Showing 198001 words to 201000 words out of 260204 words

Chapter 67 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

don haka suka nufi gidan Dr wanda tuni ankafa qatuwar rumfa da kujeru awajen, wasu kuma mutanen suka tafiyarsu saboda wasu uzurukka nasu, bayan kowa yaci yasha ya qoshi shakur yashiga har cikin gida yayiwa Rashida godiya sannan shida abokanansa suka nufi gidansu iman don d'aukar hotuna.

••• ••• •••
A can kano kuwa saida aka gama kwashe kowa aka kai can inda za'ayi walima sannan su Uncle h suka zo suka d'auki amarya batool, matar uncle Hussain da amaryar Abba wato kishiyar hajia mama su suka riqota har zuwa cikin mota, sanye take da royal blue lace yasha fararen fulawowi masu fad'i ajikinsa anyi mata d'unkin riga da sket, sai wata qatuwar alkibba fara tas itama daga saman kai ayi mata aiki da royal blue d'in zare haka agaban rigar da bayanta an qawatashi shima, kallo d'aya zakayi mata ka hango tsantsar farincikin dake tattare da ita don takasa b'oye hakan, kasancewar ita d'in kyakkyawa ce ta ajin farko yasa bata wani bari aka cika mata fuska da irin kwalliyar nan da ake yayi ba sai dai 'yar kad'an data qara fiddo mata da kyanta na asali sai qamshi take zubawa tayi matuqar kyau tubarkallah masha ALLAH abunka ga farar macce da blue d'in abu ke matuqar amsa.

Batare da b'ata lokaci ba uncle Hussain yaja motar suka bar wajen, Abba kuwa dake can bayan corridor d'akinsa zaune bisa resting chair idanuwansa arufe miqewa yayi yakoma cikin d'aki yarufe yanajin wani irin rad'ad'i azuciyarsa, tabbas yau ya yarda da bahaushe dake cewa son zuciya b'acin zuciya..Wai yau 'yarsa da yafi so fiye da komai aduniya itace ke farinciki bayan baqin cikinsa, itace tazab'i bijire masa akan zab'inta, ta yarda tarasa gatar da yake bata taje ta zauna da wani marar asali matsiyaci da baisan darajarta ba, ta zauna da mutanen da basuda wata kima da daraja a idanuwan mutane, idan kuwa hakane dole a matsayin sa na mahaifi daya reneta cikin kulawa har takawo wannan girman yanuna mata kuskurenta na fifita wasu akansa.

A can wajen walima kuwa tunda aka shiga da ita idanuwan little ke kanta ko qyabtawa bayayi, ganin an nufo wajen da ita yasa little qoqarin miqewa da sauri abbaty yaja rigarsa yakoma ya zauna.

"Little meye haka?, Duk idanuwan taron nan fa na akanka, ina zakaje idan katashi?"

Sai alokacinma little yafahimci ko meyake son yayi yayi saurin duba gefe da gefensa yana murmushi tare da sunkuyar da kansa qasa yana sosa qeyar kansa, qasa yayi da muryarsa had'e da cewa.

"Old man." Don haka yake kiransa saboda sunan marigayi baba dake garesa.

"Ya akayi?, in baka waje zaka tafine?"

"Haba! Bahaka nake nufi ba, bakaga yanda gimbiya tayi kyau bane!, Sak tafito a gimbiyarta wanda kamata yayi ace awannan lokacin nazama srki, ya kake tunanin abun zai kasance."

Saida abbaty yaui dariya sannan yakai bakinsa wajen kunnensa had'e da cewa.

"Abun zai matuqar burgewa, Amma kayi qoqarin farkawo daga mafarkin da kakeyi inba haka ba ko yanzu kazamo sarkin marasa kunyoyi awajen nan!"

Da sauri ya juyo suka had'a ido dashi ya kad'a masa kai alamun tabbatar masa da abunda yafad'a had'e da d'an turo masa idanuwansa.

Hakan yasa yayi saurin tattaro natsuwarsa zuwa ga sauraren wa'azin, bini bini yake juyawa ya kalli batool dake can kan kujera saiti dashi a gefen da mata suke, malamai sunyi wa'azi sosai akan zamantakewar aure da kuma neman aljannah, mutuntaka da kuma girmama rayuwar d'an Adam, muhimmancin riqo da addinin da kuma kariyar da take bayarwa acikin aure, tausayi tsakanin ma'aurata da taimakekeniyar juna, yiwa juna uzuri tare da fahimtar juna, kyakkyawar zamantakewa da iyaye da kuma 'yan uwa had'i da mutanen gari, haquri, juriya da Kuma yiwa juna uzuri acikin rayuwar aure, duk da ba awaje d'aya suke zaune ba alokaci d'aya zukatansu sun quduri riqe junansu amana bisa wud'annan kyawawan nasihu da suka fito daga bakin manyan malamai tare dayin alwashin aiki da duka nasihohin da suka saurara.

Ana kammalawa mutanen da aka tanada saboda su kula da jin dad'in baqin da suka halarci taron had'e da ci da shansu suka fara zagayawa da abintayye kala kala suna a'ajiyewa tare da gorunan ruwan sha masu sanyi da kwalayen lemuna kala kala, ga kaji da snacks suma sai abunda mutum kesonci zai zab'a yaci, _😅acan nahango mutanena su aunty fareeda da meamah dasu teemah gabs anbaje anata Jan gara, aunty fareeda kam sai tura kaji takeyi acikin jikka wai zata riqawasu arfatu, gani awaje an hanani shiga sai ta taga nake samun d'auko maku rahoto, nahadiyi yawu yafi a qirga amma babu wanda yakulani sai aunty maijidda data hangoni a jikin taga ta taso saye da hijab d'inta tundaga sama har qasa riqe da take away guda biyu duka naman kajine aciki ta miqomun tana fad'in, My billy ungo kirage zafi da wannan tunda sun hanaki shigowa, kece da naci komai sai kice sai kin d'au rahoto kin fad'awa mutane shiyasa suka saka maki idanuwa suka hanaki shigowa, ALLAH idan bakibi hattaraba ko motar kai amaryar ma baza'a bari kigani ba sai dai kawai kiji ance ta haihu nace, to aunty Maijidda taimakon da ruwa da lemun mana, ga samosa can da tsinken tsire guda hud'u ki had'omun dasu, dariya tayi had'e da d'aukomun tace, yo my Billy kice ke kinfima wud'anda suka samu shigowa murewa_

Saida kowa yaci yaqoshi hani'an mari'a sannan motocin suka sake kwashesu suka mayar dasu gida wasu kuma daga nan suka wuce gidajensu suna masu yiwa ango da amarya fatan alkhairi da kuma samun zaman lafiya da zuri'a masu albarka.

Batool nakomawa gida su uncle sukace aje agyarata yanzu za'a wuce da ita gidan mijinta, ai nan take jikinta yafara rawa hawaye suka soma zubo mata tashiga dube duben inda zataga mahaifinta ahankali tana kiran sunansa.

"Abba, abba, abbanah, momy Ina abbana?"

Tafad'a tana kallon matar mahaifin nata, dafata tayi sannan tace

"Ki kwantar da hankalinki kizo muje kigyara zan kaiki har inda yake kinji ko?"

Kamar wata samna batool tace.

"To.." tare da bin bayanta.

Bayan angyarota tana tashin qamshi tako Ina ajikinta mom takaita indasu uncle h suke tanzaunar da ita, hud'uba suka sake yimata kamar yanda iyaye keyiwa 'ya'yansu idan zasuyi aure sannan sukasa aka kira hajia mama ta sake yimata.

Cikin dakiya tace.

"Batool haqiqa yau kin samu cikar burinki duk da kin sab'awa mahifinki awani b'angare, Amma Ina roqon ALLAH kada yakamaki da wannan laifin ya yafe maki, Ina roqonki da kibi mijinki sau da qafa fiye da yanda nake yiwa mahifinki, ki girmama masa iyayensa fiye da yanda kike girmama naki, kishiga gidanki da niyar bautar aure ba kasuwanci ba, kaji tsoron ALLAH, kiji tsoron ALLAH, kiji tsoron ALLAH Kuma kiriqe ibada da kuma addininki, wannan shine nasihata agareki, du abunda kika yimani kuwa nayafe maki duniya da lahira, ALLAH yayi maki albarka yabaki zuri'a d'ayyaba yakareki da sharrin mutum dana aljani da kowace irin halitta, dafa kanta tayi had'e da karanto mata addu'a ta tofa mata sannan tabar d'akin da sauri saboda kukan dake neman kuccikke mata, batool kuwa tsananin kukan da takeyi ko fita sautinsa bayayi saidai sheshshekar da take famanyi kamar za'a cire ranta,

'Dagota uncle Hussain yayi had'e da riqo hannunta na dama uncle Hassan yariqota a gefen hagu suka nufi part d'in Abba inda d'akinsa yake, suna zuwa suka tarar da qofa kulle suka bubbuga yaqi bud'ewa, sunfi mintuna biyar suna magana amma bai tanka suba balle susa ran zai bud'e hakan yasa suka juyo da ita tana kuka tana waiwayen qofar d'akin had'e da kiran sunansa amma yaqi bud'ewa.

Ganin har zasubar part d'in bai bud'eba yasa ta kwace hannuwanta da gudu takoma bakin qofar d'akin tana kuka tana bubbugawa.

"Abbana don ALLAH kabud'e, Abbana, Abbana to kayimun magana ko zan samu albarkarka kaji Abbana, Abbana don ALLAH kabud'e na sake ganinka ko sau d'aya ne.."

Yana jinta yayi banza da ita harsu uncle h suka gaji suka dawo suka riqeta, wani irin kuka tafashe dashi had'e da cewa.

"Wayyo Abbana..za'a tafi dani don ALLAH kafito, abba, Abba.."

Ganin bazai tankata ba yasa taroqi su uncle subarta ko sau d'aya tayi magana dashi, bakin qofar takoma ta jingina tana fad'in.

"Abbana ina matuqar qaunarka, nasan cewa kana fushi dani bisa bijire maka da nayi amma don ALLAH ka yafemun, zan tafi cike da d'imbin kewarka azuciyata, ban sani ba zan dawo agareka ko kuwa rai zaiyi halinsa kafin nadawo gareka idan ka dena fushi dani, zan rayu cike da tsammanin cewa wata rana zaka waiwayeni da idanuwanka na rahama da kuma tausayina, Abba kacire damuwa akaina, natabbata cikin 'yan uwana da yawansu zasu share maka hawayen wannan halin dana saka, kayi haquri nakasa sarrafa zuciyata tafi qarfina akan abunda take so, Ina sonka abbana, Ina roqon ALLAH daya tabbatar da kai cikin amincinsa ya cika qirjinka da farincikinndan kasa sakaka aciki."

Tana rufe baki uncle Hussain yaja hannunta suka fita da ita kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita har suka kai bakin motar da zata shiga, tana aza qafarta da sauri ta dawo da ita had'e da juyowa jin takun tafiyar da tasan ta mahaifinta kawai ce, shine yafito yana nufato inda suke fuskarnan tasa ba walwala aciki da gudu tanufi wajensa zata rungumesa yayi saurin dakatar da ita, tahanyar d'aga mata hannu, cak tsaya batare daya damu da wud'anda ke tsaye wajen ba yace.

"Nayafe maki Fatima Amma bisa sharad'i d'aya."

Da sauri ta d'aga masa kai tana qoqarin qarasowa inda yake ya sake dakatar da ita, alokacin su uncle h suma suka matso don sauraren me zaice suma ya dakatar dasu ta hanyar cewa.

"Ina buqatar yin magana da ita kad'aine ba daku ba, kunyi yanda kuke so naqyaleki, kun nuna isarku akanta na amince da hakan ayanzu kuma Ina so in nuna maku tawa isar akanta har ma daku gaba d'aya"

"Batool kije nayafe maki Amma bisa sharad'in karki sake tako qafarki anan gidan har sai lokacin dana barsa ko kuma raina ya rabu da gangar jikina, idan kuma kika kaucewa hakan to kitabbatar babuni babu ke kuma nafiddake a matsayin 'yata, Zaki iya had'uwa da duk wanda kike so ciki harda mahaifiyarki Amma ba'a cikin gidanan ba."

Yana gama fad'ar haka tajuya yanaci gaba da cewa.

"Wlh wlh duk Wanda yasa takarya wannan umurni nawa acikinku to yakarya dangantakar dake tsakanina da ita na uba da 'ya kunji nafad'a maku."

Bud'e da baki suke kallonsa don Basu tab'a tsammanin cewa zuciyarsa zata kasa lanqwasawa ba da kalaman da 'yarsa tayinmasa sai yanzu, asali ma da sukaga yafito sun zata ya saukone ashe wata baqar zuciyarce tasa taso, ai kan su juyo batool tazube awajen some sukayo kanta aguje.

Hajia mamace tafito tana hawaye riqe da cup da ruwa aciki ta yayyafa mata ta farfad'o, tana bud'e ido tafad'a jikin mahaifiyarta tana kuka, d'agata tayi tariqata takaita har cikin mota sannan tace.

"Batool indai ni nahaifeki Ina roqon kibi umurnin mahaifinki tunda yace hakan kad'aine zaisa ya yafe maki, kici gaba da addu'a nima zanyi maki ALLAH ya sassauta masa zafin rai, addu'a ta Kuma natare dake duk inda kika shiga in Sha ALLAH dakansa zai nemeki, b'acin rai yasa dole yayi haka Amma Ina roqon saukowarsa akoda yaushe, kidena kuka kinji ko Nima zanci gaba da rarrashinsa har zuwa lokacin da zai sauko."

Ta share mata hawaye sannan tanufi cikin gida itama tana share nata hawayen da suka jiqa mata fuska...




*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___90💎

Ana fara kiraye kirayen sallar asuba little ya miqe daga kan gadon don dama baiyi bacci ba, tun faruwar abubuwan da suka wakana tsakaninsa da ita adaren jiya ya kasa rumtsa idanuwansa sai albarka yake samata, wani irin farinciki da nishad'i marar misaltuwa ya tsinci kansa aciki, tabbas batool alkhairice sosai agaresa domin adaren yau kad'ai ya gamsu da kasancewarta acikin rayuwarsa, kallon yanda take fidda lumfashinta hankali kwance tana barci yayi had'e dayin murmushi yana shafa fuskarta had'e da cewa.

"Waye yafi Abu sumayya samun mata 'yar baiwa kamarki, waye zai kaini sa'ar samun mace tagari a duniya? Gaba d'ayanki komai naki yiyi d'ari bisa d'ari bakida wata matsala, fatana ALLAH yabani ikon kulawa dake sosai ta yanda zanci gaba da alfaharin kasantuwata dake nahar abada."

A hankali tafara bud'e idanuwanta har suka sauka akan kyakkyawar fuskarsa, murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa tare da d'ora hannunta akan nasa dake saman fuskarta.

"Lafiya Abu sumayya?"

"Ina fa lafiya nayiwa gimbiyata laifi!"

"Hmm! Ai duk abunda zakayiwa gimbiyarka bazakayi laifi awajenta ba matuqar kayi hakanne don kasamu farinciki."

"ALLAH gimbiya ta?"

"Sosai kuwa." Tafad'a had'e da rufe idanuwanta kamar mai shirin komawa bacci, jawo hannunta yayi ya sumbata sannan yace.

"Nagode sosai gimbiyata ALLAH yayi maki albarka, kin sakani acikin farinciki da bakina bazai iya misaltasa ba kuma komai zsn baki aduniya bazai iya biyan wannan daren alkhairin da kika tanadarmun ba, amma nayi maki alqawarin cewa matuqar muna tare araye zan bautawa soyayyarki har iya qarshen rayuwata, zan kula dake kuma nabaki gatar da bazan tab'a bari hawaye su kwaranya awud'annan kyawawan idanuwan naki ba, Ina sonki da qaunarki acikin zuciyata, rouhina dama dukkanin gangar jikina."

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke tashiga bud'e idanuwanta ahankali tana kashe masa su had'e da cewa.

"Idan kayimun haka kagama mani komai Abu sumayya, ka biyani dukkanin dakon qaunarka da nakeyi azuciyata har kabiyoni bashi."

"To kid'auka hakanma tafaru matuqar ina raye, yanzu muje na taimaka maki kiyo wanka kafin a kirayi kiran sallah na biyu."

"Karka damu zan iya da kaina, kaje kafarayi karka rasa jam'i."

Baiyi mata musu ba ya miqe had'e da shigewa toilet ya tsarkakikke jikinsa tare da d'auro arwala ya fito ya zura babbar rigarsa sannan yanufi masallaci, bayan yafita itama tamiqe taje tayo wanka tayi sallah, tana sallamewa tasamu katsar watsar tayi azkar saboda baccin dake damunta tamiqe ta kakkab'e gadon taqara gyarasa sannan takoma ta kwantawarta tana mai jin wani irin farinciki ya mamaye mata dukkanin zuciya.

A b'angaren Shakur dai shima kusan hakan ta kasance, yasamu iman d'insa ayanda yake buqata yayita sanya mata albarka, kuka kam tashashi sosai tare da zuba masa shagwab'a shikuwa sai nan nan yakeyi da ita.

Da safe umma ta tashi dawuri ta shirya abun karyawa lafiyayye tasa shahida 'yar su Dr da yake anan gidan dady takwana tace taje takai masu, Saida tafara biyawa gidansu Shakur takai masu nasu sannan tawuce gidansu little, lokacin yana kwance a falo donnkoda yadawo daga masallaci ya isko takoma bacci, saboda bayason takurata yasa ya dawowarsa falo ya kwanta don inhar ya kwanta inda take to ya tabbata bazai iya qyale taba, gashi tamatuqar shan wahala jiya amma saboda jarumtarta takasa hanasa har saida ya samu gamsuwa, don haka bazaiso ya takura taba yanzu.

Jin ana bubbuga qofa had'e dayin sallama yasa ya tashi yaje ya bud'e, d'an rissinawa shahida tayi ta gaishesa sannan tawuce ciki ta ajiye kwandon abincin, tsaye tayi tana murmushi yace.

"Yaya aunty batool fa?"

"Bacci takeyi shahida ko a taso tane?"

"Eh yaya, Ina son mugaisa ne sai in fad'a mata saqon umma."

Tsura mata idanuwa yayi kafin yace.

"A tasota fa kikace shahida! Cab gaskiya saidai ki haqura anjima kidawo, fad'an saqon na umma sai nafad'a mata idan ta tashi."

B'ata rai shahida tayi had'e da turo baki tana fad'in.

"Yaya wato rowar auntyn tamu zaka yimani, ALLAH baran sake dawowa ba idan kace haka?"

"Eh naji! jeki abinki baza'a tashetan ba, haka kawai zakice atasheta tana bacci don ki ganta, Ina ai shikenan yanzu kullum tana tare daku? to meye na neman takurata awannan lokacin?"

"Lalle Yaya, Aikuwa saina fad'awa gwaggo wlh."

"Eh kifad'a mata, nasan ai itama bazata so atakurawa 'yarta ba."

Yana rufe baki batool nafitowa daga cikin d'akin ta taso saboda muryoyinsu data dingaji sama sama wanda sune suka tasheta daga baccin, dariya shahida tayi tare da qarasawa inda take tana fad'in.

"Auntynmu barka da safiya. Ina kwana" Har lokacin idanuwanta nakan little dake faman zabga mata harara.

Cikin sanyin muryar dake nuna tashinta daga bacci kenan tace.

"Yawwa! lafiya klw shahida ko?"

"Eh aunty." shahida tafad'a tana qara fad'ad'a murmushin dake kan fuskarta, qarasowa cikin falon batool tayi tana d'an yayyamutsa fuska saboda d'an zafin da takeji qasanta duk da dai ba irin sosai d'innan ba shahida nabiye da ita ta zauna akan kujera, kallon little dake faman binta da kallo tayi tare da sakar masa murmushi sannan tace.

"Barka da safiya ranka shidad'e, antashi lafiya."

"Lafiya klw gimbiya, am sorry wannan talkative d'in ta tayar mani dake ko?"

Fuskarta na d'auke da murmushin tajuyo tana kallon shahida da tuni sun gama burgeta tace.

"Shahidaya gida yasu gwaggo da mama?"

"Lafiya klw suke duk da dai ba'a can nakwana ba gidansu dady."

"ALLAH sarki, to yasu umma dasu ammie da aunty?"

"Kowa lafiya, umma cema ta aikoni nakawo maku abun kari, tace na gaisheki sosai kafin tazo?"

"To kice nagode shahida, Ina amsawa sosai nima ina gaishesu."

"Zasuji aunty, bara natafi kafin idanuwan Yaya su fad'o qasa." tafad'a had'e da miqewa tana dariya,

Hannu ya d'aga kamar zai mata soqo tafice aguje tana yimasu sai anjima.

Da kansa yajawo kwandon abincin zaiyi mata saving ta dakatar dashi, d'aki takoma tayo brush tafito shima yaje yayo nasa sannan ta zuba masu a plate be d'aya sukaci suka qoshi ta kwashe kayan da suka ci abincin taje ta d'auraye sannan takoma d'aki ta sake kwantawa,

Hakan yasa yashiga gyaggyara duk inda yakamata duk da bawani datti yayiba sannan shima yakoma inda take ya kwanta tare da jawota ajikinsa suka koma baccin atare.

Basu tashiba sai kusan qarfe sha d'aya na safe, shima d'in abbaty ne yakirasa awaya ya sanar dashi cewa Dr yace su shirya za'azo a d'aukesu zancen walima an mayar qarfe sha biyu na rana zuwa qarfe d'aya saboda mutanen kano da zasu koma don dama da marece aka shirya yinta to saboda su 'yan kano da sukazo kawo amarya dady yace ayita da Sha biyun zuwa d'aya saboda su samu su tashi dawuri donsu isa gida cikin lokaci.

Kasancewar lokaci yaqure yasa agurguje sukayo wanka suka fito little yafiddo mata da wasu sababbin kaya da batama san dasu ba rigar naja

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login