Showing 30001 words to 33000 words out of 260204 words
Chapter 11 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
malamin zaiyi yayi don ganin kozai iya cin nasara Amma ya kasayi daga k'arshe sema cemata da yayi ta tashi tatafi don babu abunda zai iya, domin wannan auren ko tana so ko bataso dole sai anyisa saboda arubuce yake acikin qundin qaddarar yaronta da babu wanda ya isa ya hana ko kuma ya sauyasa hakan, Wanda kuma duk yayi yunqurin hanawa to tabbas babu ko shakka dole zai mutu don bazai iya ja da alqawarin ALLAH ba.
*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUππ_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___15π
Wasa wasa gini yafara girma saboda aikin akeyi ba dare ba rana, duk wani tanadi da baffa yayi sai daya fiddosa yabawa baffa usman yace ayi duk abunda yakamata kafin lokaci yayi don baya son aikin yakai har lokacin da za'a kawo amarya, acewarsa hakan yafi da ace ankawo yarinyar mutane cikin matsuwa inda bazata samu sakewa ba, sosai duk wanda ya kalli baffa cikin natsuwa zai fahimci bakad'an yake matuqar jin jiki ba, ammasaboda qarfin hali akoda yaushe qoqarin b'oye hakan yakeyi don gudun kada adakatar da auren.
Ita kuwa yaya hawwa kullum cikin masifa take wai ama faman kashewa k'asa kud'i a banza anqi atanada Amma tun daga baffa har zuwa baffa Usman Babu wanda ya tankata inba baffa Ali dake sake zugata akan ccewa inbatayi da gaskeba duk nan baffa zai qarar da kud'in gashi yana jinya abarta da wahala, sake rufe idanuwa tayi ita ala tilasa a ajiye ginin inyaso Nuraddeen d'auki shigihwa guda a cikin shigihun dake sashen nasu a gyarawa yarinyar, nan ma baris baffa yayi da ita saima cigaba da bada kud'i da yakeyi ana cigaba da aikin, tayi masifar tayi har tagaji don kanta tabari amma babu abunda ke dad'a b'ata mata rai irin yanda taga ana narkewa wajen kud'i da irin manyan shanun da yasa aka kama aka sayar, hakan ba k'aramin takaici da bak'inciki yake sata ba idan ta tuna, gashi har yanzu takasa had'a kud'in da malam bakada imani yace tahad'o wajen yimata aiki balle tasan ko meye madafarta, wata shawara ta yanke aranta na zuwa wjen baffa ko zata samu cikon kud'in da take nema wajensa, kwance ta iskoshi duk ya had'a zufa saboda wutar da aka d'auke sai zafi ya taso masa,
"A'a malan kaid'ai kake a d'akin ba kowa? Sukuma 'yan albarka sun d'auke wutar duk zafi yataso, kai ALLAH dai ya rangwanta mana" tafad'a tana jaye labulayyen taga saboda iska yashigo sannan taqaraso wajensa ta tallabosa ya tashi zaune yana fad'in "wash! bi ahankali hawwa, bayannan inajin yana yimun zafi sosai"
"Sannu malan, sai hak'uri kasan dama shi sauqi ahankali yake shiga, ALLAH dai yabaka lafiya."
"Amin hawwa." Yafad'a yana kallonta cike da mamaki don yasan wani abun take so, bai qarasa tunanin da yakeyiba yaga ta d'auko mafefeci tafara yimasa fiffita had'e da cewa, "malan kaga aurennan ya matso gashi babu fashi sai anyisa kuma inada buqatar inyi wasu 'yan gyare gyare, shine nace mezai hana ko 'yar dubu goma ka qara mani insamu in gyaggyara kafin lokacin ya qaraso" murmushi yayi don dama uasan za'a rina, indai hawwar daya sani ce Babu yanda za'ayi kaga tana yimasa wud'annan abubuwan batare da tana son wani abu daga garesa ba, d'an nisawa yayi sannan yace,
"Hawwa dubu gomafa kikace?, Yanzu ke ko hidimar gyaran inda yaronnan zai zauna da nakeyi bakya gani har zaki zomun da wannan zance, haba hawwa ai kamata yayi ace kinkawo nahannunki anqara dasu bawai kinemi karb'a ba"
"Amma naga ainima duk hidimarce zanyi ko malan, ko kafiso akawo yarinyar nan babu wani abun kirki da aka tsinana agidan?."
"To meza'ayi tunda dai naga ba kishiyarki bace balle kice haka, in Kuma maganar abubuwan da za'aci a rarrabane to kibari lokaci yayi ina sane dasu, mufa wajen ango muke ba amarya ba balle muce wata hidima zamuyi."
"Dakata malan kawai idan bazaka bayar bane kafad'amun Amma bazai yuyu kazauna kana fad'amun yanda ranka keso ba." Taqarasa maganar had'e da miqewa ta jefar da mafefecin gefe,
"Meyayi zafi haka daga magana hawwa karki manta yaronnan d'an mune mu muka haifesa kinga kuwa gaba d'aya hidimar tamuce dani dake kuma yakamata ace kema kin kawo taki gudun mawar, ni nazatama kina can kina qoqarin had'a masa lefe ashe aiki nizai qararwa." Ya iyar da zancen yana dariya, wani irin mugun tsaki taja sannan tabar d'akin, girgiza kai yayi yace "ALLAH ya shiryeki hawwa."
β’β’β’ β’β’β’ β’β’β’
Ta b'angaren baba kuwa tuni yaga yakammala had'a kayan d'akin Rashida da taimakon d'an uwansa malan balarabe, haka itama umma bisa amincewar Rashida tasa 'yan uwanta sukazo tabasu sadakin Rashida da kuma abunda ALLAH ya hore mata da wanda suka kawo mata tace suje tare da rashidar duk abunda takeso ta fannin kayan kici dana aikace aikacen gida asawo mata, tun safe suka fita basu dawo ba har sai qarfe biyar na marece, sosai umma taji dad'in sayayyar da sukayo mata don Babu abunda basu siyoba sai wanda aka manta, shire shiren auren sukeyi sosai don tuni sun fara rabon minti da cingwam, soyayya kuwa tsakanin Rashida da Nuraddeen sai wanda yagani, cikin sati d'aya suka d'inke waje d'aya tamkar wasu masoyan da suka jima da shekaru suna soyayya, kullum cikin satin sai yaje wajenta fira da daddare wani lokacin kuma da marece, tuni d'aliban makaranta da kuma malamai suka sanda alaqar dake tsakanin malam Idris da Rashida wanda mafi yawansu sunsha mamakin yanda malam idris yake d'an kwalisa kuma wayayye da yasha boka zai auri Rashida wacce kaf makarantar babu wanda baisan da zaman taba saboda tsabar takkwalci, wasu kanyi fatan alkhairi gareta akan ALLAH yasa ta sanadiyarsa tamaida hankali ga karatu wasu kuma kanyi dariya had'e da cewa ya kwasarwa kansa daqiqiyar yarinya kuma jahila, duk abubuwan da mutane kefad'a suna dawo masa a kunne amma ko sau d'aya bai tab'a jin damuwa akan haka ba, yariga yaji ya gani aduk yanda Rashidarsa take yana sonta kuma yana qaunarta ahaka, ana gobe juma'a da zai koma gida yazo fira wajen Rashida da daddare bayan tafito tayi masa shimfid'a a zaure ya zauna takoma cikin gida ta kawo masa ruwa yasha sannan itama tazauna saman kujera irin tazaman gida dake facing d'insa,
"Sannu da zuwa malamina." Tafad'a tana jujjuya wayarta dake hannunta kafin shi kuma ya amsa mata da "yawwa habibty, kina lafiya?."
"Lafiya klau alhamdulillah, ya shire shiren tafiya?, gobe sai gida ko?"
"In sha ALLAH, ko Zaki rakani?." K'walalo idanuwa tayi waje had'e da cewa "na shiga uku ni 'yar babanta, rufan asiri kada kasa abugani ajaridu"
"Saboda kinje gidanmu ana saura sati d'aya bukinmu?, Ai ni kuwa sai nake ganin da nan da can duka d'ayane Babu wani abun aciki!."
"Hakane, Amma dai kasan hakan ma bazata faruba gaskiya."
"To naji, nima dai da wasa nakeyi amma Ina so ne idan Allah yasa nakoma ranar lahadi za'azo akawo lefe"
"ALLAH yakai ranmu kuma yasa ka isa lafiya."
"Amin habibty, amma Ina so don ALLAH kiyi haquri da duk abunda kika gani, ba haka naso ba yanayin abunne yazo ahaka."
"Malamina kenan! Ni koda duka lefenne baka samu damar yiba bazanji komai ba saboda inada yaqini da kuma tabbaci akanka, nasan idan nazama mallakinka zakayi mani fiye da abunda bana tsammani don haka ka kwantar da hankalinka, bakada damuwa akan haka." Yaji matuqar dad'in kalamanta kuma yasake samun natsuwa akan halayyarta donmin ayanda halayyar 'yan matan yanzu take basa da fahimta wajen maganar aure balle uzuri amma ita gashi cikin sauqi ta fahimcesa kuma ta amshi uzurinsa, bai wani jimaba yakoma had'e da yimata bankwana don gobe tun da wuri zai wuce saboda akwai abubuwan da yake tunanin yi idan yakoma, har bakin qofa tarakosa tare da yimasa ALLAH ya kiyaye sannan tajuya takoma cikin gida, yana barin wajen yanufi wani shagon sayarda kayan sawa da sauran abubuwa dake cikin gari don dama tun jiya ya amshi kud'in adashin da suka had'a shida sauran malamai sunayi dubu d'ari da hamsin, akwatunansa yasaye guda biyu da d'an qarami na sama naira dubu goma sha biyar sannan yasayi atamfuna guda goma masu sauqin kud'i da kuma lace guda biyu na dubu goma sha uku uku, sai shadda d'aya da material yard shima mai sauqin kud'i k'waya uku da doguwar riga k'waya biyu itama da qananan kaya suma kala uku, ya kashe kusan dubu hamsin da wni abu a fannin kaya kawai sannan yasake cire wasu dubu talatin yace ahad'a masa kayan shafa da hijabai da mayafi, kud'in sunyi kad'an sosai amma yace ahad'a mashi su yanda suka samu, takalmi da jaka kala biyu ya siya sai sauran tarkacen underwears kud'in suka qare ya rage dubu d'aya ce ta rage masa a aljihu, hakanan yakwashi kayan yakoma d'akinsa yana mamakin yanda kud'in suka shige kaf cikin 'yar wannan qaramar sayayyar gashi kuma bai qarasa had'a sauran kayan ba, dama zancen inda yake tunanin gyarawa da ya ajiyeta tuni baffa ya sanar dashi yakwantar da hankalinsa duka abunda yakamata ayi za'ayi kawai yaji da had'in lefe da kuma abunda zaiba yarinyar nabuki, hakan yasa yasamu natsuwa sosai har yasamu damar yin wannan sayayyar, safiya na wayewa ya kama hanyar zuwa gida tare da akwatunansa yana tunanin abunda zai iskowa wajen mahaifiyarsa idan taga kayan...
*_ALLAH KAJIK'AN IYAYENMUππ_*
[8/17, 10:19] Billy S Fari: πΆββοΈπΆπ»ββοΈ *SANNU SANNU*πΆπ»ββοΈπΆββοΈ
π _Bata hana zuwa..._π
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARIπ*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*π
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*π
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*π
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*β€οΈ
Page___17π
Kul Aliyu kada kasake inga hannunka yakai ga kayannan, Babu inda za'aje dasu anan za'a barsu har zuwa jibi, inyaso kyasanar da 'yan uwanki ko mutum d'ayane sai yazo aje akai kayan tare dasu bilkeesu, har tafidda qafarta d'aya awaje tana shirin aza d'ayar tajuyo da qarfi jin abunda baffa ke fad'a.
"Malan menaji kana fad'i?"
"Abunda duk kunnuwanki suka jiyo maki kuma maza kifice mun da gani."
Fita tayi ranta ab'ace ta tsaya abakin qofa tana zazzaga maseefa ita kad'ai yayin da baffa yace su baffa Usman suriqasa yana so yashiga ban d'aki suka barta can tanata kumfar baki, wunin ranar kusan aqofar d'akin ta wuni tana zazzaga masifa inda taka shiga ba nan taka fita ba tana nemn wanda zai tankata, sai akayi sa'a hatta baffa Alin dake biye mata baice da ita uffan ba ya shirya yawuce masallaci wajen sallarsa ta juma'ah, bayan sun dawo Nuraddeen ya nufi sashen da ake gyara masa cike da farinciki duk da kuwa zuciyarsa dasqare take da damuwowi kala kala,
Ba kad'an tsarin part d'in nasa ya burgesa ba, baran ganin kitchen d'insa da toilet ba'a waje suke ba, hakan ya matuqar yimasa dad'i arai, tuni an kammala komai fentine kurum ya rage, sai wearing na wutar nefa da ba'ayi ba, suma akwai komai aqasa nan da kwanaki za'a ida kammlawa, ya jinjinawa qoqarin mahaifin nasa sosai tare da yimasa godiya da addu'ar ALLAH yaqara masa lafiya da tsawon rai.
Yaya hawwa kuwa duk iya dubarunta da kinibibin da zatayi wajen gani kayan sun dawo hannunta tayi amma takasa samun nasara saboda yanda baffa yakasa ya tsare daga qarshema cewa yayi kar wanda takoma kawo masa da sunan yazo ganin lefe saboda gobe za'a kai lefen, annan ma taso tayi maseefa amma tayi shiru don taga take taken yanzu baffa daidai yake da ita, kad'an yake jira yayi mata rashin mutunci shiyasa ta aminci da abunda yace, gashi tagama zagaye anguwa da makwabta azo aga lefen d'anta takoma saidai duk wacce tazo ganin lefen sai tace mata anrufe, haka sukata fita kowa da kalar tsogumin da yakeyi akan ta aika masu suzo ganin lefe kuma tace anrufe qilan bawani abun azo agani d'an nata yayi ba shiyasa takasa gwada masu gudun kar tayi abun kunya, duk wud'annn suruttai da akeyi suna dawoma kunnuwanta wanda hakan yamatuqar b'ata mata rai, qwafa tayi had'e da cije baki tana girgiza qafa daga zaunen da take kafin tace,
"Wlh malan kayi da gwana, sai kace wannan abun daka yimun da bakayi shiba, yanzu banida lokacinka, Amma kabari idan nagama da wannan figaggiyar yarinyar da za'a kawo nadawo kanka, alokacin zaka gane cewa ka tabka babban kuskure." Ita kad'ai take suruttanta ad'aki wanda abun har ya riga daya zame mata jiki ka, sallamar Nuraddeen tajiyo abakin k'ofa tana hango yana cire takalmansa kafin yashigo, ciki ciki ta amsa masa sallamar don yanzu gaba d'aya tamaida laifin akansa tad'ora, waje yanema ya zauna ita kuma tajuyar da kai gefe, sunkuyar da kansa yayi qasa cikin damuwa kafin yad'ago had'e da cewa.
"Innarmu barka da marece"
"Yawwa" tafad'a adaqile batare data juyo takallesa ba,
"Innamu don Allah kidena wannan fushin inba so kikeyi infad'a cikin fushin ALLAH ba, don ALLAH kiyi haquri kifad'amun duk abunda kike so zanyi maki amma don ALLAH kidena wannan fushin dani" jin abunda yace yasa tad'anyi ajiyar zuciya had'e da juyowa tace,
"Duk abunda nikeso zaka yimun?" Cikin rawar muraya yace "e..e.eh zanyi maki indai bai sab'awa ALLAH ba." Fad'a murmushinta tayi sannan tace
"Ka kwantar da hankalinka bazansa kasab'awa ALLAH ba, so nakeyi ka nunamun cewa ni mahaifiyar kace, ka d'auko lefencan yadawo d'akinnan saboda nagaji da abun gori da kunya da makwabta keyimun, yanzu fisabillahi inba mahaifinka da iyayi ba, Ina ruwansa da harkar mata, Ina lefe sha'aninmu me na mata don me zaiyi wani kane kane aciki, Nima ina so ingwadawa duniya jarumtar da d'ana yayi amma gaba d'aya yazo ya hana"
"Amma innarmu naga da nan da can wajensa duka d'ayane kuma ai kayan gobe ma za'a kaisu tunda har na sanar da ita tafad'awa iyayenta."
"To.to shikenan tashi katafi, don kasanar da ita sai me, Ina ni nahaifeka Kuma nafad'a maka kayannan wasu 'yan uwana duka basu gani ba sai faman yab'a mani magana sukeyi akan haka, ai shikenan ka kyauta tinda so kakeyi nazama abun nune a anguwa" taqarasa maganar tare da fashewa da kuka, Babu banban burinta kamar ace kayan sun dawo d'akinta, don tad'au alwashin zabce rabi tabar mata rabi, don bazata yarda ba ace kura da shan bugu...ita da d'anta ace wata tafita moriya dashi tun ba'aje ko ina ba, sau biyar kad'ai yatab'a siya mata atamfa amma gashi kusan kala ashirin da wani abu yahad'awa wacce zai aura, shiru yayi cike da mamakin meye abun kuka anan da har mahaifiyar tasa zata fashe masa dashi, cikin sanyin murya yace
"Kiyi hak'uri innamu bari nakira yarinyar nafad'a mata cewa amfasa kawo lefen gobe, shikenan haka yayi maki." Da sauri tace "eh yayi, kirata yanzu agabana kafad'a mata" ba musu ya ciro wayarsa yakira Rashida, bugu d'aya ta d'aga had'e da cewa "hello malamina." Cikin jin dad'in sauraren muryarta yace
"Habibty ya kike? Kina lafiya?."
"Lafiya klw, ya naji muryarka bayanda nasanta ba, ko kana kewatane. Taqare zancen cike da zolaya tana dariya, murmushin yayi shima had'e da kallon mahaifiyar tasa data kafesa da idanuwa tana harara suna had'a idanuwa ta d'aure fuska tare da kauda kanta gefe, murmushin ya sakeyi sannan yace.
"Sosai habibty I really missed you." Murmushi tayi don tafajimci meyake nufi saboda duk k'ananan kalmomin nan na soyayya yafara koya matasu kuma tana saurin fahimta da kuma haddacewa, matsalarta d'aya bata iya rubutawa balle takaranta sai dai inda ajami za'a rubuta mata, sanin har izuwa lokacin tana kan layi yasa yaci gaba da cewa, "habibty zancen kawo lefe da za'azo gobe odan baki fad'awa su umma ba to kifad'a masu sai ranar attanin za'a kawo saboda wani dalili kinji ko."
"To shikenan, dama ban fad'aba sai yau nake tunanin fad'a masu don haka babu matsala."
"Yawwa nagode sai anjima idan nakira" da haka yakashe wayar yana kallon umma da farinciki kwance a fuskarta fal tace.
"To ko kaifa, yanzu kaga sai ad'auko lefen akawo zuwa gobe 'yan uwana sun gani an uma tsaida wud'anda zasuje jebi sai akai ko kuwa"
"Hakane innamu ALLAH yatabbatar da alkhairi." Qirikiri tayi mui da baki batare data amsa masa da abin ba don itakam Bata fatan yazauna da yarinyar ballantana tayi fatan wani alkhairi a tsakaninsu.
Mik'ewa yayi zai fita tabiyo bayansa had'e da cewa
"Nace babu d'an wani abu a hannunka nan, kasan kullum mahaifin naka nanan zaune waje guda sai abunda 'yan dubiya suka bashi, d'an tanadin da yayi kuma ya lalatashi wajen wannan ginin wahala, baice komai ba yasa hannu a aljihu yaciro d'ari uku a aljihunsa ya miqa mata had'e da cewa, "kiyi hak'uri da wannan innarmu sukad'ai suka ragemun" karb'a tayi ta saka a hab'ar zane ta d'aure tana biye dashi har waje tace "ba laifi, ALLAH yayi albarka"
"Amin innamu," inna balkisu ce taqaraso wajen riqe da leda irin poly bag d'in nan tana murmushi "A'a malan Nuraddeeni fita za'ayi" tafad'a batare data kalli gefen da yaya hawwar takeba, cikin sakin fuska da girmamawa yace
"Eh inna bilkisu fita zanyi in ALLAH ya yarda, ina wuni?"
"Lafiya klw yaron kirki dama saqone 'yan uwanka saleema da kareema suka aiko dashi sukace akawo maka ka k'ara a lefe." Washe baki yayi yana kallon mahaifiyarsa tasa da tunda taga inna bilkisu taqaraso wajen ta d'auke kai ko zata juya, karb'ar ledar yayi tare da komawa cikin rumfar d'akin mahaifiyar tasa ya jawo tabarma had'e da zazzage kayan, cike da mamaki yace
"Kai kai kai inna bilkisu kice hidima na d'orawa 'yan uwana, wannan irin abun arziqi har ina, gaskiya nagode sosai wlh ALLAH yabar zumunci km yasaka masu da alkhairi."
"Amin ya rabbhi ai ba komai yiwa kaine, kadaici da haquri abunba yawa kasan d'iya mata ne basu san amshi ba saidai karb'a" murmushi yayi yana kallon mahaifiyar tasa da tabbas yasan maganace inna bilkisu tasakar mata amma hankalinta nawajen kallon kayan dasu kareema suka aiko dasu atamfa biyu sai sarqoqi kala biyar da jikkar ribon dozin biyu da kuma hulunan sawa masu kyau qwaya biyar, murmushi inna bilki tayi ganin yanda Yaya hawwa tasaki baki sannan