Showing 225001 words to 228000 words out of 260204 words
Chapter 76 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
maida abun tamkar waqa, abunda bata sani ba ashe maganar zucin da takeyi har tafito fili sun ji abunda take cewa, shine suka maida abun gaba d'aya tamkar wasa sai faman zagayarta sukeyi suna tafi suna maimaita maganar alokaci d'aya kuma suna dariya.
Dariyar itama suka bata tasa hannu tajawo d'aya daga cikinsu wacce tafi rashin ji don itama bata fiye ganesu ba saboda tsantsar kamar da sukeyi da juna tana cewa. "Ja'ira zonan, wato so kukeyi ku koma yaran wofi ko? kun maidani sai kace wata abokiyar wasarku yau duk sai nayi maganinku?" ta d'aga hannu da niyar kai mata tulla a bayanta d'ayar tayi saurin riqe hannun tana fad'in.
"A'a kaka, ALLAH kada ki doketa, kinsan fa ba kyau mugunta ke kike fad'a mana idan muka doki ikram" yarinyar su iman da shakur ce wacce kad'an suka girme mata, d'an harararta Rashida tayi kafin tace.
"Jimun yarinya, cikamun hannu ko nahad'a dake, ai wannan ba mugunta bace, horone zanyi maku, kuda kuke tararwa ikram ku biyu kuyita cin zalinta ai shine mugunta ba nawa ba."
"To ALLAH bazaki duketa ba su abbanmu basa dukanmu, hussaina yi sauri ki gudu nariqe mata hannu." Tafad'a tana qara qaqume hannun Rashida hannu bibbuyu har tana nishi, da sauri hussainar ta tashi daga jikin Rashida ta ruga bakin qofa tana fad'in, "cikata hassana kizo mugudu wajan kaka mama."
Sakin Rashida hassana tayi da sauri ta ruga wajen 'yar uwar tata tana dariya suka fice daga d'akin suna yimata gwalo, murmushi Rashida tayi tanajin wata irin qaunar yaran har cikin tsakiyar ranta, idan tace zata iya banbance qaunar da takeyi masu da wadda take yiwa mahaifinsu to tabbas tayi qarya don bazata iya ba..
••• ••• •••
Gaba d'aya duk yabi ya tone d'akin da kuma kayansa yana bincike binciken abunda idanuwansa ke matuqar mararin gani amma bai ganshi ba, abokin nasa yayi magana har ya gaji amma kota kansa baibi ba balle yasa ran tanka masa, wani irin kuka yafashe dashi had'e da duqewa wajen yanaji kamar ransa zai fita, Saida yayi abunsa mai isarsa sannan yamiqe jiki ba qwari ya kalli abokin nasa yace.
"I most go back to my country, my nation, my everything..."
"What!" Abokin nasa yafad'a tare da miqewa tsaye yana binsa da wani irin kallo na tuhuma, cikin yaren na turanci Nuraddeen yaci gaba da yimasa bayanin cewa tabbas yau zai koma qasarsa ta haihu, wacce ta renesa ta bashi gudun mawa arayuwa wato Nigeria, yaci gaba da fad'a masa cewa shi bai san me yafaru kanshi ba da har ya zauna wannan qasar har na tsawon wud'annan shekaru bayan yabaro mahaifansa da iyalinsa da alokacin baima san inda take ba, koma dai meye yau ba gudu baja da baya sai yabar wannan qasar yakoma qasarsa, yana so yasan awane hali iyayensa da iyalinsa ke ciki, suna raye ko sun mutu duka bai sani ba, meya faru dashi ne haka?, Yaqare maganar cikin kuka da tausayin kansa akan mezai je ya riska.
Bai tsaya jiran wata shawara ba nan take ya shiga har had'a kayansa da duk abunda yake so tare da rubuta takardar ajiye aiki aqasar bisa dalilinsa nason komawa qasarsa sannan yafad'a toilet ya sakarwa kanshi ruwa, ya dad'e ruwan na dukansa kafin yayo wanka yafito yana jin wani irin yanayin da sharabon ya riski kansa aciki har ya manta,
Kamar ance ya duba gefen gadon dake d'akin wajen bed side ya hango jikkarsa acan sakad'e wacce da itace ya zubo wasu kayansa da zaizo qasar, da sauri yaqarasa wajen ya cirota duk ta d'anyi qura duk da bawai sosai bane tunda shi mutumne mai tsananin tsabta akoda yaushe cikin gyaran d'akin da kakkab'esa yake ko kuma yasa ayi masa, Amma kasancewar bai fiye amfani da ita ba yasa ta d'anyi datti yasa wani d'an qaramin towel ya kakkab'e sannan ya bud'eta, abubuwan daya ta bid'a duk ya watse d'akin sune aciki wato hoton habibty d'insa da wayarta daya shiga part d'insu ya d'auko ranar da zai tafi, bin photon yayi da kallo yana murmushi saboda tsananin farincikin kallonta da yakeyi, ko yanzu ya habibtynsa takoma?, Shin anganeta ko kuwa?, Tana nan da ranta kota mutu?, Shin idanma tana raye tana tunawa dashi ko kuwa tayi aurenta da wani ta manta dashi?, Ina abunda ke cikinta?, Shin tahaifesa yana raye shima ko baya raye duka bai sani ba, Wud'annan sune tambayoyin da ya dinga yiwa kans kenan don ya tabbata tsawon wud'an nan shekaru daya kwashe baya nan dole sai d'aya daga cikin hakan sai tafaru, ji yayi zuciyarsa na wani irin bugawa da sauri da sauri wanda ya tabbata rashin fatan faruwar d'aya daga cikin abunda yake tunanine ya jawo hakan, addu'o'i yadinga karantowa abakinsa na neman tsari kafin yaci gaba da qoqarin kunna wayar Rashidar dake hannunsa amma taqi tashi.
Murmushin qarfin hali yayi yana ganin wautarsa na tunanin cewa wayar zata tashi bayan yasan cewa jiya ba yauba, koba komai yasan cewa tuni baturin cikinta ya lalace ya dena aiki, miqewa yayi ya shirya kansa tsaf cikin qananan kaya suit royal blue sai farar riga 'yar ciki da necktie shima kalar royal blue da d'ige d'igen fari acikinsa, kallon kansa yayi a madubi yaga yanda farin gashi yasoma d'an feso masa cikin kai yayi wani irin murmushi dake d'auke da ma'anoni kala kala.
Takardar daya rubuta ta ajiye aiki ya d'auka ya saka cikin aljihu sannan ya nufi wata babbar psychiatric hospital da ake kira (Columbia Asia hospital) babbar asibitin masu tab'in hankali ce aqasar da ake matuqar alfahari da ita wacce aqarqashinta ne yake aiki, kai tsaye office d'in shugaban asibitin ya nufa wacce ta kasance macece 'yar qasar China, cikin girmama ya shiga ya gaisheta da yaren turanci ta bashi izinin qarasowa ciki ya zauna, bayan ya zauna yayi mata bayanin abunda ke tafe dashi tare da miqa mata takardar ta karb'a, Saida tagama karantawa tsaf sannan ta linke tamayar tana kallonsa kafin tace.
"Yana da kyau kafin ace kayanke wannan hukunci kayi tunanin makomarka, anan muna matuqar girmamaka tare da baka daraja kasancewarka zaqaquri kuma haziqin likita da muke dashi, bana tunanin cewa komawarka qasarka zai Haifa maka d'a mai ido saboda basusan darajar kaba, bazasu iya gane irin qwazon da kake dashi ba balle har subiyaka albashi mai tsoka da zai iya riqeka yanda kake buqata, Ina baka shawara da kayi zamanka anan, idan har salary d'in da muke biyanka ne beyi ba zamu lullunka maka shi har sau uku matuqar zakaci gaba da aiki damu." Duk wannna surutun da takeyi da yaren turanci take yimasa shi kuma ya zuba mata ido yana kallo cike da mamakin yanda kowane d'aya daga cikin 'yan qasashen nasu keda son Kai da son cigabar qasarsa sab'anin tashi qasar da a saninsa nada ba haka suke ba sai in ALLAH yasa yanzu sun canza, ajiyar zuciya ya sauke kafin shima cikin qwarewar yaren nasu na turanci da idan kaji zaka d'auka dashi aka renesa har ya girma yayi murmushi had'e da cewa.
"Ina bada haquri mah! tare da yimaku godiya sosai bisa karramawar da nake samu daga wajenku akoda yaushe, kalmomi kawai bazasu iya tabbatar maku da hakan ba amma daga qasan zuciyata zanci gaba da alfahari da aikin da nayi a wannan asibitin taku tare da yabawa agareku aduk inda nashiga had'e da kuma addu'o'in fatan alkhairi har iya qarshen rayuwata, kuyi haquri! Bazan aje aiki bane don bana so ko kuma don qasata, zan aje aikine saboda ni Ina buqatar qasata awannan lokaci kuma Ina son nakoma cikinta a matsayin cikakken d'an qasar dake alfahari da ita, qasata uwace mai matuqar girma da daraja, qasata uwace data reneni kuma tabani ingantaccen ilimi, Bata barni ahaka ba har saida ta turoni don insamu ilimin da zan taimaketa da 'yan uwana dake cikinta tare da bani cikakkiyar kulawar da duk yakamata, ashe kuwa wannan uwar baici na wofantar da itaba, baici namance da nauyin mutanen dake d'auke a kanta ba tana basu kulawa wud'an da sun kasance sashen jikina da kuma rouhina, ni Dr N.I ALIYU na amince zan ajiye wannan aiki koda zaku yimani salary da zalar gwalagwalai ne, kuma nazab'i na koma qasata in tayi mata bauta koda bazasu bani naira ba acikin kud'insu domin sun cancanci haka, infact ina da buqatar iyayena, iyalina, ahalina, abokanaina da kuma 'yan qasata don haka zan koma garesu."
Shugaban makarantar data bud'e baki tana kallonsa had'e da sauraren kalaman da yakeyi bata san lokacin da wasu hawaye suka zubo mata ba tashiga tafa masa, sosai ya burgeta yanda yanuna mata yana kishin qasarsa kuma yana martabata haka, kawai dai taji ba dad'ine saboda rasa zaqaqurin likitan daya san aikinsa da zasuyi shiyasa tazubar da qwallah, miqewa tayi had'e da miqa masa hannu daidai lokacin da shima ya yamiqe daga zaunen da yake ya miqa mata hannu sukayi sallama sannan tayi masa bayanin yanzu zata gabatar da takardarsa zuwa can samanta don haka ya kasance cikin shiri ko yaushe zasu nemesa.
Ko kad'an baiso hakan ba don a ranar yaso barin qasar amma hakan ta cutara saboda basu nemesa ba.
Nan take yashiga sa duk wasu qaddarori daya mallaka kasuwa ya sayar dasu, hatta gidan da yake ciki da motocin hawansa guda biyu duka ya sayar don dama gidan sane yayiwa abokin nasa d'ahiri ya zauna, yanzu kuma da zai bar qasar sai yakoma wani wajen shi kuma ya saida abunshi, Saida aka kwana biyu sannan aka nemeshi wajen aikinsa ashe wata gagarumar walima suka shirya masa don karramasa da kuma appreciating d'insa akan qoqarin da yayi wajen kawowa asibitin tasu cigaba sosai.
Cek d'in maquddan kud'in da idan aka canzasu i zuwa na qasar nageria zasu kai kimanin miliyan ashirin da wasu d'aruruwa akai suka bashi tare da kambun karramawa a matsayin qwararren likitan da yafi iya kula da marassa lafiyansa da kuma kambun likitan da yafi kowa hazaqa da kuma sanin aikinsa, yayi masu godiya sosai bisa karramawar da suka yimasa bazai tab'a mantawa dasu ba sannan aka watse bayan anci ansha anyi hotuna Wanda mafi yawa daga cikin ma aikatan asibitin na sama dana qasansa Saida sukayi qwallar rabuwa dashi kuma sun tabbatar masa da yanada alfarma a asibitin ya turo duk wanda take son a d'auka aiki matuqar ya amince da hazaqarsa da kuma jajircewa, sannan shima suna marava dashi aduk lokacin da yayi sha'awar dawowa qasar yaci gaba da aiki dasu.
Murmushi kawai Nuraddeen yayi aransa yana raya cewa shi da qasar waje kuma indai ba saudiya ba to sai bayan ransa, don ko kwana biyun daya qara saboda matsalar visa ne ita ta tsaida shi da tuni ya tafiyarsa qasarsa saidai suyi walimar ba dashi ba.
Duk mutanen da yake huld'a dasu saida yaje yayo bankwana dasu har wajen shugabar makarantarsu inda yayi karatu da ita tafara riqesa don awajenta ya zauna kafin yakafu da kansa, matar kama itama yanzu ta tsufa sosai yayi mata bankwana bayan yamata bayanin zai koma qasarsa, tayi kuka sosai don ta matuqar sabawa dashi tamkar d'anta na cikinta ya yimata alkhairi sannan ya wuce.
Dama tuni ya gyara komai yana dawowa abokinsa d'an qasar Thailand ya d'aukesa zuwa airport, wani irin farinciki yakeji azuciyarsa marar misaltuwa awani b'angaren na zuciyarsa kuwa tsorone fal da fargabar abunda zaije ya isko qasar tasa bayan ya shafe tsawon wasu shekaru batare daya wai wayota ba.
••• ••• •••
Kimanin sati d'aya kenan kusan kullum sai hajia mama tayiwa baffa nasiha akan yayi haquri ya yafe 'yarsa ta dawo gida, fushin ya isa haka ace shekaru kusan bakwai amma yakasa mantawa da abunda yafaru, tsananin damuwa da baqinciki yasa aduk lokacin da batool tayi yunqurin shigowa garin in ta tunada mahaifinta ya haramta mata shiga gidansu saita fasa, saboda bata san da wud'anne idanuwa duniya zata kalleta ba ace tazo mahaifarta inda iyayenta amma an hanata shiga gidan kuma matuqar tashiga garin bazata iya d'auke idanuwanta daga gidansu ba saboda qaunar da takeyiwa mahaifinta da 'yan uwansa da kuma sauran ahalinta, hakan yasata haqura tun ranar da aka d'aukota daga garin aka kawota gidan mijinta bata sake waiwayar garinba saboda kada takasa bin umurnin mahaifin nata ta taka gidansu tsinuwarsa da yafetan da yace zaiyi sutabbata agareta, taci gaba da haquri cike dasa burin cewa zai sauko kowane lokaci ya nemeta ya dawo da ita cikin ahalinta ko don qaunar da yake yimata amma fushin zuciya yasa yakasa haqura har yanzu, hakan yasa haqurin mahaifiyarta ya qare take tunkararsa da maganar akoda yaushe kimanin sati d'aya kenan, kullum saita nuna masa illar abunda yayi na tsawon shekaru bakwai da abunda fushin nasa ke iya jefa 'yar tasa aciki, yakanji zafi da rad'ad'in hakan da yayi shima amma yaqi fahimtar abunda take son fahimtar dashi, jiya da daddare bayan ya watso ruwa ya kwanta ita kuma tana gefen gado tagama sallarta ta shafa'i da wutri tayi addu'a tajuyo tana kallonsa yana sanye da farar riga doguwa jallabiya tayi murmushi.
Murmushin shima yayi mata fuskarsa ba yabo ba fallasa yace.
"Hajia mama lafiya wannan kallo haka.?"
"Lafiya klw alhaji, cikakkiyar surarka da kamalarka na kalla naga irin zubin da ubangiji yayi maka na salihhan bayi dake da matuqar hangen nesa amma kai ka kasa fahimtar hakan balle har ka hango abunda nake son lusar da kai nan gaba, fisabillahi amatsayina na mahaifiya nagaji da irin hukuncin da kakeyiwa 'yata, na d'au tsawon shekaru ina yimaka biyayya batare dana damu da akan daidai kake ba ko akasin hakan, nayita addu'a nayita jiran ranar da kai da kanka zaka fahimci kuskurenka ka gyara amma ka kasa, asalin sahabin manzon ALLAH (s.a.w) dake da sunanka tabbas yanada zuciya sosai amma ya kasance mai tsananin fahimta da saurin sauka da uzuri koda kuwa ga yarone balle babba, akwai qissarsa da aka kawo cewa wata rana yana zaune masallaci sai yaji wani bawan ALLAH na sallah a raka'ar farko ya karanta fatiha sai yakaranta qul a'uzu birabbin nas, yana jin haka ya tashi da sauri yaje gida ya d'auko takobinsa ya tsaya bayan wannan mutumen yana jiran yaji mezai karantawa a raka'a ta biyu idan ya karanta fatiha, sai yaji ya sake karanta qul a'uzu birabbinnas kamar yanda yayi d'azu."
"Mutumen na sallamewa sayyida umar ya kallesa yace wlh ka kuru, daka karanta wata sura bayan qul'auzu birabbinas dana sare kanka da wannan takobin nawa mai tsananin kaifi, sai mutumen ya tambayesa dalili sai yace baya halatta mutum ya karanta fatiha da wata surah a raka'ar farko idan ya tashi yin raka'a tabiyu yace yakaranto wata surar data yimasa dad'i sai kace mai karatun jarida, dolene yakaranta surar dake bima wacce yakaranta a raka'a tafarko ko kuma aya araka'a tabiyun, shiyasa nasan daga qul'a'uzu birabbinnas babu wata surah nazata zakayi wasa da alqur'anin ALLAH ne na d'auke maka kai sai naji ka maimaita surar wannan dalilin shiya qwaceka daga mutuwa a hannuna yau". _(to sai mu kula yin hakan laifine acikin sallah, idan ka karanta surah araka'ar farko idan zakayi ta biyu to surah dake bimata zaka karanta ma'ana ta qasanta, idan kuma ayoyine to cigabansu zaka karanta, ubangiji ALLAH yasa mudace👏)_ kaga anan sayyidina umar yayi zuciya sosai da tasashi zuwa ya d'auko makami akan abunda yaji kuma yayi hasalar da tasa har yake tunanin zai iyayin kisa, amma da yayi haquri yabi abun ahankali har zuwa qarshen sallar bawan ALLAHn nan sai ya sauka daga fushinsa tunda yaji abunda yake tsammanin zai faru ba haka bane kuma abun bai faru ba, sai ya janye hukuncin da yayi niyar d'auka akan wannan bawan ALLAHn tare da yimasa bayanin da zai ilmantar dashi anan gaba, to don me kaima bazakayi koyi dashi ba?, Kayi haquri alokacin da kaji cewa abunda kake tsammani ba haka bane?, don mi bazaka janye hukuncinka ba tunda abunda kake gudun faruwarsa bai faru ba?, Don mi baza kayi uzuri ga 'yarka ba kajawota ga jiki kafahimtar da ita dalilinka na rashin son aurenta da yaron wanda kagano hakan wataqil zaisa ta ilmantu akan girman soyayyar iyaye ga 'ya'yansu ita kesa su yanke masu hukunci cikin b'acin rai saboda qaunar da suke yimasu don tsoron karsu fad'awa halaka.?, Maganar gaskiya ni baka kyauta mani kuma baka yimani adalci, idan kai baka buqatarta akusa dakai ni Ina son na ganeta akusa dani mu zauna tare muyi fira irinta uwa da d'iya, tafad'a mani damuwarta inbata shawara akai Amma duk saboda kai narasa wannan damar, wannan wane irin son kaine kake dashi haka, kullum kai kanka baka damuwa da damuwar kowa idan ba taka ba."
"idan ma hukunci ne kake yimata ai ya isa haka, izuwa yanzu itama tasan me ake cewa d'a da mahaifi, bana tantama duk yana cikin jarabawarta da ALLAH ya karb'e mata rayuwar 'yarta saboda tafahimci irin girman soyayyar dake tsakanin iyaye da d'ansu ta fahimci pain d'in da iyaye ke shiga alokacin da wani abun da basa so zai sami d'ansu, b'acin haka ALLAH ya sake jarabtata tahanyar fasa jikinta aciro mata 'ya'ya duk da kasancewar alokacin zata iya rasa rayuwarta, Ina tsammanin ta wannan fannin kad'ai izuwa yanzu tasan me ake cewa iyaye kuma tasan girmansu, to don me bazaka yafe mata ba, ko kafiso sai ranar da akazo aka cemaka tamutu ko kuma shi mijin nata daka tsana ya mutu sannan kafashe da kuka kace kayafe mata?, Alhaji umar" tafad'i ainahin sunansa wanda ya sashi d'agowa da qarfi yana kallonta, tabbas yau yakaita qul don bazai iya kawo rana d'aya ba d'aya tab'aji ta furta sunansa haka kai tsaye, Saida ta share hawayenta da tafin hannuwanta sannan taci gaba da cewa.
"Ka rabu da mugun nama, ka rabu da dokin qarfe, ka yafi 'yarka tazo garemu na roqeka da ALLAH da girmansa, idan kuma ba haka ba wlh wannan zuciyar taka bazata kaika ko Ina ba kuma zata sa kayi nadama mai yawa arayuwa don na tabbata har yanzu kana sonta kuma kana tsananin qaunarta fiye dani, yanzu haka 'yarka nada tsohon ciki kuma shima tiyata za'a yimata akaro na biyu yarage gareka ka sauko daga fushin da kakeyi da ita ko kuma akasin haka, ita dai mutuwa rigar kowace kuma zata riskemu aduk lokacin da taga dama, ba lallaine