




_*please read this*_
_Asalam GGM, sabida Ramadan in sha Allah zan dinga muku posting duk ranan daya kamata namuku posting by 9 nadare, lokacin ansha ruwa, anyi sallan isha sanan anyi sallan asham, please starting from this page kar wacce takaranta littafin nan da rana kina azumi no kibari da night bayan kinsha ruwa ki karanta, nafita hakkin ku, Allah ya karba mana ibadun mu, Ameen._






_how to subscribe_
_zaki turo ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsap number na 07012181461 sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya, zaki iya turo katin MTN dari uku 4 those dabasu da account_












Maida kofan tayi tarufe ahankali karyay kara sanan takaraso cikin dakin ledan ta ijiye kan side drawer sanan takashe wutan dakin dakin yay duhu, hannunta takai kan bedside lamp ta kunna hakan yasa dakin yadanyi dim haske, zama tayi ahankali akasa kusada gadon sosai tadaura fuskanta kan gadon tana kallon fuskars, hannunta tadaga tadaura kan gadon tareda lalubo hannunshi tarike dan wani irin tsoro taji tanaji, hannunshi dataji har lokacin da zafi yasa taji wani irin mugun tausayinshi, ita kanta batasan iya adadin son datakema Aliyu ba, tasan duk lokacin datake taredashi yanayin beat din zuciyarta chanzawa yake, whenever she's with Aliyu she feels complete, duk wani abu nashi tanajinshi har ciki cikin zuciyanta, Ammi ce tafado mata arai, wani irin faduwa gabanta yayi yanzu tasan hankalin Ammi yatashi bana wasaba, Su Baffa dasu Khaleelu duk an bazu ana nemanta, zasuyi ta tunanin inda take, Hafiz! takira sunan Dr ahankali, fashewa da kuka ahankali tayi tasan bata kyautamusu ba, zai kalleta a matsayin mayaudariya, wanan wani irin abune saidai kawai suji tayi aure dawani daban? Ta yaudari yan uwanta da Dr, me aciki inda ta tsaya tsayin daka tanunama Mai Martaba batason Aliyu da ba'a daura musu aureba but takasa, mesa takasa jurewa, bazata iya bude ido taga Aliyu na wahala ba dan kowani yanayi Aliyu keciki tanaji aranta sosai, his happiness tanaji, his sadness tanaji sosai. Tunane tunane tacigaba dayi tana kuka mara sauti har wani wahalallen bacci yay awon gaba da ita azaunen tana rikeda hannun Aliyu gam kaman inta saki za'a sace matashine.










Kaman amafarki sama sama takejin karan tari dakuma shesheka kaman na kuka, dakuma hannun Aliyu data rike dataji kaman ana kokarin fizgewa, cikin bacci zuciyarta na ayyana mata Aliyu dawani irin sauri tabude idanunta da bacci ke ciki sosai ta kallai, Aliyu tagani idanunshi arufe sai tari yake sosai yana wani irin nishi yana dukan kirjinshi tawajajen zuciyanshi da hannu hawaye nabin idanunshi dake nan a lumshe, wani irin jumping Aneesah tayi tareda hawa kan gadon arude baccin idanunta na washewa tass, fuskarshi ta shafa arude tana sharemai hawayen tana kiran sunanshi. "Ya Aliyu, Ya Aliyu menene meke maka ciwo eh? Dena kukan kaji" tai maganan tana kama hannunshi dayake dukan kirjin nashi dashi dan hanashi yin hakan, ahankali tai placing hannunta kan heart dinshi ko ita kanta saida taji wani irin abnormal bugu da zuciyan keyi, baki yabude har lokacin idanunshi arufe cikeda tsantsan ciwo yace "ahhhhhh" yana wani irin mika kaman wajen namai ciwo sosai batasan lokacin data fashe da kuka ba ahankali tana shafa fuskarshi tana kiran sunanshi. "Ya Aliyu na wake up, meke maka ciwo? Ganinan, am here, am right here kaji, Aneesah kane am right here" tai maganan calmly dawani soft tone kaman mai whispering tana shafa fuskarshi with so much affection dakesa mutum yaji natsuwa ta shigeshi, ahankali yabude bakinshi cikin muryanshi da bata fita sosai tsabagen zafin ciwo batare daya bude idanunshi ba yace "My Aneesah, Aneesah nah!" da sauri ta matsar da fuskarta da hawaye kebi dab da fuskarshi tana kara matse hannunshi datake rike dashi gam, ahankali tace "uhmm, ganinan Ya Aliyu, am right here next to you, kedana ciwo kaji ko hankalina yadan kwanta, am right here bude ido kagani" tai maganan tana sa hannu tana share

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login