Showing 258001 words to 260204 words out of 260204 words
Chapter 87 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt
b'ace kamar bai tab'a yi ba, ita kuma yaya hawwa ganinta yadawo tas. _('yar uwa kinada buqata ko wani abu dake damunki?, to kijure kuma kijajirce dayin wannan addu'ar👇, wlh tallahi matuqar baki gajiyaba dayi kuma kikasa yaqini akan ubangijinki to zakiga biyan buqata da waraka da yardar ALLAH, itace Rashida tayi har baffa Ali da Yaya hawwa suka samu waraka ga cutukkan da ake tsammanin sai mutuwa tsakaninsu dasu)_
A kullum takan tashi da daddare misalin qarfe uku tayi arwala saita sallaci raka'a biyu ta nafila tare da 'yan ruwa agefenta kamanin rabin kofi.
_*A raka'a ta farko tana karanta suratul ikhlas, wato qul'a'uzu birabbin nas qafa goma(10) saita tofa acikin ruwan sai tayi ruku'i, idan ta d'ago daga ruku'i saita karanta wata (suratul ikhlas) qafa ashirin(20) ta tofa cikin ruwan sannan taje sujada ta farko idan ta d'ago saita karanta suratul ikhlas d'in qafa uku(3) ta tofa saita koma sujada ta biyu, idan ta d'ago ta sake karanta qafa uku(3) ta tofa duka acikin ruwan sannan saita miqe zuwa raka'a ta biyu ta sake karanto suratul ikhlas qafa goma(10) saita tofa taje ruku'i, idan ta d'ago sai ta karanta qafa ashirin(20) ta tofa sannan taje sujada, idanta d'ago saita karanta qafa uku(3) ta tofa sannan ta sake komawa sujada, to anan idan ta d'ago bazata karanta suratul ikhlas d'in ba sai tayi tahiya tagama kafin ta sallame saita karanta qafa uku(3) ta tofa sannan tayi sallama, tana sallamewa bayan tayi istigfari saita karanta ayatul kursiyu qafa d'aya(1) ta tofa duka acikin ruwan sannan tayi salatin annabi sau d'ari(100) ta tofa aciki, idan ita keda matsala bayan tagama addu'o'inta saita rufe ruwan ta ajiye, tun da sassafe kafin taci komai saita sha ta kuma shafa a inda matsalar take idan kuma ba ciwo bane to saita shanye ruwan kawai basai ta shafa ba musamman in nacan cikin jikine daba bayyananne ba, idanma tana tsoron kada shed'an ya mantar da ita da safe zata iya tana gama sallar da daddare bayan tayi addu'o'in ta saita shanye, in kuma wani akayiwa to sai arufe ruwan a ajiye kuma ayi qoqarin bashisu yasha kafin yaci komai da safe, in Sha ALLAH ko menene damuwa ko tsananin ciwo in aka nace dayin wannan sallar to tabbas za'a samu waraka da izinin ALLAH, ammafa sai an jajirce don la'anatullahi yakan bijiro da kasala sai anyi da gaske*_ (wannan addu'a sadaka ce zuwa ga mahaifina Ina bara duk wacce ALLAH yabawa ikonyi data sakashi cikin addu'o'in ta ALLAH yajiqanshi kuma yayi masa rahama da shi da dukkanin musulmi baki d'aya, ALLAH kasa adace👏)
Hakan Rashida tayi tayi har ALLAH yasa aka cimma ijaba Yaya hawwa da baffa Ali suka warke, alokacin sun sake yin kuka sosai tare da nadamar abunda suka aikata mata gashi batare da tayi la'akari da wannan ba tayi amfani da qarfinta da ilimin da ALLAH yabata tahana kanta bacci taroqa masu samun waraka da kuma magani ga ALLAH don su samu lafiya, haka ake son zuciyar musulmi ta kasance akoda yau she mai tsananin yafiya da kuma rama alkhairi ga junansu,
Haka rayuwar ahalin ta kasance cikin farinciki da kuma zaman lafiya da girmama juna, tuni anka gudanar da auren Yusuf da Rashida 'yar baffa, manyan 'yan boko don gaba d'ayansu sunyi karatu Mai zurfi Wanda baffa ke alfahari da hakan, acan asalin family house inda su baffa Usman sukayi zama Yusuf ya saye duka shiyoyin guda uku ya rushe ya qera gidansa mai kyau irin nasu na 'yan boko wayayyi haka ma Dr Nuraddeen da kansa yasama masu aiki tunda gwamnatin jahar dashi take damawa tare da shahida da itama tuni takammalo karatun daga qasar waje suka daidaita da Uncle Hussain d'an baba balarabe aka d'aura masu aure, yanzu haka suna nan zaunensu kano wajen aikinsu guda da ita da Rashida matar yusuf, little kuwa yana can borno abunsa yayi zamanninsa acan saidai idan sunyi sha'awar zuwa nan kano suzo suyi satukka ko wata d'aya su koma musamman idan yara na hutu,
Zainab ma autarsu Dr nura tana hannunsu Rashida kamar yanda Dr ya alqawarta komai nata gaba d'aya yadawo wajensu, tana samun kulawa sosai fiye da tsammani don ba kad'an suke jin taba har cikin qoqon ransu wanda tuni itama suka daidaita da shurahbil d'an wajen uncle Hussain baffan batool, amma saita qare karatu tukuna za'ayi auren, zainaba ma 'yar baffa ta biyu itama tayi aure amma acan cikin kano take zaune da mijinta bayan ta kammala karatunta itama, asiya da Bilkisu kad'aine suka rage wud'anda suma gaba d'aya sun koma hannun Rashida tare da zainab sukeyin komai hatta karatu waje d'aya sukeyi, Babu wani banbanci tsakaninsu ko fifiko don su Dr Nuraddeen sun nuna masu abu d'aya suke awajensu saboda haka suso juna, haka ma auta basha (Abba) son da Rashida keyi masa yasa da wayo da wayo ta raboshi hannunsu baffa yadawo wajensu,
Su baffa suka koma daga shi sai baba nusaiba babu yaro ko d'aya agabansu, ga masu aiki Nuraddeen ya zuba masu, banda suci su kwanta babu abunda sukeyi, nan take tufan da yakawowa baffa hari har yana neman durqusar dashi ya gudu gaba d'aya ya murmure yayi haske sosai tamkar ba shi ba, Yaya hawwa ma ba laifi saboda Rashida nakula da ita sosai kuma tana cikin qoshin lafiya daidai gwargwado, tafiya kad'aice har yau bata iyayi wataqil hakan nada nasaba da irin wahalhalun data fuskanta alokacin da tana gidan mahaukata, Kuma hakan be dameta ba, kullum cikin zikiri take da tilawa alqur'ani, tana neman gamawa da duniya lafiya, wani lokacin ma Rashida ke koya mata karatun tayita samata albarka.
Baffa Usman ma Alhamdulillah yanzu haka sai qara habbaka yakeyi a fannin kasuwancinsa saboda gudun mawar da Dr Nuraddeen yabashi, arziqinsa sai dad'a bud'uwa yakeyi idan kaganesa zaka d'auaka wani hamshaqin d'an kasuwa ne, dama ashe talauci ne ya b'oye masa cikakkiyar sigar da ALLAH yayi masa, yanzu kuma da wadata ta sauka sai ya canza gaba d'aya tamkar ba shiba, haka Inna Bilkisu abun kam masha ALLAH sai sambarka, ga arziqin miji ga na 'ya 'yanta mata da akoda yaushe cikin aiko mata da saqwanni mazansu suke suna yimata godiyar tarbiyar data bawa 'ya'yanta, Babu mai matsala ko wata damuwa acikinsu don bayan kulawar da suke samu ga mazajensu gaba d'aya Dr Nuraddeen ya sama masu sana'o'in da sukeyi su day muneera kuma ba laifi kowace tana samu daidai gwargwado.
Tuni gidan gonar baffa da Dr Nuraddeen ya sake zuba wasu kaji aka rushe gidan aka mayar dashi wajen kula da kajin kad'ai sai kifaye da aka zuba suma ana kiwo shima ya bunqasa don har cdaga cikin gari motoci ke zuwa suna saye da kuma kamfanonan dake sana'arsu, ko yaushe saidai a qirgikke kud'i akawowa baffa ya soka aljihu yana gida zaune abunsa, (kaga haihuwa mai rana, ubangiji ALLAH kabamu masu albarka.)
Baffa Ali ma little yasa anyo masa qafar roba yanda zaijin dad'in walwala da mu'amalar yau da kullum cikin mutane, hakan kuwa yayima kowa dad'i don babu Wanda wannan tunanin ya zoma arai, da haka su baffa sukayi qoqarin nema masa auren wata bazawara anan cikin qauyen kuma aka dace cikin sa'a ta amince ba tare data damu da yanayin saba musamman data san wajene inda zataje tahuta, qaton shago su baffa suka bud'a masa Dr Nuraddeen yazuba masa kayan drink masu sanyi da katam katam yana saidawa wanda nan take shima ALLAH ya bud'e masa hanyar samu don yana samun cinaki sosai, kan kace me wannan ahali sun had'e waje d'aya sun bunqasa qauyen na bebeji yayi suna sosai saboda yanayin mutanen zagayensu dake shiga harkokin kasu wanci na yau da kullum, musamman a fannin sana'o'in qwai kaji da lemuka, ga Kuma gone ginen zamani da sukayi ya haska cikin garin, don masallaci da makarantun da yaransu zasu nemi ilimi na boko da islamiya duka Dr yasa angina da taimakon gwamnatin jahar, asibitin dake cikin qauyen ma Dr yasa angyarata an sake fad'ad'ata da fitar da wasu fannona na marasa lafiya da basuda da kayan aikin da ba sai sun fita cikin gari ba wajen wasu gwaje gwaje, sun matuqar samun cigaba fiye da tunani don harda wata psychiatric clinic Dr yabud'e da kansa yana kula da masu lalurar qwaqwalwa dake da qaramin qarfi na qauyen da zagaye, tare da wayar masu kai akan abubun da suke jagorantar afkuwar wannan cutar,
A b'angaren su baba balarabe ma dasu Yaya maryam da aunty marwiyya Rashida na taimaka masu sosai da taimakon mijin nata.
Little ma tuni yakoma qaro karatu lokacin battol tasake haihuwa ta uku tasamu 'yarta mace sak sumynsu tafarko data rasu aka sake mayar mata da sunanta alokaci d'aya kuma yana qara hab'b'aka sana'ar gadajensa da katifu da sauran d'aki da dady ya d'orasa akai, don har waje yake zuwa sawo kayan d'akin shida abbaty da lokacin shima yayi aure da 'yarsa d'aya mai sunan mahaifiyarsa wato fatima ana kiranta (miemah).
Batool kuwa Babu yanda Dr da little basuyi da ita ba akan takoma karatu amma takafe akan bata buqata tafiso ta zauna gidan mijinta ta kula dashi da kuma 'ya'yanta Wanda hakan yasa Rashida tace lallae dole little yabud'e mata shagon boutique tadinga saida kayayyaki, shikuwa Dr yace Dole tahad'a da karatun kota online ne in yaso lokacin exam kawai zataje tayi tunda akwai branch d'in a a.b.u zari da sokoto duka zata iya karatu ta online batare da take ba, Dole ta amince badon tana soba sai don tayi biyayya tunda gata ce sukayi mata.
Itama umma da 'ya d'aya da ALLAH yabata tana nan tanacin ribar haihuwa don Babu abunda tanema tarasa aduniya, suci mai kyau susha mai kyau ita da mijinta dady d'an tsofo mai ran qarfe, Dr Nuraddeen ma musamman yayi gida acan lokaci lokaci su kanje can suyo kwanaki su koma, gaba d'aya mabanbanta wud'an nan ahali angame waje d'aya ba qyashi ba hasada anzama tsintsiya mad'aurinki d'aya, suna matuqar son juna tare taimakekeniyar junansu tamkar wata hatsaniya ko rigima da tsana bata tab'a shiga tsakankaninsu ba, dama ance SANNU SANNU bata hana zuwa saidai adad'e ba'a jeba, duk yanda b'acin rai yayi tsanani rabuwa takai rabuwa a zamantakewa da kuma duk girman qaddara to idan akasa haquri da SANNU SANNU za'aga zaman yayi dad'i tamkar ba'a tab'a sab'ani ba, qaddara kuma ancinyeta tamkar bata wanzu ba, ubangiji ALLAH kasanya mu cikin bayinsa masu haquri da kuma iya jurewa qaddarorin rayuwarmu.
_TAMMAT BIHAMDULILLAH_
_Ina miqo godiyata ga dukkanin masoyana da suka jajirce wajen bibiyar littafinnan, Ina jinjina maku tare da alfahari daku ALLAH ya iya maku acikin dukkanin al'amurranku da dukkanin iyawarsa👏ngd ngd ngd sosai_
_Ina kike mamana abun alfaharina NANA HAFSAT (MISS XOXO), akoda yaushe girmanki da Kuma kimarki sukan qara d'aukaka agareni, nagode sosai da gudummawar shawarwarin da kika bani acikin wannan littafi ALLAH yasaka maki da mafi qololuwar alkhairansa_
_Soyayya domin ALLAH ita nake yimaku, Ina godiya da kulawarku agareni ZAINAB AL-AMIN BUHARI & AMINA UBA AYUBA, ALLAH yabar tare ya raya maku yaranku😍👏_
_Jin jina agareki SADIYA ZANGO (MEAMEH) bazan manta da soyayyarki ga dukkanin littafaina ba, ngd ALLAH yabaki miji nagari mai albarka😅👏_
_Gaisuwarku ta dabance auntys d'inah kamar yanda soyayyarma ta dabance AUNTY FAREEDA MOH'D ABBAS, AUNTY MAIJIDDA MUSA, OUM IMAAN comment d'inku kad'ai ya isa yaqarfafa linzamin alqalamina, Ina gdy ALLAH ya albarkaci zuri'a💃🏼👏_
_Na gaisheki MAMAN AIMANA, (AUNTY JANATU B/KEBBI), sonki ga rubutuna na musamman ne, Ina godiya tare da fatan ALLAH ya jagoranci dukkanin al-amarinki💋👏_
_Karamcinki da qaunarki daban suke aminiyata SHA'AWANATU ABUBAKAR MAMAN QUEEN, ALLAH yakula mani dake da dukkanin zuri'arki👏_
_Bazan manta dake ba 'yar mutan bebeji ta hannun damar hayateey na NUCEEY BEBEJI, ALLAH yanunan aurenki musha biki👏💃🏼💃🏼_
_'Yan uwana rabin jikina, kaf littafin don kune nayisa kuma mallakinku ne, SIS ASMA'U, SIS MURJANATU, SIS ZAINAB, SIS AISHA, SIS JUWAIRIYYA, SIS FATIMA, SIS KHADIJA, SIS AMINATU (AMZAHFAZ❤️), Ina qaunarku so marar adadi kuma marar kwatantuwa, ubangiji ALLAH yajiqan MAHAIFINMU ya gafarta masa Kuma yaraya mana zuri'a, yaqara mana qaunar juna ya tsawaita rayuwar iyayenmu mata👏_
_SAI KUMA KU NA AMANATA, KUN NUNAN SO AFILI DA KUMA ZAHIRI, KUN NUNAN QAUNA FIYE DA LISSAFI 'YAN GROUP 'DINA NA *SANNU SANNU FANS 1&2* HAR KASA BANBANCE WANDA YAFI QUNAR WANNAN LITTAFI NAKEYI A TSAKANINKU 🤣🤣🤣AMMA ANZO WAJEN NA TABBATA YANZU NE KADAI ZAN IYA FAHIMTAR HAKAN TA HANYAR FINAL COMMENT D'INKU, Ina gdy da soyayyarku Allah yabar qauna tsakaninmu har a aljannah🤣🤣🤣_
_Gdy ta musamman 'yan group d'ina na kaina, S FARI FORUM, ZAUREN BILLY S FARI, DANDALIN BILLY S FARI NOVELS, ALLAH yasaka maku da aljannah fiddausi👏_
_kuma ga taku gaisuwar 'yan RANO ONLINE NOVELS & HOME OF NOVEL, Ina alfahari daku kuma zanci gaba da alfahari daku ako da yaushe, ALLAH yabiya maku dukkanin buqata._
_Wash! A gaskiya kunada yawan da bazan iya lissafeku ba, haka Kuma rashin ambatonku awannan gabar bayana nuni Dana mantaku bane, kuna nan cikin qlbina da Kuma rouhina fatana ALLAH yakare mani ku aduk inda ku, Kuma Ina fatar ni daku Allah ya yafe mana kurakuran da muka aikata acikin wannan littafi yasa muyi tarayya acikin ladar dake ciki, haka Kuma Ina roqon duk Wanda nab'atawa rai acikin wannan littafi d'aya yafeni👏sai Kuma wani lokaci idan Allah yaqaddara sake had'uwarmu acikin wani sabon littafi nawa😍,
*FILLAH AM GONNA MISS YOU AND YOUR AMAZIN G DU'AH TO ME AND MY ABBIE😭 MUCH LUV MY FAN'S*
_Ma'assalam taku akullum BILLY S FARI💎_
*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭