Showing 78001 words to 81000 words out of 260204 words
Chapter 27 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
juyowa baffa yayi yana kallon likita dake gefensa yace. "Likita don ALLAH kuyi masa allurar bacci koya samu koda 'yar qaramar natsuwa ce azuciyarsa."
"Abunda nake tunanin yi kenan nima." Likitan yafad'a tare da ciro biro a aljihunsa ya rubuta masu allurar bacci yace aje asiyo, baffa Usman ne yakarb'a da sauri ya nufi gefen da pharmacy take acikin asibitin ya siyo yakawo masa, daidai bakin qofar da zai shiga d'akinne yaci karo da baffa Ali suka shiga tare, miqawa likitan dake can gefen wani marar lafiya yana sa masa drip allurar yayi yace yadwo nan inda Nuraddeen d'in yake ya jirasa, shi Kuma baffa Ali tsaye yayi saman kan Nuraddeen yana kallon yanda ya zabge lokaci d'aya, ajiyar zuciya yayi sannan ya maida kallonsa ga baffa dake tsaye yace.
"Yaya Ashe jikin nura haka yazama, ni yanzu yaran gari sukaje suna fad'amun cewa ai kunanan asibiti da nura ya zauce saboda b'atan matarsa"
"To kadai gani Ali, jarabawar da ALLAH yad'oro muna kenan! Ubangiji ALLAH yabamu ikon canyeta."
"Amin Yaya, Amma to ba wannan ba yakamata yaronnan yasawa ransa salama, idan ALLAH yatsaro za'aga yarinyarnan to za'a ganta, in Kuma ALLAH be nufa ba to yayi haquri basai yaje ya illata kns ba zai samu wata matar tunda ba ita kad'aice mace ba, mata ne gasunan ko ina sai yazab'a ya darje, nan kusa ba nesa ba ga 'yar uwarsa nan muneera sai tamaye masa gurbinta ai inaga shikenan ko?"
Cike da b'acin rai baffa ya nufosa had'e da shaqe wuyansa ya had'a da jikin bango. "Aliyu dama kai bakada hankali ban sani ba? Mekake nufi da idan ba'a ganeta ba? Wlh damuwata tafi yawa akan b'atar yarinyar nan fiye da halinda Nuraddeen ke ciki domin nasan cewa ganinta ne kad'ai zai kawo masa sassaucin wannan halin da yake ciki saboda itace farincikinsa, shine kake fatar kada aganeta saboda ita d'in ba 'yarka bace?, Yaqarasa maganar cikin d'aga murya tare da qara shaqesa tayanda ko lumfashi mai kyau baya iyayi, kakarin d'aya farayi ne yasa baffa da likita sukayo kansa suna rirriqesa amma suka kasa cire hannunsa daga wuyansa, cikin b'acin ran daya sauya masa kalar idanuwansa dake fari izuwa jajaye yace.
"Kaje ka muri sauran mintotan da suka rage maka kafin jami'an tsaro su iso gareka, Ina tabbatar maka da cewa dukkaninku sai nasa ansa kunfad'i inda kuka kai yarinyar mutane, idan ba haka ba zanyanke duk wata alaqa da Kuma 'yan uwantakar dake tsakanina dakai nasa akulleku har sai natabbatar da kunfad'i inda take tukuna."
Yana gama fad'ar haka ya sakesa tare da wullasa gefe sannan yabar d'akin da asibitin gaba d'aya, baffa Usman ne ya tsaya har saida akayiwa Nuraddeen allurar bacci wanda duk abunda ke faruwa idanuwansa kad'aine arufe amma yana saurarensu.
Take bacci ya d'aukesa bayan an laqa masa gorar ruwa guda. Juyowa yayi yana kallon baffa Ali da har lokacin ke zaune qasa yana lalubar wuyansa saboda azabar zafin riqon da baffa yayi masa a kuma lokaci guda yana fidda lumfashi d'aya bayan d'aya yace.
"Ga d'anka nan ka kula dashi idan kaga dama, idan kuma baka gani ba zaka iya tafiya." Yana kaiwa nan shima yabi bayan baffa, har yakusa fita ya juyo had'e da cewa. "Yawwa Ali namanta in fad'a maka cewa zaka iya qarasa rayuwarsa idan kana buqata tunda bakwason ganinsa cikin farinciki balle raye." Sannan yawuce.
••• ••• •••
A gefen wani babban titi shed'anin da bargaji yaturo ya sace Rashida ya jefar da ita bayan yagama azabtar da ita lokacin qarfe hud'u da rabi na dare ko motsi batayi, abunda ke cikinta sai faman motsi yakeyi saboda azabar daya sha ga lumfashin uwa dake taimaka masa na neman yarabu da gangar jikinta, cikin iyawar ALLAH da nuna isarsa ga bayinsa da sukayi imani dashi kuma yake taimaka masu alokacin da suke neman taimako yasa sanyin asuba nafara sauka lumfashin Rashida ya daidaita ga gangar jikinta, wani dogon lumfashi taja had'e da qoqarin bud'e idanuwanta a hankali a hankali, ganinta agefen titi gashi duhu ya mamaye gari ko hasken mota bata gani saboda dogayen ciyawun da sukayi shamaki tsakaninta da titi balle ahangota yasa tafara qoqarin tashi, bataji wani dogon rauni ba a zahirance sai 'yar gugguljewar da ko ina ajikinta yayi da kuma azabar da takeji can cikin qashin bayanta da kuma mararta wanda in bata manta ba acikin wannan halin take kafin ta tsinci kanta acikin wannan yanayin da take kallo tamkar mafarki, jin an shureta cikin ciki ya tuna mata da d'an dake cikinta da sauri tasa hannu tana tattab'a cikin, duk inda taji alamun abunda ke ciki yayi motsi sai takai hannunta akai shi kuma sai ya janye yakoma wani gefen, haka ta dingayi tana murmushi kafin tafara qoqarin fitowa daga cikin ciyawun tana takawa da qyar saboda nauyin cikin. Hango wani haske da tayi acan tsallaken titi yasa tayi yunqurin tsallakawa don samawa kanta tsaro daga abun dakan iya cutar da ita awajen.
K'iiiiiiiii...kakeji da qarfi motar dake tafe gabanta da gudu matuqin yaja burki ganin mutum ya gitta masa, nan take tsananin tsoro daya gama zama abokin rayuwarta yasa tasaki wata irin qara tare da duqewa wajen, k'iris kad'an ya rage Mai motar yabugeta Amma ALLAH ya taimakesa kafin motar takai ga jikinta yayi nasarar tsaida ita, qara hasken fitillun motarsa yayi don gasgata idanuwansa dake gane masa mace da tsohon ciki agabansa, da sauri ya bud'e motar yafito jin wata irin qara da Rashida tayi tana fad'in,
"Wayyo ummata zan mutu." Saboda azabar naqudar da tataso mata lokaci guda,
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun., Baiwar ALLAH daga Ina? kike da asubancin nan haka?"
Kasa magana tayi sai yarfi da hannu takeyi tana cizon baki, kallo d'aya yayi mata ya fahimci haihuwace zatayi saboda ganin ruwan dake bin qafafuwanta Wanda bako shakka fawace tafashe.
Gabas da yamma, kudu da arewa yaduba Babu wani mahaluqi dake tahowa daga saman titin, shimad'in yayi sakkon fitowane saboda wani emergency operation da aka kirasa cewa zaiyi da safennan, shine dalilin fitowarsa cikin sauri zaije airport don ya hau jirgi sai gashi ya had'u da wannan tsotsayin, sake kallon Rashida yayi yaga she's too young da alama ma haihuwar farince duk rashin imaninsa bazai iya barinta awajen ba, gashi tana stage d'in da take matuqar buqatar taimako, bai tsaya saurarar zuciyarsa ba kawai ya runtse idanuwa yana karanto addu'a daga bakinsa ya tallabeta ya sakata cikin motar ya tayar ya nufi hanyar asibiti mafi kusa dasu acikin garin, kallon yanda take nishi da qarfi alamun haihuwar na kusa yakeyi had'e da qara gudun motarsa,
A wata qatotuwar asibiti yayi parking had'e da fitowa da sauri ya bud'e bayan motar ya sake d'aukota yanufi cikin asibitin da ita yana kiran "nurse, nurse.." da gudu suka fito suka karb'eta suka nufi cikin wani d'aki da ita, wata nurse ce tashiga da sauri cikin wani office tayowa dr dake on duty magana suka fito tare da ita, har zasu shiga d'akin da aka shiga da Rashida yayi saurin tsaishesu yana fad'in
"Dr. don ALLAH ka taimakawa yarinyarnan, haihuwa ce zatayi kuma inaga wannan itace tafari, ga dukkan alama yamatuqar Shan wahala don tadad'e tana labour, yanayinta ya nuna tayi riching final stage da zata iya haihuwa wato 10cm don ALLAH kayi iya qoqarinka wajen taimakonta ta haihu lafiya." Yaqare maganar yana had'a hannayensa waje d'aya, riqa hannunsa Dr yayi yana mai bashi k'warin guiwar cewa zai iya sannan ya wuce batare daya tanka ba.
Safa da marwa mutumen ya dingayi abakin d'akin yana mai addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya kafin yaciro wayarsa yakira matarsa. Bugu d'aya ta d'aga had'e da cewa.
"Swthrt har ka isa airport d'in." Cike da damuwa yace
"A'a fatima banma je wajen ba, yanzu haka Ina asibiti.." miqewa tayi daga kwancen da take ta tashi zaune had'e da cewa "swhrt lafiya kuwa? meya same kane? Dama tunda zaka tafi Saida nafad'a maka hankalina bai kwanta da tafiyarnan ba qara kabari sai safiya tawaye ido naganin ido amma ka nace kai sai alokacin zaka tafi." Taqare maganar had'e da fashewa da kuka.
"Haba Fatima meye haka kikeyi? Kinaji na ki saurareni kiji me zanfad'a, Babu abunda ya sameni kawai ansamu matsalace akan hanyata ta zuwa filin jirgin..."
Nan yaciga da yimata bayani dalla dalla sannan takwantar da hankalinta, cike da damuwa yaci gaba da cewa.
"Idan zaki iya munanan _mom maternity clinic_ kiyi sauri kizo kinji ko."
"On my way Dr. In Sha ALLAH." Tafad'a tana goge hawayenta had'e da kashe wayar.
Daidai lokacin shima yasaki wata irin ajiyar zuciya tare da runtse idanuwa saiga likitan yafito da sauri ya nufo inda yake tsaye.
"Dr. Lafiya?." Mutumen yafad'a yana kallonsa cikin tashin hankali, shiru Dr. ya d'anyi kafin ya kallesa had'e da cewa.
"Am sorry ansamu matsala. Dole zaka samana hannu anan." Yajuya wajen nurse d'in dake biye dashi ya karb'i takarda a hannunta yana miqa masa. "Zaka saka hannu saboda dole sai anyi mata tiyata bazata iya haihuwa da kanta ba."
"Kamarya Dr.? Inada tabbaci akan takai adadin yanda ake buqatar ta haihu mezaisa kace Kuma bazata iya haihuwa ba yanzu."
"Saboda yaron baizo daidai ba, ma'ana amai makon yazo takai sai yazo ta qafafuwa aturance muna Kiran irin wannan haihuwa da "breech presentation" wato haihuwar da tazo a baibai ba normal haihuwa ba." Shafa kai mutumen yayi had'e da cewa.
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun." Kafin yafiddo wasu i.d card guda uku had'e da license d'insa nazama likita a aljihunsa ya miqa masa da sauri, karb'a Dr. Yayi ya shiga dubawa, d'aya national i.d card d'insa ce, d'aya kuma i.d card d'in dake nuna yana aiki a qarqashin asibitin aminu kano ce dake garin birnin kano, d'ayar kuma shedar cewa shi qwararren likitane a fannin matsalar mata wato (gynicolgy) inda yaga an rubuta Dr. Nura ahmad. 'Dauke da lambobin dake nuna cewa shi cikakken likitane babba a fannin wato (consultant).
'Dago kai Dr yayi yana kallonsa ya jinjina masa kai alamar bashi tabbaci akan abunda yagani, cike da girmamawa Dr. Yasake bashi hannu suka gaisa saboda ganin shi babban sane.
"Don Allah Dr zan iya shiga na taimaka mata?. Nasan insha ALLAH zata iya haihuwa da kanta basai anyi mata tiyata ba." Shiru Dr yayi kafin ya bashi hanya yana nuna masa qofar shiga d'akin, da sauri ya shiga ya tarar da Rashida kwance ta matuqar jigata, nan take yasa handglove batare daya cire kayan dake jikinsa ba ya nufi inda take kwance, Saida yafara zuwa saiti fuskarta yace.
"Kiyi fad'a da kowace irin qadadara ce data fiddoki cikin dare awannan yanayin, ki qoqarta wajen ceto abunda kecikinki inada tabbaci akan komeye zai zamo sanyin idaniyarki, kada kibari qaddararki ta rinjayi nasararki wajen rasa abunda ke cikinki ta hanyar gazawarki, kiyi addu'a kuma ki jajirce kibamu had'in kai in sha ALLAH zamuyi nasarar wannan aikin da zamuyi." Binsa kawai Rashida tayi da kallo batare data iya tanka masa ba hawaye na tsiyaya tagefen idanuwanta, tabbas ba k'aramin tasiri kalamansa suka yimata ba hakan yasa taquduri bayar da rayuwarta ga abunda ke cikinta.
Nan take yafara ba nurses d'in umurnin miqo masa kayan aiki, cikin k'warewa da hikima irin wadda aikinsa ya koyar dashi yafar qoqarin jujjuya yaron da zimmar mayar dashi ya koma daidai, fiye da mintuna ashirin ya kwashe yana abu guda amma hakan ya cutara, kallon irin wahalar da tasha yayi amma duk da haka bata sare ba da sauri yasa hannu ya goge hawayen da suka zo masa tare daba nurses d'in umurni dasu canzo masa kayan aikin da zai karb'i haihuwar ayanda yaron yazo koda kuwa za'a rasa ranshi saboda aceto rayuwarta,
Nan take aka had'a komai yashiga fara aikin cike da addu'ar ALLAH yasa ayi nasara, kusan wasu mintuna ashirin ya kwashe sannan yayi nasarar fiddo da yaron lafiya, yana fiddosa na'ura nagwajin d'aukewar lumfashin Rashida, haka shima yaron tsabar wahalar daya sha koda aka cirosa ko motsi baya yi, da sauri yajawo oxygen d'in dake can gefen gadonta ya harhad'a ya jona mata da taimakon nurses d'in dake wajen....
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶♀️🚶🏻♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻♂️🚶♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎
_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*
_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋
_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞
*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖
*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️
Page___38💎
Juyowa yayi yana kallon Dr dake wajen tare dashi wanda yakamata ace shine ya karb'i haihuwar ya miqa masa hannu suka gaisa sannan yace.
"Nagode sosai, in Sha ALLAH zata samu lafiya, ayanayin wahalar da tasha dole nasan hakan zata kasance, nayi abunda na Nemo alfarmaryi sauran kuma nagareku." Yaqarasa maganar yana cire handglove d'in dake hannunsa, murmushi Dr yayi yana yabawa qwarewar Dr. nura tare da jinjina masa akan namijin qoqarin da yayi, wanda badon haka ba babu ko shakka saidai suyi mata tiyata gudun abunda zai iya faruwa da ita ko d'anta, solutin nasa yayi shima had'e da cewa. "Weldone sir, sunana Dr sani Bilal Ina zaunene d'aya daga cikin gidajen dake cikin asibitinnan, naji dad'in had'uwa dakai sosai."
"Masha ALLAH sunana.." saurin katsesa yayi tahanyar fad'o masa cikakken sunansa daya gani arubuce jikin i.d card d'insa ta asibiti wato
"Dr. nura shu'aib k'wararren likita afannin matsalolin mata dake aiki da asibitin aminu kano dake garin kano."
Murmushi yayi sannan yanufi gefen da nurses d'in ke gyara babyen har lokacin be koka ba, karb'arshi yayi ya d'aga qafafuwansa sama kansa na qasa yad'an twad'i d'uwawunsa sai gashi ya canyara ihu, murmushi farinciki yayi sannan ya miqa masu shi yana kallonsa, yaron kyakkyawane sosai gashi da girma tubarkallah, kallo d'aya zakayiwa jaririn kafahimci ba qaramin kulawa yasamu ba alokacin da yake cikin ciki, yana wannan tinaninne yaji wata nurse a firgice tace.
"Dr...." Saboda ganin yanda yaron yafara amai yana fizge fizge, da sauri ya qaraso wajen ya karb'esa nan take yagano yaron yasha ruwan naquda, qoqarin zuqe masa su ya shigayi da taimakon Dr sani da gaba d'aya hankalinsu ya tashi, miqa masu shi yayi yace suyi maza maza su kaishi sashen ba jarirai taimakon gaggawa, haka kuwa akayi kafin kace me har sun isa wajen nurses d'in b'angaren suka karb'esa suka fara bashi kulawa kafin likitan dake b'angaren yaqaraso, yana zuwa yashiga duddubasa cikin k'warewa da iya aikinsa.
Bayan komai ya daidaita shima yaron aka saka masa oxygen saboda yanda lumfashinsa ke kokuwar barin jikinsa.
Dr. nura kuwa nurses nafita da jaririn ya nufi inda Rashida ke kwance ya qura mata idanuwa, gaba d'aya kamannunta dana yaron sunsha banban, wataqil shi mahaifinsa yabiyo,
Yafad'a aransa, ficewa yayi daga d'akin yana tura hannuwansa cikin aljihu, sai alokacin ya tuno da wayarsa daya ajiye a can gefen gadon da Rashida take kwance da sauri yakoma ya d'auko, kusan 10missed call yagani Kuma duka na matarsa ne fatima wacce take da tabbacin tashigo asibitinne shine takirasa taji inda take, murmushi had'e da danna lambar ya sake kiranta, bugu d'aya ta d'aga tana fad'in.
"Swthrt kana inane? Tun d'azu kabarni a tsaye." Tafad'a cike da qorafi akan haka.
"Fatima kenan! Yihaquri ki qaraso tanan gyani emergency Ina tawurin tsaye Ina jiranki."
"To." Tafad'a had'e da kashe wayar sannan tanufi hanyar da zata sadata da wurin, daidai lokacin shima yanufo qofar fitowa daga wajen sukayi kicib'is da ita d'auke da kwandon kuloli har dasu qatuwar leda da flaks, zaro idanuwa yayi yana kallonta cike da mamaki yace. "Fatima duk meye haka?" dubon agogon hannunta tayi taga kusan qarfe goma da rabi na safe ta dafe kai had'e da cewa.
"Kayi haquri nadad'e ban qaraso ba ko?, natsaya had'a mata wud'annanne, Ina jarin da aka haifa? tahaihu ko?"
Tafad'a tana gyara zaman mayafinta cike da tausayi yabita da kallo, daga jin cewa ya tsinci maiciki a hanya suna asibiti zata haihu shine Fatima zata had'o wud'an abubuwa haka saboda tsananin son haihuwa da take da ita, ya ALLAH kadubemu da idon rahama muma kabamu namu masu albarka, yaqarasa fad'a aransa yana goge 'yan kwallan tausayinta da suka zubo mata.
••• ••• •••
Dr nura da Fatima mijine da mata dakeda matuqar kyakkyawar fahimta a tsakaninsu, kalla d'aya zakayi masu kafahimci aurensu auren soyayyane saboda yanda suke matuqar son juna, sunyi aure tun shekaru goma sha uku da suka wuce amma har zuwa tsawon wannan lokaci basu samu haihu ba, Fatima macece mai matuqar son yara amma jarabawa ta ALLAH ko b'atan wata bata tab'a yiba, anyi masu duk wasu gwaje gwajen da bincike bincike don agano dalilin rashin haihuwar tasu amma likitoci sun tabbatar masu dashi har ita duka lafiyarsu qalau basuda wata matsala data hanasu haihuwar kawai lokacine beyi ba, hakan yasa gaba d'aya suka tattara komai akan batun haihuwa suka watsar gefe suka rungumi junansu hannu biyu cikin so da qauna da kuma kulawar juna, fatarsu akoda yaushe da addu'arsu shine ALLAH ya basu masu 'ya'ya masu albarka aduk lokacin daya so kuma yanufa, Dr nura cikakken d'an asalin jahar borno ne amma wasu lokutan suna zama a kano saboda aiki daya kaishi can, dalilin fitowarsa yau tunda asuba shine kiran gaggawar da akayimasa tun jiya da daddare ne cewa ana buqatar ganinsa gobe qarfe takwas na safe akwai matar da zasu yiwa tiyata, shiya yayi asubancin tashi zuwa filin jirgin da zai tashi qarfe biyar na asuba don ya isa dawuri, ashe rabon ya taimaki Rashida a wannan lokacin ya fiddosa.
••• ••• •••
Wata irin ajiyar zuciya Dr. nura ya sauke had'e da riqo hannunta yace, "Kai fatima daga fad'a maki zancen matar nan zata haihuwa shine zaki tsaya kwaso kaya haka!."
Dariya kawai tayi masa batare da tace komai ba saboda Babu abunda takeso alokacin irin taga matar da yace ya tsinta da babyn data haifa, d'akin da Rashida ke kwance yanufa riqe da hannunta har suka shiga.
A bakin gadon Rashida yaja burki ya tsaya yana nunata da hannu. "Fatima kinga baiwar ALLAH da nake fad'a maki nagani tafito daga cikin wani daji tashigo gaban motata, badon ALLAH yatsare ba dana bugeta gata da tsohon ciki." Cike da tausayi tariqe hannunsa gam kamar zatayi kuka yace.
"Swthrt meya fiddota waje a