Showing 141001 words to 144000 words out of 186400 words

Chapter 48 - ATSAKANIN SOYAYYA COMPLETE By Maman Shakur .txt

20 Jan 2025

18823

"I want to shower Dad" tashi Dady yayi yataimaka mai yakaishi har cikin bayin sanan yace "mezan dafama mezakaci?" yatsine fuska yayi yace "cook Indomie for me Dad, with omelette sai coffee" da sauri Dady dudda bai wani iyaba yace "to dan Albarka na, Aliyu Hydar namiji, bari nadafo ma da sauri be fast" fita daga bayin Dady yayi cikeda murna ganin harzaici abinci yay kitchen dinshi ganin babusu Indomie a kitchen dinshi yasa yafita, flat din su Rauda yayi yasan su Hajar bazasu rasa Indomie ba, Hajar yakira daduk tai sanyi yanzu suka shiga kitchen din tare tana tayashi yanyanka veggies dan Aliyu nason veggies a abincin da kuma sea food, he's not a fan of red meat amma yanaci but not always.




Agurguje yay wankan da ruwan zafi sosai sanan yafito daure da towel a waist jikinshi amurnurde tsabagen exercise, agurguje yabude wardrobe wani sky blue VIP giznar shi dabaima taba sawaba yadauko ya shirya cikinshi bakaramin kyau yayiba, ya feffesa hadaddun turaren shi yadau wallet dinshi dake dauke da kudade da atm cards dinshi yazura herms cover shoe dinshi yana tafiya ahankali danhar jiri jiri yake gani, idanunshi ne suka sauka kan key din ferrari motar shi da dad yabashi dake cikin kwali, kwalin yadauka da sauri yabude yazaro key motar ya yar da kwalin sanan yafito ahankali yana daddafa bango kaman wanda ya sha giya harya karasa wajen motar data mugun hadu fara fat, bude motar yayi yazauna wajen direba cikin motar looks like heaven tsabagen kyau, yatada motar yaja Gate man dinsu yabude mai dawani irin masifaffen gudu dama motar badai guduba kaman zata tashi sama yakejan motar dan yanzu is 10:50 shadaya saura.






Inkika karanta batare dakin biyaba Allah ya isa
Ikon Allah ne kawai ya shigo da Aliyu garin kaduna misalin karfe daya, ganin idanunshi na juyawa kaman zai suma yasa yay parking da sauri wajen daidai signboard din Eye center kaduna yafito yana tafiya da kyar ya karasa wani babban shago dayagani, murya chan kasa yace "give me farm fresh yogurt" da sauri mutumin yace "to Alhaji" dauko yogurt din mutumin yayi yana kallon fuskan Aliyun yace "sorry Alhaji hala ba lafiya ne" gyadamai kai Aliyu yayi yana karban yogurt din yabude ya kafa abaki yafara sha saida yay kusan rabi sanan ya ijiye mutumin yace "sannu" wallet Aliyu yazaro yaciro dubu biyar yamikamai yace "hold d change" cikeda jin Dady mutumin yace "nagode Alhaji sosai, Allah kara sauki Allah kuma yabaka lafiya" ahankali yace "Ameen" yana kara kai yogurt din bakinshi saida ya shanye tass sanan ya sauke ajiyan zuciya yadanji dan karfi da dama dana dan baya ganin jirin yanzu, dagokai yayi ahankali ya kalli mai shagon hakanan ranshi yagayamai ya tambayay, ahankali yace "tambaya nike Malam" cikeda farin ciki mai shagon yace "Allah yasa nasani" ahankali Aliyu kasan please kasan gidan "Alhaji Isma'il Mai kwato da ake bikin yar wajenshi yau?" da sauri mai shagon yace "laaaa ba shakka nifa Ince naganka kaci gayu haka kaman ango, ashe kaima daurin auren kazo aiko ninasan gidan mai kwato dan abokin sana'a nane wajenshi muke sayan shanu da ragunan salla" wani irin ajiyan zuciya Aliyu ya sauke kaman ya kulle ido yabude yaganshi agaban Aneesah, da sauri yace "inane banso nayi missing daurin auren" da sauri mutumin yace "kaga kamike express road dinan sambal karkadau wata kwana kaita kallon bangaren haggun ka zakaga wani gidanmai mai suna Danaba, layin jikin danaban zaka shiga dazaran ka shiga zaka gane gidan bikin dan dandan babban mutum zata aura likita ne yaron anguwan makil yake da motoci danma wanan ruwan dayaki daukewa ne yama mutane cikas wlh da tuni ko ina yacika da hayaniya" sosai Aliyu yaji zuciyar shi namai zafi, ahankali yace "dan Allah a ina ake saida hijabi inaso nasai hijabai ne" dariya mai shagon yayi yace "hala gudunmawar ka kenan dan amaryan akwai sa hijabi, bantaba ganin yarinyar da gyale ba, kaga kaita tafiya kawai akan hanya zakaga masu saida hijabi dasu safa da nikabi" , ahankali Aliyu yace "nagode" sanan yajuya ahankali ruwa na sauka akanshi yawuce ya shiga motarshi mai shagon na leko motar yana mamaki wanan kodai dan shugaban kasane yaro ga kyau ga kudi jibidai mota mai numfashin dayake ja.


Bala'in gudu Aliyu yake yana kalle kalle har idanunshi suka sauka akan shagon da ake saida hijabi tsayawa yayi yafito yana tafiya ahankali yacema mutumin shagon "Malam hijabi nakeso kaman wanda zaima mai tsawona har kasa yanajan kasa" kallonshi mai shagon yayi yace "okay yadi shidda da kusan rabi kenan" zama Aliyu yayi kan kujeran ahankali yace "OK ayanka adinkamin yi sauri, kuna saida nikabi ne?" "eh muna saidawa yallabai" gyadakai Aliyu yayi ya daga agogon hannunshi na rolex yana kallo about 1 :15 yanzu, ganin yanda yayyafin da akeyi ke zuba kanshi yasa mai shagon yace "ka shigo ciki Alhaji kar ruwa ya jikaka" dan shigowa ciki Aliyu yayi yana kallonshi, cikin minti baifi gomaba yagama dinka hijabin sanan yace "a dauko nikabin ne yallabai" gyadamai kai Aliyu yayi yadauko yace "kudinka ya tashi biyu da dari takwas" zaro kudin dabaimasan yawansu ba yayi yamikamai yajuyo yashiga mota da gudu haryakai wajen daidai gidan man danaban kafinma ya shiga unguwan ya hango motoci shiga yayi yayi parking daga baya baya, tareda kashe motar, ajiyan zuciya ya sauke ya kalli hijabi da nikabin da aka dinkamai, ahankali yajawo hijabin ya warware yasaka daga zaunen, sanan yadauko nikabin yana gyara madubin gaban motan ya daurashi tsaf, farin glass din mai karamin lens daya daukone yasaka a idanun sanan yabude motan yafito yana numfashi sama sama dan baisababa jiyayi kaman nikabin ya shakemai wuya, kallon kanshi yayi ta jikin glass din motar yanda hijabin ya saukanmai danko takalmin shi ba'a hangowa yay kato cikin sanan yay kato ciki, kulle motar yayi yafara tafiya ahankali kaman mace yana shiga anguwan sosai ruwa na sauka akanshi yana kallon tulin mazan dake cikin wata runfa an tsaitsaya ana magana za'aja daurin auren zuwa karfe uku sabida ruwan da akeyi ga Baffan ta na zuwa dan sun fita dole ajirasu, wasu yan mata dayagani sunci gayu suna sanye da anko sun fito daga wani gida ya tare tareda lankwasar da muryan shi kaman wata mace yace "yan mata dan Allah wani gida amarya take zanganta ne is urgent" daya daga cikin yan matan ne tanunamai gidan dasuka fito daga ciki tace "nanne tana dakin su salamatu" baima tsaya musu godiya ba yashiga gidan da sauri gabanshi nawani irin faduwa ya kalli yan matan da sukacici gayu ana kwalliya, falon dayagani abude ga takalmomin yan mata yafada, yan mata ya gaggani zaune wasu nacin abinci wasu na rawa dan sun kunna wakan Zee baby a speaker falon yacika da hayaniya, wajen wata dayaga tanata kallonshi yayi tunda ya shigo da sauri yace "dan Allah ina Aneesah Ammi ta aikoni wajenta" murmushi tayi tace tana dakin su salamatu kaya ake chanza mata" da sauri yace "inane dakin?" Corridor ta nunamai hakan yasa yay corridor da sauri gabanshi nafaduwa har wani lumshe ido yake his eyes are eager to see her, kofar dakin dayagani abude surutu natasowa daga ciki yayi ahankali yakarasa bakin kofan tsayawa yayi chak yana kallon Aneesah dataci gayu sosai an mata hadadden makeup tasaka hadaddiyar doguwan riga na maroon and golds an mata daurin gwaggwaro daya mugun yimata kyau gashin gaban goshinta sun wani irin kwanta, tayi kyau kaman wata Celebrity, kayan jikinta sun mata kyau sunbi jikinta sosai, wata yarinya da ita kadai ke dakin tana daura mata agogo ahannunta dayasha wani hadadden lallen amare, chak numfashin shi ya tsaya kafin ahankali yadawo yawani irin sauke ajiyan zuciya, wani irin sanyi Aneesah taji ajikinta dayasa tadago kanta da sauri danji tayi kaman anbude fridge idanunta ne suka sauka akan wata katuwar doguwan matan dake tsaye abakin kofar dakin dasuke tana sanye da hijabi dakuma nikabi tasaka wani farin glass tana kallonsu, dan taba Salamatu dake samata agogo tayi hakan yasa salamatu ta dago kanta da sauri tace "menene Aneesah?" ganin inda Aneesah ke kallo yasa tawaiga ganin mata danikabi ta tsaya chak tana kallonsu itaba tai magana ba yasa tace "Anty lafiya wakike nema? Mama na gidan biki mune kawayen Amarya kawai ke fati a gidan nan" dago kafa ahankali Aliyu yayi yana wani irin kallon Aneesah data cigaba da gyara sarkan wuyanta tana kallon madubi tana murmushi da kanta dan ita kanta tama kanta kyau, lankwashe murya yayi da kyau gudun kar Aneesah ta dago ta yace "Ammi ta aikoni wajen Aneesah" da sauri Aneesa tadagokai ta kalleshi jin ya kira Ammi tace "Ammi na" gyadamata kai yayi yace "eh tace na kawo mata Ke yanzun nan komin hayaniyan dakuke na tabbatar nazo dake, Baffan ki dawani bakonshi da Ammi ki keson ganinki su uku, dauko hijabi kisa muje, ni muna girki ne ankusan daurawa" da sauri Aneesah ta kalli salamatu tace "ina hijabina salamatu?" hijabinta salamatu tabude wani jaka taciro tabata karba Aneesah tayi tasa hannu ta zare gwargwaron kanta dogon gashinta da aka daure dawani hadadden ribbon dayasha gyara ya sauko saida numfashin Aliyu yakusan daukewa ta zura hijabin tareda mikewa ta kalli salamatu tace "muje ki rakani" hararanta salamatu tayi tace "Inna biki wazaiji da bakin? Nidai kiyi sauri" juyawa Aliyu yayi yana tafiya ahankali Aneesah na biyeda shi suna fitowa falo akadau guda ana Amarya ina zaki, dariya Salamatu tayi tace "to iyayen gulma Ammi ke kiranta" suka fice lokacin ruwa yaragu saidai yayyafin da ake, sanin waje da maza yasa taja hijabinta gaba sosai suka fito tana biye dashi, ganin sunyi hanyar wajen layi yasa da sauri Aneesah ta cinmata tace "Ammi bata gidane?" gyadamata kai yayi yana make murya yace "gida da mutane suna gidanmu, chan layin dake kallon layin mu, motama sukasaka na dauko danna kawoki dawuri tace tundazu take kiranki dan salamatu tarakoki kizo baki dauka" da sauri tace "ayyah wayata na purse din salamatun ne saisa" ahankali suke tafiya haryakai wajen motarshi sai kallon hadaddiyar motan take yabude motar yace "yi sauri kinga wayana ma na vibration nasan ita ke kira" ko tunani Aneesah batayiba ta shige ya maida kofan ya rufe yazagaya da sauri ya shiga wajen direba ya zauna yay locking motar gabaki daya, sanan yatada motar batare daya ciro hannunshi daga hijabi ba yaja motar da mahaukacin gudu dahar saida Aneesah ta firgita gabanta nafaduwa sosai sai kallonshi take.
[21/04, 11:57] Aishat Muhammad: _*A TSAKANKANIN SOYAYYA*_










_IN BETWEEN THE LOVE_
❤ _Lies another love_❤








_✍🏿M Shakur_






6️⃣9️⃣ & 7️⃣0️⃣








Dudda batasan ko'ina ba dan ita bata taba zuwa kaduna da wayonta ba, sanan tsawon zamanta a gidan Baffa saida zasu kasuwa dawurin kapinta ne ta taba fitowa daga anguwan nan, but ganin yanda yake zabga gudu yasa gabanta yafara faduwa sosai ahankali tace "har yanzu bamu kaiba?" cikin muryan matan yace "yanzun nan zamukai, munkusa" sunyi tafiyan kaman na minti goma sha biyar saida yabari suka fita daga kawo sukadau hanyar zaria sanan ahankali ya gangara gefen titi yay parking tareda kashe motar, da sauri Aneesa datai wani irin danji tayi duk hankalinta yatashi ta kalli hanya ganin inda suke bakin dajinema kan hanya babu mutane ko daya awurin sai motoci dake gittawa daidai yasa da sauri tajuyo ta kallai gabanta nafaduwa sosai tace "anan ne Ammi na take?" ahankali Aliyu ya ciro fararen hannayenshi daga hijabin yakai hannun yazare glasses din kan idanunshi ya ijiye, wani irin bin hannunshi da kallo Aneesah take ga hannu wan farare tass kaman na ta mace kaman na namiji, ahankali yakai hannunshi bayan nikabin ya warware kullin tareda jan nikabin awanin irin hankali harya zareshi daga kan fuskarshi, wani irin mummunan faduwa da gaban Aneesah yayi saida tazabura tadafe kirjinta, dago jajayen idanunshi yayi yadaura akanta yana mata wani irin kallon So, shauki, kewa, kauna da bege dakuma fushi kafin ahankali yasa hannu yazare hijabin daga jikinshi gabaki daya ya yaye ya dunkule ya jefa a kujeran baya yajuyo ya kalleta yana gyara zaman riganshi, wani irin zabura Aneesah tayi kafin arude tasa hannunta ta shiga kokarin bude kofan motan danta fita daga motar, ahankali cikin sassanyar muryan shi yana kallon yanda take kicinyar bude motar yace "kozaki kwana kina kokarin bude kofar motar nan bazai taba abuduwan mikiba Fateema!" juyowa Aneesah tayi da sauri ta kallai hawaye yasoma taruwa a idanunta, gabanta nawani irin faduwa, bakinta narawa sosai tace "y.....y....ya akayi kasan inda nake?" kallonta yayi ido cikin ido wani irin azaban sonta na dakan zuciyan shi yace "inba dai aturbaya zaki boyeba ko ina abinda nakeso yaboye aduniyan nan zan iya nemoshi Fateemah!" yanda yake mata magana asanyaye kaman mara lafiya yasa taji jikinta yadau rawa, da sauri bakinta narawa har lokacin tace "k.....abude mini kofa nakoma gida yaune bikina kabude min kofa kafin afara nemana, kabude min nakoma gida" murya chan kasa yace "keda gida har abada Aneesah" wani irin kallonshi tayi hawayen daya taru a idanunta suka zubo sharrr, da sauri ta share hawayen tai dan murmushi tace "you are joking right? Please I take this as a joke, kindly take me back home Aliyu, kar kasa afara nemana agida, yanzun nan za'a dauramin aure" wani irin dukan gaban motan Aliyu yayi cikin fushi yay ihu dasaida ya firgitata yace "stop telling me yanzunan za'a dauramiki aure, bakida wani miji sama dani aduniyan nan cus I Love you, I love you Fateema, I love you" har zuciyanta taji kalaman I love you daya fadi mata, lumshe ido tayi da sauri tana hana kanta kukan dayake shirin zuwan mata tace "banason ka ni Aliyu, babu abinda zanyi dakai, babu abinda zanyi da wanda aka min shirin kisa akanshi, babu abinda zanyi da yaron da mahaifinshi yaturani gidan yari akai, Aliyu yanzu bada bane I don't want anything dat has to do with your family, so am telling you one last time bana sonka, bana bukatar ka arayuwata, kabudemin kofa nafita nakoma gida" wani irin girgiza mata kai Aliyu yayi yana dafe kirjinshi dakemai zafi kaman an yaba dalma akai yace "Anebaby! Society da invaders, my parents or yours, family issues ko abu makamancin haka are too small to break the bond of our love, Aneesah am sorry for abinda mahaifina yamiki, My Dad wronged you and I am sorry, I never wish for any of that to happen, kin manta soyayyar mu Aneesah? Have you forgotten the type of love we shared? Kin manta da salon soyayyar mu, kin manta da soyayyan mu Aneesah, are you willing to give it up? Are you willing ki saki soyayyan mu tabi iska sabida wasu? What about me love? Wat about my precious heart that knows no one banda ke? What about my soul, my body that yarns you only? Aneesah soyayyar mu, our love" shiru Aneesah tayi kuka kecin ta amma ina bazata yishiba, wani irin murmushi ciwo tayi tace "Aliyu kenan, mahaifinka yariga yaraba soyayyar nan dakasani, banda hakama ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu wata kyakyawar tsaftatatcciyar soyayya ta shigo, ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu akwai wata soyayya, IN BETWEEN OUR LOVE lies another love which I cherish, I have my man now da zuciyata ta aminta dashi, wanda mahaifiyata ta aminta dashi, yan uwana suka aminta dashi sanan suka soshi, mutumin daya rufamin asiri yasoni despite my flaws, he helped me rebuild my self and gain my confidence back Dr Hafiz Zaid, My husband to be wanda nake bala'in s........." "shut up!" Aliyu yamata wani irin mahaukacin ihu yana buga jikin motarshi kaman zai fasa da kafa, yasake ihu kaman wani zakin daji yace "shut up, stop telling me kinason another Man, Fateema u are my wife, u are mine, only mine, and am gonna show u that today, bakida wani miji inhar am alive a duniyan nan sama dani, ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu babu wata soyayya, babu wata soyayyar data isa ta shigo TSAKANKANIN SOYAYYAN mu, IN BETWEEN OUR LOVE lies no any love, you are mine Mrs Aliyu Hydar Gadanga, you belong to me, and inhar abu nawane baya taba zama nakowa, zuciyar ki na tareda sona we love each other, family issues ko anything is too small to break d bond of our love, we are connected, gap din da iyayenmu sukai creating ATSAKANKANIN SOYAYYAn mu zamu ciketa, me and you are inseparable, and I love you very much" yana gama maganan yawani irin kunna motar kaman mahaukaci yajata, arude Aneesah ta kallai saikuma tasaki kuka tamugun tsorata da yanda taganshi yanajan motan ko idanunshi ma baya budewa da kyau tsabagen fushi da masifan zuciya, ganin sun cigaba da tafiya ne baimada niyyan komawa baya yasa tafashe da kuka tace "na shiga uku, ina zaka kaini Ya Aliyu, ka maidani gida, Ammi na zata nemeni, ka maidani gida" ko kallonta baiyiba sai gudun daya cigaba dayi, bakaramin bakanta mata rai abin yayiba, cikin fushi tanuna shi da yatsa hawaye nabin idanunta sosai tace "zakaja namaka illa wlh, Aliyu take me back home nagaya maka, wlh zanji maka ciwo" batare daya kalleta ba yace "do me a favour and kill me, ki aikani lahira shi yafimin da in bude idona naga kina auren wani wlh I will never allow that to happen saidai in bana numfashi" cikeda fada tai ihu tace "to me ruwanka dani haaa? I don't love you bana sonkai nace, dole ne, where are you taking me to, karabu dani, kaga Aliyu ka komar dani gida kona jimaka ciwo wlh" murya chan kasa yana numfashi ahankali ahankali kaman mai shirin suma yace "ki kasheni kinji Barkono" duk zuciyanta kasamai komi tayi dan gani tayima baida lafiya karfin hali kawai yake yana mata bala'in nan kaman ma baya gani da kyau sabida yanda yake kyapkyapta ido yana tuki da masifan gudu, fashewa dawani irin kuka tayi ta kife kanta akan cinyarta hankalinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login