Showing 93001 words to 96000 words out of 260204 words

Chapter 32 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

da gomnati ta d'auki nauyin cigaba da zuwa qaro karatunsu Jeri na farko dake dakon tafiyarsu nan da watanni uku an maidosa zuwa nan da wata biyu masu zuwa saboda wani dalili, don haka su zamo cikin shiri akodo yaushe za'a iya nemansu domin tantancesu (screening), gaban sane yayi wani irin fad'uwa had'e da tuna irin kalaman da Rashida tayi a ranar da yazo yasanar da ita cewa yana cikin malaman da sukayi nasara, dafe kansa dake yimasa barazanar tsagewa yayi da sauri baffa ya kashe redion yana tambayarsa ko lafiya don shi gaba d'aya yama manta da zancen tafiyar tasa saboda tashin hankalin da yake ciki, shi kanshi Nuraddeen wannan sanarwarce ta tuno masa da ita badon haka ba har lokaci ya wuce bazai tuna da komai ba.

••• ••• •••
A can b'angaren iyayen Rashida ko duk wani bincike daya dace ayiwa umma na qwaqwalwa anyi mata, manyan gwaje gwaje (scanning) masu matuqar tsada da zasu tabbatar da haqiqanin abunda yasamu k'wak'k'war tata duka anyi amma sun tabbatarda kwakwalwarta lafiyar klw take, tsananin tashin hankaline ya jefata cikin wannan matsananciyar damuwar da sai a hankali zata iya komawa daidai, shimad'in idan tasamu cikakkiyar kulawa.

Haka shima baba yananan ayanda suka kawosa b'aren jiki ya shanye, magana ma daqyar yakeyi gashi har sun buge kusan wata d'ya a asibitin, sosai d'an uwansa ke qoqarin basu kulawa da dukkanin qarfinsa da kuma dukiyarsa duk da shima yanada tashi hada hadar agabansa amma hakan baisa yagaza wajen bashi kulawaba, Aunty marwiyya ma haka ko yaushe tana tare da umma tana bata magana da ban haquri kuma hakan namatuqar tasiri agareta, ada ba abunda bakinta ke ambata idan ba sunan Rashida ba kuma bataci bata sha, Amma yanzu cikin iyawar ALLAH da addu'o'in da 'yan uwa keyi kuma suna da anayi masu duk sun fara samun sauqi kawai maganace umma bata fiye yiba, dama can ba ma'abociya surutu bace sai abun yahad'e mata yanzu amma jinta, ganinta, hankalinta da komai nata yakoma daidai iyakarta idan ana mgana ta tsurawa mutane ido batare da tace qanzil ba ko kuma tayita bacci.

Yauma kamar kullum tana zaune bisa gadon da aka kwantar da ita na marasa lafiya sukuma su aunty marwiyya da matan bab balarabe na zaune suna fira tana binsu da idanuwa, kamar an tsikareta tayi saurin matsowa bakin gadon had'e da sauko da qafafuwanta qasa zata tashi da sauri aunty marwiyya ta dafeta tana fad'in. "Ina zakije aunty.?" A hankali tabud'e baki tana kallonsu d'aya bayan d'aya kafin tamaido kallon nata ga aunty marwiyya had'e da cewa. "Wajen baban Rashida." Qilan hakan baya rasa nasaba da fitarsa da sukeyi akan wata jayayya da suka tab'ayi shida qanen nasa malan balarabe acan gidansa shine matansa keba aunty marwiyya labari anata dariya, hakan ne yasa tayi saurin fahimtar cewa ai shima yana cikin asibitin kamar yanda taji sun fad'a.

"Kina so kidubo sane?" Aunty marwiyya ta tambayeta tana kallonta, d'aga mata kai tayi alamar eh tana so tace

"To zauna anan Bari nakira likita, idan ya bada damar kije sai muje."

Dariya su hajia larai sukayi cike da zolayar son ganinta cikin farinciki hajia larai tace.

"A'ah, Yaya ko soyayyar ce tamotsa, anjima ba'aga juna ba?."

Umma dai bata tankata ba, saima kafeta da idanuwa da tayi, ahaka aunty marwiyya tadawo ta iskota bakin gadon, d'an matsawa gefe tayi kad'an taba likitan dake tare da ita waje ya dudduba umma had'e da yimata 'yan tambayoyi, ta amsa masa wasu, wasu kuma taqyalesa sannan yace zasu iya tafiya Amma sutabbatar ba guduwa (absconding) ne zasuyi ba.

Riqata sukayi dukda tana iya tafiya lafiya lau suka nufi ward d'in da aka kwantar da baba aciki, kasancewar ana 'yan share sharene da goge goge yasa wanda ke tsaron qofar yace bazai barsu shiga ba har sai angama, bayani aunty marwiyya tayi masa sanan yace to tashiga tare da ita su kuma sauran su tsaya waje har agama itama tana kaita d'in tafito.

Godiya tayi masa sosai sannan suka wuce don dama sun san qa'idar asibitin kenan idan ana aiki ko idan likitoci na round ba'a bari kowa yashiga sai in sun gama ko kuma in lokacin ziyara yayi.

Suna shiga suka iskosa kwance baba balarabe na zaune akan kujera kusa dashi ya duqo had'e da kara kunnensa saiti da bakinsa, da alama wata magana ce yakeyi masa bayaji shine ya kara kunnensa yanda zaijisa sosai.
Murmushi baba balarabe yayi had'e da d'ago kansa jin aunty marwiyya saman kansa nayi masa magana sai yaga ashe tare take da umma, fad'ad'a murmushinsa yayi yana kallon umma had'e da cewa. "'yar halak kinqi ambato, yanzun nan maganarki yakeyi mani shiyasa kukaga na d'ago murmushi ashe kina kusa." Miqewa yayi daga kan kujerar yanaci gaba da cewa.

"Zauna yaya, ya qarfin jikin?."

Bata tankasaba sai kallon baba dake murmushin jin dad'in ganin tasamu sauqi takeyi, yayinda ita kuma hawaye ke zubo mata, aza kanta tayi agefen gadon kus da hannunta ahankali tace "malannnn.." tare da fashewa da kuka.

Aunty marwiyya naganin haka ita da baba balarabe sukabar wajen, baba ya d'ora hannunsa akanta cikin maganarsa da bata fita sosai yace "sannu maman Rashida , muyi haquri."

Haka kawai ya iya furta mata batare da yayi yunqurin hanata ba shima yana nasa hawayen.

Sosai yake qoqarin fitar da damuwar rashin Rashida aransa saboda yasmu lafiyar da zasu iya yin nesa da garin domin hakanne kad'ai zai iya bashi damar cigaba da rayuwarsa batare da wani mummunan abu ya koma faruwa akansa ba amma matuqar suna garin kuma suna ganin abubuwan da zasu iya tuna masu da ita to tabbas yasan wata rana zasu iya rasa rayuwarsa akan tunaninta, musamman idan sukaga mijinta hakan zai dinga tado masu da mikin dake cikin ransu.

Sun jima tare duk da ba wata doguwar magana sukeba face tausayawa kansu da tunanin ko awane irin hali 'yar tasu ke ciki, sai misalin qarfe tara da kusan rabi sannan umma takoma ward d'in da take tanajin wani sassauci aranta duk da halin data gansa bataji dad'i ba ko kad'an, ta fannin baba ma anga sauyi sosai don ranar ya d'an sake, ko zazzab'in dake yawan rufesa da taso masa yau da sauqi sosai, wannan na d'aya daga cikin tasirin da ALLAH kesawa tsakanin mata da miji, tausayi da soyayyar dake tsakaninsu kan haifar masu da natsuwa alokacinda sukayi musayar matsalolinsu.

••• ••• •••
Dr Nuraddeen kuwa saida akayi kwana uku da maganarsu da Rashida sannan yashirya tsaf yanufi garin kano ta dabo tumbin giwa...dama ranarce takama zai koma wajen aikinsa, kasancewar ya kwana biyu bai jeba saboda matsalar rashin lafiyar yaron Rashida yasa koda yazo yatarar da aiki sosai agabansa, wanda hakanne yasa bai fara qoqarin neman iyayen Rashida ba sai bayan kwana uku aikin ya rage masa, tafe yake cikin motarsa yana sauraren wata waqa ta Abdul d one daya yayiwa mahaifiya yana mamin d'inta ahankali har yakai qauyen nasu data kwatanta masa, wata 'yar gajeruwar takarda ya fiddo agaban aljihunsa yana karanta address d'in gidan su data fad'a masa da sunanan mahaifinta da akasanshi dashi, wajen wani mai kayan miya ya tsaya lokacin daya iso anguwar tasu had'e dayi masa sallama sannan yace....







*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___44💎

Wajen wani Mai kayan miya ya tsaya lokacin daya iso anguwar tasu Rashida had'e dayin parking d'in motarsa gefe ya kashe be sannan yafito, nufo inda mutumen ke zaune cikin rumfar tasa da yake saida kayan miya yayi had'e dayin sallama, bayan ya amsa masa cikin girmamawa dr nura ya gaishesa had'e da cewa "Sannu baba, don ALLAH tambaya nakeyi."
Sai daya sallami wani yaro dake tsaye gabansa da yazo sayen kayan miya ledar dake hannunsa sannan ya d'ago kai yana kallon Dr nura had'e da cewa.

"Yawwa d'an saurayi, yi tambayarka inaji ALLAH yasa nasani."

Murmushi kwance a fuskar Dr nura ya gyara tsayuwarsa sannan yace, "Dama gidan malam bashar mai takalma nake nema."

"To.to..to ikon ALLAH, gidan malam Bashir Mai takalma kake nema?, To kaga kabi wannan hanyar ka miqeta sosai zaka had'u da wani masallacin juma'a to daga hannunka na dama inkawuce gida na farko, to nabiyun nanne gidansa." Tsohon yaqarasa fad'a yana nunawa Dr nura hanyar da zaibi ta sadashi da gidansu Rashida. Miqa masa hannu yayi had'e da yimasa godiya sosai sannan yakoma cikin motar tasa ya tayar had'e da kama hanyar da tsohon ya nuna masa, a hankali yake bin kwatancen har ya isa daidai qofar gidan yayi parking acikin inuwar wata bishiya dake gaban gidan yafito tare da jinginawa ajikin motar tasa ya tsaya yana jira ko zai samu yaron da zai aika ayo masa sallama da mahaifin Rashidar, kusan mintuna goma ya kwashe awajen tsaye amma baiga gittawar mutum ko d'ayaba balle yaro, kasancewar lokacin wajajen qarfe sha d'aya na ranane kusan duka yara na makaranta, sosai shiyar tayi tsit bakaganin wulgewar kowa inba ta dabbobin dake kai da kawo suna kuka ba, juyawa yayi da nufin komawa cikin motar saboda ya soma qosawa da tsayin saiga wani yaro ya hango tafe aguje da taya hannunsa nariqe da sabulun wanki da omo, da alama almajirine aka aika da sauri ya taresa yana fad'in.

"Don ALLAH shiga can gidan kace ana sallama da maogidan kaji ko?"

Da sauri yaron ya gungura tayarsa yanufi gidansu Rashida, yana zuwa ya isko gidan garqame da kwad'd'o da sauri ya juya yaje ya sanar dashi, cike da tashin hankali yanufi qofar gidan don gasgata abunda yaron ya fad'a masa ai kuwa yana zuwa ya tabbatar da hakan ganin qaton kwad'o ajikin qofar,

Juyowa yayi da niyar tambayar yaron ina sukaje yaga ashe tuni shi har yabar wajen, waige waige yafarayi ko zai samu wani da zai tambaya saiga wani mutum zai wuce yanufi inda yake da sauri.

"Assalamu alaikum, don ALLAH bawan ALLAH masu gidannan nake tambaya ko kasan inda suka tafi?."
Saida yakallesa sama da qasa sannan ya kalli qofar gidan kafin yabashi amsa cikin rashin sani, don da alama ba mazaunin b'angarenne ba. "Yi haquri bansani ba gaskiya."

"Amma banan anguwar kake neba?"

"A'a acan qasa nake."

"Ok to shikenan babu damuwa ngd." Dr nura yabashi amsa cike da damuwa,

Bakin motarsa yakoma ya tsaya yana tunanin to ina sukaje?, Kar dai ace wani abu yabiyo bayan b'atar 'yarsu ne?, Yana wannan tunaninne saiga wani mutum yazo zai wuce yayi saurin tsaidashi.

"Bawan ALLAH, maigidannan nake tambayar ko kasan I sukaje, ni baqone nazone natarar da gidan nasu arufe."

"To kakirasu awaya mana."

"Maganar gaskiya kwatance akayo mani banida lambarsu."

"To gaskiya bawan ALLAH bansan inda sukaje ba, nadaiji kwanaki kamar ana rad'e rad'in cewa 'yarsu ta b'ata to amma.." bai qarasa maganarba sanadiyar kiran da akayi masa a waya, d'agawa yayi kafin Dr nura yaji yace.

"Mene? Subhanallahi to gani nan zuwa yanzu." Da alama wani abu yafaru wanda nan take hankalin mutumen ya tashi, batare daya koma kulawa kansa ba da sauri yabar wajen cike da tashin hankali.

Kusan awa d'aya yayi a anguwar yana tambaya, daqyar yasamu wani yace masa yaji kamar ana zancen suna asibiti daya tambayesa wace asibitin kuma sa yace shima bai sani ba,
Wata irin fad'uwar gaba Dr nura yaji had'e da shafa kansa yana fad'in "innalillahi wa'inna ilaihirrajiuun."

Jiki ba qwari Dr nura yabar anguwar, yana wucewa mashin na aje baba balarabe aqofar gidan yazo d'aukarwa baba kayan da zaya canza saboda yanzu yafara samun sauqi sosai don har tashi zaune yanayi idan anriqasa, bakinsa da hannunsa kawai ne basu ida saki ba Amma hatta qafarsa yad'an samu sauqi saboda ko yaushe umma natare dashi don itama ba laifi tasamu sauqi har an sallameta.

Acikin kwanaki biyu da suka rage Dr nura yakoma borno kusan kullum sai yaje anguwar ko zai samu labarin awace asibiti suke ko kuma idan ansallamosu amma yakasa samu saboda gaba d'ayama mutanen anguwar sun fara jin tsoronsa abunka da mutanen qauye sunga qatuwar mota da had'add'en mutum sai suka dena kulasa balle su sauraresa, atunaninsu so yake ya cutar dasu ko kuma 'ya'yansu, hakan yasa yakoma ziyartar qananun asibitotan dake zagaye dasu amma kasancewar bai sansu a fuska ba yakasa ganosu, har asibitin da aka kwantar dasu saida yaje, gashi ga gadon umma suka wuce shida wani likitan dake asibitin suna magana amma da yake bai santaba yawuce, duk iya qoqarin daya kamata yayi akan ganosu yayi amma baiyi nasarar had'uwa dasu ba, watak'il hakan yafarune sanadiyar rubutacciyar qaddarar da ALLAH ya tsaro wanzuwarta a tsakanin RASHEEDA DA NURADDEEN ne.

Tunda Dr nura yadawo daga kano ya sanarwa da Rashida halin da ake ciki tashiga babban tashin hankalin da baya misaltuwa, batada aiki sai kuka had'e da tayar masu da hankali cewa lallai sai sun barta taje kano don tagano inda iyayenta suke, ga jikin jaririnta daya matuqar tsananta wanda tuni tace Dr nura yayi masa hud'uba da sunan mahaifinsa wato Nuraddeen sunan da kuma yayi daidai dana shi Dr nuran. Hakan baqaramin dad'i yayi masu ba duk da basuda tabbacin cewa yaron zai tashi amma sunan da aka rad'a masa yaqarasa su jin wata irin matsananciyar qaunar yaron aransu, lallashinta suka shigayi da bata baki akan tayi haquri tunda har tasan gidan iyayen nata dana sauran 'yan uwanta da mijinta har sai yaronta yasamu lafiya sai su kaita har gida, koba komai zuwa lokacin sunada tabbaci akan ansallami iayen nata aduk asibitin da suke kuma yayi mata alqawarin zaici gaba da bincika mata inda suke kafin lokacin da yaron zai samu lafiya, idan ALLAH yasa angasu koda yaron bai warke ba sai yasa ayi masu transfer sukoma can dashi acigaba da jinya.

Batada wata madafar data wuce mata haka don bazata iya guduwa daga hannunsu ba bayan duk d'imbin alkhairin da sukayi mata ita da d'anta da tuni tanufi wajen iyayenta da 'yan uwanta domin sunada buqatar suganta su san halin da take ciki, musamman habibynta da akoda yaushe jikinta nafad'a mata cewa yana cikin wani mummunan hali,

Yaya hawwa kuwa tasha azaba kala kala kafin tabud'e baki tasanar dasu inspector najida cewa itace tayi sanadiyar b'atan Rashida saboda baqin asirin da takaita wajen wani boka akayimata, kuka takeyi tana basu labarin abunda yafaru saboda tsananin azabar da take ciki, gaba d'aya qanana yatsunta na dama da hagu anqire mata su, haka akaifun manyan yatsun qafafuwanta duk an cire matasu sai jini sukeyi, ga ijiyarta d'aya da suka jimata ciki wadda ALLAH kad'ai zaisa taci gaba da gani da ita.

Hatta blessing da take arniya Saida ta tsinema Yaya hawwa, wani qaton kulki dake hannunta tabugawa yaya hawwa akai takife qasa asume, cikin rashin tausayi blessing tace. "Shege me zuciyan duse kamutu dan iska."

'Daga mata hannu inspector najida tayi had'e da cewa.

"Noo...kibarta blessing, dole munada buqatarta saboda zamuje da ita acan qauyen da bokan yake idan tafarfad'o shima akamosa, hakan zaisa musan inda yarinyar nan take tunda shi yayi asirin, ita daga yanzu amfaninta yaqare wajen sanin inda yarinyar take tunda batada wata masaniya akai, zadai muyi amfani da ita mukama bokan nata yazo hannunmu."

Tana gama fad'a tajuya tabar wajen cike da jinjina tsantsar rashin imani irin na Yaya hawwa.





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[8/17, 10:19] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

_Alhamdulillah for d unlimited bless anytime ya rabh👏 hi sister's gaisuwa tare da fatan alkhairi ga d'aukacin masoyana kuma masoyan littafin SANNU SANNU... Ina yiwa kowa BARKA DA SALLAH tare da fatan anyi sallah lafiya,🥰 ubangiji ALLAH ya maimaita mana kasa ni daku munyi tarayya acikin d'imbin ladaddaki da gafarar ALLAH dake cikin wud'annan kwanakin da suka shud'e,👏💃🏼 ALLAH kajiqan dukkanin iyayenmu wud'anda suka rasu da wud'anda keraye Kuma kabasu aljannah da rahamarka damu baki d'aya👏 Ina fatar zamu d'ora daga inda mukatsaya kuma zaku bani 'yan barka da sallah ta tunda rowar nama tasa kun b'uya ko leqowa bakwayi a group balle atuna da littafin SANNU SANNU sai yanzu da kuka cinyye abunku,🥰😅 SANNU SANNU fans group 1&2 ina jiran 'yan barka da sallahta😅😅😅hohoho..ku kwantar da hankalinku kud'i nake so ni ba nama ba don naga wasun ku sun fara hararata, to bashi nake so ba amma dai kuci ahankli ko ince wacce duk ta zaqe da yawa ALLAH yasa tafara z....🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🤣🤣🤣🤣ahhh to bandai iyar ba balle ace Billy tayi muguwar addu'a. *LUV YOU ALL FILLAH* ❤️_

Page___46💎

Tun da sassafe baffa yakira inspector najida tayi masa bayanin bayanan da suka samu a hannun yaya hawwa tare da tabbatar masa da cewa yau d'innan zasuje da ita har dajin da bokan yake shima aka mosa, matsala d'aya basuda tabbacin kamosan zaisa asan inda yarinyar take tunda harkace ta shed'anin aljanu, kawai zasuyi hakanne don yazama izina uma tudun da zasu dafa wajen ganin sun kauda masu munanan halaye irin na Yaya hawwa da bokan, saboda Haka ta shawarci baffa da kawai atashi tsaye da addu'a in sha ALLAH ALLAH zai bayyanata, sosai baffa yaji dad'i akan matakin da tace zasu d'aukar masu, ad'aya b'angaren zuciyarsa kuwa halin yaji yasamu wata 'yar qaramar natsuwa don yanada tabbaci akan yanda Rashida tayi riqo da addininta ALLAH bazai tab'a Bari acutar da ita ba, saidai idan yaso ya jarabce tane daga cikin jerin qaddarorin daya tsaro mata arayuwa, godiya yayi Maya sannan ya kashe wayar, daidai lokacin Nuraddeen yafito wanka riqe da d'an qaramin towel yana goge jikinsa, kallonsa baffa yayi cike da tausayi lokacin daya hau shirya kansa kafin yace.

"Nuraddeen Ina zakaje ne haka tunda sassafe?."

"Yarimawa." Yabashi amsa ataqaice yana qoqarin zura rigarsa ajiki, "ehmm!..to Bari na shirya sai muje dama Ina son inje dubo aminina, jiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login