Showing 153001 words to 156000 words out of 260204 words

Chapter 52 - Sannu Sannu Complete Hausa Novel By Billy S Fari.txt

ba don yayi imanin bazai tab'a aikata abubuwan da akace ba, idanko har gaskiya ne to tabbas bayin kansa bane, Ashe duk abunda suka fad'a Inna ruqayya da zata fitowa tajisu don haka sai takoma cikin zaure ta lab'e tana saurarensu.

Tsabar farinciki da jin dad'in abunda kunnuwanta suka jiyo mata nassa taji wani irin sanyi azuciyarta kuma ta gamsu cewa tabbas haqarsu ta cimma ruwa kuma abunda suka dad'e suna dakon jira amatsayin fansar da suke son d'auka ya tabbata, fasa fitar tayi takoma cikin gida fuskarnan tata tamkar ambiya mata makka tashige d'aki tana tiqar rawa had'e da cewa da SANNU SANNU zakuga aikina da ciwa, kad'an kuka gani ai indai ina raye saina qumsa maku baqincikin da kuka qumsa mani nida 'yata akan yaronku, tashi baffa Ali da bai jima da kwantawa ba yayi yana kallonta cike da mamaki, dama dawowarsa kenan daga d'aukar hatsinsu da suka girbe ta tambayesa kud'i ya hanata shine tafita tana kumburar fuska wai zataje ta aro wani wuri, sai gashi bata jima da fitar ba yaga kuma tadawo fuskarta d'auke da farinciki tana dabsar rawa, tun kafin ya tambayeta ta shiga zayyane masa abunda taji 'yan uwan nasa nafad'a akan halin da Nuraddeen keci acan qasar.

Nan shima fa yatayata har yana fad'in wai anzo wajen!, sai su baffa sunyi dana sani da nadamar turasa qasar waje yaqaro katu, don bazaya tab'a dawo masu amatsayin wanda yayo karatu ba, sai dai yadawo masu a matsayin d'an iska lalatacce da baza'a iya tab'a banbance tsakaninsa da arna ba tunda suka zab'i turasa can akan aurar masa da 'yarsa, bayan duk walaqancin da akayi masu da wanda Yaya hawwa tayita masu alhalin ansamu damar da za'a iya aura masa ita, yazama dole yaje yabiya malan bakada imani don yanzu kam yatabbata yayi masu aikin daya dace, fatanshi kawai ALLAH yaqara duhu don girman d'ib.

Ashe duk wannan abun daya samu Nuraddeen aikinsu ne, su suka kaishi wajen malamin tsibbu sukace ayi masa asarin da zai lalace kuma idan yabar qasar ya manta da kowa nasa, asamashi tsanar qasarsa gaba d'aya yadena sha'awarta balle ma yatuna da iyayensa ko matarsa, duk wata hanyar da zatasa yaci gaba a dwad'e masa ita hatta karatun da akace zaije yi ya kasa yinsa, aganinsu yin hakan shine kad'ai zaisa su d'aukar fansar abunda baffa yasa akayi masu, fansar da batada wani tushe balle asali.

Ba'ayi wata da faruwar hakan ba su baffa sukaje sokoto asibiti wajen karb'owa Yaya hawwa sallama don ba laifi tafara samun sauqi, duk iya qoqarin su naganin ambasu sallama aranar hakan ta cutara daga qarshema sai ankace suje sai bayan sati biyu su dawo, ko kad'an basuso hakan ba amma babu yanda suka iya dole suka koma gida, sati biyu nacika suka sake komawa, awannan karonma saida sukayi da gaske sannan aka basu sallamar, itama d'in da sunan transfer ne akayi masu izuwa asibitin PSYCHIATRIC dake can kano sannan aka d'aukosu da motar asibitin.

Inna Bilkisu ita tagyarawa Yaya hawwa d'akinta kafin su iso, acan asibitin aka kaisu sukayiwa wani babban likita bayani akan suna son komawa da ita gida sugwada yimata maganin hausa idan ALLAH baisa aka dace ba sai sudawo, cikin sa'a da yake bahaushene kuma musulmi ya amince masu tare dasa hannu akan file d'in nata sannan aka aai aka ajiyesa inda yakamata, kuma ya fad'a masu aduk lokacin da buqatar kawota asibiti takama ba matsala sukawota in Sha ALLAH za'a dubata, data dai takowace irin hanyace ALLAH yabata lafiya, sunyi matuqar jin dad'i bisa karamcin daya yimasu kafin suyi masa godiya suwuce da ita gida.

Qwararrin malamai masu ruqya suka samo akayi mata ruqya, inda nan take mugun aljanin dake jikinta ya bayya yana wata qara da kururuwar shi bazai fita ajikinta ba tunda tasa aka azabtar dashi, aka naqasa shi tare da illata masa rayuwa don haka shima bazai gusheba yana azabtar da ita acikin jiki ba har sai lokacin da ruhinta ya rabu da gangar jikinta, babu irin magiyar da ba'ayi masa ba amma yaqi don haka malaman sukaci gaba da yimata karatu ana watsa ma aljanin ruwan magani yana wata irin muguwar qara saboda zabar qonasa da akeyi har saida yaqone tas, nan take jikinta ya saki malaman suka yima ALLAH godiya daya basu nasarar qona aljanin batare daya naqasa taba, sannan suka bada maganukkan da za'a dinga bata tare da tabbatar masu da cewa in sha ALLAH tasamu lafiya musamman idan aka dage da kulawa wajen bata maganin.

Cikin iyawar ALLAH da aka dage wajen kula da bata maganin sai gashi tafara samun sauqi sosai, duk wasu kuwace kuwace da wasu caccanza halittarta da akeyi tadenayi, tadena bugu balle maqura, haka kuma tana iya gane duk wanda yazo wajenta maganace kad'ai bata iyayi, yanayin yanda idan Inna Bilkisu tashiga kaimata abinci ko bata magani take kuka hawaye nazuba a idanuwanta shike qara tabbatar da cewa tasamu lafiya, don kallo d'aya zakayi mata kasan cewa ba kukan komai ne takeyi ba illa na tarin nadama, don gaba d'aya cinta, shanta, kula da tsaftaceta duka ita keyi ita da yaranta su Aisha, musamman idan basa komai d'akinta duk suke zuwa azauna ayita fira saboda kada subarta cikin kad'aici, wani lokacin saidai taqura masu idanuwa tayita kallo batare data tanka masu ba, duk da aranta babu wanda take tunani take son tambayar Ina yake kamar d'anta ya nura amma babu bakin magana saidai tazauna tayita kuka Inna Bilkisu na faman rarrashinta da bata magana.

Haka baffa ma idan yazo ganinta, Babu abunda takeyi sai kuka wanda kukan ya tabbatar masa da cewa na nadamane takeyi don haka sai yanuna mata tadena damuwa, kamar yanda yafad'a mata ashekarun baya cewa yayafe mata duniya da lahira har yanzu hakanne aransa, Kuma yasa nusaiba ta shirya ranar sukaje tare ya gabatar mata da ita a matsayin matarsa tare da 'yarsa Rashida da har tafara tafiya, sannan yayi mata bayanin duk halin da d'anta Nuraddeen keciki saboda amatsayinta na mahaifiyarsa ta tayashi yimasa addu'a, ranar Yaya hawwa kwana tayi tana kuka azuciyarta tana roqon gafarar ALLAH da kuma yayewa d'anta halin da yake ciki, tana so ta tambayi Rashida matar d'anta amma ba halin haka domin bataga fuska ga kowa ba da zata iya tambaya, Babu mai d'auko mata zancenta ita kuma babu baki balle ta tambaya.

Su baffa Ali kuwa tamkar babusu acikin gidan don sau d'aya sukaje dubata, qarama muneera takan d'anje tadubota wani lokacin shima idan basa nan.

••• ••• •••
Rashida kuwa tuni antaka matakin manyan mata don tuni an takammala karatunta na jami'a aqarqashin kulawar Dr da mahaifinsa, tasha karatu sosai fiye da tunanin mai karatu a fannin law wato shari'a, yanayin yanda tamaida hankali sosai ga karatun yasa tasamu nasara acikin kowane mataki data taka, tanada wata baiwa tamusamman da ALLAH yabata wajen jajircewa ga dukkanin abunda tasa agaba wannane yasa take nasara acikin dukkanin al'amurranta, bayan ta kammala Dr yayi sha'awar sama mata aiki Amma sai dady yahana, acewarsa hakan badacewa bane tunda tanada aure kuma dole amartaba igiyar aurenta sai kuma idan kotu za'aje araba auren tunda har yanzu mijinta bai waiwayeta ba, hakan yasa Rashida tace tahaqura duk da tanada sha'awar yin aikin, Amma har yanzu qauna da soyayyar mijinta na kwance azuciyarta da bata tunanin zata iya rayuwa da wani idan bashi ba, tasha alwashin bazata koma wani auren ba koda hakan na nufin tarabu da mijinta kenan har abada domin gaba d'aya tadena sha'awar auren, don haka sai dady yabata kud'ad'e masu tsoka sosai tafara gudanar da business, acewarsa zaifi kyau ta dogara da kanta domin ba'asan halin rayuwa ba, sosai Rashida tamurje tayi kyau tazama 'yar gayu, idan kaganta bazaka tab'a cewa wai Rashidar nance ta qauyen yarimawa matar malan nura ba.

Ana haka ranar labari ya iso mata cewa ai su Nuraddeen sun dad'e da kammala karatunsu da sukaje yi tun shekarun baya amma shi yaqi amincewa yadawo, zamowarsa qwarare a fannin daya karanta namasu fama da matsalar neorology da gaba d'aya qasar basu tab'a samun d'aliba mai hazaqa kamar saba yasa qasar tariqesa har tabashi goyon baya d'ari bisa d'ari bisa muradinsa da kuma ra'ayinsa, nan take suka bashi aiki tare da yanka masa albashi mai tsoka, ayanayin da yake aciki lokacin koda bazasu bashi komai ba yafi son ya zauna acan qasar fiye da yadawo, da gwamnatin jahar tasu tanemi tsaurara al_amarin qasar ta d'auko maqudan kud'i tabasu, kasancewar yanda qasar tamu idonta yariga ya bud'e wajen ansan rashawa da cin hanci da Kuma rashin sanin ciwon Kai ya sukayi mui basu koma tada zancenba, baffa yayi kuka da baqincikin abun sosai amma daga baya ya haqura yaci gaba da addu'a tare da yaqini akan ko yaushene zai waiwayesu, Yaya hawwa ma duk da bata um balle u'um aranta tana yimasa addu'a tare da fatar ALLAH yadawo dashi kafin ta ALLAH takasance akanta, wannan labari ya matuqar girgiza Rashida duk da aqasan zuciyarta bata gamsu cewa zaiyi hakan ba sai indai akwai wani abu aqasa da bata sani ba, amma koma meye tayi alqawarin zata zauna zaman jiransa komai daren dad'ewa,

kwatsam ranar tana kallon BBC news taga ana fira da wani likita mazaunin qasar malesia amma haifaffen d'an qasar Nigeria ne, qura masa idanuwa tayi saboda ganin yanda yake matuqar kama da habibynta amma azuciyarta sai tace shi wannan yafi habibynta qiba da kuma haske sosai asalima daka kallesa kaga d'an gayu wanda hutu ya zauna masa ajiki, badon ma yanayin haskensa dana mutanen can akwai banbanci ba da bazaka tab'a cewa shi ba d'an qasar bane, tana wannan tunanin ne taji ana tambayarsa sunansa...

Qara volume d'in tv tayi had'e da juyowa tana kallon yaransu Dr dake zaune suna wasa wato (walida da sultan) wud'anda aka haifa bayansu shahid da Shahida, walida ita ke bimusu twins sunan ammie ne da taci shiyasa ake kiranta waleeda sai sultan shi kuma sunan dady ne aka saka masa ana kiransa da sultan, tace masu suyi shiru, gabanta ne yafad'i jin da tayi likitan yace

Sunana...





*ALLAH KAJIK'AN IYAYENMU*👏😭
[11/14, 22:52] Billy S Fari: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎


_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___69💎

Musamman acikin rayuwar Rashida da mahaifiyarta da idan kazauna kayi nazari zaka fahimci dalilin daya hana Rashida yin karatu tace aure take so har ta auri Nuraddeen mahaifiyarsa ta turo mata aljanu suka d'auketa suka kawota garin borno, har hakan taja iyayenta suka baro garinsu cikin qaddarawar ALLAH kuma aka sake had'asu gari d'aya da inda 'yarsu take kuma ta ALLAH tazo ta afku akan mahaifinta da aka tsaro cewa nanne qasar da za'a rufesa, don bayan umma takammala takaba sai dady yasake bijirowa da buqatar d'ansa akan yana son Rashida ta tsaya anan taci gaba da karatu har lokacin da ALLAH zai dawo da mijinta, badon su baba balarabe naso ba suka sake amince masa akaro na biyu bisa sharad'in duk lokacin da mijin nata yadawo dole zata ajiye karatun takoma hannunsu don su mayar masa da ita, wannan dalilin yasa itama umma tace bazata komaba zata zauna da 'yarta don itama tabata tata gudun mawa wajen cikawa baba burinsa naganin tayi karatu mai zurfi kamar yanda yaso, kasancewar tanada 'yancin kanta yasa babu wanda ya tilasta mata akan sai takoma suka bisu da fatan alkhairi

Cikin sati biyu Dr nura ya ida kammala shireshiren komawarta makarantar tare da sama mata Mai lesson na musamman da zai taimaka mata don j.s.s 3 yace akaita duk da kuwa qoqarinta bai kai can ba, nan take tafara karatu ka in da na'in cikin jajircewa da qaunar cikawa mahaifinta burinsa,

Ammie kuwa tuni ta dakatar da umma batun aikin da takeyi mata tasa aka samo mata wata sai ya zamana umma bata aikin komai agidan inba kula da gyara shiyar da suke ba da kwanciya don ko girki ammie kesa ana kaimasu nasu daga sashenta idan andafa, dady kuwa akoda yaushe cikin kulawa dasu da yimasu hidima yake, kwatsam ranar yasami ammie da zancen yana son ya auri umma saboda shidai yana tsananin tausayinta aransa don tunda baba yarasu har yanzu takasa komawa daidai, kuma shi agani sa idan yayi hakan yiyi jahadi sosai tunda batawuce yin aure ba to baiga amfanin tazauna ahaka ba, asalima yana tunanin idan har tanada sha'awar yin aure Wanda zai iya damqawa amanarta kuma yariqeta hannnu biyu, hakan yasa azuciyarsa yaji ya amince d'ari bisa d'ari don tabbatar daya riqe amanarsu hannu biyu kamar yanda ya d'auka, zuciya batada qashi kuma shi kishi gaskiya ne don haka awannan lokacin ammie sai taji badad'i aranta amma saita danne zuciyarta tabashi goyon baya tare da qarfafa masa wajen aikata hakan,

Kwana biyu tayi tunda dady yayi maganar bata barin su had'u da umma saboda abunda takeji nataso mata aqasan zuciya saboda kada tayi abunda ba daidai ba, daga qarshe kuma tasaki taroqi ALLAH yasa hakan shiyafi zama alkhairi,

Hajia nafeesa kuwa da taji Babu irin maseefar da batayi ba da habaice habaice tun umma batasan abunda kefaruwa ba don bai riga ya sanar da ita ba har tasani, ta matuqar girgiza had'e da nuna qin amincewarta amma ammie tayita lurar da ita da lallashinta har saida ta amince, ba'a wata samu matsala ta b'angaren 'yan uwanta dana baba ba sboda ganin dattako da cancantar dady suma suka amince, nan take dady yasa aka rushe sashen da take da wasu wurare cikin gidan itama aka fitar mata da part d'inta abunka ga mai arziqi cikin sati biyu aka kammala komai har d'aurin aure ta tare abinta,

Duk wannan abun daya faru bisa amincewar Dr da taimakonsa dady yayis hakan kuma dashi har Fatima sunyi farinciki sosai ba tare da wata hiyana ba, Rashida ce kawai kullum take cikin jin kunya tana ganin kamar hakan da akayi ba'a kyautawa ammie ba, bayan duk taimako da halaccin da tayi masu ita da d'anta har saida ammie tazaunar da ita tanuna mata hakan ba illa bane tunda musulunci bai hana ba sannan tafara samun sakewa daidai, duk da ako yaushe idan hajia nafeesa tahad'u da ita har mahaifiyarta cikin jifarsu take da miyagun kalamai cewa wai Rashida tayi cikin shegene shiyasa tagudo suma da abun kunya ya ishesu sun kasa gano uban d'and'an dake cikinta sai suka biyo bayanta, hatta ma little da baisan komai ba kullum cikin kyararsa take tana aibantasa agaban 'ya'yanta tana kiransa da shege wanda ba'asan ubansa ba, hakan yasa har 'ya'yanta ma ke kiransa da haka amma da yake baisan komai ba baya damuwa.

Haka rayuwa taci gaba Rashida nasamun kulawa da kuma gudun mawa sosai wajen karatunta da ita har d'anta ta b'angare biyu wato dady da kuma Dr, don tuni shima little Dr yasashi makaranta lokacin itama Fatima har tahaihu tasamu qaton d'and'anta suka rad'a masa suna basheer wato sukawa baba takwara, wannan ba qaramar kima da daraja yaqara jawo masuba a idanuwan umma da Rashida harma da 'yan uwansa, sunyi matuqar farinciki da jin dad'i sosai aransu harma suna ganin aduniya yanzu basuda masoya da suka fimasu su dady da Dr nura ba.

Rashida kuwa tun tana dakon dawowar mijinta izuwa gareta ita da d'anta har tacire rai, gaba d'aya ta tattara wata rayuwar aure data tab'ayi abaya dama auren ta ajiyesu gefe taci gaba da karatunta ita da yaronta, saidai duk da hakan daidai da rana d'aya Bata tab'a yarda tayi wani abun da zaya keta mata marta da kuma darajar auren taba har ta kammala secondary lokacin little na primary 2 amma babu wani labarinsa, a lokacin fatima har tayaye basheer da suke kira (abbaty) tasake samun ciki ta haifi 'yan biyu duka mata saidai rurrutsa ce tayi a tsakaninsu, inda aka barsu da sunayensu na asali wato hassana da hussaina, murna kam awajen Dr da fatima bata misaltuwa, gashi dai SANNU SANNU cikin iyawar ALLAH suma sunfara tara nasu 'ya'yan da suke matuqar qauna a cikin shekaru uku kacal ALLAH ya arzuttasu da 'ya'ya uku, Babu wata wahalar reno da fatima kesha saboda Rashida nanan, duk wata kulawa da yaran zasu buqata tana basu tamkar ita tahaifesu.

Shekarar Rashida d'aya tana jiran saka makon jarabawar tasu tafito kuma cikin taimakon ALLAH tayi nasarar lashe kowane darasin da kyakkyawan sakamako wato exelent gaba d'aya, ranar da ita har umma sunyi kuka sosai cike da son inama baba nada rai yaga yanda tafara taka mataki na biyu akaratu da kyakkyawan sakamako, godiya kuwa sunyiwa Dr da dady da ammie ba adadi har saida suka farajin kunya.

Umma da ammie kuwa bazaka tab'a ganinsu kace kishiyoyi bane domin akwai tsantsar fahimta da mutunta juna atsakaninsu, hakan yaqarawa hajia nafeesa tsanar umma da rashida dama little gaba d'aya.

••• ••• •••
A b'angarensu baffama acikin shekarunne ALLAH ya sauki nusaiba matarsa lafiya saidai ba'a samu namiji ba kamar yanda yaso ALLAH ya arzuttasu dai da samun 'ya mace kyakkyawa kamarta sak da nusaiba baffa ya rad'a mata suna Rashida, yana matuqar son yarinyar fiye da tunani saboda sunan data zauna, sau da dama yakan tuna da baba da Kuma 'yarsa Rashida aduk sadda aka ambaci sunan 'yar tasa da taci sunan Rashida, wannan yasa ko kad'an baya son jin kukanta balle abunda zai b'ata mata rai, hakama gaba d'aya yakasa mantawa da gudan jininsa daya kasa samun labarinsa, lokacin daya tuntubi ma'aikatar da aka turasu qasar waje don qaro karatu akan labarinsa sai suka b'oye masa ainahin halin da d'an nasa ke ciki, domin koda Nuraddeen suka isa qasae waje bayan anbasu wajen zama sai yanemi wayarsa sama da qasa yarasa, gashi gaba d'aya wud'an da aka had'asa dasu zama 'yan jahohin kudu ne acan nageria babu wanda yasani acikinsu, asalima gaba d'ayansu babu ruwansu dashi saboda shikad'aine bahaushe sai suka nuna mashi halinsu qarara na qyamar jinsin da banasu ba musamman ma ga musulmi d'an arewa duk da kuwa qasarsu d'aya, hakan yasake jefasa acikin wata damuwar akan wacce yake ciki yana son yasan halin da ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login