Showing 81001 words to 84000 words out of 186400 words
Chapter 28 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt
da dagamai hannu kaman wata yar koyo taimai waving hand din alamun bye da sauri ta kalli hannun nata kaman ma batasan lokacin data dagashi ba, dan murmushi yayi tareda lumshe ido yabude su ahankali yana kallonta ahankali yay waving nata back irin waving dinan na yaron dabayason maman shi tafita, dauke kai tayi da sauri tadena kallonshi dan hakanan taji yawani irin bata tausayi kaman zuciyanta da nashi na communicating, kaman zuciyanshi nace mata karki tafi kidawo ki zauna dani.
Karasawa wajen motan tayi har direba yabude yaran duk sun shiga Hajar ne kadai agaban motan, wani matsiyacin kallo tama Aneesan tace "gasu agola nan anzo" daidai Aneesa takaraso wajen Rauda dake cikin motan dan ciwon cikin yasaketa sosai yanzu tace "kai Anty Hajar wlh babu kyau fa" ta kalli Aneesa datai kaman batajisu ba tasakin mata murmushi tace "shigo ki zauna Aneesa" murmushi itama tamata dan sai yanzu ne tagane Rauda itace yarinyan data taimaka ranan data fara ganin Aliyu sarkin kallo sai kallonta yake kaman baitaba ganintaba, shiga cikin motan tayi ta zauna kusada Rauda, Hajar ta shigo itama sanan direba yarufe kofan yakoma gaba ya shiga yaja.
Ahankali Rauda tasa hannunta takarbi hannun Aneesa data danyi wani zanen lalle ta around kumbunan ta tace "wow Aneesa wanan wani irin zanen lalle ne? Bbu kodaya a hannunki saita wurin yatsun ki it really looks nice, waya miki ya bala'in burgeni, waya miki?" murmushi Aneesa tayi tana kallon yatsun nata zanen datayi ne da bikin Ammi saitama Ammi kuma lalli mai kyau, ahankali tace "ninayi" "iyye kin iya lalle ne daman?" gyadamata kai tayi tace "na iya, kinaso namiki?" da sauri Rauda ta gyada mata kai tace "inaso mana, sosai ma" ahankali Aneesa tace "shikenan duk randa kika shirya zan miki wanda ma yafi wanan kyau" washe baki Rauda tayi tace "nagode, Awani aji aka saki dazu a hadda?" ahankali tace "aji hudu, islamiya ma aji hudu" bangaje mata kafada Rauda tayi cikeda jin dadi hira irin na kawayen nan tace "iyye ajinmu daya ashe, nima dazu dasafe cikina keta ciwo saisa banjeba wlh" ahankali Aneesa tace "sorry Allah ya sawake" cikeda damuwa Rauda tace "kema kinayin ciwon ciki idan zakiyi?" gyadamata kai Aneesa tayi batare datai magana ba she's not just comfortable sabida Hajar dake wurin, dan tana ganin yanda Hajar ke hararanta itada Raudan kaman ta bubbuge su, cikeda damuwa itama Rauda tace "sannu kinji Aneesa, ance inkai aure yana denawa" "dalla malama kimana shiru ko kina maganan iskanci agaban yara" Hajar tafada cikeda masifa, cikin tsiwa Rauda tace "to wai me ruwanki dani Anty Hajar, yaran sunsam menake cewa ne, kinamin wani ihu saikace nayi dake" ta harari gefen side din Hajar din, murmushi Aneesa tayi hakan yakara harzuka Hajar tace "dan ubanki nikekema rashin kunya?" cikeda rashin kunya Rauda tace "karki kara zaginmin uba nidai, Dady na nagida yana hutawa abinshi kina duramai zagi, kuma ai badake nakeba daga ina firana da kawata saikiyi ta zagina, dakenayi? Neman tsokana kawai" kwashe wa da dariya yaran motan sukayi, wani mugun kallo Hajar tamusu hakan yasa at ukai shiru, Hajar tai kwafa tace "zamu koma gida kaman Mama taji komi" dauke kai Rauda tayi tacigaba da hira ta da Aneesa batakara cemata komiba harsuka kai makaranta suka tafi ajinsu a binsu.
***
Wuraren magrib suka shigo gidan, derevan su yay parking yafito tareda zagayowa yazo yabude musu, saukowa sukayi Rauda ta dubi Aneesa data sauko bayan ita tace "saida safe ki gaishemin da Mummy, gobe zanzo na gaisheta kinji, bari naje part din Ya Aliy...." fizgan hannunta Hajar tayi kaman tafizgo barauniya tace "dan ubanki bazaki ba, ba Mama tahanaki zuwa bangaren shiba" cikin tsananin jin haushi Rauda tace "wai me haka Anty Hajar, wlh kisakeni kona hadaki da Dady me ruwanki dani sai samin ido kike kina sauraron conversation dina" cikin fushi Hajar tadunkule hannu ta sakin mata mugun dundun abaya da har Aneesa saida tajishi har cikin ranta sabida karan dayayi dumm! wani irin ihu Rauda tasaki kaman zata fasa gidan tai kasa tana bankarewa daidai Aliyu ya shigo gidan daga masallaci, rike ciki Rauda tayi dan har cikinta taji dundun tasaki wani irin mugun kuka tana kama cikinta, kaman Aneesa zatai kuka ta kalli Hajar dake huci kaman wata kumurcewatu😎 tace "me tamiki zaki mata wanan dukan bayan kinsan cikinta naciwo" da yatsa Hajar ta nunata tace "ke kalleni nan am 25 niba tsaran wasan ki bace, ba ruwanki idan nida kanwata na fada agol...." wani irin wawan mari da aka dauketa dashi yasa takasa karasa kalman dazata fadi tadago idanunta da sukai mata dishi dinshi tsabagen zafin marin tana sosa wurin ta kalli wanda ya mareta Aliyu ne yana sanye dawata white riga mai dark blue short hands sai dogon black jean dayasaka kamshin turaren shi yabi yacika wurin, hanunshi yadaura kan wandonshi yana kwanto belt dinshi dama bala'in haushin ta yakeji tun ture Aneesa datayi dazu tafadi, cikeda rashin kunya Hajar ta kallai tana ganin belt din dayake shirin kwancewa ita tafi karfin tagudu tace "wlh karma kasake kayi gigin ciro belt dinan kace zaka dakeni dashi agaban kannina kajamin raini agaban yaran da aka haifesu jiya, meruwana dakai nasan kane shiga shara ba shanu, wlh ka zaulamin belt dinan saina hadaka da Mama na tafito ta ramamin mugu kawai" wani irin zuciyane Aliyu yaji tarufe shi ya tsani rashin kunya, ahankali Aneesa ta saukar da kanta kasa jitake kaman tarufe Hajar da shegen duka yanda takema Aliyu rashin kunyan nan harda zagi.
Karan saukan belt da ihun Hajar dataji yasa ta dagokai, takoina Aliyu ke zubama Hajar duka kaman dama anbashi contract din dukanta ne, murmushi Rauda tayi tana share hawayen daya gama wanke mata fuska ganin Ya Aliyu na rama mata, ihu sosai Rauda take tana kiran maman su. "wayyo Allah na, Mama, Mama, Mama kinga Ya Aliyu ko, Mama zai kasheni" fara bude kofofi matayen Dady sukayi suna kallon yanda Aliyu ke kilan Hajar dake ihu da magriban nan, bude kofa Mama tayi jin ihu da hayaniya atsakar gida idanunta ne sukaci karo da Aliyu na dukan Hajar da belt gasu Rauda da sauran yaran gidan jikin mota suna kallo kaman suna kallon show, ga kishiyoyinta ko alamun kwatan Hajar bamasu yiba dan Hajar dama ta addabesu duka yarinyar badai rashin, da gudu ta shiga sauka daga matattakalar benen gaban flat dinta daidai Abba shima ya shigo gidan dan dama dawani ya tsaya magana awaje da tare zamasu shigo da Aliyun daga masallaci. "Gadanga" Dady yakira Aliyu adan zafafe dudda yasan Hajar tai wani abune saisa yake dukanta haka but he's strongly against dukan y'ay'a mata baiso dan sunada rauni. "Aliyu" kiranshi da Dady yasake yi akaro na biyu yasa yawani irin hankade Hajar da hannu, Mama dake tahowa ta tareta da sauri tanabin jikin Hajar din da kallo tana dubawa yanda hannayenta da fuskanta yay rudu rudu, mayar da Hajar din gefe tayi ta ijiye ta jikinta har rawa yake ta zabura tatashi tayo kan Aliyu tace "billahillazi la'ilaha illahuwa bazan yarda ba, y'ata ce kama rudu rudu da jiki haka, wlh saina rama mata" tai kan Aliyun dake mata wani matsiyacin disgusting look jiranta kawai yake tazo tace zata tabashi, azafafe tayo kanshi Dady daya karaso wajen yace "wlh, wlh kika tabamin yarona banga abinda zai hanaki barin gidan nan da daddaren nanba, baki da hankali ko Kareema, kan Yaya yadaki kanwar shi shine zakice zaki rama agaban kaninshi? Bismillah tabashi, tabashi ki gani" yay maganan cikin tsananin fushi yana rungume hannu a kirji yana kallon Maman su Raudan data tsaya tana kallon Aliyun da mahaifin nashi ke tsaye kusada shi, cikin fushi yace "Aliyu yarone mai hakuri, ko kyaran kaninshi bayayi, bantaba ganin yadaga hannu yadaki wani a gidan nanba danyau yadaki Hajara aisai kinsan da dalili ko, Hajara yakamata kima fada baki taso kice zaki dakeshi ba, Gadanga nawa zaki dama agabana, gaban babanshi Kareema, bari kiji daki tabamin yaron nan gwara ni ki tabani sau dubu wlh zan iya yafemiki sau dubu amma duk wanda yatabamin yaron nan kowaye shi aduniyan nan, Kareema kowaye wlh sai inda karfina yakare kinji na rantse miki, wlh kikiyayeni, ki kiyaye ni Kareema, ko gigin wanan haukan karki karayi in your whole entire life" cikeda bala'i da bakin ciki Mama tana kallon yanda Dady kemata bambami tace "ninasan babu abinda Hajar tamai tsabagen tsana ce irin ta Aliyu meruwan Hajar dashi iyee, me Hajar zatamai" da sauri Rauda tace "Mama wlh Anty Hajar ne taketa ma Ya Aliyu rashin kunya agabanmu" da sauri Dady yace "to kindaiji ko da kunenki dan haka ku tattara kowacee ta tafi flat dinta" ya kalli Hajar dake kuka har lokacin jikinta narawa yace "gobe ki kara mara kunya fitsararra, tausayi kikabani danazo nakara miki wani sabon dukan wlh, Aliyu tsaran wasanki ne, ko kallon banza naji kin karamai sainai mummunan sabamiki da idanu kaman na mujiya tashi ki wuce daki kiyi wanka kici abinci" juyawa Mama tayi ta kalli Rauda ta nunata da yatsa tace "badaike shaidaniya bace wlh bani bake Rauda, zanyi maganin ki, badai kinkini uwarki da yar uwarki ba zaki sanine, wlh bani bak...." cikin tsananin fushi Dady yace "waike kin fara zarewa ne Kareema? Me kikecema karaman yarinya bakiba ita iyyee? Mekike nufi? Zan mummunan sabamiki fa inbakibi ahankali ba" juyawa Mama tayi takama Hajar da dagata daga kasa tace "tashi muje, Allah zai sakamiki, wlh saina rama miki wanan alkawari namiki, kuma magulmata yan bakin ciki sai akoma daki masu daukan rahoto, ba kisankai akayiba ai" tai maganan tana kallon matayen Dady, tsaki Amarya tayi tace "aikin banza harara aduhu, gwara da aka lallasatan" da hannu takira yaranta dake gaban mota tace "let's go kids acire kayan makaranta" da sauri sukazo suka shiga daki, dayan matar Dady takira nata yayan ta harari Mama tace "rahoto kam yadauku saura bugawa ajarida ko yarana" tai maganan tanajan kumatun yaran cikeda wasa aiko suka fashe da dariya sukai daki tarufo kofar flat dinsu da karfi, kwafa Mama tayi tace "duk zanyi maganin kune kunyi dani, yar halak ce kumani, muje Hajar" taja Hajar sukai part dinta suka bude kofa suka shige.
Ajiyan zuciya Dady yasaki idan yace baigaji da matayen nan nashiba yay karya, bayason saki, ya tsani saki saisa bazai musuba kullum binsu yake da addu'a Allah ya shiryar mai da iyali kawai amma yasan sun lalatamai yara, dagokai yayi ya kalli Aneesa murmushi yamata yace "kama Rauda Aneesa kutafi flat dinku" ya kalli Rauda datai zuru zuru sabida kalaman maman ta ance uwa uwace koma yayatake yamata murmushi yace "don't worry okay, bi Aneesa ki kwana a flat dinsu, am coming there now yanzun nan zanzo duk muyi dinner tare, you guys should go and shower" gyadamai kai tayi suka wuce suka tafi Aliyu yabisu da kallo cikin fushi Dady ya kalleshi yace "come with me" yya hanyar shashin Aliyun.
_how to subscribe_
_zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to WhatsApp number na 07012181461. Zaki iya turo katin MTN na 300 for those dabasu da card sainai adding naki a group din a tsakanin soyyayya_
[26/03, 06:15] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_
_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤
_✍🏿M Shakur_
3️⃣8️⃣
Bude door din flat dinshi Dady yayi ya shiga Aliyu yabiyo shi abaya hannunshi ma duk zafi yakemai yadai daure baiso yanunama Dady, maida kofar dakin Aliyu yayi yarufe ya shigo ciki, cikin fushi Dady ya juyo ya kallai yana karasowa cikeda fada yace "sabida babu kyau yima babba fada agaban kaninshi ne that's d reason why bance komiba, why will you be beating Hajara like that kana so kajimata cewo ne eh? Wat if kamata illa? Aliyu kadinga controlling wanan zuciyan fa, wats up with wanan zuciyan dakake yi this days abu kadan ka harzuka eh?" daure fuska yayi tamau yakaraso yafada kan kujera ya kwanta batare dayace komiba dan yasan yay magana fada zasuyi da Dady sosai this night, cikin fushi Dady yace "ba dakai nake magana ba Aliyu? Badakai nake magana ba ka shareni haka?" kaman zaiyi kuka cikin kunan rai Aliyu yace "Daddd leave me aloneeee" baki Dady yasaki yana kallonshi, cikeda jin haushi yet bakuma jin haushin shi yakeba but yabatamai rai, cikeda fushi Dady yace "nikake cema nabarka alone Aliyu? Zan sassaba makafa, babu kyau dukan mata duk abinda su Maman yaran sukemin kataba ganin I raise my hand on them? they don't hit woman Son ba'a dukan mace" cikin fushi sosai Aliyu yace "leave me alone Dad, Allah kadamen I will leave this house for you and your wives, kun isheni, am tired, am tired Daddd, kowa hates me, what have I done haaa? Hajar doesn't respect me, my own siblings don't respect me, what have you done about it Dad? Kataba kiransu kamusu fada? Kullum they keep pretending niba wansu bane, pretending we aren't bloodties, we are not blood related, idan Rauda tazo wajena adake ta, amata this amata dat mekake cewa akai? You think am not hurt because I keep mute bana magana? Banda wata kanwa dat I can go out with and say this is my sister she's my sister, kannin nawama basu sona, common small Amal (auta) idan taganni she will be running Mama tace kartamin magana intamin magana Mama will beat her, koda yaushe am alone, am alone, am alone, am soo lonely, so soo lonely Dad, you think abin baimin ciwone? you think banson kannina ne ko bandamu da yanda suke behaving am dead to them
basu sanni ba? Dad my 19 sisters, all of them like all of them, I love them with all my heart because they came from you, dsame blood ke running in my vein shike running in their veins, sabida nahukunta Hajar which bantaba yiba shine zakazo kana questioning nawa are you also trying to show me I don't have any right over them ba kannina bane Dad? Are you telling me nafita daga harkan su kaima? Banda kanni ko Dad, banda iko a kansu ko Dad?" tashi yayi da sauri zaiyi ciki Dady yarikemai hannu zuciyar shi tai rauni sosai, maganganun Aliyu sun sosamai zuciya, sun tabashi bana wasaba kaman yabuga uban ihu yayta kuka yakeji, ahankali yace "Aliyu na, wait Gadanga na ina zaka?" fizge hannunshi Aliyu yayi da karfi yay bedroom dinshi kafin Dady ma ya iso yamaida kofan yarufe yasaka key yafada gado yaja pillow yana kara matse idanunshi yana kokarin hana kanshi kwallan dake shirin zubomai.
Wani irin sanyi jikin Dady yayi jin maganganun Aliyu, ahankali yadaura hanunshi kan kofan yay knocking murya chan kasa yace "open the door My Boy" shiru yayi baima da karfi sabida yanda yay hurting Aliyu, ahankali yace "you've made me realise that you are not more yaron nan dan shekara goma danake dauka up and down muna yawo, you've made me realise that you are now a man, namiji dazai iya rike iyali, mai hankali da sanin yakamata" shiru yayi zuciyar shi nawani iron swelling with emotions ahankali yace "am sorry Gadangana, Dady is sorry for hurting his boy, Daddy have made a mistake, his boy misunderstood Dady, am sorry Aliyun Daddy shi, open the door okay we have alot to discuss" shiru yayi kalaman Aliyu nakara dawomai zuciya runste ido yayi saiyau ya yarda cewa yay sake ya tsaya yabude ido yana kallon matayenshi najuyamai kan yara, shine uban yayan shi shine zai hada kan yayan shi idan matayenshi basa son danshi wanan is understandable not yaranshi basa son Aliyu, yau idan yafada yamutu ubanwa ye zai tsaya musu amatsayin uba? Ubanwa zai aurar dasu naba dasu aure? What was he doing all this while yana kallo matayenshi nakoyar da yayan shi cewa Aliyu is nobody he is not their brother enough is enough! Knocking kofar Dady yayi yace "Aliyu na open the door" jin ana tada sallan isha yasa Dady yace "at least kabude kofa kazo mutafi masallaci kaji" jin shiru yasa zuciyan Dady yay rauni sosai yasan Aliyu da taurin kai yasanshi farin sani, yasan yanda ranan nashi yabaci yau kome zaifadamai bazai bude kofan nanba, juyawa yay ahankali yawuce yafita masallaci yatafi, isha'i yayi yay shafa'i da wuturi sanan yadawo gidan shashin Aliyun yakoma yay yay yay dashi yafito bai fitoba hakan yasa yafito yarufo ai kofan shashin nasu yawuce flat din su Ammi.
Ahankali yabude kofan flat din wani hadadden kamshin turare ne yamai sallama, Aneesa ce kadai a falon tana sanye da dogon riga tana rubuce rubuce da alamu assignment takeyi, sallama Dady yayi ahankali da sauri Aneesa tadago kai ganin Dady yasa tasaki murmushi tace "sannu da zuwa Abba" gyadamata kai Dady yayi yasami wuri kan kujera ya zauna tareda fuzar da iska yana shafa gaban goshin shi kaman wanda kefama da ciwon kai, ganin yanda Dady yayi yasa ahankali Aneesa tace "Dady bakada lafiya ne?" janye hannunshi yayi daga goshin ya kalli Aneesan murmushi yadan kakalo mata tareda girgiza mata kai yace "No am fine, ina maman ki?" ahankali tana nazarin Dady tace "tana sama a dakinta" gyadamata kai yayi tareda dan lumshe ido yace "okay jeki kiramini ita" gyadamai kai tayi tamike tsaye tai sama dakin Ammi ta shiga Ammi datai wanka tana cikin fesa turare Aneesa tai sallama ta shigo hakan yasa ta kalleta, shigowa Aneesa tayi dakin tace "Ammi Abba na nakiranki kaman baida lafiya" da sauri Ammi ta ijiye turaren datake fesawa ta kalli Aneesan tace "kaman baida lafiya" gyadamata kai Aneesa tayi da sauri Ammi tai hanyar kofa tanunama Aneesa yan kayan da taciro daga sip tace "kimaidamin kayayyakin nan cikin sip" gyadama Ammin kai tayi tace "to" Ammi tajuya tafita da sauri, tundaga kan stairs Dady ke hango hasken fuskan Ammi dake mugun sanyayamai tana kallonshi tana zuwa da dan saurinta, ajiyan zuciya ya